Showing 66001 words to 69000 words out of 83144 words

Chapter 23 - MATA'UL HAYAT BY SAKINAT USMAN-1.pdf

02 Aug 2025

11103

ya tuna da wannan tsari, tukunna ya tunatar da sauran. Dole ba don
sun so ba suka amince da wannan zabin magaji. Ana ta gudanar da rayuwa ne cikin jin dadi da
shagaltar MATA'UL HAYAT (kyale kyalen rayuwa), babu mai tunawa da wani imani a zukatansu.
Sagir ya samu sararin bude gidan gona kamar yadda wannan buri ya jima aransa, don shi kam
yana sha'awar tsirrai. Shekarar da zai yi aure ne john ya mutu shugaban kungiya, don haka aka
hada hidimar aurensa da nadinsa shugaban kungiyar. Isan ba zaku manta ba, akwai mutanen
da suka halarci bikin da dorayin kaya ajikinsu a gurin partyn auren, harma aka so yin rigima da
wani daga cikinsu shi da wata budurwa da ta nemi cin zarafinsa, wadda ita kuma ta kasance
dama yarinyarsa ce, ta gano matsafi ne, ta rabu da shi, da kyar aka samu aka fitar da ita tana
cewa jininta ya fi karfinsa. Ina tunanin a lokacin ba wanda ya gane abinda ta ke nufi, shi yasa ba
azurfafa bincike ba aka fitar da ita, karshe kuma jinin nata bai fi karfinsu ba, domin sai da aka
mikata ga dodon tsafi ya sha jininta. An samu tsayin shekaru uku da auren Sagir, Amma ko
batan wata Karima matarsa bata taba yi ba, hakan bai dame shi ba, sai dai ita Karimar ce ta ke
cikin damuwa akan rashin haihuwarta. Duk kawaicin da ta ke da shi, sai da wata rana ta
shawarce shi da suje asibiti a auna su a gano wanda ba shi haihuwa a cikinsu, ya yi biris da ita,
sai ta saka masa kuka tana cewa, ita ta amince idan shi ne ba ya haihuwa zata ci gaba da
zama da shi muddin ranta. Yayinda idan aka samu akasin haka tana shawartar shi da ya kara
aure, saboda a duk lokacin da aka kawo Isah (lokacin yana dan yaye) gidan hankalinta tashi
yake, ta dinga fatan Allah Ya ba ta hauhuwa. Ya yi shakulaton bangari da zancen natam saboda
shi bai ga wani abin doki ga haihuwar ba, duka shekaru uku da aure har an isa a soma karafinn
rashin haihuwa? Ganin yadda bai damu da damuwarta ta rashin haihuwar tasu ba, ga kuma
fuskanta da ta yi a duk lokacin da ta yi maganar ransa na matukar baci sai ta daina yi masa
maganar, ta rungumi hakuri tare da rokon Allah ba dare ba rana akan Ya bata haihuwa. An
samu shekaru biyar cur da yin auren Sagir babu wani bayani na game da haihuwa, don haka su
duka ma sun fitar da rai da samun haihuwa a gare su, suna ganin dama can su din ba masu
kwan haihuwar ba ne. Wata ranar litinin ce aka yi zama cikin sirri irin nasu na masu sirri, 'yan
kungiya suka taru kamar yadda akasari suke gudanar da taronsu a ranakun littinin domin ta fi
kowacce rana muhimmanci a gurinsu, kasancewar a ranar ta littinin ne aka kafa kungiyar, kuma
airin ranakun littinin din ne shuwagabannin da suka shude suka hau kujerunsu, don haka sun fi
yin taro a wannan rana. Sai dai idan wata bukata ce ta taso musu ta gaggawwa, wannan za a
iya gudanar da taron a kowace rana ta kama. Taron na wannan ranar ba shi da armashi, domin
sun taru ne akan korafin tun da Sagir ya hau karagar mulki bai fitar da Magaji ba, ga shi har ya
shafe shekaru biyar, wanda azahirin fitar da Magaji, domin yadda yake jin dadin Mulkin nasa,
yana ganin kamar idan ya fitar da Magaji to wa'adi na iya riskarsa a kowane lokaci. Amma a
ranar 'yan kungiya suka uzzura masa har suna ikirarin ya karya doka daga cikin dokokin da
kudin shugabancin nasu ya tanadar, wanda bijirewa hakan akwai hukuncin da aka tanadar.

