Showing 18001 words to 21000 words out of 87333 words
Chapter 7 - Nazir Bok Complete Hausa Novels by Janafty.txt
Shirin daka Taba gayyata ta akai"Yafada idonsa kur akan Manaja,manaja ya furta cikin Rawan murya"Wa...Wani..shiri kuma yallabai? Nazir yace"na tambayeka kuma ka Tambaye ni"Yafada da wani bata rai,manaja zai yi mgana kenan Nazir yadaga masa hannu da cewa"Bana son jan zencen kafini sanin shirin danike magana..Inaso yanzu ka bada Sanarwan za"a gabatar da shirin yanzu da karfe takwas din nan"Ya kareshe Fada da bada Umarni manaja ya yi kasake yana kallon Nazir kan yace"to yallabai..Kai kadai zakayi Shirin"mirmishin jin Dadi Nazir yayi yana Fadi Aransa anzo gun.
Kai Tsaye yace"Ni kadai aka tsara zan gabatar"Girgiza kai Manaja yayi Nazir ya cigaba dacewa"Da yarinyarnan da aka Tsara zanu gabatar da ita nakeson mu gabatar,koda sau dayane kawai"Manaja yayi jim aransa ya Fadin,koda naji..Marairaicewa yayi yace"Yallabai dadai kayi Hakuri mu samu wata cikin dalibai Masu Sanin makaman Aiki kuyi tare,Nusiba na riga da nakaita wani shashen.
Kallon Da Nazir ya bishi dashine yasa ya mike Da Hanzari har yana Tuntube ya fice dakin continue announce yafara Nufa yafadama wanda ke kan Aikin gabatar da shiryeshirye Alokacin cewa yabada Sanar shirin da"ake ta dako tun kwanaki gashi zai zo yanzu tareda Fittacen Dan Jaridan nan wato NAZIR ADAM GALADANCHI..."Nan da nan kuwa akafara Sanarwa.
Fitowar manaja kenan yaga ficewar motar musty daya ijiye Nusiba ya juya,takama Hanyar office dinsu da sauri ya kwalamata kira"NUSIBA...!cak ta tsaya tana waigowa taga manaja yana Tafe jiki na rawa mamaki yacika,manaja ya kariso yana Haki yace"ke nake Nema wlh.."Nusiba tace"gani yallabai lpy? ya karbe dacewa'lpy lau wlh sai ma Alheri"Nusiba ta gyara tsayuwa tana cewa"Allah yallabai to gutsiramin "manaja yace"yau zaki fara mgana kai tsaye agidan nan...Sabon shiri zaki gabatar yanzu Nusiba kai tsaye"Dafe kirji Nusiba tayi tana Fadin"Kai tsaye kuma yallabai"yace"eh man,don Allah kizo muje..Ba lokaci"yafada yana wucewa Nusiba tai tsaye tana tararradi wani barayin kuma na zuciyarta na cewa"dallah banza kije kinsamu daman dazakiyi suna,garin kano tadau lbrinki"Tunanin haka yasa tabi manaja da Sauri,ilu dake cikin mota yana kallonta yace"Ina ina ma...ina ma zan iya baki shawara danace karki sake kishiga don dai Nasan zuwan nan Naki ne.
Suna Tafe manaja nakaramata bayanin yadda shirin zai gudana ammh sai yasamu kanshi da kin gayamata kowaye zasuyi shirin tare,Sun na isa dakin gabatar da shirye shiryen,farinciki ya cika Nusiba manaja ya nunamata wata kujera dake facin mark ma"ana Abun magana yana Fadin"ki zama ready bari nazo,yafice da sauri.
Sukuwa jama"a na gida dana waje suna jin sanarwan suka tsare suka dake suna jira,manaja koda yaje yasamu Nazir inda ya barsa yadora kafa daya kan daya,yanata latsa wayarsa gyaran murya Manaja yayi kan yace"Ranka yadade komai yazama ready yanzu haka tana dakin gabatar da shiri tana jiranka"Sai da yabata lokaci kan ya mike yana Nunama manaja hanya da hannu,jiki na rawa manaja ya shige gaba yamai jagora.
