Showing 21001 words to 24000 words out of 83144 words
Chapter 8 - MATA'UL HAYAT BY SAKINAT USMAN-1.pdf
aiko kiranki za ki ce babu Shuhuda a
gidan nan?
Shuhuda ta juyo ga Inna yaduwa idanunta jajur tace: To ina Shuhudan? Ina ce ni sunana
YAKUB?
Inna yaduwa ta sake kulewa, ta kaiwa Shuhuda bugu da hannu. Amma kafin hannun ya isa jikin
Shuhuda sai ya sandare, Inna Yaduwa ta ji gaba daya jijiyar hannunta sun daskare kamar babu
jini a tare da hannun. Shuhuda tace:
an fada miki ana dukana? Ko don kinga ina raga miki? To sauke hannun.
Bisa ga tsanani al'ajabi sai hannun ya koma Shafal, Inna yaduwa ta tsorata ainun ga wannan
lamari, shi kuwa yaron dariya ya kama yi, don bai da isasshen wayo.
Shuhuda ta dubi yaron tace: Ka je ka cewa wanda ya aiko ka nan gidan babu Shuhuda. Yaron
ya juya yana dariya, ita kam Inna yaduwa gaba daya tsurewa ya yi. An ya kuwa wannan
yarinyar ba aljana bace?
Jikinta na 6ari ta mike ta nufi dakinta. Waya ta dauka domin kiran 'ya'yanta ta sanar da su abin
da yake faruwa. Amma wani rudanin da ta lalubo lambar da zata kira, tana kira sai kawai wayar
ta kashe kanta, kuma ga cikakken caji, amma kiran ya ki yiyuwa.
Ta yi jigum tana mamaki, wannan aikin jinnu ne, babu tababa Shuhuda aljana ce, idan ta yi
la'akari da kwararan hujjoji. Misali: An tsarga yatsanta an ga nono na zuba. Anje asibiti allurar
da aka yi mata ta karye, daga baya labari yazo likitan ya rasu. Mas'ud ya ji mata rauni an ga
nono maimakon jini, sannan tana wasu dabi'u wadanda sun zarce ace lalurin ta6uwar kwalwa
ce.
Anya kuwa lokacin da za a haifi Shuhuda jinnu ba su yi musayarta da diyarsu ba?
Ba shakka wannan haka yake, jinnu sun dauke diyar Karimatu a ciki ko bayan ta haihu suka
sauya mata wata 'yar da tasu.
Idan haka ne me ye abin yi? Zuciyarta ta ci gaba da bugawa ta rasa abin da ke yi mata dadi a
rai. Tana cikin wannan hali Shuhuda ta shigo dakin a rude tana cewa:
Wayyo zai kashe ni Inna, ki taimake ni. Wallahi mugu ne! Ga shi can an hana shi shigowa ,
kashe ni zai yi! Kafin Inna yaduwa ta samu damar tofawa tuni Shuhuda ta 6uya a bayan Inna
yaduwan. Sai kuka ta ke tana kiran taimako.
Kan Inna yaduwa ya daure sosai, tsoro ya sake shigarta ba tasan lokacin da ta rukunkume
Shuhuda ba tana cewa.: Waye?
Shuhuda ta kasa magana kuka kawai ta ke yi kamar zata shide a gurin.
Cikin jarumta Inna yaduwa ta 6am6are jikinta daga na Shuhuda ta nufi falo. Ba ta ga kowa ba,
tana tafiyar sanda ta fito harabar gidan. Nan ma ba ta ga kowa ba, hatta maigadi babu shi babu
alamarshi, sai dai a kofar gida ta jiyo hayaniya, don haka kai tsaye can ta nufa.
Ta tarar da kofar gidan dankam da mutane, wai wani 6arawo ne aka kama ya shiga wani gida a
layin yayi sayar Generator.
Da ta dawo gidan iske Shuhuda ta yi kwance dai-dai akan gado yadda kasan ta dauki lokaci
tana bacci.
Inna yaduwa ta kai hannu tana bubbuga kafafun Shuhuda alamun tayar da ita. Shuhuda ta
bude idanunta sun yi jawur saboda bacci ta ke kashir6an. Inna yaduwa tana hada ido da
Shuhuda sai ta rasa me zata ce mata, hasalima duk sai ta ji ta manta abubuwan da suka faru a
dazun.
