Showing 72001 words to 75000 words out of 83144 words
yake kissimawa a ransa
Alhaji Rabi’u ne ya kawar da shirun nasu da cewa .
“ lallahi mun tafka kuskure da muka dauki kowace cuta akwai maganinta a asibiti mun manta
cewar duk inda aka bar Alkur’an i sai an samu ba dai -dai ba, domin shi Alkur ‘ani shi ne zuciyar
kowace irin ciwo.
Amma mun gode wa Allah da ya kawo mana ku cikinm rayuwarmu , shin yanzu ta wace hanya
zamu kubutar da Shuhuda?
Yakub y a ce, “ gaskiya kubutar Shuhuda daga tarkon da ta ke ciki yana da matukar wahala,
amma da yake Allah yana tare da mu, da izininsa zamu samu nasara.
Shuhuda kam na cikin wani mawuyacin hali na azabtarwa, idan har ana son kwatota daga
hannun matsafa akwai SADAUKARWA, ma’ana a fita da zummar za a dawo da rai ko akasin
haka
Kuma ba lallai ne a samun nasara ba, sai dai addu’a bat a bar komai ba, rubutaccen al’ amari
kuma ba wanda ya isa ya kankare shi
Tsuburin da Shuhuda ta ke yana can jihar sokoto a can kungurmin daji, dole sai an yi tattaki
daga nan Kano zuwa Sokoto sannan za a sadu da inda ta ke , kuma tafiya ce da za a yi a cikin
sirri ba tare da idanun masu sirri sun san da ita ba.
Daga ban garenmu za mu dauke nauyin tafiyar har kusa da tsuburin , sannamn za mu bada
wata addu’a ta makantar da makiya daga ganika
Mu ba zamu iya tunkarar tsuburin bas hi yasa tun tuni ba mu kwatota daga hannun masu sirri
ba, hakan kuwa ya biyo baya ne akan wani sinadari da saka a tsuburin da zarar jinsin jinnu ya
ratsa gurin to kuwa zai soye ne rumus`
Karmar yadda na fada muku a baya masu sirri suna tunnanin isah da inna yaduwa suke hana
shuhuda zuwa kungiya, shi ne suke ganin a kowane lokaci su isah za su iya sanya malamai su
tura jinsinmu (jinnu) a dauko ta, don haka suka yi wanna surkulle amman bani’adam yana iya
keta tsubrin har ya isa inda shuhuda ke duare ba tare da wani abu ya same shi ba. Matsawar idanun masu sirri bas u san da zuwan bani’adamu din ba, ma’ana bas u ga wanda
yatunkara guri ba
Idan an samu nassar isa inda ta ke , hannu ba zai iya kunce daurin talalar da aka yi mata ba,
akwai surar WAKI’A, karantata a koda yaushe yana kawo tsari, ita za a karanta a dai-dai inda
shuhudan ta ke, idan Allah ya yarda daurin zai kunce hart a dawo hayyacinta da ta rasa tun
lokacin da aka daureta a tsuburin. Ina mai tabbatar muku da cewa, daga lokacin da daurin ya kunce, dukkan wadandan ke
kungiya sai sun ji a jikinsu, don haka za su yi saurin zaburowa domin sun dauki matakin
gaggawa.
To a wannan lokacin Allah ne masanin yadda zata kasance, ko a mutu ko a yi rai, fatan ma dai
a yi ran ga godiyarmu.
Idan har aka samu nasarar fitowa da shuhuda daga tsaburin komai zai iya faruwa ga kungiyar,
imam ta tarwatse ko kuma ta ci gaba da wanzuwa ana farautar rayuwar shuhuda da duk wanda
ya shafe ta.
Idan bat a fito daga tsuburin ba, shi ma wanda ya yi jarumtar zuwa tsuburi ba zai fito ba, kuma
dukkan su zasu zamo kyautarwa fa abin tsafi.
Fitowar su daga tsuburin na tafiya bisa kalubalen tarwatsewa kungiya ko akasin haka!”
Yakub ya yi shiru da ya karashe maganarsa. Alh. Ahmed ya karbe da cewa. “Idan aka samu
nasarar fitowarta daga tsuburin kungiya bat a tarwatse ba, wane irin taimako za ku ba wa
lamarin?”
Abubakar ya magantu.
