Showing 6001 words to 9000 words out of 83144 words

Chapter 3 - MATA'UL HAYAT BY SAKINAT USMAN-1.pdf

02 Aug 2025

11067

samu Shuhudab ne???
.
Isah yace Rauni ne a hannunta. Yace To gani nan zuwa. Inna Yaduwa ta dubi hannun Shuhuda
har yanzu nonon ne yake tarara iya rudewa kam ta rude da wannan murdadden al'amari.
Ita kuwa Salmai tsuru-tsuru ta yi hankalinta a matukar tashe ta rasa yadda aka yi hakan ta faru
ita dai a saninta jini ne a jikin kowanne dan Adan, to ya akayi ita Shuhuda aka samu akasin
haka?
Gaba daya jikinta nono ko kuwa a yatsan nata kadai ne ke da nonon a maimakon jini? Idan a
yatsan kadai ne ke da nonon shi ta ke tsotsa maimakon kiwo(feeding) nata? Wannan wani
bakon al'amari ne mai rudani da daure kai. Su dukkansu aka rasa mai abin cewa kowa yayi
shiru da abin da yake sakawa a cikin ransa. Ba a fi mintina goma sha uku ba Alh Sada ya dura a gidan Ko da ganin abin da yake faruwa
hankalinsa ba karamin tashi ya yi ba ya dubi Inna Yaduwa yace; Inna ta ya aka yi haka ta faru.
Inna Yaduwa tace To tsautsayi ne da ba ya wuce ranarsa Ba musan hikimar tsotsar hannun da
Shuhuda take ba na sa aka tsarga hannun ashe nono ne take sha a jikin yatsan?
Alh sada ya jimanta lamarin sannan yace; To shikenan Allah ya kyauta gaba ku taso muje clinic
a dinke mata yatsan. Inna Yaduwa Isah gami da Shuhuda suka mike tsaye yayin da salmai take
zaune a guri guda ta yi tsuru-tsuru da ita sai kace kazar da aka tsamo a cikin ruwa.
Kai tsaye suka nufi kofar fita sai a sannan Salmai ta samu damar matsawa ita ma tabi bayansu

suna fita mota suka shiga ita kuwa Salmai ficewa tayi daga gidan da jakar kayanta tana tafiya
sukuku kamar mai tsoron taka kasa.
FABCY CLINIC suka je Dr Ya'u ya jagorancui dinke yatsan /huhuda wanda har suka iso asibitin
bai dai na ambaliyar da ruwan nono ba.
Abin mamaki duk inda aka sa allura don dinkewa a jikin yatsan sai gurin ya 6ule nono yayi ta
tarara. Shi kanshi Dr Ya'u ba karamin firgici ya shiga ba da ganin yadda lamarin ke gudana.
.
.
Toh pa, ni ma se da na rude har waya ta ta pada ruwan jikin shuhuda...
Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)
¤¤06¤¤
Da ya ga haka sai ya dauko wani garin allura ya zuba a cikin raunin ya kawo bandeji ya lika
