Showing 75001 words to 78000 words out of 83144 words

Chapter 26 - MATA'UL HAYAT BY SAKINAT USMAN-1.pdf

02 Aug 2025

11102

cikin zuciyarsa shi ne, addu’a Allah ya bas hi juriya da jarumtar da zai iya
sadaukar da rayuwarsa saboda Allah ba don wani ba, ya sanya a ransa idan ya samu nasara ta
sanadinsa, shuhuda ta kubuta falillahi hamdihi, ya yi hakan ne domin Allah ba don shuhuda ko
wani nata su yaba masa ba, domin shi a rayuwarsa ya tsani abin da zai yi don wani ya yaba. Shi yasa ko lokacin da yana Senegal idan suna group discussion ya kawo idea da zarar ya ji
wani ya fara yi masa godiya zai bar gurin, haka ko irin assignment din nan aka bas u ya
taimakawa wani bay a bukatar a yi masa godiya, har ma wasu suka yi masa lakabi mai
sadakatul jariya musulmai ken an! Isah yana da kyakkyawar zuciya abar so da koyi ga kowa, don da ace matasa zasu yi koyi da
irin halayya ta Isah, ko shakka babu rayiwarsu zata inganta, ta zamo abar kwantance.
Daren ranar asabar Isah da Uncle Hamza bas u runtsa ba, kowanne da yanayin da yake ciki.
Kusan a tare zan ce sun sami bacci, bayan sallar asuba ken an, wanda sun farka ne sun gansu
a wari daya su duka biyun a cikin kungurmin daji bisa wasu buzaye.
Mamaki ya cika su ta yadda lamarin ya faru har suka soma tunanin ko a mafarki ne suka samu
kansu a muhalli daya.
Isah ne ya soma yin Magana bayan dogon lokacin da suka dauka suna duban juna, inda yake
cewa.
“Ta ya na ganni a wannan guri, ko mafarki nake yi ne?”
Shi ma Uncle Hamza hakan ya furta, su duka biyun suka rasa amsar da za sub a wa inna, sai
dube-dube da waige-waige suke a tsakaninsu, babu gida a gaba bare a baya ko gefensu.
Daji ne sosai ga manyan bishiyoyi suna ta rangaji fiska na kada rassansu.
Duba da yanayin da gurin ya nuna zai iya shaida musu rana bat a yi sosai ba, hasalima za a iya
kiran lokacin hantsi ya daga gari ya shaaa, saboda ransar ba ta da kaifi.
Suna cikin wannan yanayi na tababar gaske ne ko mafarki suka hango Yakub na saukowa daga
wata bishiyar Rimi, fuskarsa dauke da fara’a.
Babu wanda ya samu dammar furta wata kalma har ya karasa saukowa ya iso gabansu. Tare
da mika musu hannu don yin musabiha,bayan sallama da ya yi musu.
Babu wandan ya noke suka ba shi hannayensu suka yi musabihar, don sun yardarm wa
kawunnansu yakub ba mai cutar da su ba ne,kuma ganinsa ya tabbar
Musu da duk yadda aka yi shi ne sanadin wanzuwar su a gurin.
lle-kuwa bayan gama musabihar yakub ya dora da cewa.
‘’kada ku wahalar da zukatanku wajen tunanin wanzuwarku a wanna bigire, domin ni ne na