“Allah shi ne masanin yau da gobe, don haka shi ya bar wa kansa sani. Shi yasa aka ambaci
SADAUKARWA a cikin lamari. Ma’anar da muke nufi da sadaukarwa shi ne, ku sadaukar da
rayuwarku don yin jidadi.
Amma ki sani mu ba mu isa mu ba ku kariya ba facea bin da Ubangiji ya tsara, idan ya nufe mu
da ci gaba da ba ku kariya za mu ba ku kamar yadda ya nufe mu da sanin sirrin da wayonmu ko
kasantuwaru jinsin jinnu ba mu isa mu sani ba.
Tun a nan za ku gane shi (Allah) gwani ne, mai hikima ne a dukkan lamuransa, kamar yadda
suratul Ikhlas ta bayyana tsarkin Ubangiji.
Abin da muke so ku sani shi ne rayuwar dan Adam da dukkan abin da yake bisa doron kasa na
sarari da na boye, da abin da yake a kiyama duk Allah (S.W.T) ne ya yi su, kuma Annabi
Muhammadu (S.A.W) dan gatansa ne!
Idan kun yarda da hakan babu tababa a cikin duk rokon da zaku yi, shi roko ana son yinsa da
tsarkakkiyar zuciya, madamar ana son Ubangiji Ya karba, don shi (Allah) mai tsarki ne, ba ya
karbar ibadar marar tsarki.
A cikin suratul Bakara aya ta 186 an bayyana yadda bawa ya kamata ya yi roko da tsarkin
zuciya.
Duk zuciyar da ta kasance cikin wasi-wasi akan tabbatuwar Ubangiji, ko kin amincewa da
Annabi Manzon Allah ne, lallai ba za a taba amsa rokon mai zuciyar ba”.
Shahuda Ibn Khaddab ta dora da cewa.
“An karbo daga Abi Hamzata anas bn Malik (R.A) hadisi na sha uku, manzon Allah (S.A.W) y
ace, “ka so wad an uwanka abin da ka so wa kanka”.
Dukkan mu nan ababen halitta ne, banbancin jinsi shi ke tsakanimun, amma mu duka
wajibinmu ne mu bautawa Allah.
Tun da kuwa mun yi tarayya akan abu daya (bautar Ubangiji) sai mu yi amfani da wannan hadisi
mu sowa ‘yan uwanmu a musulunci abin da muke so wa kanmu.
Kiran da zan yi a gare ku, ba ku kadai ba duk wata al’umma da wannan labara zai kai gare su
shi ne, kada mu yi sakaci da neman kariya daga shidan mai kawata mana MATA’UL-HAYAT
(Kyale-kyalen rayuwa) a zukatanmu.
Iyaye su tsaya tsayin daka gurin sauke nauyin da Ubangiji ya dora musu na tarbiyyantar da ‘ya
yan dashi (Allah) ya bas u amana.
Idan yaro ya samu dukiya a bincika cikin hikima a ga ta ya ya sameta?
Wane irin aiki yake da dukiyar?
Su waye mutanen da yake mu’amala da su?
Hakika idan iyaye suka bi wadannan hanyoyin ‘ya’ yansu za su kasance tsakanin Katanga daga
shaidan, Allah zai kare ‘ya’ yan nasu daga fadawa halaka ba domin saka idanunsu ba, a’a shi
(Allah) Yana kare bawansa a duk lokacin da ya so, amma wanna ma hakki ne da ya rataya a
wuyan iyaye na kula da yadda ‘ya‘yansu ke a rayuwa.
Allah Ya yi mana jagoranci a bisa aikin a gari, Ya kare mu daga sahrrin shaidan (La’ananne), Ya
shiryar da zukatan mu bisa tafarki na gaskiya alfarmar Sayyidul sadati”. Gaba daya gurin aka
amsa mata da.
“Amin”.
Uncle Hamza ya dago kansa da ke rusune a kasa, y ace. “ni na sadaukar da rayuwata, zan je
tsuburin domin kubutar da Shuhuda”. Jin abin da ya fada ya harzuka Isah, wato ma Uncle
Hamza har ya fi shi son Shuhuda ken an da zai sadaukar da rayuwarsa a kanta?
