Showing 39001 words to 42000 words out of 83144 words
wani abu da ya
faru, don haka ya fice daga dakin ya nufi dakinsa cike da al'ajabin yadda abin ya faru.
Washegari da yammaci misalin karfe biyar, rana ta yi sanyi, Isah yana kokarin bude murfin
motarsa don shiga zai je cikin gari wajen abokinsa da suka yi za su hadu. Da sauri shuhuda ta
karaso gurinsa tana cewa. Yah Isah! Don Allah tsaya!! Ya dakata da bude murfin motar tare da
juyawa yana kallonta. Ta tsaya a gabansa tana sanye da doguwar riga ta atamfa mai gajeran
hannu, ta daura dan karamin bakin gyale a kanta, kafarta da silifas. Ta sunkuyar da kanta kasa
ta kasa magana. Yace: Ya aka yi ne shuhuda? Muryarta a raunane tace: Yah don Allah ka yi
hakuri na tsayar da kai ko? Ya girgiza kai. Kada ki damu, me ye matsalarki? Ta sake rusunar da
kai kasa. Ni ma ban san abin da ya sa na tsayar da kai ba. Mamaki ya bayyana a fuskarsa,
yace: Aha! Ban gane ba kui san abin da ya sa kika tsayar da ni ba?
ada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤19¤¤
.
Tace: eh yaya, shin hakuri zan baka, ko kuwa albishir zan yi maka? Ya yi murmushi, ya jingina
da mota yace: Duka. Sai ki fada ina saurarenki. Tace: Ka yi hakuri akan kin kar6ar soyayyarka
da na yi, hakan ya faru ne bisa tunanin da na yi kamar ban cancanta da zamowa abokiyar
rayuwarka ba a matsayinka na wayayyen mutum, wanda ya rayu a cikin masu jajeyen kunne, ni
kuma BAGIDAJIYA, bakar fata, wadda ta rayu cikin 'yan uwanta bakaken fata! Sai na ga yin
soyayyar akwai matsala.
Tana karashe fadar hakan ta yi shiru, shi kuwa murmushin ya sake saki, sannan yace: Sai kuma
aka yi rashin sa'a duk da kasancewar na rayu a cikin masu jajayen kunne, sai Allah bai sa na ga
wata daga cikinsu da zuciyata ta aminta ta zamo uwar tuwona ba kamar ke.
Hasalima tunda nake mace daya ce na ta6a gani, wadda zan ce ta burge ni. Wato SHUHUDA
IBN KHADDAB, wadda na fada miki mun hadu da ita a birnin misra, ita ma burgeni ne kawai ta
yi ba wai ina son ta zamo mata a gare ni ba.
Saboda haka ke din dai ke ce wadda asalin sona yake a tare da ita, wannan tsinkayen naki
raunanna ne, bai isa ya zamo jigon da zai hana soyayyarmu ba.
Ya yi shiry yana sauraren ya ji daga gare ta, amma ba ta tanka ba, ya ci gaba da cewa: Wani
albishir ne zaki yi min?
Ta dan dago kai ta dube shi, suka hada idanu ta mayar da idanunta ta rusunar kasa, murya a
sanyaye tace:
Na amince da soy.......
Maganar ta makale a kasan makoshinta, yayin da farin ciki ya cika masa zuciya, ya daga hannu
sama yana cewa:
Alhamdulillah, godiya ta tabbata ga Allah ubangijin Talikai, masani akan dukkan SIRRIN 6OYE
da na BAYYANE.
Ya sake dubanta, yace:
Idan na ce na fi kowa farin ciki a wannan rana ban yi laifi ba, saboda na tabbata duk wanda ya
dace da mace irinki, lallai ya yi dace da uwar 'ya'ya ta gari, irin wadda ake son samu, wadda
aka yi hasashen idan mutum ya same ta lallai zai yi katari da madauwamin farin ciki.
lokaci daya fara'ar dake fuskarshi ta raunana, sakamakon abin da ya faru SHERAN JIYA, da
kuma JIYA na ganin cikin shuhuda yana juyawa kamar kwallo. Ya so ya yi mata magana akan
haka, amma suna hada idanu da ita sai ya ji nauyinta ya kama shi, tabbas wannan ba muhallin
da zai furta abin ba ne, domin gudun kada ta zarge shi akan yana son fakaitar idanu ya 6ata
mata rayuwa......
