Showing 57001 words to 60000 words out of 83144 words
rubutata me yasa ba a damkata a hannunsa ba? Me ma
wasikar ta kunsa wanda har aka sanya mata suna da "budaddiyr wasika"? Ya kalli rubutun da
kyau kananan rubutu ne matuka wanda kana gani ka san da biro mai karamin kai aka yi
rubutun,kuma falle biyu kowanne gaba da baya an cika shi. Cab! Aiki ja, sai ya soma dube-dube
cikin falon. Shirye yake da manyan kujeru sabanin nasa kala ce kawai, amma yanayin tsarinsu
iri daya ne. Sannan akwai kayan kallo nau'in duk da ke da akwai a nasa gidan, sai dan karamin
firij daga can gefen kusuruwar yamma. Center table a gaban kujerun. Ya jijuna kai, sannan ya
nemi daya daga cikin kujerun ya zauna ya tsurawa takardar idanu, tare da soma karanta abin
da ta kunsa a sarari.....
.
.
BABI NA GOMA SHA HUDU
Budaddiyar Wasika
"Na san lokacin da zaka sami wannan wasika tawa hankalinka zai tashi, ranka zai dagule,
zuciyarka zata shiga kissama maka abubuwa da dama. Misali, me yasa na zabi rubuta maka
abin da nake son sanar da kai a wasika sabanin na same ka kai tsaye na yi maka maganar da
nake son yi maka? To akwai dalili mai karfi, ida kuwa aka ce dalili ana nufin abu mai girma da
muhimmanci. Dalilin kuwa shi ne, ba zamu samu isasshen lokaci ba, tunda nasan idan na fada
maka maganganun zaka so na amsa wadansu tambayoyi daga gareka.
Ture wannan gefe daya, mu dora akan makasudin wasikar, don sji ne abu mai muhimmanci a
gare ka da gare ni. Wasu matsaloli sun faru da tsatsonku wadanda suka rudar da tunanin duk
wanda yasan kanwarka Shuhuda. Musamman hasashe da mafi yawancin ku suke yi na cewar,
ALJANA ce, ko kuma MAHAUKACIYA ce! A cikin jinsin bil'adama akwai wadanda Allah ya
horewa kaifiyya gami da yakana ta fahimtar abubuwa da dama. Akwai kuma wadanda a
rayuwarsu MATA UL HAYAT (Jin dadin rayuwa ko ince kyale kyalen rayuwa) ke rudarsu har
yasa su assasa wani gagarumin laifi wanda zai buwayi al'umma ba tare da tsinkaye da
sakamako ba. Baya da haka akwai wadanda laifin wasu ke shafar wasu ba tare da su suka
aikata laifin ba. A cikin wani boyayyen sirri ne kadai za a iya fahimtar badinin Shuhuda, har a iya
kawo tallafin samun jin dadi da nutsuwar zuciya a gareta.
.
(Allah Sarki Shuhuda)
Sadin Mama.
.
Yi hakuri Isah, na rasa hanyar da ya dace na yi mak maganganun da nake son sanar da kai, illa
wannan da nake ganin zata fi cancanta. Sai dai idan ka bini sannu a hankali ne kadai zai sa ka
fahimtar, idan kuwa ka rudar da tunaninka ba zaka tab fahimtar tawa ba. Shuhuda tana cikin
wani hali na rashi tun wani lakaci da ya shude, don ko lojacinda muka yi karatu da ita a
makaranta ba ta da nutsuwa, awa biyu ta ke da hankali, idan hankalinta ya gushe kahin ta dawo
dai-dai sai ta samu awa biyu, ke nan gaba daya rayuwarta ta makaranta yini cur tan yinsu na
awanni uku da hankali, wanda in bacin da Allah Ya sa ita din mai kaifin kwalwa ce babu inda
iliminta zai kai. Kada ka yi mamaki akan duk abin da nake zayyana maka, domin nasan sirrikan
Shuhuda da dama wanda babu wani mahaluki da ya sani.
