Showing 51001 words to 54000 words out of 83144 words

Chapter 18 - MATA'UL HAYAT BY SAKINAT USMAN-1.pdf

02 Aug 2025

11090

Yaduwa fuskarta a daure ta ce. "Yo mutum ya zo nemana sai
ace masa bani nan, bayn kuma ina cikin gidan don kawai a raba hanta da jiji?" Inna Yaduwa ta
ce "Amma tunda an bayar da ke, maiye amfanin tsayawa da wani?" Shuhuda ta ce, Ni fa ba zan
auri mutuminda yake da tsattsauran ra ayi ba, mutuminda komai sai ya tuhumi mutum". Isah ya
langwabe kai, yasan har yanzu fushin ne bai sauka ba. Inna Yaduwa ta ce, "Ai shi zaman tare
haka ya gada, dole sai anyi hakuri da juna, kuma ina amfanin mace ta auri mijin da baya
tuhumarta akn abubuwan da suka shafe ta? Idan ba ta haka ba ta ya zata samu ingatacciyar
rayuwa?" Bata tsaya sake tofawa ba, ta sa kai ta fice abinta. Inna yaduwa tace da Isah. "Wai
me yake faruwa ne haka?" Shiru Isah ya yi gabadaya wutarsa ta dauke, kada fa abin ya zama
da gaske, Shuhuda ta daina sonsa,tana son mutuminda bai dace da rayuwarta ba, mutuminda
zai kai ta cikin tsatson da za a dinga aibatata. Tsayin lokaci shi da Inna Yaduwa suna yanayin
shiru, daga bisani kamar wanda aka tsikara da tsinken allura, firit ya mike tsaye ya nufi kofa,
Inna Yaduwa ta ce. "Ina zaka je?" Ba tare da ya juyo da dubansa gareta ba ya ce. "Ina zuwa".
Ya fice.
Tun daga nesa ya hango Shuhuda da Uncle Hamza sai faman dariya suke alamu da ke nuni
suna jin dadin hirar da suke. Wani abu mai kaifi (kishi) ya soki zuciyarsa, ya tsaya kamar ba zai
karasa ba, sai kuma ya ci gaba da takawa cikin kasaitaccen takunsa wanda duk wanda zai yi
tozali da shi zai tabbatar nagartaccen namiji ne, domin Isah namiji ne mai kyakkawar shiga
game da cikar haiba.
Cikin takunnasa ya isa inda suke zaune akan fararen kujerun roba, a gabansu akwai yalwar
korayen ciyayi (grass carpet) don haka gurin sai tashin kamshin ciyayin yake. Lokacin da ya isa,
su duka biyun sai suka gumtse fuska, dariyrsu ta dauke a lokaci daya. Isah ya mikawa Uncle
Hamza hannu da nufin suyi musabaha a matsayinsu na Musulmai su duka. Uncle haamza bai
tsallake tayin ladar da aka masa ba, ya mika masa hannu suka yi musabiha, daga bisani Isah
ya dora da cewa.
"Ban so ka kasance cikin mutane masu taurin zuciya ba, ta hanyar yin nema cikin nema, wanda
ko a musulunci ya haramta". Uncle Hamza ya ce kamar yadda ban so kai ma ka kasance cikin
mutane marasa yiwa soyayyar gaskiya uzuri ba" Isah ya ce. "Ai babu uzuri ga abin da aka san
haramtacce ne". Uncle Haza ya dan yi malalacin murmushi, ya dora da cewa. "Idan haka ne sai
na ce ni aka yiwa hawan kawara, aka naushe ni kuma ake son a hanani zubar hawaye". Cikin
takaicin maganarsa Isah ya ce, "ita ZUCIYA MUGUN NAMA ce, idan mutum bai dace da zuciya
ta kwarai ba sai ta hada masa ZAFI BIYU, na radadin zuciya da kuma na kaskanci, don haka

sai a yi ta ganin mutum yana abubuwa wanda basu dace ba, amma shi da yake bai dace da
zuciyar ta kwarai ba sai ya ga duk abin da yayi dai-dai din ne a gareshi".
Maganganun Isah masu shiga zuciya ne, da kuma zafafata, to amma sai Uncle Hamza ya bude
baki da nufin mayar masa da martani cikin sanyayan kalamai, kafin yiwuwar hakan Shuhuda ta
riga shi da cewa.