Shuhuda ta katse shirun da cewa: Yauwa, Yar Isah, wai don Allah ya kamannun shuhudan da
kuka hadu da ita yake, ina ganin kamar na ta6a ganinta.
Ya girgiza kai, yace: Bana tunani, tunda ta ce ba ta ta6a zuwa Najeriya ba. Ko ke kin ta6a zuwa
Misra bayan tafiyata?
Tace: A'a amma ba ta ta6a zuwa Najeriya ba ya aka yi ta sanni? Yace: Eh, ni ma abin da nake
mamaki kenan, tace: wai bincikenta ne ta sanki, wata 'yar fara doguwa, irin matan Misran nan
dai.
Shuhuda ta yi dariya, tace: Kai Yaya, su matan Misra har kala daban gare su? Yace: Sosai ma
kuwa, domin kina ganinsu kin san su 'yan asalin kasar Misran ne.
Ta jinjina kai, tace: Ni kam zan so na ga wannan shuhuda mai bincike haka. Yace: Nima zan so
hakan.......
Ya kawar da maganar da cewa: Jibi ne tafiyarmu katsina ko? Tace: Haka ne. Yace: Ya kamata
ki shirya gobe dai mu yo tsaraba ko? Ta narke idanu cikin shagwa6a, tace: Kai Yah Isah ni fa
bana son zuwa super market. Yace: Ko akwai dalili?
A'a, haka kawai bana sha'awar zuwa super market. Cewarta.
Yanzu ya kamata ki koyawa kanki sha'awar zuwa tunda ra'ayina ne. Shi ma ya fada yana
kallonta. Sai tayi shiru ba ta ce komai ba. Yace: Yanzu ma ba don mun yi alkawari da Salman
Alparis zamu hadu ba, ai da yau zamu je, amma yau da gobe duk kayan Allah ne.
Tace: Haka ne, bara na koma tunda fita zaka yi......
Ya katse ta, idn babu takura mu je ki raka ni mana? Tace: Anya? Akwai wani nazari da na ke yi.
Yace: Shike nan, sai na dawo. Ai ba jimawa zan yi ba.
Tace: To Allah ya dawo da kai lafiya.
Ya amsa, Amin.
Yana kokarin shiga mota, ita kuma ta juya ta koma cikin gida. A ranar da dare hira suka sha mai
tarin yawa, da amfani ga Isah, domin a cikin hirar ne ya kara tabbatarwa kansa lallai ya yi sa'ar
samun mata mai kaifin hankali da basira. Wadda ta san makamar rayuwa, ta kuma san yadda
zata farantawa wanda ke tare da shi rai. Saboda dik hirar ta su ta ta'allaka ne akan yanayin da ma'aurata suke kasancewa idan sun sami
matsala. Ya dinga dangantawa da su. Misali: Ace ya aureta matsala ta shigo ta karin aure ba
tare da ya sanar mata ba, sai ranar daurin auren ko kuma ana gobe daurin auren.
To idan irin wannan matsalar ta shigo ta ya ya zata magance ta?
Murmushi ta yi, tace: Yah Isah ai ita soyayya ta gaskiya wadda ta zamo jigon aure mutumtata
ake yi, kuma a yi uzuri tsakanin juna, tare da kar6ar uzuri. Zata iya yiwuwa saboda tsananin
kaunar da kake yi min ne yasa ka kasa sanar da ni zaka yi nin kishiya. Kasan a rayuwar aure
nagartacciyar kauna da fahimtar juna ake nema, muddin aka samu haka to kuwa dole ne a
samu uzuri.
Kuma duk macen da ka gani ko jin mijinta zai kara aure ta tayar da kayar baya, da tasa rayuwar
auren na su ta samu tangarda. To ka tuhumi asalin tushen kafuwar tubalin auren. Mai yiwuwa
ne dama can ba kaunar mijin ta ke ba, sha'awa ko burgewa ce ta sa ta aure shi. Ko kuma ta
kasance daga cikin jinsin mata wadanda suka dauki KISHI dabi'a mai kyau a gare su. Wannan dogon bayanin da ta yi masa ya sama masa nutsuwa da gamsuwar cewar, lallai ya yi
dace da samun mace ta gari.