Ba Shuhuda kanwarka kadai ba, idan ba ka manta ba a haduwar mu Misra na ce maka nasan
adadin Shuhuda da ke da akwai a birnin Kano ciki da wajenta, saboda bincike na mai sunana. A
haduwarmu da kai Misra na ji dadin samunka da saukin kai, har na yi tunanin kai ne mutumin
da DUHu zai yaye ta sanadinsa, sai aka samu akasin haka. Munhadu da kai a birnin Katsina na nuna maka ban sanka ba, ba wai don ban gane ka din ba
ne, a'a saboda wani dalili wanda idan da a lokacin na bayyana maka kaina Shuhuda zata Shiga
rudani matsananci, watakila ma har numfashinta zai iya fita daga gangar jikinta. Ka ga kuwa
amatsayina na musulma bai dace na yi abin da zan firgita dan uwana Musulmu har ya rasa
ransa ta sanadina ba. Shuhuda ba tasa na je Misra ba, ba tsan kuma ina zaman aure a garin
nan ibadan ba, hasalima akwai abubuwa da yawa da suka shafe ni wanda ita ba ta sani ba.
Amma duk wani motsi nata na sani, nasan da a gabanka nake zaka tambaye ni ta ya na sani?
Kamar dai yadda na fada maka a Misra na kasance mai zurfin bincike akan mai sunana, duka
da wannan bai isa ya zamo hujja a gareka ba, illa kawai ka share duk yadda zuciyarka ta
kissama maka game da yadda aka yi na sani ka dauke shi a hakan. Maanufar dai itace ka
fahimci RUFAFFEN SIRRIN da na ke so ka gane. Lokacin da Shuhuda ta shiga aji hudu a
makarantar sakandare an yi wani zama na sirri aka shirya wani shiryayyen sirri mai
MURDADDIYA da daure kai.
Matsayi mai girma ya wanzu a gare ta, ta kuma zama hazika a wani bangare bisa wani
boyayyen sirri kamar yadda wasu rayuka suka shude bisa boyayyen sirri. Abin tambayar anan
shi ne, wannan wane irin boyayyen sirri ne haka? To sirrin yana tattre da sirrantaccen sirri
kwatakwacin sirrin haduwarmu. Kwatankwacin sirrin tsotsar hannun da Shuhuda ta ke yi.
Kwatankwacin sirrin fitar ruwan nono a jikin Shuhuda sabanin jini. Kwatankwacin wani abu mai
kama da almara da ya faru a tsakaninku bisa wani boyayyen sirri. Isah zan so matka ka saita
kwalwarka da tunaninka wajen fahimtar maganganuna duk da dai kai tsaye ban fito fili na sanar
maka ba, gudun dai abin da na fada maka, 'MATSAYINA NA MUSULMA bai dace nayi wani abu
da zai razana dan uwana musulmi ba har ya rasa numfashinsa".
Idan aka ambaci kalmar SILA tana nufin SANADI, Shi kuma sanadi yana nufin faruwar abu ta
dalilinta wani......
(Shin WAYE MUSABBABI na padawar Shuhuda cikin wannan boyayyen lamari?) Ku biyo ni dan
jin karshen BUDADDIYAR WASIKA. Sadin Mama.
Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
27
.
CI GABAN BUDADDIYAR WASIKA………………
Zan iya ce maka dukkan rudadden al’amarin day a rudaka da ma duk wanda yasan Shuhuda ya
faru ne sanadin ABOKI, shi ya sa ake so mutum yasan abokan da zai yi mu’amala da su, koda
yake faruwar sanadin ma rubutacce ne da ga Lillahi, duk hikima da wayon zillewa ba zasu yi
tasiri ba, duk gudun Rago ba zai hana a dora masa wuka don yin layya da shi ba. Hamza yana
son Shuhuda har cikin ransa, sai dai ba shi da kwanjin zamowa miji a gareta, idan aka yi
la’akari da kasancewarsa akan matsalolinta. Haka kai ma akwai kasawarka, shin wa ya dace da
wannan muhallinta? Amsar it ace ZABIN ALLAH domin Shi Yake da SANIN GOBE. Daga
karshe zan diga DANBA akan tunatarwa. ‘a duk lokacin da aka manta da mayar da lamari ga
Ubangiji akwai tarin da na sani.Addu’a aba ce ga duk musulmi ya dimanci yenta ba wai sai wata
matsala ta faru ba. Sannan akwai cutuka wadanda likita bai isa gano makasudin samuwarsu ba
bare yasan magungunansu. Shawarar d azan baka, ka kasance mai yin addu’a ba dare ba
rana, ko me kake ka yawaita neman tsari daga:-
MIYAGUN MUTANE
MIYAGUN SHAIDANU.
