Showing 1 words to 3000 words out of 87333 words

Chapter 1 - Nazir Bok Complete Hausa Novels by Janafty.txt

Compiled By Umar Dalha Funtua.







🏻NAZIR🧑🏻*

    _*(The journalist)*_


*(Based on Lov and Romantic story)*
     
    *Na*

    _*Janaf ce*_✍

*WATTPAD:janafnancy*

_*INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION*_


*DEDICATED TO U MY SAHIBA HAFSART HAFNAN....Kisani ki kara sani Ni jameela janaf ina miki so Filla babu algus*




*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



_*Ya janaf iz back again...Akarona uku yana tafene da sabon salo mai Tafiya da salon zuciya...Duk abunda mutum yagani yayi dai dai na suna,kona gari,kona halayyah,to ansane domin kawata lbri....lbrin basira tace nina na sarrafa kwakwalwata wlh juyamin lbri zai sa aga fushina....Janaf*_


_Note:Duk wanda bai fara daga farko ba....to kada sai nayi Nisa kunji ana zuzuta abu a groups kudameni da tambaya ta pc....Wannan karan babu uziri so start from d begining guyzs_




1/2




*Kano*

Zoom Road



Dahanzari ta fito Rataye da yar jakarta a kafadarta tana Fadin"Anty ni nayi Harama fa"Wacce aka kira da Anty ta waigo tana kallonta wata matashiyar macece wacce ashekaru baxata wuce 34 da haihuwa ba tana dukene a tsakiyar falon da babu komai sai wani kafet daya malale dakin fulas ruwan zafine agabanta da kofuna tana tsiyayawa tace"Haba NUSIBA Bafa ki karya ba"Wacce aka kira da Nusiba na kallah matashiyar budurwa wacce ashekaru bazata haura 24 ba doguwa ce tana da fadin fuska hancinta dan daidai da shi shi ba dogo ba shiba gajere ba bakinta nada dan fadi kadan idanunta manyane sunmata kwanya dauke da gashin ido sanye take dawata atamfa riga da zani jikin atamfan green and white sai ta sanya hijabinta fari bakin takalmi ne akafarta sai jakartama bakace wata tecno ce ahannunta taji robali take ta faman dubawa data latsa sai tayi wani tsuwa 😂😂😂



Tafiya tafarayi Tana Fadin"Anty wlh banson na makara....Sai dai in nadawo...."Dawo ki karya Nusiba"Sukaji anfada daga bayansu koda bata waigoba tasan waye cikin sanyin jiki tadawo falon ta zauna shikuma ya kariso dattijune akallah zai kai shekara47 sanye da jallabiya baka gefenta ya zauna yana Fadin"Suwaiba fifitamata ruwan shayi ya wuce tasha da sauri"Da hanzari kuwa tahau fifitamata shikuma ya jawo buredin yana Fadin"kyaje aiki da yunwa Nusiba aigwara kici ko dan yayane...Don fa ke Suwaiba tai tashin Asuba"Mirmishi tayi tana kaloonsu cike da kauna da soyayyah kan ta mikamata kofin tea din ta amsa tana sha shikuma yana gutsiramata buredin kotace takoshi sai yace tadan kara Ahaka dai sai da ta shanye mikewa tayi tana rataya jakarta tace"Kawu zan wuce bani son zuwa na na farko nayi african time...Kagani sai da na sha wahala kafin su daukeni aiki"Jinjina kai kawu yayi yana Fadin"gaskiyane komai mutum zaiyi to yayi tsakaninsa da Allah da jajircewa wurin rike aikinsa da daraja...Ungo dari biyu ce kiyi na mota saura kici abinci kada kifara ki zauna da yunwa"Noke hannu tayi zatayi mgana kallon dayamatane yasa tasa hannu ta karba ta godiya har waje suka rakata suna mata fatan alheri da fatan samun Nasara.