Cikin bacin rai ya yi SUBUL-DA-BAKA ya ce. "Tunda kun matsa lallai sai na fitar da Magaji
kamar yadda kuka sani, Shugaba ne kadai yake da damar zabar magajinsa, idan kuwa ya zba
ko shi bai isa ya ce ya sauya da wani ba. Don haka ni ma a yau zan bi jerin takwarorina, zan
fitar muku abin da kuke so, zan fitar muku da Magaji yanzu-yanzun nan. Magajin kuwa shi ne,
duk abinda na haifa, ma'ana dan cikina shi ne magajina, shine wanda zai ci gaba da mulki
bayan gushewata daga doron kasa".
Dukkansu sai suka kama kallon-kallon, domin dai sun san Sagir bai taba haihuwa ba, amma
wai dan da ya haifa shi ne magajinsa. Alh. Sammani shi ne ya soma magana, ya ce.
"Honourable, dama kana da da ba mu sani ba?" Sagir ya girgiza kai, ya ce. "Ba ni da ko kwai,
amma hakan da na fada shi ne hukunci fakat!" .
(Wato bai son sauka daga KAZAMAR MULKI!, ni kuma na ce da kyakkyawar mulkin ma ai,
MUTUWA BATTA KYALE WANI DAN WANI........(Sadin Mama))
.
Alh. Nuraini ya ce. "Isan kuma ka gushe ba ka haihu ba fa?"
Bai ba shi amsa akan hakan ba, sai ya ce. "Na sallami kowa bana bukatar jin wani cece ku ce
daga gare ku".
Shi a tunaninsa wannan karamin al'amari ne, sam bai taba nadama akan wannan hukunci da ya
yanke ba. Sai da aka wayi gari Karima ta samu ciki, wannan rana ita ce ta zamo RANAR
NADAMA agare shi, ya shiga kuncin zuciya, ya shiga damuwa ainun har Karima ta rasa gane
kansa. Yayin da ya kai labarin a kungiya ba karamin dadi suka ji ba, musamman mutanen da
suke adawa da shi, dalili kuwa shi ne, suna ganin Sagir ya gina ramin mugunta ne ta zabar
abinda ya haifa ya zamo magajinsa a tunaninsa ba zai samu haihuwa ba, sai ga shi ramin ya
burma da shi tsulum!
Babu wanda ya jajanta masa bare ya ba shi wata shawara don gujewa faruwar subul-da-bakan
da ya yi, shi da kansa ya shiga laluben hanyar da zai magance matsalar abin ya ci tura.
Ya yi tunanin ya fita daga kungiyar, amma gudun abin da zai biyo baya shi ya hana shi fita, daga
baya ya yi na'am da wannan BAHAGON HUKUNCI da ya yiwa kansa, ganin cewar ai da bai
taba haihuwar ba, hasalima bai yi tunanin zai haihu ba. Tunda kuwa yanzu za a soma akwai
alamar za a ci gaba da haihuwar agidansa, shi ba komai yake jiwa tashin hankali ba, sai ganin
shi da kansa ya kai abinda ya haifa kungiyar shan jinin mutane, ina zai kai wannan abin kunyar
yayin da kwai ya fashe? Dole dai ya hakure rayuwa taci gaba da tafiya har aka samu watanni
takwas rannan abib tsafinsu ya bukaci jinin dan Alh Sammani, ai kuwa duk ya rude ya kidime
ganin cewa da daya yake da shi, amma yana gani zai rasa shi? Ga shi yana yiwa dan
matsanancin so, yayi juyin duniya akan a hakura da jinin dansa, amma ba wanda ya kula shi
saboda sanin ka'idojin kungiya.
Daga karshe ma wani da ke kira Madu ya harzuko masa da ruwan masifa cewar, lokacin da
dodon tsafi ya bukaci jinin mahaifin Madun waye ya hana? Alh Sammani wani irin bahagon
mutum ne, yana da bakar zuciya, sannan ba ya hakuri da daukar fansa. A dalilin bukatar jinin
dansa da dodon tsafi ya yi ya sa shi shiga cikin rudu da tunanin hanyar daukar fansa ta ayyana
masa ya bi duk hanyar da zai bi ya kawar da Sagir in ya so daga bisani ko ta halin kaka shi sai
ya hau karagar mulkin yadda zai fanshe jinin dansa, ya dinga yiwa 'ya'yan kungiyar dauki
dai-dai da iyalansu.