Allah Ya taimakeka ka tsallake siradin da kake a kai, Allah Ya taimakeka ka zamo mutum mai
himma wajen SADAUKARWAR da rayuwa akan tafarkin addinin musulnci. Akwai zobenka da
yake hannuna wanda ka ba wa Shuhuda lokacin da ka dawo daga Senegal, watakila kaga
irinsa a yatsana a haduwarmu burnin Katsina? To na hannunta ma ya dawo hannuna bias wani
boyayyen sirri. Wassala! Sai Allah Ya yi mana dawowa idan da rabon ganawa!
Tun kafin ya karasa karanta wannan zungureriyar takarda mai taken ‘Budaddiyar wasika’ gumi
ya jike Isah, ya yi sharkaf, idanunsa sun sauya launi, zuciyarsa ta jagule.
Bat a yi karya ba kamar yadda ta fada, dole ne ya shiga rudani akan wannan takardar, ba ma
shi kadai ba dak wanda zai karanta takardar dole ne ya shiga rudani. Idan zai iya tace
abubuwan day a karanta a cikin wasikar to abu na farko da zai kissima, wannan wani labari ne
day a fito daga hannun AJJANA SHUHUDA IBN KHADDAB, bias hujjojin sanin wasu abubuwa
da ta ked a su, wanda ya fi karfin sanin bil’adama, koda ace ma wani bil’adama zai zansu, to sai
dai ya kasance mai yawan shekaru, kuma wanda yake da alaka da wanda abin yake faruwa
akansa. Ita kuwa wannan a yadda ta ke din nan ba zata wuce shekaru ashirin ba, idan ma ta kai
ken an. Kuma ba ta zaune da Shuhuda koda yaushe bayan makaranta da ta hada su, bare
tasan komai na rayuwarta wanda ita kuma Shuhudan ba tasan wasu abubuwa da suka shafeta
ba. Isah mutum ne mai kwanji, amma bai ga alamar yana da kwanjin da zai iya jure wannan
sha’ani ba.
Nadama ta zo masa a karo na biyu na dawowars kasarsa ta haihuwa, wato Najeria tunda tun
lokacin day a dawo bai samu nutsuwar zuciya ba. Abin day a lura da shi matsawar yana bukatar
zaman lafiya da fita daga tarin rudanin da yake ciki game da wannan murdaddiyar al’amari to
kawai ya yi kaura da Najeria ya koma Misra ya yi aiki a karkashin kamfanin da malaminsa Dr.
Outhman Ibn Abdulfatah ya so ya yi tun da farko.
Sai dai inda yake hangen matsalar bay a wuce ta bangaren mahaifinsa, tunda a farko ma ya so
hakan amma mahaifin nasa ya kiya masa, yanzu day a fara aiki a Nigeri zai kuwa yiwu ya
amince masa aiki a Misra? Shirme, hauka gami da tsabar rainin hankali shi ne muraran abin da
yake ganin su Shuhuda na yi masa. Tunda yasan kauracewa zamansa Nigeria ba abu ne mai
yiyuwaba, to kawai ya dauki matakin fatattakar duk wani lamari da zai sada shi da Shuhuda
tundabai ga wani abun anfanu a hakan ba. Ya ja wani dogon tsaki yana yarfe gumin day a jike
shi, tukunna ya mike tsaye ya tunkari kafar fita daga falon.
Tsau! Yaji wani abu ya ratsa ta dukkan sassan jikinsa, kamar tsoro n eke dirar masa.
Cak! Ya ja tunga ya tsaya tare da waigawa da sauri, ya duba ko’ina bai ga wani abun da zai
tsoratar da shi ba, illa dai haka nan ya samu jininsa da tsinkewa ya yi tsururu tamkar ruwa. Ya
dau mintina biyu a haka, sai ya ji kamar zuciyarsa na yin shakulaton bangaro (sharewa) da
lamarin Shuhuda, musamman la’akari da abinda budaddiyar wasika ta kunsa. Sai dai a wani
bangaren yana karfafawa kansa sharewa da Shuhudan, domin budaddiyar wasika babu abin da
ta kuma sanya shi illa wani firgici. Sam bai hango wata hanya da zai shawo kan matsalar
rudanin da yake ciki ba. Da azamarsa ya sake ‘yunkurin ficcewa daga falon, amma kamar an
daure shi, domin ji ya yi gaba daya babu wata gaba da ke iya motsi a jikinsa. Hatta kansa ya
kasa juyawa zuwa bayansa, illa gabansa kawai da yake kallo. A bayan nasa kuwa yana jiyo
kamar ana motsi, kamar ma taku yake jiyowa. Da sauri ya ambaci…..