Lallai ba zai amince da hakan ba, domin shi ne mutumin da yafi cancanta ya yi komai akan
Shuhuda, shi ya fi dacewa da wannan sadaukarwar ko da ace ita zata rayu shi ya mutu, yasan
har karshen rayuwarta ba zata manta da sadaukarwarsa ba.
Amma kuma idan ya mutu a gurin sadaukarwa Shuhuda ta rayu, shi ken an sai ta auri Uncle
Hamza, ya same ta a sanga? Zuciyarsa ta karaya, ya ji wani kunci ya dirar masa a zuciya, karo
na farko tsanar marigayi Alh. Sagir ta tsira masa dukkan bargon jikinsa domin bas hi ba hakan
da ta faru ba. Ga shi ya tafi ya bar su da azal mai razanarwa da rudar da hankali! Wani bangare na zuciyara
kuma ya shawarceshi, kawai ya sadaukar, ko da ya mutun Uncle Hamza ya auri Shuhuda haka
Allah Ya tsaro, kuma bas hi doron kasar bare abin ya dame shi.
Wannan shawara da zuciyarsa tab a shi ya sa yayi saurin cewa.
“ni ne zan sadaukar da rayuwata don ceto ‘yaruwata Shuhuda , tunda daman can ni din na
sadaukar da rayuwata a gareta saboda a dalilin Shuhuda tsayin zamana a kasar Senegal ban
taba mu’amala da wata ‘ya mace ba, itace na ba wa zuciyata tun kuruciya, don haka yanzu ma
zan bata rayuwata don inganta rayuwarta”. Uncle Hamza yaji gaban say a yanke ya fadi, tsoro
mai tsanani ya shige shi, a yadda ya ga fuskar Isah ya ayyana zai yi bakin naci kuma ga alama
yanzu ma nacin zai yi!
Shi kam yana son Shuhuda kuma yana son nuna bajinta,ko don duniya ta shaida irin son da ye
mata tsayin lokacin da ya soma ganinta (RIYA)
Kafin ya tanka Yakub y ace. “Dukkanku za ku iya jarraba sa’a domin mai nema yana tare da
samu, kuma ba a san maci tuwo b sai miya ta kare. Sai dai ina so dukkanku ku nutsu ku san
cewa Allah (swt) Ya haramta riya (yi don wani) a cikin littafin Ahlari an bayyana hakan. Idan kun
san zaku yi aiki don riya ku sani aikin naku haramtacciya ce. Su duka biyun wuta ta dauke musu, domin kowannensu ya gano kuskurensa akan abin da
zuciyoyinsu suka kissima musu, wato zasu sadaukar da rayuwarsu domin duniya ta sahaida irin
son da suke yiwa Shuhuda. A bangaren Uncle Hamza sai ya ga abin da zuciyarsa ta kissima
masa bai isa ya zamo riya ba, tunda dai hark ace ta ceto masoyi daga halaka. Yayinda bangaren Isah ya gano lallai idan ya sadaukar da rayuwarsa akan ceto Shuhuda don
duniya ko ita Shuhudan su san irin dumbin son da yake mata, babu “Inna lillahi wa’inna ilaihi
raji’un, La haula wala kuwwata illa billahil aliyul azim, subhanaka inni kuntu minaz alimeen”.
A cikin zuciyarsa, sai ya ji ya samu nutsuwa, ya kuma tabbatar zai sadaukar ne domin Allah
makagin duniya da lahira da dukkan abin da suke cikinsu. Yakub ya yi murmushi , tukkunna y
ace , ”Dukkanku kun amince wa zukatanku zaku iya sadaukar da rayuwarku domin ceto
rayuwar Shuhuda Alhamdulillah kamar yadda na fada muku mu zamu dauke muku nisan tafiyar,
ba gudu ba ja da baya kuma har kullum kamar yadda muka fara hidima Khashim Tsagem zuwa
tsatson sa insha Allah zamu ci gaba da yi har karshen rayuwarmu”.
Alh. Rabi’u ya jinjina kai y ace, “mun godewa Allah mun gode muku, Allah Yayi mana jagoranci
akan komai”. Shuhuda Ibn Khaddab ta dubi inda matasan samarin suke, t ace, “Isah da Hamza
ina so na baku shawara, ku zamo mutane masu hankali da nutsuwa, idan n ace hankali ina
nufin masau amfani da baiwa da Ubangiji Ya yi musu, masu jajurcewa da mayar da lamari ga
Ubangiji, wadanda bas u dauki rayuwar da zafi ba. Masu so wa dan uwansu abin da suke so.