"Yah Isah amatsayinka na yayana bai kamata kayi min wannan rashin adalcin ba, ina hira da
wanda na ke so ka zo kana jifarsa da gugar zana. Ai ai ita mace uzuri ake yi mata, musamman
da ya kasance na fada maka, ba zan iya auren mijin da zai jefa rayuwata cikin takura ba. Dona
haka ka saurara mana, ka daina shigar min rayuwa".Gaba daya jijiyoyin sadar da magana da
suke aiki a jikin Isah suka tsinke saboda jin maganganun da Shuhuda ke amayarwa a gare shi.
Ba shi da abin da zai iya fada mata, saboda haka ya juya ya koma cikin gida cike da kuncin
zuciya. Bayan tafiyar Isah daga gurin, Uncle Hamza ya dago kai ya dubi Shuhuda, ya ce.
"Yayan nan naki yana da tsananin kishi, wanda kuwa bai dace da shi ba, domin mace idan tana
budurwa, ma'ana tana a gidansu ba ta yi aure ba, kakarin da zaka yi ka kimtsa soyayyarka gare
ta, wannan shine babban kishi mai amfani. Idan ka aure ta kuma sai ka nuna kishinka ta hanya
wadatata da dul abin da yake hakki gare ka. Ka yarda da ita don gudun zargi kada ka ganta da
dan uwanta ka zari wani abu".
.
TOH PA MAZAN WANNAN GROUP! Da patan kun ilmantu!!!
.
Shuhuda ta jinjina kai, hirar da ba a karasheta cikin dadin rai ba ke nan. Suka yi sallama ta
koma cikin gida. Inna Yaduwa ta watsa mata wani mugun kallo, yayin da Isah yake zaune kansa
a sunkuye, gabaki daya ba shi da sukuni . Shuhuda ta ce. "Kinga ni ban san harara ba sai
kwayar ido ta fado. Haka kawai a takurawa rayuwata, in bacin tausayi da kuma shakuwa da tuni
ba a kaddamar da mutum ba, amma sai a takurawa mutum a hana shi rawa gaban hantsi?
Wallahi ba zata sabu ba bindiga a ruwa, ba zan juri wannan matsin ba, don ba da ni za a yi
gamin gambizar nan ba". Inna Yaduwa bata tanka mata ba, Shuhudan ta shige daki. Isah ya
mike tsaye ya dawo kusa da Inna Yaduwa, murya a raunane ya ce. "Inna ki taimaki rayuwata,
wallahi Shuhuda ita ce zabina, matsawar na rasata hakika na rasa wani bangare na daga farin
cikina. Ina son Shuhuda Inna, itace burin rayuwata, ki taimake ni kada na rasa ta!" Yanayinsa
gaba daya ya sauya zuwa launin tausayi kallo daya zaka yi masa ka fahimci tsananin son da
yake yiwa Shuhuda, wanda dama shi so na gaskiya ba ya buya, a cikin farin ciki ko akasin haka
kake. So na gaskiya ba zai taba boyuwa ba.
.
Hmm, Isah da badan sunan ka ba, sai ince Sadin Mama zata yi da kai, amman ba laipi idan
zaka canza zuwa sunan larabawa.... Lol
.
Isah kam yana son Shuhuda har cikin kalbinsa, ta zame masa NURUL KALBI, ta zame masa
tauraruwa mai haske da kyalli, ta zame masa mahadin rayuwarsa idan kuwa ya rasa soyayyarta
tabbas ba karamin rashi ba ne a gareshii. Cikin tausayawa inna Yaduwa ta ce. "Isah shawara
zann baka ka yi hakuri da Shuhuda ka nemi wata". Tar! Tar!! Kwalla suka suka zubo masa, cikin
sanyin jiki yana girgiza kai ya ce. "Bazan iya ba Inna, ba zan iya rabuwa da Shuhuda ba idan
kuwa har zan iya rabuwa da ita, to hakika ba ta a doron kasa ne". Tausayinsa ya kara narkar wa

Inna Yaduwa zuciya, ta ce. "Ba ka lura da abin da na ke so ka lura da shi game da yarinyar nan
ba. Akwai abubuwa da yawa da suke faruwa wanda yasa nake tababa.........."
