Showing 66001 words to 69000 words out of 87333 words

Chapter 23 - Nazir Bok Complete Hausa Novels by Janafty.txt

Da Inna zainaba tsaye agefensa suna zabgamata harara Nusiba takallesu cike da mamaki kafin tasaki dariyan yake tace"A"ah tare kuke da baki...Sannunku da zuwa inna"Tafada tana basu hanya direba yafara shiga da kayan ya ijiye atsakiyar falon,Jidda ce kan gaba tana wani takun isa bakinta kuwa tana taunan cuwgum cikin rashin aji da babu burgewa kana inna zainaba tatake mata baya,suna bin ko"ina da kallo cikin son gano wani nakasu,shiko direba yana ijiye kayan yai waje cikin mota.




     Nusiba kichen ta Nufa tadauko musu ruwa da lemo ta kofuna tajera kan daya daga cikin farantin ta ta fito falo ta iskesu tsaye kamar wasu sabbin zakaru,center table din dake tsakiyar falon taja ta ijiyemusu akai kafin ta mike tana kallonsu tace"Sannuku da zuwa,kunsha hanya ku zauna don Allah"Tafada tana nuna musu gun zama.

Tsaki mai karfi Inna zainaba taja kan tace"mtewww...lalle ansamu dama ana ta damawa ko"Tafada tana kallon Nusiba,wacce ta sanda kai tana karanto ko wacce addu"a domin tasan cewa zuwansu ba alheri ba ne"Jidda ne ta wani rausayar dakai tace",Mommy just ki manta...Muyi Abunda ya kowomu don kinsan ita bata isa ki zauna kina maida mgana da ita ba"Tafada tana hararan Nusiba.

  Inna zainaba tace"Wane mutum inji mutuwa...Ke ina Nazirun? Tafada cike da isa Nusiba tace cikin sanyin murya"Yana wajen aiki"Inna zainaba tace"To ai zai zo ya sameni don na lura sam yaron baida mutumci"Tafada tana zama itama jidda zaman tayi tana dora kafa daya kan daya tana wani yatsina.

Nusiba dake tsaye kikam,Inna zainaba tadago ta kalleta tana fadin"Dallah malama bacemana da gani....Kinzo kin mana tsaye akai kamar kin bamu ajiya"Nusiba bata ce komai ba tajuya takoma kichen gas din data dora abinci tayi kashe takoma daki ranta nakuna,Inna zainaba tabita da kallo kan tace"Sai kinsha fama,don kin hadu da munafukar kishiya"Jidda tawani bata rai kan tace"Mommy ni wlh bata gabana inyi waje da ita kema kinsan bawani babban aiki bane ko"inna zainaba tace'Nasani mana kawai ina kara gayamiki ne kikara datse damtse.

  Sunan zaune,Babu Nazir ba samantashi dole suka zuba lemon data zubomusu suka sha,ita kuwa Nusiba tana daki taga har la"asar tayi kawai saita fada bayi tayi wanka wannan karon riga da wando ta sanya pick ne wandon shikuma rigar farace ammh tana da zaneen pick ajikinta tana da hula cap ita tadora bayan ta tufke gashinta da band,fitowa tayi falo ko kallon inda su jidda suke batayi ba ammh tace musu"Sannunku..."Tafada kichen galala suka bita da kallo inna zainaba tace"Lalle dan kauye yazo birni...Ke kinga iskanci kiri kiri"Jidda tayi mirmishin gefen baki tace"Mommy mommy...Ki barta tayi lokacinta kalilan ne"

  dama ruwan tuwo tadaura sai kawai ta tada gas din Tuwon shinkafa tayi miyar agushi da manshanu sai ferfesun kan rago,Sai lemon kankana da ta yumusu Suna zaune suna binta da kallo tadinga jera komai kan dininng batare da ko kallo inda suke ba,tana kammallawa tafada bedroom tashiga wanka.