Cikim muryar bacci Shuhuda tace: Inna lafiya kika tashe ni? Inna yaduwa tace: Kin gama cin
danwaken ne? Ta girgiza kai. Ai na fada miki ya lalace, ba shi yasa na shigo daki ba don
takaici?
Inna yaduwa ba ta san ya aka yi ba, sai cewa tayi. Af! Anyi haka fa! Amma duk da haka ki tashi
baccin nan, ki dora mana girkin dare, kinga har uku ta gota. Shuhuda tace: Wallahi Inna ba zan
iya kuma shiga kicin ba, har yanzu raina bai gama yin sanyi ba.
Inna yaduwa ta yi murmushi tace: Ai dama kallonki kawai nake amma yaushe zaka yi danwake
ka zuba gishiri a cikin kwa6in? Shuhuda ta koma ta kwanta.
Ai na gama yin danwake har abada, ni sam ya fice min daga rai. Ta karashe maganar tare da
lumshe idanu alamun zata koma bacci. Inna yaduwa ta koma falo ta zauna akan kujera
tunaninta ya dan dawo, ta tuna abubuwan da suka faru ko kuwa a mafarki ne?
Ta shiga tababar yadda abubuwan suka faru kamar gaske, kamar kuma a mafarki? Mikewa
tsaye ta yi a lokacin da zuciyarta ta gama yanke mata yanke mata duk abin da ya faru a
bayyane ne don haka zaman gidan bai ganta ba, zama da aljana?
Sai dai me? Tana mikewa da wannan kudirin sai ta ji wata irin kasala ta zo mata ta ji kamar ta
manta yanda abubuwan suka faru.
Bayan sallar magriba Inna yaduwa da Shuhuda suna zaune a falo tamkar kurame haka suke.
Babu wadda ke yiwa wata magana, kowacce da abin da yake yi mata yawo a rai.
Alh Sada ya yi sallama tare da shigowa. Ya gaishe da Inna yaduwa. Shuhuda ta gaishe shi, sai
suka yi shiru. Inna yaduwa na son sanar da shi abin da ya faru amma ta gaza daga harshenta
bare ta furta.Wani irin nauyi ta ke ji harshen nata ya yi mata.
Shirun ya dauke su wani wani lokaci kafin daga bisani Alh. Sada ya katse musu shirun da
cewa:: Inna jiya angonki yana tambayata ku wai ba ya samun wayarki.
Inna yaduwa ta yi gajeran murmushi tace: Bar ja'iri bai neme ni ba. Amma ni da wayata kullum
ta ke da caji? Shima Alh Sadan murmushi yayi. Yace; Ni ma abinda nace kenan. Tace: Yaushe
zai kare karatun na shi ya dawo ne? Alh Sada yace: Saura Shekara biyu ya fada min kila ma a
can zai yi aiki. Saboda tun yanzun gwamnatin kasar ta fara kyarkyararshi. Kin san angon naki
akwai himma.
Tace: Dama haka ake so. Alh. Sada ya dubi Shuhuda yace: Ke ya 6angaren naki karatun? Na ji
an ce ba ki mayar da hankali. Wani malaminki ya same ni yace idan kin je makaranta babu abin
da kike sai wasa, haka ne? Ya karashe maganar cikin yanayi na zolaya.
An ta6owa Inna yaduwa inda yake mata kaikayi, amma koda ta hada idanu da Shuhuda sai ta
ga kamar tana yi mata gargadi kada ta yi magana. Ta daure cikin jarumta da niyyar furta abinda
ke ranta, amma sai sa6anin hakan ya fito daga bakinta.
Ai kuwa ba a ce Shuhuda ba ta karatu ba, yarinyar da kullum ba ta da wani aiki sai na karatu?
Kawai dai ina ganin irin wadannan malaman ne da suke da kyashi akan kwalwar da dalibansu
suke da ita. Alh Sada ya fadada murmushinsa yace:
Gaskiya shi ma shaidar kirki ya yi mata yace duk cikin dalibansa babu wadda ya yaba da
kwalwarta kamar Shuhuda, kawai na yi hakan ne don na tabbatar da abin da ya fada.