Nusiba na zaune bakin yaki rufuwa ta gilashin data hangan dakin da mai gabatar da shirye shirye ma"aikatane cike agun wasu suna tsaye,wasu suna zaune,don dai kawai aga ya zata kaya tana chan hankalinta yayi gaba sai da taji manaja nacewa"Bismillah yallabai..."Ahankali tadago kanta caraf ko suka hada ido yana zama akujerar dake gefenta shima da Abun mgana agabansa,cikin mamaki da al"ajabi ta mike tana kallonsa bako kifawa,shiko kallo daya yamata yakauda kai,cikin muryansa ta yanga yace"Bana son dogon kallo...Be carefull Nageria lady"yafada da izgili,lakwas takoma tazauna tanajin jikinta na rawa,gabadaya Farincikinta yatafi zuciyarta na bata ba alheri bane tayi wannan shirin,to ammh in takiyi kenan ta tsorata,kuma tsoro bashi acikin tsarinta,dole zata nunama wannan gayen ita ba kallansa bane.
Gyara zama tayi kan tadaga Hannunta,nan da nan mai gabatarwa ya latsa na"ura yasanya wakar gidan Freedom din wanda tadau tsawon minti biyar kafin mai gabatarwa yafara jawabi kamar haka.
""""_*Yanzu karfe takwas,kuma Adaidai wannan lokacin ne zaku saurari shirin dakuka dade kuna jira wato FEEDOM TAKU CE...Wanda Nusiba Saddiq bunza zata gabatar tare da gayyatan Nazir Adam galadanchi,Ayi sauraro lafiya*_
Yana gama gabatarwa yamai da wakar tadanyi mintina kana aka cire ta,cike da kwarin gwiwa Nusiba tafara mgana kamar haka.
_*Assalamu Alaikum jama"a masu sauraren mu,kamar yadda kukaji mai gabatarwa yayi jawabi, ni dai Sunana Nusiba Saddiq bunza,atare dani akwai abokin Aikina*_
tana kawo nan tayi shuru,ma"ana tabashi dama yagabatar da kansa,Nazir dake zaune kansa aduke yana latsa waya,koajikinsa kamar ma baisan wani abu mai muhimmanci yake gabatarwa ba,bai dago ba ammh cikin sanyin murya tace"Na fi karfin zama abokin Aikin ki young girl...Yafada kafin yadago Yana cigaba da Fadin"Even my house girl baki kai wannan mtsayin ba,balle har ki goga kafada dani agun Aiki,ok"yafada yana kallonta.
Ba Nusiba ba kadai ba,ba ma"aikatab dake freedom ba mutanen dake gidajensu ,da wanda kejin radion su Amota dana office haka sukayi kasake suna ganin tsabar,mulik,aji da girman kai gun Nazir Hade da rashin mutumci,Nusiba da idanunta suka kawo kwallah tadago tana kallon manaja ta gilashin daya rabasu girgiza mata kai yayi shima cikin sanyin jiki.
mirmishin yake Tayi kan tacigaba da cewa.
_To ai babu laifi koda bankai mtsayin goga kafada dakai a aiki ba na tabbata acikin faifan tarihin rayuwarka za"a Rubuta kataba gabatar da wani shuru da Nusiba_
Tana gama fadar Haka taciga da cewa.
_Kamar yadda kuka Sani shirin Freedom takuce,sabon shiri wanda wannan gidan radion ta kirkiro domin bama masu sauraranta dama Sani game,da ita,shin game da wani shiri ne da"aka gabatarwa k/k da tambaya ko/ki wani Abu ya shigemuku duhu,ko game da ma"aikatanmu ko ke Neman Sani akansu,to duk wannan Shirin yabaku dama zaku kira,kuyi tambayanku mukuma,mu fayyace muku komai,ina fatan zakuyi mara badamu_
Daga haka ta dakata aka Sanya waka,na tsawon minti uku kafin Adawo Ana dawowa Aka bude layin waya kan kace kwabo waya Tafara shigowa,ammh Abun mamaki duk wanda yakira baya kokarin tambaya kan kowa Sai kan Nazir,yana da mata,shekararsa nawa,a ina yayi karatu,meye burinsa anan gaba...Kai tambayoyi dai dayawa.