kawo ku bisa alkwarin da na dauka na yanke muku nisan tafiyar da ke tsakanin kano da sokoto.
A halin yanzu kuna cikin jejin da shuhuda ta ke a daure, tafiya kadan ce zaku karasa tsuburin.
Kamar yadda na fada muku jiya cewar idan kun isa tsubum bannu ba zai iya kunce shuhuda ba,
tabbasa haka abin yake.
Suratul waki’a ita za ku kalanta a yayin da kuka isa inda shuhuda ke daure, da
yardar.Assamadu za ku kasance masu nasara. Sai dai abin da nake so da ku shi ne, ku zamo
masui sadaukarwa, ma’ana ku yi rai ko akasin haka’’.
Ya dan saurara yana dubansu daya bayan daya, su din ma dubansa suke yi a nazaree
Tsayin mintina ba tare da wani ya tanka ba,sai can daga bisani yakub ya ci gaba da eewa.
“masu sirri wasu irin hatsabiban mutane ne, dole sai kun kasance cikin neman tallafi daga
basani yakub ya ci gaba da cewa
“masu sirri wasu irin hatasabiban mutane ne , dole sai kun kasance cikin neman tallafi daga
lillahi , ko da yaushe ku yi ta rook don shi mai rook ga mahalicci bay a zama kaskantancen
bawa . kuma mahalicci yana son bawan da yake rokonsa ba don rokon yana amfanar da shi
(Allah) kamai ba, face shi bawan da ya mayar da lamiri gare shi (Allah ) don haka abin da zan
ce, GA FILI GA MAI DOKI , Allah ya ba wa mai rabo sa’a, yak are ku daga hatabibancin masu
sirri, ya makanatar da su daga ganiku. Ya kawo tallafi da zaku zamo sila ta rushewar majalisin
da ake farautar bayin Allah .
Majalisin da kafuwarsu bai zamo riba ga addinin musulunci ba, sai dauki dai- dai da ake yiwa
bayin da ba su jiba ba su gani ba
Gaba dayansu suka amsa masa da
Amin
Yakub ya nuna hanyar da ta yi arewa ya ce
I dan kuka bi wannan hanyar tafiya kadan zaku yi ku tarar da wani fili daga nan sai tsuburin
Allah Ya bada sa’a
Yana karashe fadar hakan suka neme kallon –kollo a tsakaninsu , kowanne fuskarsa turbine
babu almar fara’a ko kadan
Uncle hamza ya dan ja gajeran tsaki ya soma taku da nufin tunkarar hanyar da yakub ya sanar
musu zata sada su da tsuburin da shuhuda ta ke
Ganin uncle hamza ya nufi gurin sais hi ma isah ya yunkura da karkarfan takunsa ya tunkari
hanyatr, su duka biyan sauri da azama suke ba tare da wani ya kula wani ba, a kasan
zukatansu kuma suna ta yiwa kawunnasu addua
Wani ma keken fili suka yi tozali da shi fari fat da shimfidadden yashi ya yi shamal tsaye suka yi
suna fuskantar juna, domin iya hangensu ba su iya hango karshen wannan fili ba, alhalin kuma
an ce tafiya kadan ce za su yi su ruski inda shuhuda ke zaue
Ga su dukkansu sun kasance masu son abu daya bare us tambayi juna shawara
Yanayi fuskokisun kadai zaka kalla ka gane karayar da zukatansu suka yi muraran .
“ akwai matsala “
Isah ya ambata a ransa wannan yanayi da suka sami kansu ciki kadai ya is is aya sanar musu
babu nasara a wannan yunkuri nasu
Tsayin mintina babu wanda ya mostsa, dace kuma wanda ya iya lalubo abin da ya dace ya yi a
cikinsu
Isa shi ya yi jarumatar daga kafa ya soma tafiya yayin da uncle ya yi isah idanu yana yaba