mata sannan yayi mata allura. Yana cire tsinken allurar daga jikin Shuhuda zance ya sake shan
bam-bam domin tsinken allurar ya karye a jikinta.
Da sauri aka shiga theater room da ita aka samu da kyar aka tsinke allurar daga jikinta koda
yake ita dakanta ta cire. Daidai lokacin ruwan nonon ya daina tarara sai wani irin nannauyan
bacci ya sure ta.
Dr Ya'u ya fito daga dakin tiyatar ya dubi Alh sada yace Alhaji dole sai ta kwana saboda gaskiya
yanayin jikin yana bukatar kyakkyawar kulawa.
Kaga bayan an samu an yi mata tiyata an cire tsinken allurar sai wani zazzafan zazza6i ya rufe
ta. Yanzu dai ta samu bacci don haka ku yi hakuri ta kwana zuwa washegari sai a sallame ta
idan komai ya dai-daita.
Alh Sada ya sauke gauron numfashi cikin matukar jimami yace: 8abu komai Allah ya kaimu
goben lafiya ya kuma bata sauki.
Gaba daya suka amsa da ameen. Alh sada ya dubi Inna yaduwa yace Bari naje na kawo miki
abubuwan da zaki bukata na amfani. A'ah bara mu je tare ai bacci take har maje mui dawo.
Yace To. Suka shiga dakin da shuhuda take tana kwance tana ta sharar baccinta don haka suka
fito su duka ukun suka nufi gida. Sun isa gidan Inna yaduwa ta shiga ciki ke nan wani yaro ya
shigo yace; Inna wai ance a fada maki SALMAI MAI HAJA ta RASU. Inna yaduwa ta zabura
tare da doka sallallami ido waje tace Salman ce ta rasu? Yanzu fa muka rabu da ita? Yaron
yace Eh mota ce ta kade ta take wuyanta ya KARYE, Yanzu ma za arufo ta.
Inna yaduwa ta sake jan sallallami ta dure tace; IDAN AJALI YA YI KIRA koba ciwo sai an tafi.
Yanzun nan fa tabar gidan nan? Ta karashe magana tana nuna matukar alhininta. Yaron dai ya
yi shiru yana sauraren ta.
Alh sada ya shigo cikin gidan ganin ta jima bata fito ba. Ya tarar da ita cikin halin jimami yace;
Inna ya baku fito ba? Kada fa ta farka babu kowa a kusa da ita.
Tace.
Tace Mhm kai dai bari wai Salmai ce ta rasu!! Yace wace Salmai? Tace salmai mai haja mana
yanzun nan fa ta bar gidan nan bayan ta tsaga hannun Shuhuda wai mota ta kade ta.
Ya ce Allah sarki kila tsabar rudewa ce ta sa ko gabanta ba ta gani har hakan ta faru. Allah dai
ya jikanta ya rahamsheta. Tace Amin jiki ba kuzari ta hada kayan da zata hada suka nufi
asibitin. Har lokacin Shuhuda bata farka ba bacci kawai take yi.