Inna yaduwa ta rasa me yasa ta kasa fada masa cewar: Shuhuda aljana ce, babu abinda ta
sani sai shirmen aljanu! Shuhuda kam rusunar da kanta ta yi kasa kawai ta yi. Nan ya dan ja
Inna yaduwa da labari yana sanar da i2a abinda malamin ya fada masa. Daga karshe yace:
Yaron yana da nutsuwa da maida hankali game da dalibansa. Yace min shi dan asalin katsina
ne, sunansa Hamza. To yadda ya ga yarinyar na da kokari ne yasa ya biyo sawu ya yi tambaya
ya gano ko su waye iyayenta, shi ne yazo. Da a ce za a dinga samun malamai irinsa lallai da
iyayen yara sun ji dadi, don gaskiya ba karamin dadi na ji ba da har wani malami ya wanko
kafafunsa ya zo musamman don ya yaba irin kojarin da Shuhuda take da shi ba.
Inna yaduwa dai ta yi shiru, don ta kasa furta abin da ya faru din, Da ta yi yunkurin hakan sai ta
ji harshenta ya yi mata nauyi. Don haka har Alh Sada ya gama maganganunsa ya yi musu
bankwana ba ta iya furta abin da ya faru ba.
Hutun 'yan makaranta ya kare, don haka daliibai da ke makarantar kwana suka soma komawa
tun a ranar lahadin farko, Shuhuda kuwa da ke jeka-ka dawo ta wanke kayanta har ma da
sabbin kayan makaranta da Alh Sada ya dinka mata.
Ta hada komai na komawa makaranta gari kawai ta ke jira ya waye ta ganta a cikin makaranta.
A cikin satin nan gaba daya Shuhuda ta sauya ta koma wata irin yarinya mai tsananin natsuwa
hankali da kula da addini.
Inna yaduwa tana ta tsananin mamakin yadda Shuhuda ta sauya kamar ba ita ba. Sam babu
wannan shirmen nata, koda yake har yanzu Inna yaduwa ba ta aminta Shuhuda mutum ce ba.
Sai dai ta rasa yadda aka yi ta kasa bayyanar da hakan ga wani, ko shuhudan ma ta kasa yi
mata magana bare ta sake tabbatarwa aljana ce. Washegari ranar litinin Shuhuda ta tafi makaranta, kasancewar makarantar ta kudi ce, shi yasa
dukkan dalibai sun dawo gudun kada a hukunta su. Sa'adatu wadda suke kujera daya da
shuhuda ita ta fara lura da sauyin da aka samu a tare da shuhuda, sannan sauran dalibai ma
suka fahimta. Kowa yayi murnar yadda Shuhuda ta samu lafiya, domin sun dauka cutar tata ta ta6in hankali
ce, to yanzu kuma gashi ta warke. A ranar unlce hamza bai shigo ajin nasu ba, duk ma tsayin
makon bai shigo ajin ba har sai da wani makon ya shigo.
da Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤12¤¤
Da ya shigo ajin ya yi darasi yaga sauyin da aka samu a tare da shuhuda anin ya ba shi
mamaki, shin da gaske dama ta6uwar kwalwar ce gare ta? Ko kuwa kaifin kwalwarta ne ya
soma da kushewa? Da aka fita break fast ya shigo ajin amma bai tarar da ita ba kamar yadda ta
saba zama a ajin idan an fita break. Sai da aka kusa komawa ya hangota tana tafiya. Ya yi wuf ya fito daga dakin malamai ya sha
gabanta. Ta rusuna ta gayar da shi, ya amsa tare da cewa: Yau ya aka yi kika fita tara ke da
kika ce daga gida kije ciwo abinci? Tace: Yau ban ci komai ba doki nake na zo makaranta.
Yace: Wata kila don kina son ganin malaminki ne mai shisshigi ko? Ta yamutsa fuska cikin
rashin fahimta, amma ba ta iya cewa komai ba, ya daga gira sama kafin yace: Eh mana, ko ba
a fada miki na je can gidanku Misra ba?
