Showing 45001 words to 48000 words out of 83144 words
Haj.Asmo daga dakinta. Ita ma tana ganinsu ta washe fuska.
"Ni kam na yi fushi, yanzu saboda Allah Isah sai yau kake zuwar min?"
Yana sosa keya irin na maza, ya ce,
"Ayi hakuri Goggo".
Ta ce "idan ban yi hakurin ba ai da ba zaku ma gane gidan ba, duk da kuwa ka dauko wannan
marar son zumuncin. Ta hana min 'ya zaman lafiya, kullum kuka wai ita akaita gurin Aunty
Shuhuda".
Su duka suka yi murmushi, Shuhuda ta dora da cewa.
"Ki yi hakuri Goggo, dama karatu ne yake hana ni zuwa, to yanzu kuma an gama kafin a tafi
wata".
Haj.Asmo ta ce.
"Idan an daura aure ko? Ai ni an fada min kun hada kanku....."
Kunya ta lullube Shuhuda har shi kansa Isah, aka rasa wanda zai ce wani abu.
Haj.Asmo ta lura da hakan, sai ba ta ja zancen ba, ta dubi Sajida da har lokacin ta ke makale a
kafadar Shuhuda ta ce.
"To a sauka a bar Aunty ta zauna ko?"
Ba musu yarinyar ta soma kokarin sauka, Shuhuda ta sauke ta, ta zauna akan kujera. Haj.
Asmo ta ce da daya daga cikin matasan matan.
"Nafisa a kawo musu abinci da ruwa ko?".
Nafisa ta nufi kicin don hado musu abinci.
Isah ya dubi sauran yan matan, ya ce.
"Ku taso mu je ku kwaso tsarabarku".
Sun kwaso kayan tsarabar wanda suka ware na gidan, sauran kuma suka barshi a mota.
Sai da suka soma gaisawa sannan suka ci binci, aka shiga hira.
Karfe shida na yamma, Isah da Shuhuda suna zaune a falon Haj. Asmo da ita kanta Haj.
Asmon suna hira, Musabahu ya shigo falon hannunsa rike da waya yana murmushi ya ce.
"Afuwa, wani uzuri ne ya tsayar da ni".
Isah ya kawar da kai, ya ce.
"Ba ni zaka bawa hakuri ba, kanka zaka baiwa, domin yiwa wani yiwa kai ne, kuma duk wanda
ya gyara ya sani".
Musbahu yana kokarin zama akan kujera ya ce.
"Kin ji shi ko Sister?"
Shuhuda ta kawar da kai, ta ce.
"Ni kyale ni, bani da lokacinka. Bayan tunda muka zo aka sanar maka isowarmu, amma ba ka
tashi zuwa ba sai yanzu da ka ga dare ya yi, don kada mu fita zaga gari ko?"
Musbahu ya saka dariya, ya ce.
"Shi yasa ina shigowa na soma neman afuwa, kuma sha kuruminki tunda dai kwana zaku yi ai
magana ta kare, gobe idan muka dinga yawo sai kin ce kin gaji".
Haj. Asmo ta saka musu baki.
"Ai sun ce da safe zasu wuce. saboda zasu karare. Kuma a goben zasu koma kano".
Ya ce "shi ke nan, sai a yi min uzuri".
Bayan sallar magariba Isah da Musbahu su ka fito daga masallaci. Wayar Musbahu tayi kar.
Yana dubawa ya ga wande ke kiransa, kafin ya duba ya dubi Isah ya ce.
"Ina ji se ka rakani wani guri saboda wannan kiran da aka yi min nasan mafita".
Kafin Isah ya magantu, Musbahu ya kara wayar a kunnansa, yana cewa.
"Ya aka yi ne Malami?"
Ya dan saurara kadan don jin abinda ake fada masa, sannan ya ja fasali ya ce.
"Malami ni a ganina ka baiwa Allah zabi idan Zuwai din ce alkhairi. Allah Ya tabbatar, idan kuma
Dodoridon ne.... Don Allah tsaya.... Na daina.. Kana jina? Ba na son ka sanya kanka a cikin
taskun rayuwa, ka yi hakuri...."
Ya sake saurarawa na wani lokaci, sannan ya ce.