jaruntarsa, bai sani ina ya nufa ba.
Duk yadda yake ganin zai iya sadaukarwa don ceto shuhuda yanzu ya samu karaya ., koda
yake a gurinsa bai ga laifinsa ba, iyakacinta ba, kwatan –kwacin a ajiye ka dakin da babu digon
haske ace ana so ka lalubo kofa
Isah kuwa tafiya yake cikin rashin tsammani , yana kuma karanto duk adduar da ta zo bai san ,
abin da ya sanyanwa ranshi koda ace zai karashe rayuw a ta tsayin shekaru goma a wannan fili
yana da fadi ba tare da ya san inda shuhuda ta ke ba, lallai ba zai yi kasa a gwiwa ba zai ci
gaba da wanzuwa a gurin Kamar yadda cikin littafin alhlari aka ce, wanda ya yi hijira domin Allah da Manzonsa, hijirarsa
nag a abin da ya yi niyya, ya riga ya sanyawa ransa zai yi komai don ceto shuhuda mastsawar
bai kaucewa addini ba, domin Allah
Ya yi nisa sosai a tafiyar tasa, har ya kasance nisan da ke tsakaninsa da uncle hamza zai kai na
kilo mita ba zato ba tsammainni ya hango wani katon dutse a samansa turun hayaki ne yake
tashi karmar an hura wuta.
Gabansa ya yanke ya fadi , koda ya yi rayuwa a senagal inda suke zuwa gurin duwatsu don yin
nazari bai taba jin faduwar gaba ba idan ya ga hayaki sai da ya samu kansa a cikin firgici
Watakila hakan bay a rasa nasaba da lokacin da suka soma hango filin ba su ga karshiensa ba
karmar yadda sam bas u hango wannan katon dusten ba , tunda tunda kuwa yanzu dutsen ya
bayyana baa bin wahalar da kai ba ne , don an yi mamaki .
Samum saukin raguwar faduwar gaban nasa ya biyo bayan saurin lalubo aduo I da ya yi sai ya
samu nutsuwa, har ya ji wani karfi ya zo masa. Ckikin azama ya tunkari katon dutsen ,ya
matsen masa sosai , sai ya hango shuhda daure cikin sasari, irin wanda ake daure dawaki da
su Ta yi ligib idanunta a rufe ruf da alamas ko baccie ta ke, ko kuma babu numfshi a jikinta
Kusan rikicewa ya yi , har ya manta da yin tsinkaye da gargdin da yakub ya yi masa ya ruga da
gudu da nufin isa gurin, zuci yar sa na harbawa kamari zata tsago kirjinsa ta fito .
Bisa tsautssay I kafaluwansa suka harde ya fadi a cikin yashi . ya jima kafin ya dago kai yana
hango shuhuda , ga ta kamar a kusa da shi, amma akwai tazara sosai kafin ya isah inda take
Cikin rashin kuzari ya mike tsaye , wannan karon nutusuwa t a zo masa , ya yi saurin ambaton .
“ innallahi wa inna illahi raju un “
Tukunna ya soma taku bisa diga -digan kafarsa babu ko takalmi , hasalima bai san ta ya ya
watsar da sub a
Ya isa gab da inda ta ke ya yi tsaye yana kare mata kallo , sannan ya soma karanto suraturl
wikia daga farkonta zuwa karshe
Yana dire aya , duk igiyoyin da jke daure da shuhuda suka tsinke, ta bude idanunta da sauri
kamar wadda ta farka daga nannauyan bacci, ta ambaci
“ subhannaallah”
Cikin attausan lafazi , sannan ta soma akarewa gurin kallo
Ganin a inda ta ke da kuma isah da ke gabantan ya daga mata hankali , ta fashe da kuka tana
cewa
Yah isah me yasa zaka yi min haka ? me na yi maka zaka kawo ni a cikin wannan bakar dajin?
Ina rokonka alfarma kada ka keta min haddi , kayi min hakuari kada ka bata min rayuwa
Jin kalaman da ke fitowa daga bakinta ya tabbatar masa ba tasan duk wainar da ake toyawa ba