"Eh, ai ni mahaukaciya ce! Ba sai kin maimaita ba!" Muryar Shuhuda suka tsinkayo daga bakin
kofa. Su duka biyun suka mayar da kallonsu gareta, fuskarta a daure babu ko digon fara'a.
Sannan idanunta jajur sai ka ce jan gauta, babu wanda ya tanka mata, ta ci gaba da cewa.
"Wallahi kuyi hankali da ni a cikin gidannan, ina nuna muku ni mai tausayinku ce, amma kun
kasa fahimta. Duk ranar da na cire imani a kanku zaku sha mamaki.." Kausasan kalaman nata
sunyiwa Isah tsauri, ya kasa jurewa ya mike tsaye tare da daka mata tsawa. "Don ubanki waye
sa'anki a cikinmu da har zaki zo kina fada mana wadannan kalaman, ko don kinga ana kyaleki
shi ne za ki juya mutane? To bari ki ji don na ce ina sonki ba yana nufin bani iya hukunta ki ba
ne".
.
Su Isah MAZA!!!
.
Dariya ta fashe da ita.
"Allah ko? To ga fili ga mai doki, idan har ka isa ka sanya hannu ka buge ni. Idan kuwa ka kasa
baka haifu ba, ku....."
Ya yunkura sai kai mata duka, inna Yaduwa ta yi saurin tare shi. "Kada ka dake ta, kyale ta da
halinta". Ta juya ga Shuhuda, ta ce. "Ke kam ba ki ji dadin halinki ba, ace ba ki ganin mutumcin
kowa a idanunki, rashin kunya da fitsara su kika sa agaba?"
Kai tsaye Shuhuda ta ce. "Gadon gidanmu ne!" Inna Yaduwa ta ce. "Karya kike wallahi, duk
gidan nan babu fitsararre, amma ke....." "To ya fa isa, kuma fitsara da rashin kunya yanzu na
soma". Isah ransa ya kuma baci ga shi Inna Yaduwa ta hana shi dukan Shuhuda, sai kawai ya
ficce daga falon. .
Da kuwa Isah anga sarkewar hannu. (Sadin Mama).
.
Shuhuda ta ce.
“Idan hark u masu zuciya ne kada wanda ya kara kulani a cikin gidan nan, kowa yayi abin da
yake so ban hana ba”. Inna Yaduwa t ace da ita. “Ai mu ba kafurai ban e, bare mu zamo masu
zuciyar kafurawa. Ke dai da kika ji zaki iya yin gaba dam u sai ki yi. Sai dai ina me tunatar da ke
cewa, gaba dad an uwanka Musulmi haramun ce, bare kuma ga wanda suka zamo tsatsonki”. Shuhuda ta murguda baki t ace, “Sai ki yi, ni dai na fi karfin dauk wani mai hankali”. Tana
karashe maganarta ta sanya kai cikin daki. Inna Yaduwa ta bi tad a kallo tana girgiza kai, halin
Shuhuda yana bat a mamaki, da daure mata kai, wani lokaci ta fassarata zuwa mara hankali,
wani lokaci kam gaba daya ta fi dangantata da aljana ba mutum ba. Wannan ke nan! BABI NA GOMA SHA UKU
MURDADDIYA
Isah ya tafi Ibadan cike da takaicin Shuhuda, a lokacin da zai tafi ma ko fitowa daga daki bata yi
ba bare suyi sallama, shi ma bai damu da hakan ba don t agama kaishi bango, kiris ya rage ya
fashe don haushi da takaicinta.
Mamaki yake wai yarinya karama kamar Shuhuda ta iya wannan fitsara da cin fuska. Ba don
Inna Yaduwa ta yi masa togaciya ba, da sai ya nada mata shegen duka inyaso gobe ma ta

kiyaye harshenta. Shi yanzu baa bin da ta yi masa na juyawa soyayyarsa baya yafi damunsa
ba, a’a mummunana halin da ta tsira.
Ya sauka Ibadan cikin rashin walwalar zuciya, dama komai ya kammala na muhallinsa, da
makullan ofis dinsa, don haka kai tsaye gidan da aka mallaka masa ya nufa, a unguwar
Shasha, a layinda yak e gidaje ne jeer masu kyau da kayatarwa, komai na layin a shirye yake
gwanin ban sha awa, haka cikin gidajen ma an saka duk wani abu na jin dadin rayuwa. Idan da akwai abin da zaka nema ka rasa a cikin gidajen, to ba zai wuce na abin da zaka ci ba,
wanna hakkin duk mazaunan gidajen ne, kasancewa gidaje ne da masa’antu suka gina, kowace
masa’anta idan ta dauki ma’aikaci sai tab a shi gida daya inda zai zauna.