  Nazir da mamaki bayan ya shigo da motarsa compound din gidansa yaci karo da motar gidansu Ammi gabansa yafadai kardai ace Abbu ko Ammi suka zo,bayan ya faka motar ya fito direba dake zaune yana hutawa ya karisa yana gaisheshi cikin mamaki Nazir ke kallansa kan yace"Ammi...Ka...Kawo"Yafada cikin son tabbatarwa,Direba yace"A"a yallabai...Hajiya na kawo ita da jidda"Nazir yace"Hajiya...? Wacece Hajiya kuma"Yafada yana kallonsa shiko direba ya rasa wani kwatance zai masa kawai sai yakama sosa keya,lura da hakan yasa Nazir ya wuce kawai batare da yayi mai mgana ba.

   Cikin amon muryansa ta cikkakun maza yayi sallama ya ratso falon yana sanye cikin suit black and white wuyansa daure da tie wanda ya mtse wuyansa dashi,hannusa na rike da caot dinsa daya kuma yana rike da wayarsa,cikin so da kauna jidda ke bin Nazir da kallo tana mirmishi shiko da mamaki yake binsu da kallon,Kafin ya karisa yana fadin"Inna...Kece tafe'yafada yana zama kandaya daga cikin kujerun falon.

  Inna zainaba tagyara zama tace"eh...mune..Zaka ce ko baka lura da matarka bace"Tafada tana kallonsa,Kallonta yayi kan ya kauda kai bai ce komai ba sai ma mikewa da yayi zai wuce inna zainaba tace"Kai dawo nan...Ina mgana zaka tashi kabarni"Tafada ranta bace,juyowa yayi ya zubamata ido yana kallon inna kan yace"Inna just go to d piont...Sam hayaniya ciwon kai yakesani "Yafada yana gyara tsayuwa ammh fuskarsa ba Annuri,Inna zainaba tarike haba tana fadin"!Oh.ni ce zansa ka ciwonka ko...Don uwarka ni sa"ar wasanka ce"Tafada tana mai dakuwa.

   Tsuke fuska yayi kan yace yana daga hannu"Look inna nifa kinsan halina wlh bana jurema hayaniya just kawai kifadi meke tafe dake period"Yafada kai tsaye,kallonsa inna keyi ammh ganin yadda yasha mur yasa taji shakkarsa saukan da murya tayi tana fadin"To..Naji zauna muyi mgana"Tafada cikin lallaahi zama yayi yana duba agogo.

  Inna zainaba zatayi mgana kenan Nusiba tafito cikin shigar wata bakar doguwar riga kirar Armani tayane kanta da mayafin kayan kamshin turaranta yafarama Nazir maraba yadago da kansa yana kallonta lokaci daya yana sakarmata mirmishi itama tamaidamai tana Fadin"Sannu da zuwa...tafada tana karisawa ta duka tasakamar kiss a kumatu kafin ta amshi coat dinsa da wayoyinsa zata wuce kenan Yasaka hannu ya jawota tafado gefensa cikin wani yanayi take kallonsa shima ita yake kallo kan yace"Stay wit me..."Yafada cikin saukin murya.

  Inna zainaba ta saki baki kan tace"Kai meye haka...Mgana fa nace zamuyi shine kakiramin wannan baren"Nazir yace"Inna yanzu fisabilillahi Matatace zaki bude baki kice bare ce"Yafada ransa yadan baci, Inna zainaba tace"Kai badai rashin mutumcin naka zaka nuna min ba,inamaka mgana kana kokarin rainamin wayau",Tafada tana hararanshi.

  Tsam yayi yana kallonta kan yace",Look inna...Wlh indai bazaki fadi meke tafe dake ba zamu tashi mu baki guri,Nusiba fa matatace daban da kamanta ammh kina kokarin nuna kamar bakison komai ba"yafada kansa tsaye Inna tadake zaune ta bi Nazir da kallon mamaki Nusiba ta mike taba cewa"a"a N hrt bari na shiga cikin inkun gama nadawo"!Tafada tana kallonsa hade rai yayi kan yace'Bani son gaddama...Kikoma ki xauna"Ganin yadda yahade rai ne yasa Nusiba takoma ta zauna.

