Showing 36001 words to 39000 words out of 87333 words

Chapter 13 - Nazir Bok Complete Hausa Novels by Janafty.txt

mgana sai yace kungama mgana,ko karyan sane"Nusiba tadata gano wautan datayi tace da sauri"A'a...Ammi banji ki bane dazun,eh munyi mgana dama yanzu nake shirin gaya miki"Kallonta kawai Ammi tayi bawai don ta yarda ba tace"shikenan,sai kikoma ranar monday kenan,motar ki ma tana haraba ta iso in kinfita kiduba"godiya tashiga yima Ammi itakuwa tana cewa tabari bata so ai koda bata auri Nazir ba ita din yata ke agareta.


Koda Nusiba takoma gidanta afalo tazauna karo na farko kenan tunda aka kawota gidan tagumi tayi tana mamakin dakara jinjina tsanar da Nazir kemata tunda harzai iya tafiya bata sani ba,kuma har ya ingayamata karya,wata zuciya tace"toke meye naki tunda kinsamu yabarki ko banza ka rage zaman kadaici.Dawannan Tunani ta share tunanin Nazir takama sabgarta tun zuwanta gidan yau tafara girki danwake tajefa don shi take sha'awa,tunda store dinta cike yakeda kayan abinci wanda basu da iyaka,tafito da filet din danwaken kenan taji sallaman Rahma ai da sauri ta ijiye shi kan kujera ta nufeta suka Rumgume juna,sakin ta Rahma tayi tana mata hararan wasa tace"sannu da mantawa da mutane"Nusiba taja hannun Rahma tana Fadin"haba dai kema kinsan bahaka bane,kinsan banda waya ko"tafada lokacin dasuke zama.


Rahma tabi Nusiba da kallo yadda cikin sati daya tacanza tayi kyai da kiba kichen Nusiba tashiga tadaukoma Rahma maltina da ruwan faro mai sanyi tazo ta doramata kan center table din dayayi ma falon kwanya,tana fadin"Hala daga wajen aik kike"Rahma tagyada kai Nusiba dake zubamata ruwa tace"Nima ranar mondaya zan dawo aiki"tafada tana mika mata ruwan, karba tayi tasha kan tace"Wani aikin kenan? tafada cike da mamaki Nusiba tace"wani aiki nakeyi"tafada tajawo filet dinta na dan wake tana Fadin"kinzo nayi abunda baki so'Rahma data suma saboda mamaki tace"wai kina Nufin yabarki kicigaba da aikin ki"Nusiba tagyada mata kai jinjina kai kawai Rahma tayi kan tace"Har komai ya daidaita kenan.

Nusiba tamata wani kallo kawai ta basar itakuma lura da Nusiban bata son mganar yasa ta kyaleta sai ma cewa datayi tace"ke nifa kisamin Abunda zanci yunwa nakeji"Nusiba tayi lum da ido tace"Kishiga kichen kisamama kanki malama,don ni kinga wannan har gobe bazan nemi komai ba"tafada tana nunamata filet din danwaken,Rahma batace komai ba tacire mayafi tafada kichen indomie tadafa hade da hanta tazo tazauna sunaci Rahma na bata lbrin Abunda su inna saude sukayi dasuka zo mirmishi kawai Nusiba keyi kewar Innanta ya isheta zatama Ammi mganar waya saboda dama tatace dazata taho tabarma Innan nata.

Sai yammah Rahma tayi shirin Tafiya tarakata suka gaisa dasu Ammi da Anty kana ta nunamata jan motar 306 dinta tasa albarka kana suka rabu cikin kewa..Gun Ammi takoma suna hira kuma koda wasa bata bari har yanzu Ammi ta fahimci irin zaman dasuke da Nazir ba.










*ZARIA*



     """Tun bayan dawowarsu inna Saude gidan Nusiba bata zauna ba itada uwarta lami yawan gidan boka,duk inda sukaje sai ace musu ankasa ganin komai game da yarinya gawani duhu nan ya lullebata wanda Allah bai basu ikon ganin komiye ba,sai wani boka dan dugaje dayake chan maradi niger wata kawar yawace yawacen lami ce ta musu Hanya,Saude bata da kudi ammh hatsin baba tasata ta saida tahadama Lami kudi tatafi maradi.