Saboda haka shige da ficensa ya yi yawa wurin ma shahuran bokaye duk da kasancewarsa
gogaggen matsafi masani sosai a harkar, hakan bai sanya ya san wasu hanyoyi da zai assasa
mutuwar Sagir cikin sauki ba, don haka bin bokaye shi ne abin da ya ke dacewa a gareshi.
ada Hausa Book stories
MATA’UL HAYAT(JINDADIN RAYUWA)
¤¤30¤¤
Kafin a samu nasarar abin da yake so, said a aka yi wani gagarumin aiki, wanda ya boye duk
wani shiri da Sammanin ke yi bare har Sagir ya gane ya dauki mataki, shi ma shirin kafin yinsa
said a aka halakar da mutane uku, don wani shahararren boka ne mai gain har hanji ya yi aikin.
Bayan ya tabbatarwa Alh. Sammani cewar, matsawar ana son kawar da Sagir sai an yi wannan
shirin. A cikin wannan shiri da aka yi akwai wasu bayin Allah guda uku da suka so tarwatsa
shirin, to suma said a bokan ya daure, daurin talala cikin boyeyyen sirri da surkulle irin na
mushirikai wadanda Allah ne kadai yake iya karya shirinsu, tunda yasan shi bai isa ya kawar da
su daga doron kasa ba. An samu nasarar kowanne shiri da aka yi, wanda ana gobe rasuwar
Sagir aka zo gidan gona cikin sirri aka kafa tarkon a dai dai inda yak e ajiye motarasa.
Washegari da safe shaukin abin ne ya dinga fizgarsa har yah an masa sukuni, yana son yin
kiran gaggawa a kungiya don tattaunawa, amma kasala ta hana shi. A lokacin ne Haj. Karima ta
kira shi a waya ta sahida masa Haj. Asmo ta zo daga Katsina. A lokacin kuma ne da zai tafi
gida Alh. Sammani ya zo a ofis dinsa, wanda y agama bulbule jikinsa da turarukan da bokan ya
ba shi. Ma’anar turaren shi ne, matsawar ya yi tozali da Sagir ya ji kamshin turaren kafin mai
afkuwar ta afku, to ba shakka shi ne zai hau karagar mulki sabanin abin da matar Sagir zata
Haifa akasin da aka samu bokan y ace kada ya yarda ya yi Magana da wani yayin day a saka
turaren, har sai ya je gurin Sagir. To amma day a shigo gidan gonar akwai wadanda suka
gaishe shi ya amsa musu, wannan shi ne sanadin day a sa Sagir bai ji kamshin turaren ba.
Bayan sun gama tattaunawa game da batun daukar dan Alh. Sammani da za a yi abai wa
dodon tsafi, suka rabu lokacin ne Sagir ya fada tarkon da aka kafa masa, ya yi tuntube da
kahon LIBHAS wanda aka samo daga kasar Sin, cikin surkullen bokan Alh. Sammani, ya dinga
aman jinni har zuwa asibiti…”
Ko da Abubakar ya zo nan alabrinsa sai ya ja baki ya yi shiru, yayin da su kuma duk kasala,
damuwa, firgici da komai ma suka lillube musu jiki. Inna Yaduwa kuka ta ke kamar ranta zai fita,
shi kansaAlh. Rabi’u kwallan ne a idanunsa, Alh. Sada yace, “Subhan Allahi, tabbasa biri ya yi
kam da mutum, akwai lokuta da dama da na dinga mamakin irin dukiyar da Sagir yake da ita,
ashe akwai sanadin samuwarta?”
Yakub ya karbi zancen da cewa, “wannan shi ne sanadin duk wata matsala da ta faru, abin
al’ajab ko rudani da kuka ga sun faru da Shuhuda duk sanadin hakan ne.kamar yadda na fada
muku labarin yana dauke da bangare uku, kuma kowane a cikinmu yana da bangaren da zai
bayar, to kun ji bangare daya, sannan muna rokonku da kada ku yi fushi ku yafewa da uwanku,
kuma danku abin day a aikata, ko don ya samu sassauci”. Babu wanda ya tanka, shi kuma ya ci
gaba da cewa.”kafin wani daga cikin mu biyun nan y ace wani abu zan sanar da ku wani abu
day a faru, yayin da Sagir ya zo rasuwa Alh. Ahmad ya ga idanuwansa sun sauya launi daga
fari da baki kamar yadda idanunsa suke, zuwa launin KORE, DORAWA da BAKI. Tabbasa
hakan yana da nasaba da sirrin tsafinsu duk wanda zai mutu dan kungiyar ko kuma aka sha
jininsa ta wannan hanyar to sai anga wadannan launuka a idanunsu” ya karashe maganarsa