. maganar yakub ta fado masa a rai inda yak e cewa , da zarar igiyoyin suka tsinke a yi kokarin
barin jejin , domin a lokacin komai zia iya faruwa, masu sirri za su ji kubutar shuhuda a jikinsu
Sai ya ji wani karfi y a zo masa ya samu karfin gwiwar fizgar hannaunta yana mai karantao
audo’iI ya soma gudu da ita
Yayin da ita kuma ta ke ta tsala kuka tana rokonsa kada ya bata mata rayuwa
Kamar hadari suka hanga a gabnasu iska mai matukar karfi ta taso wanda har ba su iya bude
idanunsu illa yana ambaton Allah akan harshensa. Ya kuma rike hannun shuhuda gam, iskar ta
raba su kamar daukewa wutar lantraki, sai ya ga komari ya yaye
Shuhuda ce a hannun wasu irin mutane sun kai mutun shida , kowance da shuhuda a
hannunsa tana kuka, tana cewa .
“ yah isah . wyyo yah isah za su kase ni, za su sha jinina , ka taimake ni haya isha “
Kansa ya daure hankalinsa ya tashi , ya rasa wa zai kwata, wace ce shuhuda ta gaskiya a cikin
su shiddan da ke hannun miyagun mutanen
Cikin dakiyar zuciya ya yi kabbara yana kiran sunan shuhuda , gaba daya dajin amsawa ya
yake
“yayana ka zo gare ni, n ice shuhuda ka taimake ni ”
A fusace ya yi kan wani mutm wanda shi ne mataimakin shugaban kungiya , shi ke rike da
shuhuda ta gaskiya , ya ce .
“mhm , kifi na ganinka mai jar koma (ANTY RAISAT KINDE JI lol….) , ko ka dauka duk yunkurin
da kake na fita da shugabar mu a wannan guri ba ma ganinka ? bude kunnuwanka da kyau ka
ji, kmar yadda basarake ba zai satu ga barawo ba saboda dogarawa , haka muma ba ma wasa
da shugabar mu , don haka kan sani aa mu sha jinin shuhuda don ya halatta ga abin tsafinmu ,
kamar yada muka sha jinin dr ya’u,
Kamar yadda muka sha jinin masa’ud da zarar mun sha jinin shuhuda za mu jinin wannan
jemammiyar tsohuwar sannan mu sha naka mai yi mana karamabani
Dama mun dade muna burin shan jininka , tunda kuwa ka kawo kanka faduwa ta zo dai –dai da
zama . sannan za mu hada da tsoho rabi’u don kun ci kuin jini, kun sha kudin jinni, kun ji dadi
da kudin jinni dole mu kaddamar da ku jiniku ya yi kuka
Cikin tsananin jarumata isah y ace
“ allah ya fi ku , do domin kuidn jinni ba mu da masaniya a kansu , allahi bay a kama bawa akan
lain da bai sani ba .
Ina rokon allah kariya a bisa sharrinku, saboda ku mushirikai ne, ina mai tabbatar muku da ku
tuba ga allah , don ka sha jini domin samun kyalen rayuwa me ka yi ? me kuka dauki rayuwa ne
?
Akwai fa tsufa, idan hisabi”
A fusace mataimakin shugaba ya yiwa Isah wata razananniyar tsawa bakinsa na fidda yahaki,
idanusa na awalkiya suna sauya kaloli KORE, DORAWA zuwa BAKI.
Isah dai ya budi idan ya ganshi a daure, sun zagaye shi yayin da shuhuda ke faman rabsar
kuka tana ba su hakuri, tana fada musu matsayin Isah da muhimmancinsa a rayuwarta.
Sun tabbatar mata cewa, yau za su sha jinin Isaha yanzu kuma ita zata yi jagorancin kisan nasa
kasancewarta shugaba kuma sarauniyar matsafa.
A hankali ta tako gaban Isah idanunta dauke da wasu sirrika, amma zuciyarta na kuka akan
abin da tasan yanzu ya zamar mata dole ta kasha Isah, anya zata iya bayar da jinin Isah wasu