Suna zuwa boka dan dugaje yafara zayyana musu lbrin Nusiba da uwarta har karshe da asirin dasukama uwarta da ita kanta daga karshe boka yace"Allah ya karesu sunyi saurin zuwa,dabadon haka ba komai na gabda lalacewa"Ammh tunda sunzo to su tabbata komai yazo karshe,Buga kasa yahau yi yana wani surutai ga wata karya gabansa dayayi surutan sai ya kalli Kwaryan cikin razana yake jan baya,yayi yafi sau uku ammh Abu daya yake gani,wato hoton Nusiba ta bayyana tana zaune afalonta ammh Abun mamaki wani haske ne yake nannadeta da ita wanda yake ta washewa Har Nazir ya bayyana,boka yayi ta buge bugensa kan yagano waye Nazir ammh abu yaci turashi shiyasa ya karkace ya kyalkyace da dariya yamikamusu wani laya,yana Fadin"kunga wannan to kuje ku binne shi cikin gidan data ke,zaku ga Abunda zai Faru"jiki na rawa lami ta amsa tareda zubemai kaf kudin datazo dashi suka fice.

Cike da Nasara lami tadawo ta mikama saude mganin tace"sai kin san yadda zatayi ya isa gidan Nusiban"Saude ta amshe mganin tare da kudirn cewa da kanta zata gidan Nusiban ta aiwatar da aikin.




*Monday*

   "monday tushen aiko ko bature na tsoronki tun safe Nusiba tagama duk shirinta dayake gidan ba datti yakeyi ba sama sama ta share sai wanke wanke datayi tana kammallawa tafada wanka agurguje ta shirya cikin wata Atamfa super wax mai ruwan shudi,tayafa mayafinta shima mai ruwan shudi tarataya karamar jakanta tafito kofar falon kawai taja ta rufe,sallama tama sallau tafice,gidan su Ammi tashiga suka gaisa,kana tashiga gun Anty tamusu sallama motarta ta shiga tabata wuta( Dama Ammi takoyamata in sunfita tare) musty ne shima dazai tafi asibit yake faman mata tsiya dacewa sabon shiga dariya kawai tayi batace komai ba tare suka fice tana gaba yana baya,ganin yayi tafiyan nata na yan koyo ne yasa yakara gaba yana mata hon da jinjina.


Bata dade da barin layin Ba saude mai Napep din daya sauke ta,tana raba ido,tana so ta tantace gidan tsakanin na su Nazir dana Nusiba ganin tsayuwa ba bazai fissheta ba yasa ta karisa kamar zata na farko sai kuma ta karisa na biyu tahau bugawa sallau ya bude da sauri,saude ta washe baki tace"sannu mallam"


Kallon sama da kasa yake mata kan ya amsa da "yauwa...Lpy? yafada yana kara bake kofan Saude tagyara tsayuwa tareda da zaman mayafinta tace"Don Allah nan gidan Nusiba ne"tafada idonta kur akanshi sallau yace"eh...nace lpy" yafada cike da kosawa.

"Saude tace"ni innanta ne gun tazo daga zaria"Kara kallonta Yayi yana mamakin wannan almajiran matan ne dangin Hajiya tab,cemata yayi "bata nan yanzu tafita aiki"Saude tawashe baki jin cewa Nusiba bata nan sai tace"bakomai zan jirata"kan yasamu zarafin mgana tayi wuf ta bangajeshi tashige ciki,cike da mamaki da tsoro yabita da kallo jin kofar falon akulle yasa tazauna abakin kofar tana kallon sallau shima yana kallonta.