"Kai kasan yadda ta ke, mu kam ba ka taba nuna mana hotonta ba, don haka maganar musun
kyawunta ko kwarjininta bai taso ba.... Kuma yarinyar da aka tabbatar maka da MAYYA ce na
me zaka....... No! Wallahi na fi kowa son ka, son da nake maka din ne ma yasa nake nusar da
kai tarin kalubalen da kake neman fadawa.... Shi ke nan, zan shigo, baki muka yi ma ai da tuni
ka ganni.... To sai na shigo din".
Ya kashe wayar cike da alhini. Isah a tun soma wayar ya tsurawa Musbahu ido, mamakin
kalaman da suka tattauna yake, don haka Musbahu na kashe wayar ya ce.
"Me ya ke faruwa?"
Musbahu ya yarfar da kai, ya ce.
"Wallahi wani aboki na ne yake cikin rudani. Wata yarinya ce Allah Ya hada su da ita, yana
matukar sonta amma matsalar ne barkatai, ka ga dai na farko wani yayanta Yakub ya same shi
ya fada masa auren zumunci za a yi mata, amma shi ya kasa hakura da ita, kuma fa akwai wata
kanwar mahaifinsa da ta ce yarinyar mayya ce, shi kansa yana tunanin kasantuwarta jinsin
mutane, saboda kana kallonta zaka ga tsabar kyau kamar aljana.
Amma sonta ya makantar da shi kana ji yanzu har an kai fagen da yake tunanin tuburburewa
lallai sai ya aure ta".
Isah ya girgiza kai cikin tausayawa.ya ce.
"So ke nan! Kasan idan mutum ya na son abu hankalinsa ba zai taba kwanciya ba har sai ya ga
ya mallaki abin"..
Musbahu ya ce. "Ai ko dai, amma wani lokacin yana da kyau mutum ya dinga ragewa kansa
kaifin son abu idan har ya soma katari da matsalolin da abin zai saka shi".
A dai-dai lokacin suka karaso gidan.
Sun gama cin abinci, Isah da Musbahu suka mike zasu fita. Tsam! Shuhuda ita ma ta mike tana
cewa.
"Ina zaku?"
Musbahu ya yi murmushi, tukunna ya ce.
"Zamu je wani guri ne mu dawo".
Ta ce, "Ai kafarku kafata".
Nusaiba kanwar Musbahu wadda zasu iya zuwa kai daya da Shuhuda, ta ce.
"Yaya ai wannan cingam ce, don haka kada ka damu tunda dai ka dauke mai jan kunne ai ita
ma sai ka dauka".
Sukayi murmushi, Isah ya ce.
"Idan dai da ita za a fita, to ke ma sai ki taso mu tafi tare, don ba zamu tafi da mace daya tsikau
ba ace maza biyu mace daya".
Musbahu ya dubi Nusaiba ta gafen ido, ya ce.
"Dama abin da ta ke so ke nan, don tasan ni ba zan fita wani guri da ita ba, Amma kin ci arzikin
su".
Nusaiba tana dariya, ta ce. "Na dai ji, komai zaka ce ka fada".
Haj. Asmo dai ba ta tanka ba, haka suka tafi su hudu. Musbahu da Isah a gaban mota,
Shuhuda da Nusaiba a kujeraa baya.
Suna tafe suna hira irin ta abokan wasa(Dan mace da dan namiji).
Sun isa Kanada Quaters inda gidan Malami yake, Musbahu yayi hon maigadi ya bude kofa suka
shiga. Su duka hudun suka fito daga cikin motar, Musbahu a gaba, Isah a bayansa, sannan
Shuhuda da Nusaiba.
Yana zaune akan kujera cikin falonsa, sanye da wando (3quater) baki, sai karamar
riga(roundneck) ja. Kayan sun kara fito da kyawunsa, duk da dama shi din kyakkyawa ne, don
da wahalar gaske ka ga dan asalin Ruma mummuna, yawancinsu farare ne dogaye masu cikar
haiba. Sai da Musbahu ya shigo sosai sannan yayi tozali da wadanda ke bayan Musbahu.
Zumbur! Ya mike cikin RUDANI, ya ambaci sunanata.
"SHUHUDA!"
Ita ma cike da rudanin ta ambaci sunansa.
"UNCLE HAMZA!"
Musbahu, Isah gami da Nusaiba suka kama kallonsu cike da tsananin mamaki, ina suka san
juna?