‘INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN, LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAH……’
Kafin ya karasa ma tuni ya ji wani irin kuzari ya zo masa, ya kuma fice daga falon yana mai
takaicin shigowarsa hurumin dab a nasa ba. Cikin rudanin ya yi saurin rufe gidan da makulli ya
koma gidansa, ya zube a falo tare da rafka tagumi.
Hakika duk abin day a faru da shi a cikin gidan su Abubakar lamari ne na sihiri, ko kuma gaba
daya ma y ace jinnu idan haka ne kuwa daga Shuhuda Ibn Khaddab har mijinnata Abubakar Ibn
Khaddab duk jinnu ne? idan hasashensa ya zama gaskiya ta ya suka samu wannan gida da
suke ciki? A matsayinsu na jinnu zasu iya zama a gidan, to amma ina asalin mutanen da ke
zaune a gidan? Ko kuwa sun z one a sigar mutane an dauke su aiki har aka bas u muhalli
kamar yadda shi ma kamfanin da yake aiki suka yi masa wannan gatanci? Hakika akwai
boyayyen al’amari mai matukar rudani da daure zuciyar tunanin duk mai tunani.
(nima n ace, Isah ba kasan dawn garin ba, Shuhuda Ibn Khaddab ta baka haske sosai ta yadda
zaka warware lamarin cikin saukakar hanya, (sadin mama)).
BABI NA GOMA SHA BIYAR
TARIHI YA MAIMAITA KANSA
An wayi gari yau laraba, Inna Yaduwa na kishingide a falo idanunta a rufe, ta kara ‘yar karamar
radiyo (kachbo) a kunnenta tan a sauraren wani shiri ‘Ku karkade kunnuwanku’ wanda Aisha
Bello Mahmud ke gabatarwa a tashar FREEDOM RADIO wanda suke karanta wani littafi mai
suna MACE BAIWA na jinjirar marubuciya mai tasowa Naja’atu Haruna Sale. Tana jin dadi labarin, saboda yadda aka dauko rayuwar da mata suke a karkara aka rubuta, duk
wasu tarin matsalolin mata sun kunshi wannan hadaden labari. Da yake yau din it ace rana ta
farko da aka soma karanta littafin, sai Inna Yaduwa ta ke ji, ina ma kada lokacin da aka dibarwa
shirin ya cika ba tare da an kamala karanta littafin ba? Kusan da gudu-gudu, sauri-sauri Shuhuda ta fito daga daki da nufin isa bandaki, sai dai kafin ta
isa tuni ta soma kyelaya amai, wanda yunkuri da karar sautin zubar aman ne ya farkar da Inna
Yaduwa abin da ke faruwa, hart a hanzarta mikewa zaune daga kishingiden da ta ke tana
ambaton.
“lafiya”
Amma Shuhuda shiru ta kasa Magana illa ci gaba da kyelaya aman da take yi kamar zata
amayar da duk abin da ke cikinta. Hankalin Inna Yaduwa ya tashi matuka, ta isa gaban
Shuhuda a rude tana tambayarta abin day a same ta tare da tattaba jikinta. Sai da kyar aman
ya tsagaita, amma duk ta galabaita ta fita hayyacinta. Inna Yaduwa ta kamata zuwa bandaki,
tab a ta ruwa ta kurkure bakinta, sannan suka dawo falon, Shuhuda ta kwanta akan doguwar
kujera, yayin da Inna Yaduwa ta goge gurin da aman ya bata ta dubi Shuhuda cikin tausayawa,
t ace “sannu” bat a amsa ba, Inna Yaduwa ta mike ta nufi kan dan karamin firij da wayarta ke
ajiye a kai, ta dauko ta duba lambar Alh. Sada wadda ta sanya wa alamar mota, don duk wanda
ke cikin wayar akwai alamar da ta ke gane lambarsa da ita. Kasancewar ba ilimin book ta yi ba.