Kusan awa daya tana xaune tana add"an Allah yasa ya tashi illai kuwa sai ya tashi yashiga dan dakin dake gefe yana shiga tayi wuf ta mike ta isa ga bakin windon falon inda shukan fulawa suke taciro yar wukan datake cikin lalitanta tahau haka,tanayi tana waige,shiko Sallau ganin yadda saude ke fiki fiki da ido yasa yasan bata da gaskiya shiyasa yahada wayau yashiga ciki ammh sai ya labe abakin kofa yana lekanta,yana gani tayi haka ta ciro wani laya tasanya ciki ta maida kasa ta kakkabe jiki takoma tazauna kamar ba ita ba.


Sai daya bata lokaci ya fito fitowarsa badadewa saude ta mike takariso tana Fadin"bari naje gidan wata goggonta nan gadon kaya..Zan dawo anjuma lokacin tadawo"kallonta kawai sallau yayi harta fice tana fita ya shiga daki yadau fatanya ya nufi inda yaga tayi haka yahako layan yazo yasamata wuta yana Fadin"Kai Allah karabamu da sharrin mutane,yanzu ita hajiya mai tama wannan matarnan ne"ganin baida amsa yasa ya tattara tokan yazuba abola yakoma yazauna yana mamaki.


Saude kuwa na fitowa tasha tayi tahaye motar zuwa zaria ran kal ,saboda gani take kamar komai ya kare.



Nusiba cike da kwarewa take driving harta karisa Gidan radio koda megadi ya budemata get ta sulala ciki,tayi parking tafito cike da takun Natsuwa,mutane sai kallonta suke cike da mamaki da burgewa wa"inda basu iya gani su kyale suna ta mata fatan alheri da kuma cewa ina nasu kayan bikin dariya kawai take musu tace"duk mai so yazo gida ya amsa,office din manaja tafara isa wanda sai da ya murza idonsa daya ganta shiwai bai yarda ba,dariya takama Nusiba Manaja yace"What all dis Nusiba kodai mafarki nake"Nusiba tace"ba mafarki bane da gaske nadawo bakin aikina yallabai fatan ana maraba dani"cikin rawar baki manaja yace"why not Ranki yadade😂😂😂" _Wai ranki yadade lalle manaja an iya ladabin dole_

Nusiba tayi mirmishin dajin sabon sunanta da yallabai yakirata dashi ta dade affice din yana fadamata shirin nasu na FREEDOM TAKUCE fa yasamu karbuwa masu saurare suna rokon tacigaba da musu shirin don Allah.


Nusiba ta kalli manaja tace"To yallabai nikadai zan dinga yi kenan"manaja yace"yadda kika tsara kozaku cigaba dayin ne keda yallabai,don naga yanzu kunfi kusa"yafada cike da zolaya waskewa Nusiba tayi tace"A"a bazai yuyu ba,cos shi aiki yayi mai yawa saidai anemo wani ko wata"Manaja yace"ok babu damuwa zuwa gobe dai komai kenan zaki ji'sallama tamai tafice yabita da kallo yadda tazama classic baby.

Duk inda tawuce kallonta ake ana gaisawa da ita ana mata fatan alheri,Aranta kuwa dadi take ji tace afili"ko yanzu kasuwa tatashi dan koli yaci riba wlh"tafada tana mirmishi ita kadai.

Chan ma office din su Haka akaita mata surutu gawani sabon girmamawa da ake mata duk inda ta gilma itakuwa kanta na fashewa u know irin kowa son mgana yake da ita kusan feeling din,yau shirinta na Muma ya"ya ne kai tsaye tashi da aka bude layin waya zo kuga mutane sai fatan alheri ake mata da fatan nasaran rayuwa,ranar farincikin da Nusiba ta tsinci kanta baya misaltuwa karfe shida tatashi aiki,yau ita tayima Rahma lif ta ijiyeta kan Hanya tawuce.




  Koda takoma Ammi batanan tana asibiti,gidanta tawuce suka gaisa da sallau yamata barka dadawo ammh bai fadamata zuwan saude ba,agajiyae take wanka kawai tayi taje kichen tadauko sauran furanta da musty yasiyomata jiya tasha tazo falo tazauna kan kujera tana kallon mbc ana wani seris film Sakaratus Zauji tana yi tana shan sassanyan furanta cikin kwanciyar hankali.