Inna yaduwada yake babbar mace ce, tuni ta fassara maganganun nasa, ta yi dariya tace: Isah
kenan, ga dukkan alamu kana daga cikin mazan da ke sha'awar tara mata fiye da daya.....
Ya yi saurin katse ta da cewa: Ko daya Inna. Ai samun sahihiyar mace guda daya ya fi ka tara
mata hudu da suke tayar maka da hankali. Ni kam a ra'ayina mace daya nake son aure,
musamman don na samu zaman lafiya tsakanina da iyalina.
Inna yaduwa ta sake murmusawa tace: Sai aka ce maka idan mutum ya auri mace fiye da daya
ba zai samu kwanciyar hankali ba?
Yace: A'a, amma ni dai ra'ayina mace daya ne, saboda nasan idan na auri biyu daya ta fi
kayutata min, sai na nuna rashin adalci a tsakaninsu.
Shuhuda ta shiga cikin zancen tace: Ni kuwa a nawa ra'ayin ina son zama da kishiya, domin
'yar uwa ce, akawai matan da suke mantawa da girman amfanin zama da kishiya, suka dauki
kishiya a marsayin abokiyar gabarsu.
Wasu sun iya KISHIN BIRNI su 6oye kishinsu a zahiri, sai dai karfar baka, ko kuma KISAN
MUMMUKE, yayin da wasu kishin na su ke gaza 6oyuwa zaka ga ma wasu har buge-buge da
yage-yage suke yi a junansu.
An sani dukkan mace an halicce ta da kishi, to amma babu mafi dacewa a yi kishin na nuna
kyautatawa ga miji, a ririta shi, a mantar da shi damuwa ba wai a saka masa wata damuwar ba.
Tun da ta fara wannan bayanin ya ke kallonta, mamakin yadda tasan wannan mas'ala yake, a
matsayinta na karamar yarinya wadda ba ta ta6a yin aure ba bare zama da kishiya, kuma ta
rayu a gidan da babu kishiya.
Hakan ya tabbar masa ko wane mutum da irin NASIBINSA, ita kam ta samu nasibi mai kyau,
sai fatan Allah ya sa ta dore da wannan halayya nata.
Inna yaduwa tace: Ke duk ya aka yi kika san haka?
Shuhuda ta yi dariya, tace: Haba Inna, kada ki ba ni kunya mana? A tunanina kinsan mace tana
da sani game da lamuran kishi ko da kuwa ba ta shiga fagen ba, sai dai wata idan tana da
raunin tunani ba zata gane hakan ba har sai ta shiga fagen. Ni kuwa na sani, kuma ina da
ALAKAR da zan sani. Inna yaduwa tace: Saboda kin zauna da kishiya ko? Shuhuda tace: Ko ban zauna da ita ba, zan
iya sani, saboda ALAKAR na sanin.
Inna yaduwa tace: Lallai kam tunda ubanki yana da mata biyu(Alh Sada take nufi) dole ki sani.
Sai duk suka yi shiru saboda girman maganar.
Inna yaduwa tace: Ja'iran kawai, ni ka tashi ka bamu wuri haka nan zamu kwanta.
Shuhuda dai ce, idan ba ka manta ba tun kafin ka je kasar masu jajayen kunne na sanar da kai
ba zan ba ka aurenta ba.
Shuhuda ta yi tsagal tace: Haba dai! Ai ko ba ki ba shi aurena ba, ni sai na aurasa masa kaina.
Inna yaduwa ta daga hannu zata kaiwa shuhuda duka, sai ta tuna da abin da ya ta6a faruwa
lokacin da ta yi yunkurin dukan nata, don haka ta yi saurin sauke hannunta, tana cewa:
Rufe min baki rasa kunya 6eran tanka. Isah yace: Yauwa amaryas, fada mata ta ji da kyau. An
fada mata har yanzu kambun nata yana tasiri? Ya karashe maganar yana kokarin mikewa.