Iadan kuma n ace ku kasance masu nutsuwa ina nufin, kada ku yi sakaci wani abu kalilan ya
hargitsa ku, ya juyar muku da tunani hark u diga wasu-wasi wajen mayar da lamari ga Ubangiji.
Idan kuka kasance masu hankali da nutsuwa, hakika bau wani abu da ba zaku cimma nasara
ba insha Allah”. Abubakar ma ya dora da cewa.
“hakkun ‘yar uwa, idan mutum ya kasance mai wadannan dabi’o’in lallai y agama dacewa, shi
yasa ma ake so bayan mutum ya mallaki hankali da nutsuwa ya kasance kuma maizurfin ilimi,
don su hankali da nutsuwa sun a samuwa ne ga bawa musamman baiwa daga Allah. Amma
samun ilimin sai yakarawa bawa kwarjini a idanun wadanda ke kallonsa”. Uncle Hamza ya kasa hakuri ya boye kishinsa, fuskarsa ta nuna hakan muraran, amma bakinsa
bai furta ba. Shi kam Isah ya kosa ya je sadaukarwa, yana son ganin Shuhuda, yana kuma jin
tausayin halin da ta samu kanta a ciki , ashe duk wannan rudaddun al’amuran da ke faruwa
game da ita akwai boyayyen sirri? Hakika ba don Allah Ya so su da rahma ba Ya kawo su
Yakub a cikin rayuwarsu lallai da sun yi BABBAN RASHI na tsatson su.
.
To 'yan uwa masoya Shuhuda, wa zai sadaukar???
ada Hada Hausa Book stories
MATA’UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤32¤¤
.
WANNAN PAGE IN, SADAUKARWA CE GA DUKKAN MASOYA NA WANNAN GROUP MAI
ALBARKA
.
Wannan ma abin godiya ne matuka ga makagin sammai da kasai.
Shuhuda Ibn Khaddab ta kai dubanta ga Isah fuskarta da yalwa ta ce.
“A cikin budaddiyar wasika na fada maka zoben da ka ba wa shuhuda yana hannuna bisa wani
dalili, kuma a cikin labarinmu ba mu yi maganarsa ba, to ka sani dalilin da yasa na dauke zoben
shi ne, za a yi amfani da shacin yatsanka ta jikin zoben a shaye jininka, shi yasa ni ban ga
amfanin zobe ba, wannan shi ne dalilin da yasa na dauke zoben”. Isah ya yi godiya da wannan karamci da aka yi masa.
Dakin ya dauki shiru na wani lokaci, kowanne da abin da yake cikin ransa.
Sai zuwa can Yakub ya buda baki, y ace.
“Gobe idan Allah ya tashe mu lafiya ya kamata a yi tafiyar zuwa sokoto, saboda wasu dalilai da
nake ganin alamun nasara ta hanyarsu.
Na farko dai, goben ta kasance lahadi, ranar jajibirin kafuwar kungiyar EROSU mai tambarin
kwalwar kai, kuma a irin ranar yan kungiya sukan huta hasalima ba sa shan jinni a irin wannan
ranaku.
Kum a irin wannan ranar ma ko da ace za a tarwatsa kungiyar ne to za a iya samun nasara,
wata kila kuma akasin haka. Don idanun masu sirri kaifin haske gare su na sirri, amma da ya
kasance an samu kaifin haske na ALKUR’ANI to la shakka kaifin haske na masu sirri zai koma
DUHU.
Saboda haka lahadi it ace ta cancanta a yi wannan tafiyar, sai ku zamo cikin shiri karfe bakwai
na safiya Insha Allah zamu tafiyar.
BABI NA ASHIRIN
GA FILI GA MAI DOKI…
Tun bayan da Uncle Hamza ya baro Gidan su shuhuda ya shigo dakinsa ya yi zugum, zuciyarsa
na ayyana masa abubuwa masu yawa.
Hakikanin gaskiya shuhuda it ace mace ta farko da ya soma so a rayuwarsa, so kuwa ban a
was ba, bayan ita bai taba son wata ‘ya mace ba’.