Ya karashe maganar cikin yanayin zolaya. Kanta na sunkuye kasa ba ta dago ba. Ya ci gaba da
kallonta, yace: Har ma muka gaisa da dan'uwanki YAKUB? ya karramani, ashe dai gidanku
babban gida ne?
Har yanzu ba ta ba shi amsa ba. Ya gyara tsayuwa yana murmushi yace: Ai na fadawa Yakub
ina so ya ba ni aurenki, kuma da yake da ne mai karamci da yakana, sai ya ya bani har yace zai
shige min gaba a gurin neman aurenki.
: Ta dago kai da sauri alamar ta razana amma ba ta tanka ba Shi kuwa Uncle hamza murnushi
ya kuma yi, yace: Ko ba ki sona nw? Bata amsa ba sai kawai ta yi gaba , bai yi yunkurin dakatar
da ita ba, saboda a ganinsa kunya ce ta hana ta tsaya. Sai ya cizi la66ansa ya koma dakin
malamai ya zauna. Wani irin nishadi yake ji a zuciyarsa. A da ya dauka shuhuda ba mutum bace, to amma tunda ya je gidan yayan mahaifinta ( Alh
sada) ya tabbatar mutum ce sai kuma da ya je gidan Inna yaduwa. Dan'uwanta yakub ya fito ya
karrama shi, shike nan ya sake sakankancewa, ya kuma yadda lallai ya kamu da son
Shuhudan. Hakan ne ma yasa ya gaza 6oyewa har sai da ya tunyu6i yakub din. Kuma sai ya
samu hadin kan Yakub inda har ma yake yi masa bayanin Shuhuda lafiyarta kalau. Kwalwa ce
ta yi mata yawa, amma zai sha mamaki ranar da zai ganta a makaranta da sauyawar abubuwa
da dama.
Don ya hanata yawan karatun nan na kure rai da ta ke yi da rana. Kuma sai ga shi din ya sha
mamakin tunda ya ga sauyawar abubuwa da dama a tare da Shuhuda.
A ranar yana da darasi da su, har kosawa yayi lokacin ya yi ya shiga ajin ko don ya ji muryar
Shuhuda cikin tsadadden turancin nan nata wanda ko dan kasar Amurka sai haka.
Lokacin na cika cije da doki ya nufi ajin nasu shigar da ya saba wadda ta ke kar6ar fatar jikinsa,
wato shigar dogayen kaya, na danyar shadda ta tsadaddiyar hula gami da takalmi 'yan asalin
kasar spain sai agogonsa kirar kasar Germany.
Duk wanda zai ga uncle hamza zai yaba da tsananin kyawun da ya yi don shi din mai kyau ne.
Ga kuma dorinar ado da yake da ita. Zai yi wuya ya yi shiga ba a ga zahirin kyansa ba. Yana
shiga ajin ya dora idanunsa a kujerar da Shuhuda ta saba zama. Yau din ma tana zaune kanta
na sunkuye ga dukkan alamu littafin da ke gabanta ta ke dubawa. Amma jin hayaniyar gaishe
da uncle hamza da daliban ajin ke yi yasa ita ma ta bi sahunsu ta gaushe shi.
Ya ba su umarni da su zauna . Kowacce ta zauna a hankali ya fara yanyara turanci yana yi
musu bayani game da Equalibrium?
Kowacce ta nutsu tana saurarensa har ya kai ga yi musu tambayoyi ana ba shi amsa. Amma
sai bai ji Shuhuda ta yi magana ba, shi kuma abinda yake so yaji muryarta.
Don haka kawai sai ya jefo musu tambaya akan Wave wanda ya shafi darasin physics kuma
yana da yakinin ba su kai gurin ba. Ya dai san Shuhuda ce zata iya amsa wannan tambaya.
Sa6anin hasashensa sai ya ji ajin ya yi tsit! Babu wanda ya koda motsa da nufin amsawa.
Ya sake saurarawa Shiru, sai ya yi murmushi yana duban Shuhuda yace: Ke ya baki bamu
amsa ba? Ita ma murmushin tayi tace: Ban sani ba uncle. A kalla ya dai samu abinda ya ke so
tunda ya ji kalma daga bakinta.