can su sha?
Isah da ke kallonta a ci kin zuciyarsa yana karanto ayoyi daga cikin alkur’ani bakinsa ya furta.
“Allah ga bawanka kada ka bar wadannan bayin naka su halaka ni, Ya Allah, Ya Ubanjigin
Jibrilu da Mika’ilu da Israfilu, mai kaga halittar sammai da kassai, masanin fake da sarari. Kai ne
kake hunkunci tsakanin bayinka cikin abin da suka kasance suna sabawa a gare ka na gaskiya.
Ina rokonka ka shiryar da su don su kasance masu saba maka, Allah idan ka so kai ne mai
shiryarwa, Allah ka shiryar da su izuwa tafarki madaidaici.
Idan kuma ba masu shiryuwa ba ne, Allah bayinka ne na barka da su, ka tsare ni daga
sharrinsu, ka kuma kwato min baiwarka shuhuda wadda azal ta fadawa ba ta ji ba ta gani ba,
tunda tun tuna da kuruciya suka sanyata hanyar halaka. Allah ka tserar da mu daga sharrinsu”.
Ya yi kabbara mai karfi, y ace.
“Allahu akbar! Allahu akbar!! Allahu akbar!!! Walhamdu lillahi kasiran! Walhamdu lillahi kasiran!!
Walhamdu lillahi kasiran!!!.
Take ya sake karanta suratul Waki’a sai ga daurin jikinsa duk ya zube. Cikin zafin nama ya
janyo hannum shuhuda, amma sai ta soma togewa.
Ya sake yin kabbara, ya kuma maimaitawa sai kawai ya ji ita ma ta dauka, suka soma gudu.
Ba su dade suna gudun ba sai suka tarar da miyagun mutanen a gabansu. A yanzu zuciyar
Isah ta soye bay a shakka, kuma bay a fargaba bakinsa dauke da Ayatul Kursiyyu yana
karantunta a fili yana karanto surorin karshe na Suratyl Bakara a fili.
Tsoro tare da firgici ya shiga cikin zuciyoyin matsafan, don suna mamakin irin barnar da Isah ya
yi musu, suna kuma ji suna gani gas hi yana neman samun galaba a kansu.
Cikin tsirkewar zuciya mataimakin shugaba ya kwo hannu da niyya shaker Isah, sai hannun ya
kama da wuta, ganin haka sai gurin ya yi tsit, babu su duk sun bace.
Isah da shuhuda gudu suke bas u yi aune ba ga su jikin dutsen nan na kasar Sokoto, wato
Dutsen Kwatarkwashi, suka fadi yaraf.
Shuhuda ta zabura ta kankame inna yaduwa ta ce.
“Don Allah kada ku bari su sake tafiya da ni, suna wahalar da rayuwata, sun takura min, ni dai
wallahi ban yafe masa ba, cuce ni!”
Inna yaduwa tana kuka tana rika da shuhuda tana tuno rayuwar da ta yi, lallai akwai sakayya,
shi yasa Hausawa suke cewa wata shari’ar sai dai Allah.
Ita ma addu’a aka ci gaba da tofa mata har bacci ya yi awon gaba da ita.
Zuri’ar Alh. Rabiu sun shiga fargaba da tarin tsoro saboda halin da suka tsinci kansu na samun
jinisu cikin matsafa.
“Ina zargin kaina a bisa lalacewar Sagir, saboda tun farko shi yaro ne mai son kyale-kyalen
rayuwa, a gaskiya na taka rawa wajen shigarsa kungiyar matsafa”.
Gaba daya suka zubawa tsohon ido, ya ci gaba da cewa.
“Abin da yasa na fadi haka shi ne, me yasa lokacin da Sagir ya soma tashen kudi farad daya ya
zam mai arzikin gaske ban bincike shit a ya ya same su ba, wannan yan faruwa bag a ni kadai
ba, al’umma baki daya. Me yasa ba zamu ringa bibiyar rayuwar ‘ya’ yanmu ba tare da sun sani
ba mu gano su waye abokansu, ko a ofis ko kasuwar, amma idan yaro ya taka matakin balaga
shi ken an sai mu zuba masa ido ba zamu san me rayuwarsa ta ke ciki ba.
Anya mun son samawa rayuwar iyalanmu jin dadi? Wai me muka dauki MATA’UL-HAYAT
(kyale-kyalen rayuwa) ne a wannan zamani? Me muka dauki rayuwar kanta ma? Mu yi gida, mu

sanya suture na alfarma, mu shiga motoci na gani a fada, mu auri mataye, me yasa
kyale-kyalen rayuwa ya fi tasiri a cikin al’umane?”
Kuka sosai Alh. Rabi’u yake yi yana jin ciwon abin da dansa ya aikata.
Ya dago idanunsa fal da hawaye, ya ci gaba da cewa.
“misali akan Sagir, ya dauki shuhuda ya bayar da ita cikin matsafa, tun farkon rayuwarta cikin
kunci ta taso, cikin maraici, ana yi mata wasarere da hankali, da muna yin kafi a gidajenmu irin
wadannan shu’uman mutane da bas u shigo ba.
Ita shuhuda ya addinta ya ke? Ya karatunta ya ke? Amsar it ace, an birkita rayuwarta, an hanata
jin dadin rayuwarta, an hana ta zam mutum. Ni abin da ya fi daure min kais hi ne, su matsafan
bas a tsoron yadda rayuwa ta ke juyawa, ma’ana shin suna ta salwantar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login