Kwallan dake shirin zubomata ta maida Aranta tana girmama darajam wa"inan bayin Allah da suka inganta Rayuwarta Alhalin mahaifinta na raye yana da abun zai iya mata komai aduniyar nan ammmh kash rashin dace da uba na gari duk shine silar komai....lokacin damuna ne adaren jiya ankwana tsala ruwa kamar da bakin kwarya harda wajajen Asuba shiyasa harta kariso bakin titi babu ko mahalukin data hadu dashi titi kamar anshare tayi tsaye tana addu"an Allah ya kawo yar kurkura cikin gaggawa,tafi minti goma ko kare bata gani ba dayake kuma lokaci tayi sassafe sosai wayar hannunta take latsawa tana duba lokaci tsaki taja Aranta tana fadin"Kai Allah ka azurtamu yanzu inda inada motata mezan tsaya jira'!mtswsss wani tsakin takara ja ammh sai me tundaga nesa ta hangi wata bakar mota range cover ta rugo da gudun bala"i tundaga nesa Nusiba ke tsinema mai motar saboda yadda taga yana gudu kamar zai tashi sama yazo giftata kenan kawai sai ji kake facal!facal!yamata wanka da ruwan kwatamin da ya taru adan gefen titin sakamakon ruwan dakayi ta laftawa jiya tundaga sama har kasa ruwan jar kasan ya wanke har idonta cikin bakin da takaichi Nusiba ke bin jikinta da kallo kan tabi motar da kallo cikin bakin ciki hawaye ya zubomata bata san sanda tace da karfi ba"Allah ya isa kuma wlh ban yafeba"tafada hawayen na ida zubomata kawai ta juya takoma hanyar gida da sauri tana zubar kwallah.






Ilu direba ne ya rage gudun DA motar wata murya abaya cikin sanyi ammh cikin FADA yace"Ilu meke damunkane kana jana kamar kana tuka sa"anka ko kagaji da aikin ne"Aka fada cikin slow voice ilu ya rausayar dakai yana fadin"Am sorry sir Da...Dama..Wata yarinyace na wtsama ruwan kwatami....What"to ka nufin in sauka inbata hakuri kenan ko yaya"Da sauri ilu yace"bahaka nake nufi ba Sir naga....Shout up ur dirty mouth wlh in kasake mgana zan sauke KA...If not kuma"daga haka ya tsuke bakinsa ilu yakada kai kawai ya karama motar wuta aransa yana kara mamakin ina ogansa ya Debo mugayen halayyah na rashin daraja mutane duk da uwa da ubansa kowa yasansu wurin mutumta na kasa dasu.






Da kuka ta shiga gidan kamar karamar yarinya kawu da Anty harsuna rige rigen fitowa turus sukayi ganin yadda jikin Nusiban yadawo kawu yayi karfin halin cewa"lpy kuwa Nusiba ko kin fadine"Tace"Kawu wlh wani dan iskan mai motane ya wtsamin ruwan kwata ammh ko tsayama yaban hakuri baiyi ba"kawu yace"Ashhh....Kinga share hawayenki Allah zai saka miki ke suwaiba kawomata ruwa ta daureye jikinta kawo jakar"Amsan jakar yayi itakuma ta fada dan karamin bayin dake tsakar gidan da hanzari Anty suwaiba ta kaimata ruwan saboda takaichi wanka ta sake agurguje ta fito ta shige daki kamar zata kifa kawu yana kallonta yana girgiza kai yana fadi cikin ransa"Allah yasa karshen wahalarki kenan Nusiba"Cikin minti goma ta fito cikin shigar doguwar riga mai adon ja ajikinta shiyasa ta sanya jan hijabi jakarta ta dauka ta fice tana musu sallama da ido suka rakata suna mata fatan alheri.