Inna yaduwa ta aika masa sakon harara, tace: Na ce ka wuce ina so mu kwanta. Yace: Ba sai
kin kore ni ba, ni ma baccin nake ji. Ya soma tofa musu addu'o'i yace: Mu kwana lafiya. Bai jira
amsarsu ba ya ficce.
A ranar bai yi mummunan mafarkinsa ba, tunda ya kwanta ko motsawa bai yi ba sai gabanin
sallar asuba.
Lallai addu'a makami ce ga dan Adam, dubi dai kwanaki biyu matsalolin da ya samu akan
rashin addu'a, amma yau da yake ya yi addu'ar sai ga shi da yin bacci cikin nishadi.
Koda ya gama sallar asuba dakinsu ya nufa, sai dai ya tarar da shuhuda zaune akan sallaya
tana Azkar din safe, yayin da Inna yaduwa ta ke kujiba-kujibar dama koko, don ita Allah ya yi ta
ba mai ganda ba ce, don haka ma ko 'yar aiki ta ki aminta a ajiye mata.
Zaunawa yayi a gefen gadon ya na jiran ta kammala lazimin su gaisa, amma har tsayin lokaci
ba ta dakata ba, shi kuma yana son ta datse su gaisa ya koma daki don yin sababben baccinsa,
hakan ta gaza samuwa.
Da ya ga ba ta da niyyar tsayar da lazimin nata su gaisa, sai ya mike tsaye ya fice daga dakin.
Yana fitowa falo suka yi kici6us da Inna yaduwa ta fito daga kicin. Ya rusunar da kai yana
kokarin shigewa sashensa, Inna yaduwa ta ambaci sunansa, ya juyo yana kallonta. Ita kuma ta
zauna akan kujera fuskarta a dan daure.
Ganin ta zauna ya tabbatar magana ta ke son yi da shi, sai ya dawo falon ya zauna ya yi shiru
yana sauraren abin da zata fada.
Ta sauke gwauron numfashi, sannan ta dora da cewa: Isah magana zamu yi da kai ta fahimta,
kuma shawara da gargadi ne a gare ka. Ka ga wannan yarinyar shuhuda da kake gani ko, bana
son abin da zai ta6a ranta ko sakata a damuwa.
Abin da yasa ka ji na fadi wannan maganar wani abu ne yake yi min ciwo a rai, na rasa wanda
zan kama na sanar da shi abin.
Yanayinta ya sauya gaba daya, ta koma kalar tausayi, hakan ya sa shi ma Isah yanayinsa ya
sauya, ya dai kasa kunnuwa yana saurarenta.
Zata ci gaba da magana ke nan, shuhuda ta shigo falon, Inna yaduwa ra dago kai suka hada
idanu, sai ta ga kamar launin idanuwanta sun sauya daga fari da baki zuwa wata WALKIYA, don
haka da sauri ta rusunar da kwayar idanunta kasa.
Isah kuwa da ya dago bai ga komai ba, illa ya ga shuhuda tsaye a bakin kofa sanye da hijabin
sallarta. Shuhuda tace:
Yaya don Allah kayi hakuri, wallahi idan ina azkar ba na son tsinkewa saboda idan na koma ba
zan iya yin adadin da nake yi a kowacce rana ba.
Yana murmushi yace mata. Kada ki damu. Tana kokarin zama, tace: Hala wannan tsohuwar ta
zaunar da kai zata yi maka shirme ko?. Babu wanda ya tanka mata. Bayan ta zauna tace: Yaya
barka da kwana. Yace: Min tashi lafiya?.
Tace: Kalau, don na fi wannan tsohuwar, tunda na lura yau tunda ta tashi a suku-suku ta ke, ko
kuwa neman rigima ta ke? Ba shakka don mun ce ba zamu je katsina da ita ba ne ta ke neman
ayi rigima da ita.
Inna yaduwa ta yi murmushin karfin hali, tace: Sha kuruminki idan dai ni ce ko da kunce ba zaku
je da ni ba, ba zan damu ba. Shuhuda tace: Ke dai ki ce kin yi abin nan da Hausawa sukan ce,
Wai abin da baka samu gama shi da baka so, ko kuwa yaya? Ya girgiza kai yace: Kwarai kuwa.