To shi Isah tun kafin zuwansa ma’aikatar da ta dauke shi aiki tuni t agama tanadar masa komai
kan abinci, musamman da suka samu tabbacin a kasar da yayi karatu sun san cimar da ta dace
da shi. Yana shiga ciki ya tarar da ma’aikatan da aka sanar da shi suna jiransa, ma’ana
wadanda zasu yi masa hidima, wanki, dafuwar abinci da sauransu. Duk da basu sanshi a sarari ba, sai taswirarasa da suka sani a hoto, amma suna ganinsa suka
gane shi. Gaba daya suka mike tsaye cike da girmamawa, gaisuwa da kawo kayan sha duk
suka yi masa, sannan aka kai masa rowan wanka bandaki. Ya fito ya shiga bedroom ya tarar da
duk abin da yake bukata na jin dadin rayuwarsa. Sai dai kash! Baya da jin dadin, hasalima jin
kansa yake kamar ba shi ba.
Washe gari ya soma fita gurin aiki, ofis kam yayi kyau, ya kuma matukar dacewa da shi. Kwana
biyu yana cikin ayyuka na ofis, ranar na uku da daddare misalign karfe takwas na dare yana
tsaye a barandar gidansa, sanye da pyjamas jajaye, don yana gama sallar Isha’I yayi shirin
bacci ba don yana da tabbacin baccin zai yi ba, kawai yayi hakan ne don ya san babu inda zai
kuma zuwa musamman a matsayinsa na bako, bai da wani wanda ya saba da shi. Kamar an ce
ya daga kansa, sai kuwa idanunsa suka hango masa kyakkyawar fuskar dab a zai manta da ita
ba, ta fito daga mota har tana kokarin bude wani gida daga cikin jerin gidajen da ke layin.
Daram! Gabansa ya yanke ya fadi.
“SHUHUDA IBN KHADDAB!”
Ya fada a sarari cike da tsananin mamakin yadda aka fara ya ganta a nan. Lallai wannan
yarinya shu’umar gasket ce, ba don haka bay a ganta a birnin Misra, ta zo masa a bakuwar
fuskar da ta san kanwarsa ba tare da ita kanwar tasa ta sanshi ba.
Ya ganta a Katsina ta nuna bata taba saninsa ba, yanzu kuma aiki ya kawo shi Ibadan ta biyo
shi, dama ‘yar Ibadan ce? Wani burin e gare ta game da shi? Abin da bai sani ba kenan, amma
mamaki kam ya nunka hauhawa a zuciyarsa.
Kafin yayi wani yunkuri hart a shige cikin gidan, zuciyarsa ta ayyana masa yabi ta zuwa cikin
gidan don jera mata gwanon tambayoyin da suka cike masa ruhi, amma kuma sai ya fasa
wannan yunkurin nashi, sakamakon tunowa day a yi hakan da yake son yi haramun ne ka
shigarwa mutum gida bad a izininsa ba. Wata tambayar ma ta sake zuwar masa, ta dade a
gidan tana zaune, ko kuwa ma dai gidan wasu ‘yan uwanta ne? idan gidan wasu ‘yan uwanta
ne ai makulli ya ga ta saka ta bude gidan, hakan yana nufin ba kowa, ita dai ce yazu ta bude ta
shiga. Tabbas haka ne, sai dai ko iada masu gidan suna da tsarin rufe gidansu a kowane lokaci,
idan mutum zai shiga sai yayi amfani da makulli. Wannan tsari ne na wasu mutane da ke
kasasjen Turai, amma mu kam a Nigeriar mu ba mu san wannan tsari ba, to ya abin yake?