Sharada phase3 layin ganduje naga sun Nufa bakin wani tamgamemen gini naga ilu yayi hon inadaga kaina naga ansa da manyan Haruffa *FREEDOM RADION....*security yana lekowa yaga motar da sauri ya wangale get dun jikinsa na rawa abun mamaki koda motar da sulala ma"aikatan na tsaye aharabar gidan harda uban gayyah wato manaja motar tana sulalawa parking space manaja ya isa da sassafar jikinsa na rawa ammh baiyi wani karambanin budewa ba ilu ne ya fito da hanzari ya isaga bayan ya bude yafi minti uku kafin ya fara sanyo kafarsa wata farar kaface mai dauke da gargasa ta fara bayyana sanye cikin wani rifaffan takalmi na fatan damisa sai hannunsa daya zuro fari tas dashi shima sanye da wani agogon Na kamfanin RADO yana rike da jarida ahannunsa kafin shikanshi ya bayyana....Masha Allahu shine abun furtawa domin wani kakkarfan Namjine tsayayye mai tsawo da dan kiba yana da cikar kirji kamar salman khan,fari ne shi tas dashi kamar bature doguwar fuska garesa mai dauke dawasu fitunannun idanuwa masu rikita yaya mata wanda suke zagaye da gashin ido wanda inba ka kallah da kyau ba sai kace picsing yayi hancinsa dogo ne har baka yana da dan madaidaicin baki wanda wani bakin saje yazagaye gashin kansa kuwa saboda santsi da laushi har wani murdewa yakeyi gashi ya kwanta yana kyalli kamar wanda ya shiga relezer kallo daya zakamai kagane yana da kwarjini da haiba cikar halittarsa kesa yake kara kima a idon jama"a wani sirin farin gilashin ne manne a idonsa, sanye da suit masu ruwan toka na kamfanin DKNY ya daure wuyansa da tektie wlh ba mace ba ko Namji bazai iya kallon sa na tsawon minti biyu ba tareda daya sadda kai ba baiwarsa kenan.




kawai sai ya coge jikin motar yana cigaba da kallon jaridar daily Truths ko daga kai ma baiyi ba shikuwa ilu yana tsaye ya kame kamar wani soja wayoyinsane ahannunsa yana jiran umarni manaja yaji kunya ta kamasa matuka ganin yadda Nazir yauma zai kara cimasa mutumci gaban na kasa dashi...Lokaci bayan lokaci kuma yana kallon get kamar mai jiran wani abu,karfi hali yayi ya mikamasa hannu yana Fadin"Brk da zuwa ALHAJI NAZIR"yafi minti uku da mikamasa hannu harsai da hannun ya kusa kagewa kafin yadago hannun nasa cikin yanga da iko ya mika masa sukai musabaha yakuma maida hannunsa ya cigaba da abun da yakeyi manaja yayi tsuru cikin fargaba Sai da yagama jan ajinsa kana ya wurgama ilu jaridar cikin wata irin sanyi murya yace"Manaja mu muke jira ne wai"yafada idanunsa kyar akan manajan inda inda yafarayi kan yace wani abu ya katsesa da cewa"I hop dai wannan karon kasamo kwabi kwabi...Kasan dai yadda muke samun mtsala ko"Manaja yace bakinsa na rawa"am...Am yallabai yarinyar da zakuyi shirin tarene bata iso ba tukun but Nasan yanzu zata....."What"Ya furta cikin daga murya rai bace kamar wanda akacema ubansa ya mutu ya Nuna kansa yana cewa"Ni _*NAZIR FREEKING ADAM GALADANCHI*_ zan zauna ina jiran wata mace,macen ma yar Najeria wanda basusan komai ba sai kidahumanci...No...It porssible wlh duk duniya mace dayace ta isa in zauna ina jiranta komai ko dadewar ta itace UWATA...Wlh bayan ita babu wata mace mai daraja data isa Ni NAZIR ADAM GALADANCHI na zauna ina jiranta"Afusace ya juya ilu ya budemasa mota da hanzari manaja yace"Am srry sir....Dagamasa hannu yayi kan yace'Kaf Nageria baku da kudin dazaku biyani nayi aiki da ku sai dai kawai inayi ne don Nima KASATA CE...Wannan karon ne na karshe da zan dawo nan"Daga haka ya shige mota a fusace ilu ya mikamasa wayoyinsa kan ya rufe motar ya zagaya ya shiga shashen direba yaja da gudu suka fice.