Alh sada ya yiwa Inna yaduwa sallama ya tafi tare da Isah suka barta a nan. Sai a washegari ne
misalin shida da rabi na safe shuhuda ta farka. Karfe takwas yan uwa da mutanen arziki aka yi
ta zuwa ganinta da yi mata sannu da jiki. Misalin sha biyu na rana aka sallame su suka
dunguma gida. ******** ********* ******
Zaman gidan Alh jamilu dai babu dadi domin sam karima ba ta da sukuni matansa ba sa sonra
sun tsane ta musamman yadda suka ga yana riritata yana kulawa da ita.
A ganinsu ya bam-banta su shi kuwa duk abin da yake yiwa karima ya na yi ne don mantar da
ita alhinin rashin tsohon mijinta saboda a zahirin gaskiya karima ta yi rashi babba wanda take
bukatar samun wanda zai maye mata gurbinsa.
Alh jamilu adalin namiji ne kuma jarumi gwarzo yasan duk wani salo na soyayya don haka ya yi
amfani da wannan damar ya mantar da karima bakin cikin da matansa ke kunsa mata.
Koda yake a wani 6angaren ba ya da masaniyar irin zaman doya da manjan da ake yi a cikin
gidan nasa. Saboda ya kasance mutum ba mazauni ba dan kasuwa ne da ke kewaya kasashen
duniya.
Ta 6angarenshi kam karima bata da matsalar komai domin ta samu nagartacciyar kulawa daga
gare shi matsalarta ga matansa take su ma yayan nasu basu kyalle ba ne domin sam yaran
basu da yarbiyyar to su ma ba ta ishe su ba bare su baiwa wasu.
Rashin kunya kamar sa doke ta duj ranar girkinta yaran da iyayensu sun dinga yi mata korafi
kenan.
Rashin kunya kamar sa doketa duk ranar girkinta yaran da iyayensu sun dinga korafi kenan wai
tana rage kudin cefane. Bayan komai akwai shi a cikin gidan tsakanin mai gidan da matan alheri
ne ba ya baiwa mace kudin cefane amma don rashin adalci sai suke cewa tana rage kudin
cefane. Wannan dalilin ya sa karima ba ta zama a falo koda yaushe tana cikin dakinta.
Idan ka ganta a waje to kicin ko bandaki zata shiga kasancewar bandaki daya ne a tsakar gida
wanda kowa yake amfani dashi sai kuma na shi mai gidan shi kuma idan ba mace ke da girki ba
ba ta da damar shiga.
Duk cikin yaran babu wanda yake kulata da maganar arziki ko gaishe da ita ba sayi to bata
damu da hakan ba domin ba zamansu take yi ba. Zaman aure take shi kam zaman aure dan
hakuri ne dama da mijin ta ke samun matsala wannan da da ciwo. Duk da wannan din ma da
ciwo saboda zaman tare wani babban al'amari ne mai girma yana bukatar shakuwa da juna
kyautatawa juna gami da taimakekeniya. To su lamarin matan Alh jamilu ba haka bane irin
wannan banzan kishin ne suke na kauyanci kai yanzu ko a kauye a daina irin wannan kishin na
hauka. Sam babu ragayya ba ta da ikon ta kwanta ta huta muddin aka ce ranar girkin ta ne.
Habaici ko da yada bakaken maganganu abin ba a cewa komai har ma ta saba. Karima na kicin
tana dafuwar miya ta gama kwashe tuwo miyar ce take son kadawa. Binta uwargidan Alh jamilu
ta shigo kicin din tana bangaje karima ta dauko roba. Karima ta ja da baya sam batayi mamaki
ba idan da sabo ta saba da irin wannan cin kashin da ake yi mata a gidan. Sai dai a ganinta
izuwa yanzu yaci ace sun tsaya sun gina rayuwa mai kyau a tsakaninsu wannan zafin kishin
babu inda zai kai su illa halaka. To amma ba yadda za a yi matan ne gasu nan dai kurum. Binta
har ta kai kofa zata fita sai ta juyo tace; Allah wadaran naka ya lalace jakin dawa ya gana birni,
Mace ba kyau ba ba siga ba amma sai shegen kilibibi da karfar baka to ni dai wallahi karyar duk