.
Sadin Mama 'yar Anty na ce "WAI! Ni ma na rasa inda su ka san juna".
ausa Book stories
Kyan Alkawari........
.
MATAUL HAYAT
¤¤22¤¤
Saboda yadda suka ambaci sunan juna yanayi ne da ke bayyana sun dade da sanin juna kuma
sun dade basu hadu ba.
Shuhuda ta sake dubanshi, tace.
"Uncle Hamza dama zan sake ganinka? Dama kana raye a duniya ka manta da dalibarka, kuma
kanwar ka?"
Wannan batu da ya fito daga bakin Shuhuda ya baiwa su Musbahu amsar tambayarsu ta inda
suka san juna, kuma kalaman dai ne suka haskowa Musabahu wannan ita ce yarinyar da
Malami ya ke so, wadda kuma yake cikin tashin hankali a game da ita.
Shi kam ya san Shuhuda mutum ce tunda a tsatsonsu ta fito, mahaifiyarsa da mahaifinta uwa
daya uba daya, sannan ya sani duk cikin tsatsonsu babu MAYE, don haka wannan ma wata
hujja ce da zai kafawa Malami, sai dai kash! An makaro. Domin an sanar masa Isah zai auri
Shuhuda a yadda ma suka zo Katsina tare shaida ce ta cewa sun aminta su zamo ma aurata. Abinda ya ke bashi mamaki ma ta yadda akayi duk labarin da ya bashi game da yarinyar da ya
ke son suka faru akan kanwarsa Shuhuda.
Uncle Hamza ya kama mustuke idanu, gani yake kamar abinda ya saba faruwa da shi ne na
gizon da take masa, yau din ma gizon take masa, ba don haka ba, ta ya zai ganta da Musbahu
mutuminda ya kasance abokinsa tun kuruciya, kuma suka san juna sosai?
Isah ya kashe shirun da kuma al'ajabin ta hanyar zaunawa ragwab! Kan kujera yana cewa.
"Ya kamata ku zauna sannan a tattauna duk abinda ya dace".
Ba su bijirewa tayin sa ba, dukkansu suka zazzauna, amma al'ajabin ya ki boyuwa ko wanne ka
dubi fuskarsa ka san yana cike da rudanin yadda aka yi hakan ta faru.
Shiru na 'yan mintoci suka gilma kafin daga bisani Uncle Hamza ya dubi Musbahu ya ce.
"Wai Musbahu da gaske ko kuwa a mafarki ne ka zo min da Shuhuda don ka sani a rudani?
Idan da gaske ne, taya ka samo Shuhuda har ka kawo min ita a cikin gidana? Ka yi min
gamsasshen bayani da zai fitar da ni daga rudanin da nake ciki, don na gaza fahimtar a
matsayin da zan dora wannan rudadden al'amari".
Musbahu ya matsa kusa da Uncle Hamza, ya ruko hannunsa yace .
“Ina tunanin ruko hannunka da na yi ka ji dumin hannuna ya is ya tabbatar maka a ido biyu
muka bayyana gabanka. Sai dai kamar yadda ka samu kanka cikin rudani mu ma ka saka mu a
rudani.
Amsa day ace wadda zata warware tambayoyi masu yawa a lokaci guda. Shin mai ye alakarka
da Shuhuda. Itace yarinyar da kake so a makarantar da ka ke koyarwa can jihar kano? Ita ce
yarinyar da kake zrgin aljana ce, wadda kanwar mahaifinka ta kira MAYYA? Wadda kake
kokarin yi………..” Uncle Hamza ya daga masa hannu cikin sarewa, y ace.
“Tsiyar dan Nigeria kenan. Ya ce zai maka tambaya daya,amma saiya jero fiye da goma ba tare
day a bari ka amsa masa daya ba”.
Isah yace, “ina ganin manufar hakan warwarar lamari ne ko?”
Ba tare da Uncle Hamza ya bari Musbahu yayi Magana bay a ce,
“Shuhuda it ace dalibata wadda na koyar daita karatu a MARIAMA AJURI reshen jihar Kano.
Maganar ina zargin aljana ce bat a taso ba.domin ina da tabbacin mutum ce kamar kowa.