Nusiba dake bawa mai Napep kudi taga wata mota tazo ta wuceta fuu kamar zata tashi sama da harara tabi motar da kallo tana so tagane motar ammh bata ganeba abu daya tagani kuma ta rike shine *NAZIR1* chanjinta ya bata ta karisa ciki da sassarfa kamar zata kifa ammh sai me ganin manaja da sauran ma"aikatan a farfajiyan ne ya dauremata kai ammh saboda karfin hali irin nata yasa ta karisa tana fadin"Am srry sir wlh abun hawane...."Hararan dayake ballamata yadakatar da ita yace cikin bacin rai"Srry for ur self mrs Nusiba domin lattinki yajamana asara kuma kema kinjama kanki...So u can leave plz"yafada yana wucewa binsa Nusiba tayi murya na rawa tace'Yallabai...Ban...bangane mekake nufi ba"Tsayawa yayi yana kallonta kan yace"kinsan dai na fadamiko kowani office ya cika da ma"aikata daman gurbin da zan saki shine na gabatar da wannan shiri to kinyi nukusani har ya Tafi kuma yace bazai kara dawowa ba"Nusiba ta furta cikin halin ko inkula"Ammh yallabai ai yamun uzuri ko sanin nifa ba"a motar kaina nazo ta haya na shiga,"Mirmishi ya mata kan yace"Kin manta na fadamiki sharuddansa bayasan jira ko kadan shi baya jira sai dai ajirasa"Yana fadar haka yakama hanyar shiga ciki da Sauri Nusiba tace"Yallabai shiko waye wannan yana mutum ammh tamkar wani aljani"Bai juyo ba yace"Haka yake wani lokaci jama"a dama kan kirasa da Hakan ammh mutum ne irin mu sai dai ya bambanta damu _*NAZIR ADAM GALADANCHI*_ kenan yaro maiji da tashen masoya na fadin duniya ga Tarin dukiya.."Sororo Nusiba tayi tana kallon manaja har ya kule Nazir"ta maimata sunan kan ta zakuda kafada tace afili"ohon masa shi yasani kana dan adam kace bazaka jira ba tab kanada aiki"Tana fadar haka ta bi bayan manaja chan office dinsa ta sameshi yana waya da dakin gabatar da shirye shirye kan subawa mutane hakuri kan cewa yauma shirin dasuke dako bazai samu ba bisa wasu dalilai ammh ko ke nan zasu ji daga baya.


Bayan ya kammallah wayar ne Nusiba ta hau rokonshi ko katin zabe ya bata zata karanta ita dai tasamu aiki kallonta yayi yaji tsausayinta kan yace"Iz ok kije kidawo gobe zan duba miki inda yadace"Godiya tahau yimai kamar tamai sujjada tana Fita ya bita da kallo kafin ya furta afili"Wasu suna neman adaukesu koda mafi darajan aiki ne ammmh wasu da kudinka ma wulankaci sukema"...Girgiza kai kawai yayi kafin ya kara jawo kan wayar



Sukuwa jama"a masu tsumayin shirin ransu yadan sosu domin wannan ne karo na bakwai ana sa mu su ran shirin ammh har yau bai Samu ba to Daman Samun Nazir ai ba bakaramin abu bane domin kaf Nageria babu gidan radion dabata turamasa takardar gayyata ba ammh ko takansu bai ba ammh kwatsam sukaji Freedom na bada sanarwan zai dunga gudanar da wani shiri maisuna *FREEDOM TAKUCE* daga karfe takwas na safiyar litini zuwa tara na Safe ammh kuma har yau shuru kakeji.