Jidda ta kalli Inna zainaba idonta yakawo kwallah ta gyada mata kai,Inna tace"Hmmm...Dama matarkace na wanke nakawomaka tunda naga alaman cewa ka raina mutane,inkana da tunani ai itama yanzu tana da hakki akanka,kamar yadda zaka tsare na wannan abar itama haka zaka tsare nata...Ehe.."Tafada tana wani gyara baki.

  Rike baki Nazir yayi kafin yace"Gaskiya inna wani lokacin baki abu da tunani gaskiya"yafada kansa tsaye ba inna zainaba ba hatta jidda da Nusiba sai da mganar ta shigesa Shiko ko ajikinsa illa ma cigaba da  cewa"Haba don Allah kudinga yin Abu da tunani ma,awannan dan gidan ne zan ijiye mace fiye da daya,kuma who force u to bring her here....Kibarta chan ai baki fini sanin haka ba ko"Yafada yana kallonta bai bata daman mgana ba yakarisawa dacewa'Take her back...chan zata zauna ba nan ba,ammh nan gidan is for one wife....Kuma itace my Nusi"Yafada yana kallonta kan ya mike yana fadin"Inna safe landeed agaidamana su Abbu sai munzo.

Inna zainaba da bakinciki da takaichi suka mata rufdugu lokaci daya batasan sadda tamike tana fadi cikin tsawa"Kaci ubanka Nazir..Kagamin dan iskan yaro mara mutumci har kamar ni zaka kallah kace ban Abu da tunani oh shiyasa kazaunar dawanan banzan matan naka don kacimun mutumci ko,to wlh tallahi baka isa ba kuma ko uwarka Fatima bata isa ta hana jidda zama anan gidanba"Tafada cikin fushi cak Nazir ya tsaya bayan ya juyo ransa abace yatako zuwa gaban inna yana kallonta cikin bacin rai Kan yace yana mai daga mata hannu",Look inna wlh kija girmanki kin ganni nan bantaba sa baki game da rashin da"an dakike Ma Ammi ta ba bawai don bana jin zafi bane a"a ni am a simple Man bani son duk Abunda zai dameni...yadakata kan yacigaba da cewa"And bazaki zo gidan danta kina cima mata mutumci ba kana kina cima my Nusi ba,bilayil lazi zanmiki Abunda har ki mutu bazaki manta ba so plz take ur time"Yafada yana kada mata hannu.

Ai hannu inna zainaba ta dora akai tana kuka take cewa"Wayyo nikaina...Ni Nazir kake zagi ni kake zagi kan wanchan banzan yarinyar"ko kallonta baiyi ba ya juya zai wuce jidda na ganin haka sai tafadafe hannu akirji tana wani kakari da sauri inna zainaba ta isa kusa da ita ta rikota tana fadin"Shikenan zaka kashemin ya...Wlh in ta mutu ta dalilinka kotu ce zata rabamu"Tafada tana jijjiga jidda wacce take wani kafewa tana fitar kumfan miyanta.

Nusiba tayi saurin wurgi da rigan Nazir dake hannunta ta isa ga jidda tana kiran sunanta,Nazir dake tsaye kawai sai ya saka duka hannuwansa a aljihunsa yana kallonsu yana dariya,Nusiba taga idanun Jidda na kafewa sai tadago tana fadin"plz ya Nazir kazo kagani kada fa ta mutu"mirmishi yayi mai kayatarwa kan kuma yahade rai yace"Ta mutu mana...Who care"yafada hankalinsa kwance inna zainaba tadago tana cewa"Wlh in dai ta mutu hukuma ce zata rabamu kajima na rantse"Nazir yace"Fine....Nan ai ba gidan Abbu bane balle ace adauki mutum aje asibiti,kuma ma banda batan basira i Nazir adam galadanchi by name  a journalist wanda nayi goggaya a aikin jarida duk da ba low na karanta ba ammh am sure kowani makirci nasan kalansa balle dan wannan little din"yafada hankalinsa kwance,Inna zainaba ta rude tayi tsam tana kallonsa hatta jidda da idonta ke kafe sai gashi ta bude,tana kallon Nazir,Nusiba tayi galala tana kallonsu.