yana duban Uncle Hamza, ya dora da cewa. “nasan daga kai Hamza har Isah kun yi tozali da
abubuwan al’ajab daga ciki hard a sirrin NETWARK, sirrin sauya suffa dama dai sauransu. Tun
da zare daya na labarin ya kamala, Shuhuda ita zata kamo zare na biyu wanda ke dauke da
sirrin NETWORK da wasu abubuwa da suka faru su ma cikin sirri”. Ya yi furucin yan duban
Shuhuda Ibn Khaddab. Ita kuwa ta gyara zama sosai tana fuskantar mutanen da ked akin,
sannan cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, ta soma fadin cewa:-
BABI NA SHA TAKWAS
SAKAKKIYA
Yayin da aka haifi Shuhuda ‘ian kungiya sun ji dadi matuka, koda yake akwai alhinin rasuwar
shugabansu a tare da su da suka wayi gari bakatantan, to amma wannan bai hana su farin ciki
ba. Idan an cire Alh. Sammani wanda tunda ya bar gidan gonar bai zame ko ina ba sai gurin
bokansa ya sanar masa ya aikata duk abinda y ace ya aikata. Bokan ya fashe da dariya,
sannan y ace. “sammani ka yi kuskure gurin aikata abubuwan da an ace maka tun a gida
lokacin da zaka fito ka yi amfani da ruwa, wanda n ace maka kada ka kusanci ruwa yayinda ka
fesa turaren. Sannan da ka je gidan gona kafin ka isa gurin Alh. Sager ma’aikata sun gayar da
kai, kuma ka amsa musu, ko mantawa ka yi, ko kuwa duk girma da isr ce suka janyo maka?
Don haka aiki bai yi kyau ba sam-sam. A bangare daya ne aka sami nasarar wato mutuwar
Sagir, domin tabbas ya yi tuntube da kahon dama ka’idarsa na muddin mutum zai yi tuntube
dakahon libhas shi lallai babu makawa sai ya tattara inda ba a dawowa. Sai dai an haifi ‘ya
mace wadda it ace magajinsa a kungiyarku kamar yadda tsarin kungiyar ta ke, samun galabrka
kuwa zai yi wuya”. Tun day a ji wannan bakin labarin hankalinsa ya dugunzuma ya tashi, sun
rabu da bokan akan idan wata bukata ta tashi zai dawo masa. A lokacin da aka haifi Shuhuda
an ganta tana tsotsar hannu wanda aka yi tunanin sanadin bakunta ne ko kuma tana jin yunwa,
wanda a zahiri ba haka ban e, babban makasudin tsotsar hannun Shuhuda shi ne, don nusar
da ku akwai wani boyayyen al’amari a tare da ita mai bukatar tallafi, amma ba wanda ya yi
tsinkaye da hakan. Idan ba ku manta ba a labarin da Abubakar ya bayar yanzu ya sanar da ku
cewa, akwai wasu bayin Allah guda uku da aka daure yayin hada tarkon kawar da Sagir daga
doron kasa, hakika su wadannan bayin Allah ba mutane ban e , ALJANNU ne masu alaka da
KHASHIM TSAGEM, ai kun gane ko wan a ke nufi ko?” cikin mamakin yadda yarinya karama ke
ta lailayo labari Alh. Rabi’u y ace. “Idan na fahimce ki, kina nifin kakana wanda ya haifi
mahaifina?” t ace, “Tabbas shi nake nufi, wadannan bayin Allah sun kasance masu yiwa Khashi
Tsagem hidima tun zamanin yana mahaifarsa (Tsagem) lokacin da yake haziki kuma hafizi don
a gurinsa bayin Allah suke daukar karatu, har ya baro Tsagem suna yi masa hidima. Sun ci
gaba da bin tsatson Khashi Tsagem suns bas u kariya daga miyagun aljannu, bas u taba
sarewa ba, to lokacin da aka daure su aka gudanar da wannan aiki na kafa kahon libhas, Sagir
na mutuwa aka kunce su, iya kuka sun koka, duk da dama can suna kuka akan shigar Sagir
kungiyar matsafa. To lamari ne wanda yake rubutacce wanda babu wani mahalukin daga
bil’adama zuwa jinnu da suka isa su hana ikon Allah tabbatuwa, don haka suna ji suna gain
babu yadda suka iya Sagir ya fada wannan kungiya ta matsafa. Damuwar da suka shiga ta
ta’azzara, haka ya sa daya daga cikinsu yayi kaura daga kasar Nigeria ya koma can Misra.daya
daga ciki kuma ya assasa tsotsar hannun da Shuhuda ke yi, sannan da ta soma girma wata
rana da aka yi yunkurin tsaga hannunta ya samara da rowan nono maimakon jinni, don dai a
fahimci matsalar da ke tattare da ita, amma ba a fahimatar ba. A can kungiyar matsafa kuwa