Inna yaduwa ta mike tsaye, tace: Isah bai so tashin Inna yaduwa ba, ya so ta sanar da shi abin
da yake damunta har ya ji tausayin 'yar tsohuwar ya kama shi. Wata kila ba ta jin dadin zama da
shuhuda.
shi kam a yadda yake ganin shuhuda ba ya tunanin tana da wani mugun hali da wanda yake
zaune da ita zai koka. Domin ta kasance kamilar budurwa, da ace irin 'yan matan yanzu ne
yadda ta ke zaune da kakarta, da kullum sai ta sakata kuka, amma sam shuhuda ba ta da
wannan hali, ba ta son ma yin irin wannan haramtaccen wasan na JIKA da KAK , don da yawa
wasu wasanni da ake yi jika da kaka ya haramta. Wasa na rashin ganin girma da nuna kuruciya
a zahiran.
Bayan tafiyar Inna yaduwa shuhuda ta dubi Isah tace: Yauwa Yah Isah, wai kana da Umdatul
Ahkam? Yace: Me zaki yi da shi? Tace: Karatu. Yace: A'a ba ni da shi, amma anjima idan mun
fita siyayyar tsaraba sai mu nemo ko?
Tace: Allah ya kaimu. Yace: Amin, amma kafin nan bari idan na shiga daki zan fito miki da wani
littafin addini, don na lura kina son karance-karance.
Tace: Sosai ma kuwa, don littafan da na karanta na addini suna da yawa, ka ga kamar littafin
Fikhul Wadii na ji dadinsa sosai, yadda aka yi bayani game da yadda al'adar mata ta ke zuwa,
da kuma yadda take daukewa, har ma idan ta zowa mutum da matsala.
Kasan mafi akasarin mata ba su san jinin haila ba, ba su san rabe-rabensa ba, da kuma yadda
idan sun dauki lokaci ba su yi ba, ba su san me ya haddasa hakan ba, su ba ruwansu kawai
sun san cewa, idan wata ya zo karshe suna fitar da jini, babu maganar akwai matsala ko akasin
ta idan ba gani sukayi sun kwanta ba...... Isah ya katse ta da cewa: Me ye matsalar matan? Sai ta yi murmushi tace: Au, na fa manta kai
namiji ne ko?. Ta mike tsaye cike da jin kunya ta koma daki. Bai yi yunkurin tsayar da ita ba, ya
yi mata uzuri, sai ya tashi ya koma dakinsa, don dama bacci ne ke cinsa.
Da yammacin ranar suka je Sahad store da Alh. Shehu super market suka yo siyayyar
abubuwan da zasu yi tsaraba da shi, sannan suka wuce kasuwar kurmi shuhuda ta za6o littafan
addini, daga bisani suka dawo Gida.
Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)
¤¤20¤¤
Duk yadda ya so kadaicewa da Inna yaduwa don jin damuwarta hakan bai yiyuwa ba, saboda
duk lokacin da ya shigo falon sai ya tarar da ita tare da shuhuda.
Washegari ma tun da safe ya nufo falon bai ga Inna yaduwa ba, ya leka kicin wai ko ya tarar da
ita kamar yadda tayi jiya, amma sai ya tarar da shuhuda.
Bai wani jata da labari ba, saboda yana ganin dama ce ta samu, kawai ya je daki ya tarar da
Inna yaduwa ya ji matsalarta tunda shuhuda na kicin.
Yana zuwa dakin ya tarar da ita kwance akan gado, idanunta a lumshe, yace: Matar bacci kike?
Sai ta bude ido ta kalle shi tace: A'a jikina ne yake ciwo. Yace: Ayya, Allah kawo sauki. Tace:
Amin, ai da saukin, kawai surutu ne ban so, ga shi ina so na dama koko.
Yace; Ai ga shuhuda can na yi. Sai suka yi shiru na wani lokaci, kafin daga bisani ya katse
shirun da cewa: Jiya muna magana ba mu karasa ba shuhuda ta shigo?. Tace: Eh wallahi, ga
shi kuma na manta abin da nake son sanar da kai. Ya dube ta cikin tuhuma, sai ta jinjina kai