   Dariyan renin hankali yayi musu kan yace"!Wai kuna mamaki ne...bai kamata kuyi mamaki ba domin mai ciwon zuciya  ai ba haka suke  ba"Kallon Nusiba yayi kan yace'Ke...Muje kimin wanka kidaina biyewa ma wannan shirman"Yafada yana zakuda kadafa dole ta bishi suka shige bedroom dinsu.

   Jidda tayi saurin mikewa tana fadin"Mommy mun shiga uku....Yafa ganomu"!Inna zainaba tayi shuru  tana raba ido kan tace"To sai me...Ai dai andaura auran kuma bai isa ya sakeki ba..."Tafada tana mikewa Jidda itama tamike zumbur tana fadin"Mommy ina zaki kuma"Inna zainaba tace"Kano zan koma nayi Abunda yakawoni"Jidda tace"Tabdijam mommy kina nufin nazauna tab..Wlh kafata kafarki don yadda broda Nazir yayi miki kina Tafiya i swear sai ya cimin uwa"Harara Ta sakarmata kan tace"Yama kasheki...Kinjimin sakarci ko,so kika mukoma tare amana dariya ko,to tun wuri ki cire tsoro kema gidan mijinki ne bance ki ragama kowa ba atoh."Tafada tana rataya jaka kan jidda tayi mgana Inna zainaba ta fice ranta na kuna,tana zuwa tafada mota direba yaja suka mika.

   Jidda takoma tazauna kan kujera tana raba ido itakuwa Nusiba Nazir tuburewa yayi sai da tamai wanka gun wankan ma sai daya tsomata ruwa yasata dole tasake wanka,ita ta shiryasa cikin wando 3quater bai ko sanya riga ajikinsa ba,Fitowa sukayi falon hannunsu sarke da juna ayayinda Nusiba ke sanye da wata yar shima wacce iyakarta cinyarta,Jidda take zaune falo yunwa yakusa illata ta tabisu da kallo.

Sai bayan sun isa dinning din ne Nusiba ta lura da jidda ta rike baki tana fadin"La...Ya Nazir kalli ashe su jidda na nan"Da kallo yabi inda ta nunamai mamaki yakamasa baisan sanda ya mike ba ya isa tsakiyar falon yana fadin"Ke....Mekikeyi Anan? Yafada cikin tswa jikin jidda yafara rawa ammh sai ta dake tace cikin fari"Mena keyi kake tambaya? Mutum da gidan mijinsa har a tambayesa"Tafada harda fito da harshe tana lasan gefen bakinta idonta na kan kirjinsa yadda gashi ya kwanta.

  

   Cikin bacin rai da tsawa yace"Ina tambayanki kina raina min wayau...Sa"anki ne ni..Eye"Yafada cikin fushi ganin haka yasa ya tashiga taitayinta,kallonta yayi kan yace"Kin ki bin inna ki koma ko? Kinzabi zama anan ko,inbanda ma kina sauna sakarya ama look like wanda zai zama mijinki shiyasa duk hauka ya dibeki keda uwarki kuka hada wannan banzan plan din wanda even mai bawa fulawa ruwa yasan u r not smart,"Yafada yana haki kan ya cigaba da cewa"!Since kin nace to dole kibi yadda nake so....u already know bani son Tashin hankali keko yar hayaniya ce...Kuma u must be a gud gal don wlh bazan zauna da ke kina min yadda kika ga dama ba at d end My wife dole ki girmamata domin ta isa ne kuma kada ku fara ki kuma min kallon miji don ni bandaukeki mace ba balle har ki amsa sunan matata Abi"Yafada yana xare mata ido.