Haka maganar cewa ita mayya ce har tayi sanadiyyar mutuwar wasu bayin Allah ban yarda
ba,saboda kwararrun hujjoji na. Da ace Shuhuda zata zamto mayya ba zamu shafe shekaru
uku da ita ba tare da ta lashe kurwata ko wani a gabana ba.
Na yarda na amince dukkan wanda ya rasu ake zargin Shuhuda ce sanadi mutuwa ce ta Allah
da Annabi.
Wadda ko wane bawa yak e hawa siradinta da zarar lokacin amsa kira yayi.”
Bayan karshen bayaninsa, Shuhuda ta fito da idanu waje, ta ce. “Uncle n ice za ka aura?” ta
dafe kirji, ta ce. “Na shiga uku ni Shuhuda, aure kan aure? Aure da ci……” maganar ta makale
sakamakon tangadi da suka ga ta na yi alamar za ta fadi.
Nusaiba tayi saurin tallafar ta, idanta biyu tangaram babu alamar suma ko mutuwa a tare da ita,
amma tan a cikin yanayi na fitan hayyaci.
Su din ma hankalinsu ya tashi matuka. Sai dai Musbahu ya dauki maganarta akan labarin day a
sani na cewar Isah zai aure ta.
Su ma Isah da Nusaiba duk haka su ka fahimta, amma shi Uncle Hamza sam shi bai fahimta
ba, abin daya dauka shi ne, har yanzu Shuhuda na nan da SHIRMENTA!
Nusaiba ta soma girgizata tana cewa. “Shuhuda! Shuhud!!”
Ta bude ido fayat tana kallon Nusaiba, hakan ya tabbatar wa Nusaiba ba suma tayi ba, don
haka ta sauke ajiyan zuciya tare da jin wani sanyin dadi.
Musbahu ya dubi Uncle Hamza murya a sarke cikin tsananin sarewa y ace.
“Malam ina me baka hakuri ka taushi zuciyarka, ka sa lumana a dukkan komai, ka yi hakuri ka
karbi Zuwairiyyah a matsayin matar da Allah ya zaba maka ka rabu da soyayyar Shuhuda tunda
a halin yanzu an bada ita ga Yayanta!”
Cikin firgici Uncle Hamza yace.
“Ga wa aka bayar da ita? Yayanta Yakubu? Shi yasa dama y ace min auren zumunci za a mata
, ashe shi ne mugun?”
Musbahu ya nuna masa Isah yace.
“Ka ga wannan, shi ne aka bai wa ita, sunansa Isah, bata da wani yaya Yakub”. Uncle Hamza y
ace. “Ya za a ce min bat a da yaya Yakub, bayan shi ya fara burbusamin ba za a bani aurenta
ba, saboda yasan anyi min katobara?”
Isah da Musbahu suka dubi juna, su dai sun san duk cikin family din su ciki da bai basu da mai
suna Yakub, amma ya cije akan wai wani yayanta Yakub ya sanar da shi ba za a ba shi aurenta
ba.
Shuhuda t ace.
“Uncle Hamza da gaske kake za ka iya………”
Nusaiba ta yi saurin rufe mata baki, tana gudun kada ayi abin kunya, tun da ta fuskanci tan a
son ta aminta da soyayyar Uncle Hamza bayan ga Isah wanda ke sonta tun tana jinjira. GIDA
BE KOSHI BA. Ai bai kamata a bai wa DAWA ba. Kuma ko banza Isah shi ne wanda zai riketa
bias gaskiya ba tare da ta fuskanci tsangwamar dangin miji ba. Sabanin Uncle Hamza da tun
kafin ya aure ta an soma kiran Shuhuda da MAYYA. Duk mutumin da aka kira nasa maye ba
karamin bakin ciki zai samu kansa a ciki ba. Wannan babban cin zarafi ne. dan haka koda
Shuhuda na son Uncle Hamza kuma tana da burin auren sa, in shaa Allahu zasu ruguza abun,
ba zasu bari taje inda za a dinga jifarta da miyagun kalamai ba. Uncle Hamza ya ji wani takaici
ya tokare masa a makoshi, wannan wane salon rainin hankali ne su Musbahu suka zo masa da
shi? Sai ya dinga zargin mafarkin dai ne yake yi, hakika duk abinda ke faruwa a mafarki ne,
yanzunnan zai bude idanunsa ya ga komai ya koma a matsayin mafarki. Don karfin hali hard a
rufe idanunsa, ya bude cike da fatan hakan ya zamo a mafarki, amma hakan bai samu ba,
domin suna zaune a gabansa kamar yadda ya barsu a lokacin da zai rufe idanunsa. Wannan
al’amari da me yayi kama? Shuhudan da yasha mafarki ta zama matarsa har m da ‘ya’ya a
tsakaninsu it ace ake ikirarin an baiwa wani ita? Shin meye ribar wahalar sonta da yake sha?