_*To ya kukaga salon acigaba ko Atsaya....Commet dinku kadai nake bukata....Saina dora*_







Commet
share
Vote





*Janaf*✍
[4/11, 2:09 PM] 0mmer Farouk: *🧑🏻NAZIR🧑🏻*

     _*(The journalist)*_

*(Based on luv and Romantic story)*

  *Na*

*Janaf ce*✍

*Vote me on WATTPAD:Janafnancy*

_*INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION*_

*DIDECATED TO SAHIBA HAFSART HAFNAN*


_*Wannan Shafin nakune Anty Sainah Ummu meenal,da ke Swt Anty Sis Naja"atu...Ku sani wlh ina muku son kaunah mai dorewa har Abada*_


```Mamn Afra ko nace maman baddo...Aishatu m yusuf kina ina ina so ki sani ko na ambace ko ban ambaceki ba kina cikin kokon Rainah...Allah yarayamana Afra da baddo cikin Addinin islama```


3/4


Nusiba tana ficewa batayi kokarin hawa Abun hawa ba sai ta rage sauran kudi takoma a kafa tana shiga gidan ta iske kawu na goge yar mashin dinsa zai Fita Anty na gefe tana rike da hularsa tayi sallama ta Shigo gabadayansu suka zuba mata ido suna kallonta cikin kuzarinta ta kariso tana jan kujeran yar tsugunne dake wurin tana Fadin"Kawu har zaka fita"Kallonta yayi yace"Nusiba yana ga kindawo Allah yasa ba latti da kikayi bane yajawo miki mtsala ba"Yamutsa fuska tayi kan tace"Oho musu dai kawu wai koda naje wanda zamuyi shirin tare yatafi wai kajifa kawu wai baya jira sai dai ajirasa"Kawu yace"Topha shiko waye wannan mai tsautsaran hali haka"Nusiba ta tabe baki tace"Nama sanshi wai wani NAZIR ADAM GALADANCHI..."Kawu ya dakata da sauri yana maimata sunan abakinsa Nusiba da Anty suka zuba masa ido kafin tace"Kawu kasanshi ne hala"Kura mata ido yayi kan yace"Dashi aka hadaki aiki"Tagyada kai zatai mgana kawu ya katseta dacewa"A"a Nusiba ki hakura da aikin nan...Bani so sam inga anci zarafinki"Nusiba tace"Meyasa kawu basshi da kirki ko"Yayi ajiyarzuciya yana fadin"Nasanshi Nusiba a office din mahaifinsa nake masinja wlh sam yaron baisan darajan mutane ba bakaramin aikin sabane ya tozarta ka ko ajikinsa sam bai biyo halin mahaifinsa ba"Nusiba ta kalli kawu idanunta ya ciko da kwallah tace"Wlh kawu tunda naji sunanshi naji na tsaneshi ashe basshi da mutumci kawu fadamin yataba maka wani abu wlh in ya tabamaka sai na rama maka" kawu yayi saurin cewa"Bai tabamin ba Nusiba kawai bani son ya tozartamunke ne in har basu chanzaki miki aiki ba kidawo gida munema awani gurin"Nusiba tace"Allah ma yatsareni manaja yace gobe nadawo ya chanzamin inda zanyi aiki"Anty tace"shikenan ma kinga kin huta ammh meza ai da marasa mutumci"Kawu yace"Allah dai ya kyauta.Sallama kawu yayi musu kan yafice suna mai Allah yadawo lpy.




*WACECE NUSIBA*