°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°



      """"Cikin sati daya sunan Nusiba ya famtsamu akano domin shirinsu na Freedom takuce,yadawo da karfinsa sau biyu ake sati tareda abokin aikinta Nura Dabo,wanda ada ma"akacine a liverty radio dake kaduna yadawo nan,tare suke gabatar da shirin ga shirinta na muma ya"ya ne daya samu karbuwa fiye da zatonta wanda yanzu ma ankara musu lokaci yakoma 30mins  saboda yadda shirin ya karbu gun jama"a,Ammi ita ta siyamata tamfatsetsiyan wayan ta i phone 7 dashi suke waya da innanta kullum tana jin Halin data keciki duk da bata gayamata ammh wayan dasukeyi kadai ya isheta sabida hakan nasata Nishadi.












*Comment*
*Share*
*Vote*





   *Janaf*💞
[4/11, 2:13 PM] 0mmer Farouk: *🧑🏻NAZIR🧑🏻*

     _*(The journalist)*_

*(Based on luv and Romantic story)*

  *Na*

*Janaf ce*✍

*Vote me on WATTPAD:Janafnancy*


© _*INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION*_🖊



*```DIDECATED TO SAHIBA HAFSART HAFNAN```








*AM SICK...NEED UR PRAYER*



20/21



    """"""Lokaci ne fa ke Tafiya cikin haka kwanakin mutuwarmu ke ta karatowa,gashi har Nazir yashafe sati biyar ko duriyansa babu wanda yasake ji,kullum sukayi waya da Abbu sai ya yanka masa karya yace aiki ne yamai waya,kuma nunawa yake yana waya da Nusiban,itama ta iya duniyanci sai tacemasu Ammi yana gaishesu sukuwa suyi ta jin dadi,musty ne kawai yasan komai cos yafi kowa sanin waye Nazir in yace baya son Abu.



Inna zainaba tunda dukiyarta tadawo hannunta,Alhaji hassan kanzil baicemata kuma itama bacemai ba,ita dawata kawarta hajiya kilishi sukayi mgana kan zata dinga zuwa dubai saro kayan domin tafara kasuwanci,shibaima da lbrin harsaida visan tafito take fadamai,saboda takaichi adawo lafy kawai yayi mata don bazai iya hanata ta hanu ba,sai da tashafe sati kana tadawo da niki nikin kaya,wanda dafarko kamar abun arziki hajiya kilishi takawo kawayenta yan duniya suka jide kaya bashi,kana itakanta kilishin Achan dubai din saida ta ranta four hundred thousand agunta.

Jidda kuwa ciwon sone yakamata haikam na Nazir,don tun Ana daukan Abun wasa yazo yawuce tunaninsu wani ciwo datayi har jininta sai da yahau,ada inna zainaba tayi alqawari fita daga sha"anin yaya da ya"yansa ammh kuma saboda yarta zata koma tamai mgana ta karshe inyaduba Allah da zumuncinsu to,inkoma bai duba shikenan,itakan tayi iya bakin kokarinta.







***********

Yau weeked ce bata je Aiki ba sai wajen 12 tatashi daga barci sanye take dawata Nigt gown pick colour wacce iyakarta gwiwanta hannun vest gareta tanada taushi talafe ajikinta kanta kitson kalabane kanakana,sun zubo bisa bayanta,har suna rufemata ido,tanayi tana gyarawa silifas dinta tazuro tana hammah ta nufo falon,saboda yunwa data keji kichen tayi direct tabude fridge tadauko ruwa tasha,gas ta kunna tadora ruwan zafi ganyen Na"a Na"a tasanya aciki yana tafasa ta juye afulas,kana tafasa kwai guda hudu tasoya tasanya a filet,Na"a Na"a tazuba akofi tadauka tanufo falo cikin rawan jiki ko kallon gabanta batayi saboda yunwa,kan daya daga cikin kujerun tama kanta mazauni tadora filet din kan cinyanta tafara cin kwan tana hadawa da Ruwan Na"a Na"an dake Hannunta tayi nisa acin Abincinta ne daga cikin faskeken tibin bangon daya kusa cika rabin dakin tahangi kamar mutum zaune kan kujeran dake fuskantata,sanin itakadai ne yasa tashare ammh sai me tana kara kallo taga fa tabbas mutum ne kallon gun tayi da sauri aiko taci karo da mutum kwance kan kujera ya mike fararen kafafunsa masu cike da gargasa kan kujera bakin wando ne ajikinsa,sai farar vest yasanya hannunsa ya tallafi kanshi ma"ana yayi filo dasu idanunsa a lumshe suke,