Nazir dake Zaune dariya tadan kamasa kai tsaye yace"Nazir Adam Galadanchi ba ma"aikacin Freedom ba ne..So karku tsallako hurumin daba naku ba"yakareshe fada harda zakuda kafada irin ko ajikinsa,ai mutane Sandarewa sukayi saboda mamakin wulakancin wannan gayen wasu suna da lbri hallayansa ammh basu zaci Abun nasa yakai Haka ba.
Cigaba dadaukan Waya akayi ammh Abun Takaichi mata ne ke tafe kira suna zubda kansu,wanda ko tak bai ce ba,Nusiba takaici ya kumeta ta kosama agama shirin kawai kwatsam wani yakira yana tambaya shin Nusiba matar aure ce?ko kuwa budurwace? Nusiba tayi mirmishi da wannan tambaya Tana Shirin bada amsa ne kawai taji Nazir na Fadin.
```Ba matar Aure bace,hasalima bata taba Saurayi ba...```
Yafada kai tsaye kuma yana kallonta,gaban Nusiba yafadi ras!kamar yadda na musty ma Fadi wanda ke cikin motarsa kan hanyar komawa gida yayi mantuwa,cikin tsautsayi ya kunna radion motar sai ko yaji muryan Nusiba baigama mamaki ba yaji muryan Nazir,A"a suprise brodan da yakoma Abuja kuma bai gama mamaki ba yaji sanda yake cewa kar masu saurare su tallake hurumunsu,yana Saurare yanaji kwatsam yaji cin Mutumcin da Nazir yayi ma Nusiba,cikin sauri yazaro wayarsa yakara akunni da sauri naji ya Furta"Ammi keda Abbu ku kamo freedom radio yanzu.
Ammi dake kusa da Abbu tace"Freedom kuma? miyi meye dashi kuma"Musty yafada cikin bacin rai "Ammi ki kunna ku saurari cin mutumcin Da Broda kema Nusiba"yana gama fadar haka ya latse wayar ransa na masa kuna.
Ammi da Sauri tashiga daki tadauko radion Abbu tazo dashi da sauri takamo tashar daidai lokacin da Nazir ke Fadin.
```babu wanda yataba cewa yana sonta,ko cikin mata bata da farinjini balle ga da Namiji,sabida bakin jininta yasa kaf yan layinsu suka kare harta kannenta sunyi aure ammh ita babu ma ko mashinshini,dalilin Haka yasa ya ubanta ya koreta daga gidanshi don yace bazai iya zama da wacce takusa haifansa acikin gida ba...Mallam mai tambaya in kana so to sai kazo kayi mgana don kamar kayi jihadi ne```
Yana gama Fadar haka ya mike ko kallonta bai yi ba yafice,Nusiba kuwa gabadaya hawaye yagama wankemata Fuska kirjinta namata zafi kafafunta sunyi sanyi kalau,masu sauraro kuwa harda wa"inda suka ma Nusiba kuka saboda tsausayi,manaja kuwa dafe kai kawai yayi yanaji kamar ya kurma ihu wannan wani cin mutumci ne.
Ammi kuwa Da Abbu mutuwar Zaune sukayi suna mamakin wai wannan kalaman daga bakin Dansu yafito gudan jininsu,Kawu ma Anty dake shashensu ashe suma sunji domin Anty dama tashar jintace tana ko latsowa sukaji wannan cin zarafi wanda ba"a sama sa suna akunnen dubban mutane,kawu hawaye kawai ke zubamai na tsausayin Nusiba.
Nusiba ta mike da gudu tana wani irin kuka tafice daga dakin gabatar da shirin tana rufzan kuka mai tsaya aran wanda yaji,ficewa tayi daga gidan Radio tana kuka ko Abun hawa bata tsaya hawa ba tamika hanya tana kuka kamar zararra.