NUSIBA SADDIQ BUNZA....shine cikakken sunanta ita din yace ga shahararren Manomin nan dake garin zaria wato Alhaji Saddiq bunza wanda yakasance mahaifisa dan jahar kebbi ce akaramar hukumar bunza shima din cirani ya kawosa har yafado zaria,yayi zaman noma tunyana yi da kansa har yakai mtsayin sai da yasa ayimasa yana da matar aure gudaya mardiyah suna kiranta Dada Sai dansu kwara daya Saddiq wanda yataso cikin gatane da tattali mahaifinsa  suna zaune ne a tudun jukum dan gidansu mai kyau da tsari bai rasu ba sai da yayimasa auren fari dayake ba boko yayi ba iyaka kawai yana sauka a allo lokacin shekaransa 23,Aduniya matarsa ta fari Fatsima sunanta ita yar zarian ce agwarbai  Fatsima dai bata da kowa aduniya sai yayanta guda daya mai suna jibril wanda ya kasance jigo agareta Fatsima itama batayi boko ba iyakarta allon yayan natane ma yagama sakandiri.



Auren Fatsima da saddiq auren soyayyah ce sukai susuka hada kansu har iyaye suka shiga ciki...aurensu da wata biyu fatsima tafara fuskanta matsi wurin mijinta saboda ta fahimci mugune kansa kawai ya sani duk da iyayensa ke musu komai ammh dan abu in yasamu bayama son tasan yasamu dan balagun nan kuwa haka zaizo dashi yazauna yanaga Abunsa wlh koda zata mutu bazai bata ba tun Abun baya damunta har ya fara damunta domin ko Abu Alhaji yabada amata shi da Dada zasu hana wlh baza su bata ba,awurina daya take samun Sauki gun Alhaji kuma Allah yazo ya karbi Aransa tundaga lokacin Abubuwa suka fara nisa Fatsima bata samun sauki ta wurin Saddiq kuma bata samu wurin Dada domin Dada irin tsofaffun nan ne masu shegen kwadayi ga sa"Ido da gulma duk wani motsin fatsima tana sane dashi,wani lokacin in Abun ya isheta sai dai tafadama yaya jibo to shima din saidai yabata hakuri saboda bai da yadda zaiyi shima da sana"ar facin dayakeyine yasamu yafada Fce zaria shine in yasamu wani Abu yake dakewa yakaima kanwarsa.



Ahaka Ahaka Fatsima ta haura shekara biyu agidan aurenta ammh ko batan wata bata taba yi alokacin Dada tasaka bala"In sai Saddiq yakara aure wanda ita ta auramasa yar Aminiyarta Saude wanda daman uwarta tatai zuga Dada saboda tana so yarta ta auri shi Saddiq din saboda dai shima likkafa tacigaba domin bayan rasuwar mahaifinsa shi yayi gadonsa babu abunda baya nomawa kama daga shinkafa,masara,dawa,gero,waken soya,gyada dai dai sauransu sai yayi noma gonaki sunfi goma sai ashekara ya tashi da daruruwan buhuhuna, shigowar Saude cikin gidan shi yakara dagula komai domin Saude makirace kuma hatsabibiyace ta karshe ita da uwarta lami sunsan kan tsiya harta Dada shakkarta take Ita kuwa fatsima banzama ya fita daraja kwatsam wata biyu da auransa da saude ciki ya bulla ga Fatsima hakika tayi murna dama kullum addu"anta kenan yabata wanda zata gani taji Dadi Saddiq yaji dadin samun cikin ammh kuma shi Namji yake son ta haifamasa shida Dada domin sundauki buri sun dorama cikin wanda kadan yarage Saude bata hadiyu zuciya tamutu ba ammh lami tace kada ta damu tabasu lokaci kuma kada ta nuna bakincikinta aikuwa haka akayi Saude ta daukema Fatsima komai na gida ita keyi wai sai ta haihu Fatsima tasan kawai dawani abu aranta ammh tabita yadda take cikin tashiga wata na Tara hatta kayan haihu na maza suka siya hatta sunan zai sanyama dan ya riga ya zabi abinsa itadai kawai kallonsu take domin ita fatanta ta Haihu lpy....Ranar wata jumma"a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login