Zuwairiyya ita ke haukan sonsa, shi kuma ko a kwalar rigarsa, bai ga inda zai dasa wata kwayar
son Zuwairiyya a zuciyarsa ba bare hart a yi tsirran da sonta zai samu muhalli a tare da shi.
Kallon da ya yi wa kwayar idanun Isah sai da zuciyarsa ta harba, domin ya ga sirrikan so masu
tarin yawa a cikinsu, so irin wanda ya jima datsirga jinin jiki.
Ke nan zai sha fama da zogin zuciya ko da ya auri shuhuda tunda akwai alaka tsakaninta da
Isah, dole wata rana za su hadu, idan sun hadu wane irin kallo Isah zai yiwa shuhudan?
Irin wanda ya gano a cikin kwayoyin madarar idanunsa?
Cab! Ashe shi ma dai yana a nasa salon kishin bai sani ba?
Ya yi juyi akan gado tare da rungumar filo, ya tuna yadda murdaddun al’amuran suka dinga
faruwa har kawo wannan lokaci, hakika akwai so mai karfi da yake yiwa shuhuda.
Sai ya soma ayyana yanayin da ta ke ciki a yanzu, wai gat a can a tsakiyar jeji daure cikin
sasari irin wanda ake daure dawakai, numfashinta na fita sama-sama.
Zumbur! Ya mike tsaye cike da tsoron abin da ka iya samun shuhuda.
Hannayensa ya soma bugawa a hankali, tare da cizon lebensa na kasa yana tattaki, wata
zuciyar ta yi masa matashiya me yasa tun farko bai jajurce don gano sahihin abin da ke damun
shuhuda tun kafin a kai ga wannan matsayi
Tabbas ko a zantukanta ya kamata ya gane wani abu makamancin haka, sannan kuma daukar
hoto da suka yi da shuhuhan ya yi sabaninta da kiran waya wadannan duk sunyan jigogi ne da
ya kamata ya gano abin da ke faruwa da shuhuda.
Ta tab ace masa ita sarauniya ce, ashe da gaske sarauniyar c eta matsafa?
Wa’iyazubillah, rayuwa mai kunci ken an, yarinya karama bat a san hawa ba bare sauka amma
azal ta fada mata.
Shin ya matsayin mutanen da aka hallakar ta sanadinta? Hakkin kisan akan way a rataya? Bai
sani ba, amma yana da yakinin shuhuda bat a da kamasho, saboda baita ke yin kisan ba, ana yi
ne saboda ita.
Kuma ba ita ta kai kanta kungiyar matsafan ba, an kai ta ne tun kafin hankali ya shige ta.
Shin zai iya sadaukarwar ma don ceto rayuwarta?
Idan su duka biyun suka yi nasara suka dawo da ita ba tare da wani ya hallaka ba, ya za a yi?
Wa zata zaba cikin su biyin biyin shi ko Isah? Tunda dai dole namiji daya ne zata aura, ba duka
biyun ba.
Har dare dai bai samu kwanciyar hankali ba, akwai son shuhuda a ransa, haka kuma akwai
tsoron abin da zai biyo baya idan shuhuda ta kubuta ta zabi dan uwanta sama da shi!
Shi din ma bangaren Isah bai samu nutsuwar ba, tunaninsa bai wuce ta ya zai yiwa Uncle
Hamza kub daya ba.
Lallai so marurun zuciya, duk irin son da Uncle Hamza ke yiwa shuhuda a hasashe ba za a
kwatanta shi da wanda Isah ke yi mata ba, domin salon son Isah daban ne mai tafiya ne a jinin
jiki, wanda yak e tsittsinka jijiyoyin jiki, ya makantar da kurumtar.
Dai-dai lokacin da y agama gyara makwancinsa, ya kishingida akan katifar yana tuno
abuburwan da suka faru tun haduwarsa da shuhudan Misra har kawo yau, ashe boyayyen
al’amuri ne zai fito fili?
Ya tuna lokacin da suka je Katsina, Shuhuda ta ce zata yi masa kyautar dan mutum har tana
tambayarsa ko ba ya so, ken an dama manufar furucin ke nan?
Ya dai shiga rudani da shi da kansa ya saka kansa, domin da ya yi la’akari da labarin da aka
bas u da bai ja ba, lamari da aka saka jinnu a ciki zasu aika.
Yanzu abin da yake