Musty daya kariso gida cikin tashin hankali yafado Falon yana Yana Fadin"Don Allah Abbu ka amincemin in Aure NUSIBA'"Yafada idanunsa jawur,Abbu dake sunkuye dakai yadago cikin wani yanayi mikewa yayi yana Fadin"*BAKAI KADACE DA ITA BA,SHINE YADACE ITA*"Abbu yafada babu wasa Amagarsa kan yace"Fatima dauko min Hula na,kai mustpha shiga bangaren Mallam jibo kace ya shiryo zamu fita"Cikin Tashin Hankali Musty yace"Don Allah Abbu kada kuyi haka kafasan Bro....Shout up mustapha Abbu ya furta cikin tsawa kan yace"Do as i say"dole musty ya fice yana jan kafa ya isa ga shashen su kawu ganinshi cikin wani hali yasa suka biyoshi afarfajiyan gidan suka iske Ammi Da Abbu fuskansu babu Annuri kawu na karisowa Abbu yace"Mallam shiga mota muje'yafada yana shiga bakar benz din dake gabansu babu musu ya rufa masa baya shiko direba yaja suka fice sai da suka hau titi direba yace"Alhaji ina muka Nufa...Cikin bacin rai Abbu ya kalli mallam jibo yace"ina ne Mahaifar Nusiba"Cikin tsoro kawu ke kallon Abbu kan yafurta cikin al"ajabi da tsoro mai yawa"ZARIA.....Muje chan garba,Abbu yafada yana kauda kai.
*Karakarakara ga Akuya ga kura,wai shin wannene,Tabbas Nazur ya debo ruwan dafa kansa,iz just d begining guyzs*
*comment*
*share*
*vote*
*JANAF*✍
[4/11, 2:11 PM] 0mmer Farouk: *🧑🏻NAZIR🧑🏻*
_*(The journalist)*_
*(Based on luv and Romantic story)*
*Na*
*Janaf ce*✍
*Vote me on WATTPAD:Janafnancy*
© _*INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION*_🖊
*```DIDECATED TO SAHIBA HAFSART HAFNAN```
_*Alhamdulillahi nasamu sauki,ina mika sakon godiyata gareku wa"inda suka kirani da wa"inda suka min text message da wa"inda sukamin mgana ta chart da wanda na amsa da wanda ban amsa ba,nadaga kiran wasu,wasu kuma bansamu Hadi ba,da wa"inda sukaitamin addu"ion su A groups duk ina godiya Allah yasaka da alheri yabar kauna,nagode nagode sosai*_💕💕
14/15
""Ina kike mara mutumci,wacce batayi gadon Arziki ba"Inna zainaba tafada tana shigowa tsakiyar falon bayanta Jidda ce tana wani karkade karkadan jiki,
Ammi dake kichen suna aiki da Su mero suna hada breafsat taji hargowan Inna zainaba ,su mero takallah tace"Ku karasa aikin bari nazo"Tafada tana ficewaa
Da mirmuishi takariso tana Fadin",A"a zainab kece tafe da sassafe haka"Inna zainaba tace"eh kyace ina Tafe da sassafe mana,ba gidan dan"uwana bane,koda kudin mai dattin hula aka tara aka gina? takareshe Fada tana wani mata banzan kallon Ammi taji mganar ta soketa ammh Saita share dariyar yake tayi tace"Babu kam Allah baki Hakuri"Tafada tana kama Hanyar shiga bedroom inna zainaba tadaga murya tace"naji munafuncin dakika hada,kin hana Nazir ya auri jidda ammh kinyi kin fita kin auramasa danginku dankin mayu"Tafada tana matsowa kusa da ita.