    """Jikin Nusiba yafara kyarma filet din kwan yafadi daga jikinta kofin dake hannunta yafadi kasa yafashe hannu tasa rarufe bakinta tana shirin saka ihu cikin karfin Hali take maimaita innalillahi wa"inna Alaihirraju"un cikin rawan jiki,ammh ko gizau baiyi ba ita atunanita aljanani ne yazomata asuffar Nazir shiyasa dataga ko motsi sai tatashi dagudu tashige daki harda bame kofa tana kuka.


Nazir da kwance tun fitowarta yaganta Aransa yana mamaki yadda yarinyarnan ta waye ji yadda take yawo cikin gida,an samu guri,har shigan ta kichen da fitowarta da tsoratan datayi duk akan idonshi,sai da tashiga daki yagyara kwanciya Aransa yana fadin"villager girl kawai"



itakuwa Nusiba bayan tagama zikirin jiki tasake bude kofa taleko still tasake ganinshi ammh kuma sai ayanzu ta lura da kafansa irin na mutane,wata zuciya tace"ke kila fa shine,tunda kinsan inzai dawo basani zakiyi ba"gyada kai tayi tasalalo tazo har tsakiyar falon tana lekenshi,shiko yana kallonta ta gefen ido,so take tatabbatar da shine ko bashi bane.


Tana nan tsaye taji muryansa cikin sanyi yace"Karki kara kallona..."da sauri tajuya ko waige ta shige daki hankalinta yakwanta tunda tattabarta da shine,shiko mamaki yake yadda yarinya karama ta iya karema Namiji kallo, haka kamar wata mayyah.





Tunda tashiga daki ko lekowa bata karayi ba,shiko Nazir dayayima kano shigan safe,ganin weekend ne yasa bai shiga bangaren su Ammi ba yashigo nan,yau kawai yaji yana ra"ayin zama afalo karo na farko.



Sai bayan sallah tafito falon babu kowa,alamun yatashi kenan,gyara gun da glass din yafashe tayi,kana tafada kichen tafara girki,tuwon semo tatuka musu da miyar danyen kubewa wanda aka murje tsokan kaji aciki aka markade,kunun aya tayi musu tasanya masa kankara yai sanyi acikin wasu manya kulale tamulmule tuwon cike in leda tajera,tasanya cikin wani babban kwando,wanka tafada agurguje tafito ta shirya cikin wata doguwar rigan shadda blue wacce ta amsheta batayi make up ba hoda kawai ta sanya tayafa wani farin mayafinta,tasanya wani flat shoe takimkimi kwando ta fice,gaisawa sukayi da sallau megadi kan tafice zuwa gidan su Ammi.





Tana sallama cikin falon ta iske Ammi zaune kan kujera gefenta Nazir ne zaune gefe ya kishingide idanunsa a lumshe kamar mai barci,da sauri Ammi ta mike tatarota tana amsan kwando tareda cewa"Dota kina dauka Abu mai Nauyi haka"tafada tana sauke kwando Nusiba tace"Ammi forvurite dinki nayo miki"Ammi ta washe baki tana fadin"Aiko ngd sosai dota Allah yayi miki albarka"Nusiba ta amsa da Amin.