Tana kiran wayar yayin da take dawowa don zaunawa kan kujera. Ya dauki wayar cikin ladabi
ya isar da sakon gaisuwarsa tukunna t ace masa. ”Shuhuda ce ba lafiya, tana ta amai, idan
kana da hali ka zo a kai ta asibiti” y ace “ina direban gidan ne?” t ace, “sun fita da Alhaji”, y ace,
“to ni yanzu na yi nisa sosai, amma bari na turo Nuruddeen sai ya kai ku” t ace, “ba damuwa”,
Ta kasha wayar tare da tsurawa Shuhuda idanu cike da jin tausayinta. Ba jima sosai ba
Nuraddeen ya shigo gidan yana kada makullin mota, fuskarsa a sake y ace,”yar tsohuwa ke
bakin cikin shan gumba zaki yi mana, an ce na zo na kai ki asibiti?” ya fadi maganarsa cikin
sigar wasa na kaka da jika, fuskarta a daure t ace,” da yake ba ka da idanu shi yasa ka gaza
gane ba nice ba ni da lafiya ba…………. Yayarka ce Shuhuda gat a nan bat a da lafiya, it ace za
mu kai asibiti”. Sai lokacin ya lura da Shuhuda da ke kwance akan doguwar kujera y ace,”A’a
Aunty Shuhuda me ya same ki”? Inna Yaduwa t ace masa. “ka ga muje asibitin tunda ka ganta a
kwance ai kasan akwai matsala”. Ta fada tana kokarin tallafa Shuhuda, suka fita su ukun zuwa
inda ya yi fakin, ya bude musu gidan baya ta saka Shuhuda. Nuraddeen ya ja motar cikin
azama suka isa ZAHTY MEMORIAL HOSPITAL, aka shiga da ita emergency, Tashin farko
likitan day a dubata ya bukaci fitsarinta, aka shiga da ita wani ban daki tayi, sannan ya basu
magungunan taimakon gaggawa tare da cewa a dawo anjima a karbi sakamako. Bayan sun
dawo daga asibitin gidan ya dinga daukar harami, nan da nan ya cika da ‘yan dubiya. Karfe
hudu da rabi Alh. Ahmad da Nuruddeen suka je karbo sakamako. Likitan ya tsayar da su kafin
ya basu sakamakon, ya dubi Alh. Ahmad fuskarsa cike da fara’a y ace. “Alhaji ina taya ku
murna, da fatan Allah ya raba su lafiya. Amma zan so nab a ku sahwara, duk macen da take da
farkon ciki kafin ya yi kwari ana bukatar ta rage yin ayyukan da za su wahalar da ita gudn
zubewar cikin…………………..”
Zai ci gaba da dogon sharhin nasa Alh. Ahmad ya daga masa hannu fuskarsa a turbine yana
cewa, “Dakata don Allah doctor! Ban fahimci mai kake nufi ba fa?”
Ran likitan ya dan baci sai ka ce bad a yaren Hausa yake masa bayani ba?
Yanzu haka irin mutanen nan ne da suke auren yara kanana amma bas a son haihuwa. Don
haka sai ya dauki sakamakon gwajin ya mika masa. Alh. Ahmad ya sa hannu ya karba cikin
zumudi, ya duba abin da takardar sakamakon ta kunsa. Ba wani abu ba ne face Shuhuda tana
dauke da danyen ciki na wata daya da kwanaki biyar. “INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN!” Alh. Ahmad ya ji gabansa ya soma faduwa, idanunsa
suka sauya launi, cikin wata rikitacciyar murya y ace. “Shuhudan ce da ciki? Mun shuga uku!
Ina zamu kai wannan tarin abin kunyar?”
Jin kalaman da ke fitowa daga bakin Alh. Ahmad ya sa jikin likitan yayi sanyi, da farko ya dauka
Shuhuda mat ace ga shi Alh .Ahmad din, amma yanzu ya fahimci ‘ya ce a gareshi. Sai ya shiga
kwantar masa da hankali cikin sanyayan kalamai. Alh. Ahmad y ace cikin dafe kai. “Likita anya
ba a samu akasi an sauya sakamakon Shuhuda da na wata ba? Wallahi budurwa ce ba matar
aure ba, ta ya kuma za a ce tana da ciki?”
Likitan