Hawayen suka ciko idon Jidda takasa mgana tswa yadaka mata kan yace"Bakiji na ne"Da sauri ta gyada kai cewa yayi"Ok...Bakinki ciwo yake yi ko"Da sauri jidda ta bude baki tace"Naji...."Cikin takaichi da bakin ciki Nazir yakada kai yana Nunamata dakin dake kusa dana su yace"Ki kwashe wannan uban kayan naki ki shiga nan,nan ne dakinki kita zama har zuwa ranar dazaki gaji da kanki ki kara gaba"yafada yana nuna mata hanya.

  Jidda tatashi sokai sokai ta fara jan akwatunanta tana shiga dasu dakin Nazir dayabita dawani tsaki yace"Mtsewww... Bush gal.."Daga haka yashige daki afusace ko Nusiban bai kallah ba,ajiyar zuciya Nusiba tadauka kan takarisa kofar dakin jidda tana fadin"Ammh...Ga abinci chan inkina da bukata"Ko kallonta jidda batayi ba duk da ko tana jin yunwa sai da ta kwashe kayanta kaf takai ciki,kana ta tsaya tana karema dakin kallo gado ne da wardrope sai mirror sai tiolet sai kafet shiken adakin ammah babu laifi kam.


Yamutsa fuska jidda tayi kan tace tana bin ko"ina da kallo"Hmm...Garin dadi na nesa..Ai ka makaro tunda kabari igiya uku ke yawo akaina wlh ko zanyi yawo tsirara saina dandani zumarka"Tafada tana wani matse kafa tare da cizan baki,nan tafada gado tana matse matsen kafa domin sha"awace mai karfi take fizganta gashi ba kano bane balle ta fice ta nemi wani ya dan rage mata zafi,datagaji ne tafada toilet tayi wanka kana tafito falon kau tsaye dinning din ta nufa ta sanya filet ta dibo abincin ta koma daki,sai da taci tayi nak kana ta rama sallolin dake kanta,Tabi lafiyan gado.




  Shiko Nazir tsabar haushi ma yasa ko abincin ya fitarmai aka,koda Nusiba ta shigo ta iskeshi zaune kan gado ya tasa system gaba yana sarrafata,Gefensa ta zauna tana fadin"N..Hrt Don Allah kadaina saka damuwa Aranka har ta hana ka cin abinci" tafada tana kallonsa taga baice komai ba kuma ko kallonta baiyi ba"Sai takara cewa"Kada ka manta itama matarka ce...Kuma Amarya  ta....."Shout up yafada cikin tsawa kafin yace"Plz...ur way here"Yafada yana nuna mata hanya fita fuskarsa babu Annuri,Tsam Nusiba ta mike tana cewa"bakomai kasan dama ita amarsu bata laifi'Cize baki yayi kamar ya rikota sai kuma ya fasa,kichen takoma tadafama kanta ruwan lipton tasha hankalinta kwance tazo ta raba gefensa ta kwanta aranta tana fadin daga Taimako Sai Abu  yadawo kaina.