wata juya bata isa ta fitar da ni a gidan mijina ba kowacce shegiya nan tazo ta tarar da ni don
haka idan ban fidda mace ba ta yi kadan ta fidda ni.
Karima tace Me ya kawo wannan maganar kuma? Binta tace Ban sani ba sai na ji makara don
na lura kwanan nan wani karfi karfi kike ji idan kina magana tamkar zaki daki mutum. To idan kin
isa kina ganin kanki ke wata abace ki kwa6e mu daku, kiga idan akwai kutumar da zaki diba a
jikina. Karima ta girgiza kanta tace Ni kam bazan iya fada da ke ba ba ma ke ba ni a rayuwata
ba na fada kowa kika ganni da shi burina na zauna da shi lafiya. Binta ta daka mata tsawa tace
Rufe min baki bakar munafuka baki fada da kowa amma kin iya karfar baka ko? Kin iya ki
kalallame miji ki raba shi da matansa ki raba shi da 'yayansa? To wallahi kin ji na rantse miki kin
yi kadan kin yi tsururu a gidan nan muddin kika ce wannan mummunar dabi'ar zaki tsuro a
gidan nan. Karima tace: Allah ya baki hakuri? Wannan kalami ya sake tunzura Binta tace Kin sa
Alhaji ya bugi Mas'ud to idan dai ni na haifi Mas'ud har aban abada ba zai ta6a gayar da ke ba.
Duk wani ahali nawa ba zai ta6a yin wata mu amala da ke ba, idan kina so ki burge ni kisa
Alhaji ya sa wuka ya yanke kawunan duk wani ahali nawa akan ba sa gaishe ki sannan zan
tabbatar da sunanki karima matar so. Ta ja wani dogon tsaki tace Shi kuma Alhajin yayi na farko
ya yi na karshe don bashi ya sha min wahalar daukar cikin ba bare ya kama min 'yaya da duka
akan wata banzar bazara ruwan kaka, juya wadda tun da ta shigo gidannan komai ya
ta6ar6are. Tana karashe maganar ta sa kai ta fice daga kicin din ta bar karima nan tsaye sororo
cike da takaici don halayen Binta ba su ba ta mamaki, sai dai tsoro. Ta tabbatar da ace za a
bata umarni ta kashe ta ko jinkiri Binta ba zata yi ba zata iya kashe ta saboda wannan zafin
kishin nata yayi yawa. Cikin rashin sukuni ta kammala miyar ta dawo daki da nufin ta huta kafin
a dawo daga sallar azahar ta zubawa kowa nashi. Tana nan zaune ta jiyo sallama a falonta ta
shaida muryar dattijuwa ce mai YAKANAH wadda ta nuna mata halacci ta sota a lokacin da take
tare da ita wato Inna Yaduwa. Ai kuwa da sauri ta fito falon ta na lale marhabun da zuwanta.
Bayan Inna yaduwa Shuhuda da Isah sun zauna Karima ta je ta zubo musu tuwon shinkafa
miyar agushi ta kawo musu gami da ruwan sanyi. Ta zauna suna cin abincin suna gaisawa har
suka kammala Inna yaduwa tace: Karimatu ki yi hakuri don Allah da jinkirin da aka samu na
kawo miki Shuhuda tsayin watanni tara. Kinsan lamarin zaman gidan wani wuya gare shi
musamman ma yadda na lura halayen abokanan zamanki ba ya da kyau. Karima tacr Lah!
Wallahi Inna ba komai ai ana kawota don wannan karon an samu jinkiri sai ya zama wani abu?
Wallahi ba komai. Shuhuda ta mike tsaye Inna yaduwa tace Ina zaki? Tace Fitsari zan yo? Ta
fita Inna yaduwa ta dawo da dubanta ga karima ta ce; Ga fa danki kin san dul cikin satin nan ba
zancen da yake sai naki yau dai ya takura sai na zo. Karima ta yi murmushi tace Isah ke nan?
Ai shi kam da Mamansa sai Allah. Inna yaduwa ta dan saka nutsuwa tace. A nan zamu bar
Shuhuda za ta yi miki sati biyu saboda mako mai kamawa zata soma zuwa Makarantar boko
kuma kin san yaro idan ya na karatu baya da wani sukuni bare ga kuma Islamiyya.
Karima taji dadi har cikin ranta da jin wannan batu saboda a yau zata kwana da gudan jininta
'ya daya tilo ta mallaka a duniya. Wadda in baci ita da sai ta aminta da maganar su Binta ke
fada akanta cewar ita din juya ce to amma kasancewar ta san ta ta6a haihuwa sai zancen na su
bai dauke ta ya nana da kasa ba. Ta san cewa tsawon shekaru biyar data shafe a gidan Alh
jamilu Allah ne bai hukunto haihuwar da shi ba idan lokaci yayi zata haifa din. Kukan Shuhuda
da suka jiyo ne a tsakar gida ya sa gaba daya suka mike tsaye a zabure suka nufo tsakar gidan.
Mas'ud yaro dan shekaru sha tara suka hango ya kama Shuhuda yana jibga kamar wata tsaran