Tsayuwar waata bakar mota kirara Odessy a kofar gidan da Shuhuda Ibn Khaddab ta shiga ta

dau hankalinsa. Wani Balaraben matashi ne ya gani ya fito daga cikin motar,sanye da Fakistan
a jikinsa, fuskarsa da karamin tabarau. Isah yana kallo shi ma Balaraben ya sanya makulli ya
bude gidan ya shiga, haka dai ya tabbatar masa duk wanda zai shiga gidan da makulli yake
amfani. Waye shi wannan matashin Balarabe da ya shiga gidan? Babu amsa gumi ya gama jike shi
sharkaf! Duk wata nutsuwarsa tayi kaura ta rabu da gangar jikinsa. Kanwarsa Shuhuda ta
tabbatar masa Shuhuda Khaddab 'yar asalin jihar Katsina ce, kuma mazauniyar jihar Katsina,
wadda ta yi karatun sakandire dinta a jihar Kano. Wane sanadi ne ya kawo ta birnin Ibadan? Ga
shi ba ya shiri da kanwarsa Shuhuda da ya tuntubeta shin ko dama Shuhuda Ibn Khaddab tana
zuwa Ibadan ko ta taba zama a can ne? Komawa yayi cikin gida, ya zauna a gefen gadonsa
yana tunanin abin yi, shin ko dai ba Shuhuda ibn Khaddab bace ya gani ba? Ta ya ma zai ce ba
ita ce ya gani ba? Lallai ita ce to tababa babu. juyawa yayi ya dauko wayarsa da ke kan
bedside(gefen gado) wata zuciyar ta shawarce shi kawai ya kira Shuhuda yayi mata
tambayoyinsa. Har ya laluba lambar Inna Yaduwa, sai kuma ya fasa sakamakon wani kunci da
ya ji ya mamaye masa zuciya. Abin da ta yi masa akan Hamza ya yi masa ciwo, wai har ta iya
son bare akan na gida?
Karar kwankwasa kofa yaji, a hankali yace. Alwaye ne?" Daga bakin kofar dakin nasa ya jiyo
muryar Beka (daya daga cikin masu yi masa hidima) ya ce. "Ni ne yallabai". Cikin harshen
turanci yayi maganar. Isah ya bashi umarni ya shigo, ya ce "Yallabai an kawo wuta za a sauya".
"Ok, ba matsala". Isah ya mayar masa da amsa. Beka ya fice daaga dakin. Isah ya maida kai ya
kwanta, tunanin ma aka rufe babinsa, amma damuwa da rudani sun kaura daga zuciyar sa. Da
yaga abin zai masa tarnakinda zai iya haddasa masa matsala, sai ya janye wani littafi 'lobe sick'
ya soma karantawa. Washegari sai misalin karfe takwas da mintina arba'in ya tafi gurin aiki. Bai
dawo ba sai yammaci sosai, yau ma a barandar ya tsaya har lokacin magaruba ya yi, da yake
akwai masallaci a layin,sai ya fito ya samu jam'I. Ana gamawa ya dawo, bai shiga cikin gida ba,
a harabar ya tsaya. Yana kallon motar ta tsaya, Shuhuda ibn Khaddab ta fito, yau sanye ta ke
da material mai ruwan sararin samaniya (sky blue) sabanin jiya da take sanye da leshi ja. Da ta
fito daga motar ba ta bar gurin ba, jingina tayi da motar tana dube-dube tamkar mai neman wani
abu. Zuciyarsa ta ayyana masa kawai ya isa inda take, sai dai yana yunkurawa da nufin haka,
sai yaga ta rabo jikinta daga motar ta soma taku tana nufan gidan da ta shiga jiya. Fasa zuwa
wurin nata yayi, don yana da tabbacin kafin ya zagaya ya fita tuni ta dade da shigewa gidan.
Har tsayin mintina ashirin da uku da shigarta cikin gidan bai ga matashin Balaraben ya shiga
kamar yadda ya faru a jiya ba.
Kamar walkiya ya hangota ta fito a sukwane gurinsa ta nufo. Kallo daya zaka yi mata kasan a
rude ta ke, sam ba ta cikin nutsuwarta.
Sai da ta karaso daf da barandar maimakon ta zagayo ta get ta shigo ciki sai ta tsaya daga
nesa musryarta da dan sauti mai karfi ta ce.
"Don Allah yah Isah ka taimaka min, mijina ne ba shi da lafiya, ba zan iya tuki ba, ka taimaka
min don Allah".
Ta karashe maganar cikin raunanniyar murya, kwalla suncika gurbin idanunta. Maganarta ta
hargitsa masa tunani tabbas dai Shuhuda ibn Khaddab ce, tunda har ta iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login