Ya zakuda kafada. Yace: Shike nan ya zama aikin gida(home work) zan kar6a gobe idan Allah
ya kaimu. Yana karashe fada ya sa kai ya fice daga ajin. Washegari gaba daya Shuhuda ta
hana kadaituwarsu, don lokacin da aka fita break fast ya shigo ajin bai ganta ba. Bata kuma
komawa ajin ba har sai da aka shiga. Babu sararin kadaicewa da ita. Da aka tashi kuwa yana hangota tana tafiya zuwa inda direban da ke kawota makarantar yake
tsayuwar jiranta. Da saurinsa ya fito daga dakin malamai amma koda fitowarsa sai ya ga tuni
har motar ma ta tashi.
Yaja turus ya tsaya yana cizon la66ansa. Ya yi tunanin ya bita har gidansu. Amma sai ya tuna
maganar Alh Sada inda yake ce masa, ya ji dadin yadda ya zo har gida don yaba kwalwarta,
amma ba su bukatar wata doguwar alaka tuinda Shuhuda yarinya ce, karatu ne yanzu a
gabanta. A lokacin uncle hamza ya yi matukar mamakin yadda farat daya Alh sada ya fahimci abin da
yake cikin kwayoyin idanunsa, har ya yi masa irin wannan gugar zanan.
Wannan tunani da ya yi shi ya hana shi bin bayan Shuhuda ya yanke shawarar idan ya koma
gida zai kira lam;bar da yayan Shuhuda(yakub) ya bashi don dama tunda ya kar6i lambar bai
kirashi ba.
Kullum yana son ya kira sai ya yi tunanin abin da zaice da shi shi yasa bai kira shi ba tun can
baya. To amma yana ganin yau yana da cikakkiyar dama ko don ya ji muryarta.
Hakana kuwa ce ta faru, bayan ya koma gida ya yi wanka ya ci abinci tare da sallah. Yana
zaune a falo ya dauki wayarsa ya lalubo lambar yakub. Ya kira:
Mamaki ya kama shi lokacin da yaji sautin kiran maimakon trin-trin sautin da ake ji idan an kira
layin MTN ko ZAIN, sai yaji Triiiiiiin! Kamar ya kira layin GLO ko ETISALAT. Shi dai yasan layin
da layin da YAKUB ya ba shi MTN ne mai 0803, to amma sai ya ci gaba da kasa kunnuwa yana
saurare. Har wayar ta ganma kara ba a daga ba, bai hakura ba sake nema ya yi a karo na biyu.
Nan ma ba a daga ba, sai ya ajiye wayar a gefensa ya janyo laptop dinsa yana dube-dube.
Kira ya shigo a wayarsa, ya dauka ya duba, bakuwar lamba ce kuma ga dukkan alamu daga
kasar waje ne, saboda yadda CODE din lambar ya fara da +2011.
Cikin rashin sanin wanda ya kirashi ya kara wayar a kunne bayan ya latsa malatsin O.K.
Sallama aka yi masa wadda kana ji kasan mai sallamar harshensa ya karye da larabci. Uncle
yace cikin Harshen Hausa. Waye akan layi? Daga can 6angaren aka ce:
ABUBAKAR IBN KHADDAB ne, an kira wayata ba ni kusa da wayar na gani kamar a kasar
Najeriya ne, wa ke magana? Uncle hamza ya zabura saboda shi sam duk yau bai kira wata
lamba ba idan ba yanzu da ya kira Yakub ba. Yana girgiza kai kamar Abubukar din na ganinsa
yace: A'a gaskiya ban kiraka ba, domin duk yinin yau wayata a kashe ta ke. Abubakar ibn khaddab
yana dariya ta cikin wayar yace: Amma na yi mamaki, saboda na dauka ko su Yusufa ne suke
son magaba da ni. Don Allah kada ka zolaye ni ka fada min waye?
Uncle hamza ya kara cika da tsananin mamaki yace: Abin da na fada haka ya ke, ni ban sanka
ba. Babu wani da na sani a wata kasa da ta tsallake Najeriya bare na zolaye ka.:
Abubakar yace: Ni ma cikin makon nan zan dawo Najeriyar idan ma ka 6oye min shike nan na
gode. Ka gaishe min da su Alh BABBA.
Yana gama fadar haka wayar ta katse, tsoro da fargaba suka cika zuciyar uncle hamza