sun ci gab da kulawa da karagar mulki, domin bayan Alh. Sammani ya bar gurin boka bai
hakura da son hawa karagar mulkin ba, don haka da aka samu shekara daya wata rana kawai
yah aye karagar a zuwan ya zama shugabansu kamar yadda burinsa, amma nan take ya
daskare suka ga naman jikinsa na zagwanyewa har ya zube kaf sai kasusuwansa. Bayan shi
ma Izra’el da kwadayin mulkin ya shiga ransa ya jaraba hawa karagar mulkin ya daskare naman
jikinsa ya zagwanye. Hakan ya daga musu hankali matuka, amma da dodon tsafin nasu ya
sanar musu babu mai iya hawa karagar mulkin a zauna lafiya face wanda aka zaba ya zama
magaji sai hankalinsu ya kwanta, sun san akwai wanda zai shugabance su a gaba. A sirrance
suna zuwa ganin Shuhuda amma ba a taba bat a wani abu day a danganci naman mutane ko
jinni ba, suna dai zuwa dubata a matsayinta na Mgajiya wadda zata zamo shugabarsu nan
gaba. Lokacin da Slmai mai haja ta tsaga hannun Shuhudan ‘yan kungiya ne suka kasha Slmai,
saboda ta raunata magajiyarsu su kuma ka’idarsu ken an, ba a taba musu shugsba a zauna
lafiya. Maganar kwalwa da Shuhuda ta ked a ita, hakan Allah Ya yita ita din mai kwakwalwa ce,
sai dai akwai abubuwan da ta yi wanda daya daga cikin bayin Allah nan guda uku ne ya yi
jagorancin yinsu. Misali lokacinda tana aji hudu ranar da aka kawo wannan………”
Ta nuna Uncle Hamza ta cigaba da cewa.
a Hada Hausa Book stories
MATA’UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤31¤¤
“a matsayin sabon malami, ya yi musu tambaya akan RADIOACTIVITY ta bayar da amsa,
amma a zahiri ba it ace ta bayar da amsar ba, saboda a duk lokacin da hankalinta ya gushe bat
a ma inda ake tsammaninta. Sannan irin haka tta sha faruwa da Shuhudan, a dauketa a samara
da wata. Mas’ud ya bugi Shuhuda a lokacinda suka je Katsina har ya ji mata rauni don huce
haushin dukan da mahaifinsa ya yi masa saboda mahaifiyarta Karima, shi ma yan kungiyane
suka halaka shi. Dr Ya’u ma ya rasa ransa net a sanadin kungiya saboda su a ka’idarsu
shugabansu bay a rashin lafiya ya je asibiti kai tsaye,suna da likitocin da ke kula

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login