Shike nan ya tashi a tutar babu? Ya watsawa Nusaiba harara cike da takaici, y ace. “Ki barta ta
fadi abunda zata fada mana”.
.
Ko me zata pada, oho! Sai ku canka!!!!!!!
Taku har kullum Sadiq Halima(Sadin Mama) 'yar Anty lol....
ausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤23¤¤
Isah ma ya harzuka, shi ma ya san Shuhuda niyyar maida masa zance ya kwana take, shi
dama tuni yasan ta taba yin soyayya, dama ya yi has ashen wani dalili ne ya sad a yayi mata
bayanin soyayyar ta kama yi masa kuka, har tana ikirarin ba zata iya soyayya ba.
To yau dai an yi walkiya ya ga komai tangaram! Babu inda za alayance masa, hakan ma ne ya
darsar da kishin nasa wanda yak e da shi na halitta, a harzuke ya dubi Musbahu y ace.
“Ya kamata ka tashi mu koma, don ko da ace ba ni zan auri Shuhuda ba, ba azan bari ta yi aure
a inda za a wulakanta tab a. Shuhuda amanita ce, b azan saurarawa duk wanda zaici zarafinta
ba”.
Uncle Hamza ya dubi Isah ido tsakar kai yana mamakin yadda Isan ya yake yana wannan cika
da batsewa, ya tuna lokacin yaje wurin Alh. Sada ya karbe shi hannu biyu, amma bai ba shi
dammar kadaicewa da Shuhuda ba har sai ta kamala sakandire dinta. Haka Yayanta Yakub ya
amince masa aurenta da farko. Sai yanzu da kaunarta t agama mamaye masa zuciya sannan
za a nemi a tarwatsa masa rayuwa? Ina! Ba zai lamunta ba. Ya dai fahimta Shuhuda na sonsa,
wanda dama hakan shi ne ribarsa, saboda haka zai nuna KWANJINSA don karbo soyayyarsa
da ke barazana kubucewa.
Muryarsa babu kyawun amon sauti y ace,
“Malam ka taka a sannu, don kana neman aurenta ba wai ka aureta ban e. Shuhuda tana da
dammar da zata zabe ni ko kai, don haka ka sanyawa ranka mun yi gamayya akan son abu
daya, kowa tasa ce zata fisshe shi, amma b azan juri cin zarafi ba, don ban ma sanka ba, ba
zaka ci mutunci nab a, ok?” Maganar ta batawa Isah rai, y ace,
“Duk abinda ya samu kuda shi ya jaw a kansa, idan kuma hankaka yana yin dan kansa ga fili ga
mai doki”.
Hankalin Musbahu ya tashi, saboda yadda ya ga kowanne yana muzurai tamkar zasu rukume
da kokawa, da sauri ya mike tsaye ya dubi Shuhuda. Yace,
“Ku tashi mu tafi”.
Ya maida kallonsa ga Uncle Hamza, y ace,
“Malami ka yi hakuri, mu bakinka ne kada kayi fushi dam u”.
Isah ya ja wani dogon tsaki y ace,
“Hkurin me za ka bashi? Kai baka san muna da hakki a gurinsa ba? Ko yanzu bari ganin yana
abokin ka idan yakama mu nemi hakkin mu, waLlahi sai mun nema sai muji ta yadda aka yi
Shuhuda ta zama mayya”.
To a nan Uncle Hamza bai iya tankawa ba, illa wani mugun kallo day a ke watsawa Isah, ji yake
a duniya babu wanda ya tsana sama da Isah, da ace za a bawa wani dammar kashe wani ba
tare da zunubi akan wanda yayi kisan ba, hakika da zai iya dauke Isah, saboda shigar hanci da
kudundunen daya soma yi masa.Gaba dayansu suka mike tsaye, Shuhuda idanunta taf da
hawaye, suka fice daga