*Comment*
*Share*
*Vote*












*JANAFI*💋
[4/11, 2:16 PM] 0mmer Farouk: *INTELLIGENT WRITERS ASSO*📝

```{onward together}´´´

*NAZIR*
_*(The journalist)*_

*Based on luv and Romantic story*

 
*Na*   

*JANAF CE*✍

*SADAUKARWA GA SAHIBA HAFSART HAFNAN*






36/37


      """Kusan Raba dare Nazir yayi yana faman aiki kan system kafin barci yafara fixgansa ya tattara komai ya ijiye,bayan Nusiba yakoma ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya,Rumgumeta yayi tareda zagoyo da hannumsa kan cikinta ya mtseta suka cigaba da barci.

   Koda da safe ma Kim Nusiba tatashi da rai taki ko kallon Nazir shikuma yanata so suhada ido tunda yasan laifinsa ammh taki yarda ficewanta tayi tatafi kichen tahada musu breafsat koda tadawo daki,ta iskeshi daure da tawul zai shiga wanka shigowanta yasa ya isa gareta sai ji tayi ya rumgumota ta baya,ajiyar zuciya tasaki kan takara hade rai.

  Mirmishi Nazir yayi kan yace"Mena yi wifey...Yau aka ki ko kallona balle azo Amin wanka na tafi aiki"Kwace kanta Nusiba tayi bai ankara ba tajuyo Fuskanta babu Annuri tace"Kaje Amarya jidda ta maka..."!Tafada kai tsaye tana kokarin wucewa ta gefensa,hannu kawai yasa ya turata ta fada kan gado,tana kokarin tadowa yabita yaddane kallon juna suke cikin rashin hayyaci kan ya dalle mata baki yace"Yaushe kikayo Rashin kunya"yafada yana mtsameta kirji har sai da tayi kara marairaici fuska tayi kan tace"Ni...Kadagani..Wlh..Kamanta abunda kamin jiya"Tafada tana kalloshi,..Menayi miki"yatambayeta yana kokarin zaremata yar rigan dake jikiinta bata fuska tayi kan tace"Ba korata kayi ba"Tafada harda Tura baki.

   Bakin yake shafawa da hannu kafin yamaida bakinsa gun yafara kissing dinta in A romantic way tun Nusiba tana turjiya har dai tabada kai bori yahau,bayan komai ya kamkama tare suka fada wanka bayan sunyi na tsarki suka fito,ita ta shiryasa agurguje saboda ya makara,ko breasfsat ma tafiya yayi dashi saboda sauri.


   Duk Abunda ke wakana jidda na jikin wimdow dakinta tana kallon komai har zuwa fitowan dasukayi rumgume da juna har rakasan datayi kyabe fuska tayi kan tace"Hmmm..Tabbas yarinyar nan sai na gyara mata zama don naga kanta narawa ita a dole miji na kulata ko"Kan gado takoma kan tajawo waya takira inna zainaba sun dade suna mgana kuma duka mganan yadda zata ci uban Nusiba ne da yadda zata jawo hankalin Nazir zuwa gareta.


  Wunin Ranar ma Nusiba bata zauna afalo ba hakama itama jidda sai bayan la"asar Nusiba tafito ta shiga kichen dora girki kuma alokacin ne Jidda ta fito cikin shigan wata arniyan riga iya cibiya wanda rabin nonuwanta ke waje,dan wando ne tasanya amtse kamar tayi ihu yayage gabadaya cinyoyinta awaje ta zubo kitson atta din kamar wata mahaukaciya,Tana taunan cimgam kamar wata sakarya fitowa tayi ta kure wata tasha ana wake wake harda taka rawa wai duk don Nusiba takula ta,itakuwa ko kallo domin duk Abun Nusiba bata kula wanda bai kulata ba.





     Tana kammallah girkinta dama sakwara tayi da miyar wake wacce taji hanta sai kunun aya bayan tagama jera komai itama takoma daki tafada wanka tadade tana dirzan kanta abayi kan tafito,itama cikin wata arniya riga ta fito wacce da kadan ta wuce cibiyarta rigar hannu vest gareta kuma sharasharace domin kamar kyallan tatane komai ana gani saboda Nusiba tanunama jidda tafita iya iskanci pant kawai tasanya ko bra bata saka ba,gashinta kuwa a tsakiyan kan ta cogeshi fuskarta babu wani make up ammh kallo daya zaka mata sai ka kara.



turaren humra wanda Anty tabata shi tadinga ma kanta bari dashi,tana cikin fesawa taji dirin motar Nazir sai da tadan dakata kana tabude kofa ta fito daidai lokacin daya danna kararrawan kofa Jidda ta mike tana Tafiya ta isa ga kofa Nusiba kuma tana bayanta tana tafiya daidai Jidda ita ta bude kofar cike da yanga tana Fadin",Sannu da zuwa.."Tafada tana kokarin amsa briafcase din dake hannunsa kawai sai taga yasaki baki yana kallon bayanta juyawan dazatayi taga Nusiba tsaye tana sakin murmishi,kafin tagama mamaki taga Ya Nazir yasaki jaka yana fadin"Wow....my Angel...Kice haka...Oya come here"Yafada yana waremata hannu aiko da gudu tafadamai tana rufe fuska wai ita kunya,Jidda dake tsaye da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login