Tare suka kama suka kai kichen kafin sudawo falon,Nusiba tana kallon Nazir tatabe baki tace"kai wannan mutum akwai lalaci,mutum kulllum kwance"itama kan daya kujerun tahaye taja rimot tana sarrafa talabin Ammi tazo tazauna suna hira jefi jefi cikin Hirar ne Ammi tace"Dota kinga yadda shirye shiryeki yasamu karbuwa kuwa? tafada tana kallonta Nusiba tamaida hankalinta kan Ammi kafin tace"Da gaske Ammi"Tafada tana bayyana murnan ta afili"Ammi ta gyara zama tana cewa"Wlh kinga a hopt dinmu wlh haka ake ta zencenki mutane sunajin dadin shirinki expecially na muma ya"ya ne"Nusiba ta washe baki Ammi tacigaba da cewa"kinga wata doc Tani asibitinmu wlh tana sonki sosai tace u are very smart"Nusiba tayi dariya tace"Kai Ammi duk kinaji"Ammi tace"ita take fadamun ma ai tasan ke matar Nazir ne tazo bikinku aie"Nusiba tace"Allah sarki"Ammi tace"Nima zan fara saurara insha Allahu"




Duk hirar dasukeyi akunnen Nazir takaichi yakusa kasheshi,wai har yaushe yarinyarnan take balle har tayi suna agari har ana zuzutata ana labrinta,Abun ban Haushi itakuma Ammi harda bada lbri tana dariya,gabadaya yana zaune ammh kamar yayi kuka saboda Haushi.





Mikewa yayi tareda sakin tsaki mtewwwss yayi nufi hanyar dakin Ammi yana wani tafiyar takama,Ammi da Nusiba suka bishi da kallo Ammi tace"Kai kuma kaidawa,kai da baka raina abun jin Haushi" ko kallonsu baiyi ba yawuce cikin kan gadon Ammi yadane yana kunkuni wai duk sun hanasa hutawa da shirmen surutunsu.




Tuwon da Nusiba tayo shi suka hadu sukayi dinner harda kawu da Anty Abbu yaci tuwon sosai shida kawu suna santi,Ammi harda na rage nagobe da safe wai zata dumduma,musty kuwa kunun aya yatafi dashi yaita sha Abunshi,shiko Nazir daya fita sallar ishha"i daga chan gida ya wuce ko sake dawowa baiyi ba,sanin hali yasa ba wanda ya nemeshi.




sai wajen goma kowa ya nufi bangarensa Musty yaraka Nusiba har gida kana yakoma,wanka kawai tayi tabi lafiyan gado hankalinta kwance.



To Haka wannan weekend din yakare tsakaninta da Nazir gaisuwa,wanda bako da yaushe yake amsa mata ba sai yaga dama,wani lokacin itama ba kasafai take gaisheshi ba,sai sunyi mugun kilashin Yanzu gabadaya batajin tsoronshi zamanta take afalo sai dai shi ya tashi yashige ciki,itako ko ajikinta,abinci kuwa kullum sai ta girka ta ijiye kan dinning ammh ko kallo bai isheshiba haka zai kwana sai dai ingari ya waye ta zubar shiyasa takama kanta sai taga dama take girkawa dashi.





Ahaka suke har yasake dawowa haka suke,babu ruwan kowa da kowa,bangaren aikinta kuwa sai dai muce masha Allahu domin kaf garin kano ansan waye Nusiba saddiq bunza ake sa domin jajircewanta akan aikinta,itakanta freedom tajawomusu masoya text kuwa awaya har gajiya take kira kuwa shima,ana cewa ana mata fatan alheri.





**********



"""""Kusan Abunda hausawan kance,jiki da jini to hakane tafaru Da Nazir domin Satin dayakoma sai zazzabi amai sai da aka karamasa ruwa karfin hali kawai yakeyi bash ne yadinga kula dashi tunda yahana akira gida afada,to yadanji sauki har satin ya wuce baizo gidaba sai upper week din yazo wanda tun amota zazzabi ya rufemasa zuciyarsa na tashi shiyasa daga Nusiban har Su Ammi babu wanda yasan dawowarsa yana shigowa yahaye sama yana rangaji atsakiyar falon sa ya zube yana ta kwara amai cikin wahala da ciwo.











*Comment*,
*Share*
*Vote*











*Real janaf ce*💕
[4/11, 2:13 PM] 0mmer Farouk: *🧑🏻NAZIR🧑🏻*

     _*(The journalist)*_

*(Based on luv and Romantic

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login