shi. Sai dai suka ja tunga suka tsaya, Inna yaduwa ta dubi karima cike da tsananin mamaki ita
karimar Inna yaduwan take kallo. Isah kam tuni ya kaiwa 'yar uwarshi dauki ya cakumi wuyan
rigarshi ya yi wurgi da shi tare da kai mishi wani irin wawan naushi. Rigima ta raku6e tsakaninsu
Shuhuda kuwa tana kwance. Karima ta yi saurin shiga tsakanin su ta raba su amma Mas'ud ya
tattakura ya kaima ta naushi a gefen cikinta ba arziki kuwa ta ja baya. Inna yaduwa ita ta raba
fadan yayin da Binta ta fito daga dakinta dama duk abinda yake faruwa akan idonta ne abinda
yasa tun dazun ba ta fito ba tasan Mas'ud yana da taurin rai mawuyaci ne ayi fada da shi bai
samu galaba ba amma yau sai ga shi zance ya sha bam-bam. Duk girman jiki irin na Mas'ud
amma Isah ya fi shi zafin nama da karfi domoin ba don Inna yaduwa ta raba fadan ba wata kila
sai dai a dauki Mas'udin ranga-ranga. Binta na fitowa daga dakinta ta balbale Inna yaduwa da
masifa har tana kiranta tsohuwar akwala wai tana shiga fadan yara. Inna yaduwa ta rike ha6a
kawai tana karewa Binta kallo mamaki take yi 'yar da ta haife ta a cikinta amma ita ce take yi
mata wadannan munanan furucin. Binta jin ba wanda ya tanka mata sai ta kama hannun
Mas'ud tace: Mu je ciki Alhajin ya dawo Ni na gaji da wannan masifa mata kin zame min ciwon
ido mai wuyar magani a gida? To wallahi ba zata sa6u ba bindiga a ruwa yau alo tsiya alo danja
sai an san mai yiwyuwa. Inna yaduwa suka karasa inda Shuhuda take kwance duk ya farfasa
mata jiki, amma a madadin a ga JINI a gurin da ya farfasa mata sai suka ga RUWAN NONO fari
kal yana zuba. Wannan lamari ya hargitsa tunanin karima don bata da masaniyar wancan
al'amari da ya ta6a faruwa. To ita kanta Inna Yaduwan da Isah abin ya kara hautsina masu
kwanya shin ita Shuhuda wacce irin halitta ce da gaba daya jikinta babu jini sai Ruwan nono?
Dama akwai mutumin da jikinsa yake dauke da ruwan nono sa6anin jini kuma yana rayuwa?
Amsar data yi musu wuya kenan suka taitaye ta zuwa daki. Kwallah ne kawai ke zuba a idon
karima yayin da Inna yaduwa tace. Karima shin dama baki zaman lafiya da matan gidan nan
ne? Sam ta kasa magana zubar hawaye kawai take. Inna yaduwa ta jinjina kai tace; To Allah ya
sauwake tunda abin haka ne bazamu bar shuhuda a gidan nan ba.
ada Hada Hausa Book stories
MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)
¤¤07¤¤
Karima ta girgiza kai da sauri amma ba ta iya cewa komai ba Inna yaduwa tace; A'a ba za mu
barta ba ba zan so sanadinta ki sake samun rashin jituwa tsakiniki da abokan zamanki ba har
yayi sanadin mutuwar aurenki. Idan dai an kwana biyu za a dinga kawota ta yinar miki a koma
da ita amma don Allah kici gaba da halinki na hakuri, shi dama zaman aure gaba dayansa
hakuri ne jigonsa, da zarar aka ce babu hakuri to babu zaman aure. Ba yadda yi haka ta hakura
sai dai abin na damunta a rai ganin ruwan nonon da ya zuba a raunikan Shuhuda amma ta yi
alkunya ba ta tanka ba saboda kasancewa Shuhuda 'yar fari ce. Ita din ma Inna yaduwa ba ta
maida kai kan al'amarin ba ta sa ruwa ta wanke wa Shuhuda raunukan. Da yammaci su kayi
bankwana suka ta fi cike da alhinin abinda ya faru. Bayan sallar magruba Alh Jamilu ya dawo
gida a gajiye saboda aiki da yayi masa yawa. Kai tsaye bandaki ya shiga yayi wanka. Yana
fitowa ya tarar da Binta zaune akan kujera sai huci take tamkar kububuwa. Yana ganin yanayin
ta ya san korafi ne ya kawota dakin don haka ya gumtse fuskarsa ya zauna gefen gado yana
murza mai a jikinsa. Binta ta kara kulewa ganin yadda ya banzantar da ita cikin 6acin rai tace:
Gaskiya Alhaji na gaji wannan matar ko 'yar gwal ce sai haka bare kuma ba abinda ta fi wani
cikin gidan nan. Ya dago kai ya dube ta. Mai kuma ya faru? Cikin isa-isa tace; Kawai ta gayyato

gayyar danginta sunzo sun kama Mas'ud da duka ba don na fito ba kila da kashe shi za su yi.
Domin na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login