Cak Ammi ta tsaya tajuyo tana kallon inna zainaba daga Sama har kasa kafin tamaida kallon kam Jidda yamutsa Fuska tayi kan tace"Kifara Natsar da yar"taki tukun nan kafin kiyi rigimar taki Auruwa"Kutumar ubanchan..."inna zainaba tafada tareda yin wani kukan kura ta nufi Ammi,
"Dakata..."Abbu ya furta lokacin dayake Fitowa daga bedroom din yakarisa fitowa yana Fadin"Dakata mutuniyar Banza,saboda kina sakara,kizo har gidanta kice zaki daketa don kaniyarki"yafada ransa bace kafin yacigaba dacewa"Wanki Fa take Aure ba kaninki ba,ammh kinbi kin Takuramata acikin gidan Aurenta,to wlh kul dinki inhar kinsan fitina zai kawo ki kibar min gida,kuma wlh dagayau sai yau matukar ba arziki zai kawoki ba kada kisake dawomin gida,tunda ke shashasha ce"Yafada yana Nunamata Hanya.
kuka Inna zainaba tasaka tana cewa"Ai dama kaima yaya ta shanyeka sai Abunda tace kakeyi,inko Hakane Nima abani dukiyata mana,don nima inada Hakki aie"Tafada harda face majina,Abbu dake tsaye yayi kasake yana kallonta kan ya girgiza kai yace"Zainab kenan ki kwantar da hankalinki koda bakiyi mgana ba ni tuni nadade da hadamiki kan dukiyar zan baki abarki,kije kizo da shedan ki nima zanzo danawa kikarbi dukiyar ki Allah yagani biyar banci da gumin kiba"yafada ransa na bayyana tsantsan takaichi.
Ammi tace"A"a Abbu baza ayi haka ba,kada kabiyemata kaifa ne babba"Abbu yace"Fatima kenan kunfi kowa sanin waye Adam,kaifi dayane ince eh,to eh din billahil azim yau dukiyarta bazata kwana ahannuna ba,kinjima na Rantse"Yafada wit full confident Ammi tajuya ga inna zainaba tace"to ke kibashi hakura mana,baki tunanin kina kokarin TAFKA KUSKURE"Inna zainaba ta ballamata harara tana cewa"Ke kikaga kuskure har abada da inbar dukiyata hannun yaya,yana miki hidima keda dangin mayu gwara na karbi abata nima nasan kasuwanci aie"Tafada harda yarfa Hannu.
Abbu yakalli Ammi yace"Kinga muje ciki,ke kuma inkin kawo shaidan naki ina jiranki"yafada yana wucewa,Ajiyar zuciya Ammi tasaki kafin tabi bayan Ammi inna zainaba tayi tsaki tajuya tana cema jidda"Ai gwara na karba abata inyadawo cikin Hayyacinsa na maida masa"Jidda tace"Tab mommy yanzu saiki mayarmai? kiduba yadda yasakamar yayansa komai suke famtamawa kardai broda Nazir yaji lbri"Tafada tana kallonta inna zainaba tace,"Yo daman,Abbanku yanzu zan turo yanzu dama ta inda aka hau tanan ake safka"jidda tace"Dat my momzy,shiyasa nake sonki"tafada tana rumgumota.
Abbah yaji mamaki da razana lokacin inna zainaba kefadamasa zata amshi dukiyarta hannun Adam baigama mamaki ba saida Abbun yakirasa da kansa yace yazo da komai dayake arubuce suzo tareda zainaban domin ayi komai agabanta,yayi kokarin yima Abbun mgana ammh yaki Sauraran sa,yasan wayeshi tunda yayi fushi tokuma shikenan.
Sunzo tareda da ita,dama komai sun Rubuta domin bayan dukiyar zainaba akwai ta Fatima,ga tashi kuma,dama tuni suka raba dukiyarsu shida Alhaji Hassan yakasance daga Nashi sai na zainaba da Na Fatima ke karshinsa,cikin lokacin aka cire mata nata,bayan an fadi iya adadin gadonta tun mutuwar mahaifansu,sai kuma aka dawo aka raba riba har kawo zuwa yau din Inna zainaba tatashi da tsabar kudi kawai milayan Arba"in bayan gidajen guda goma,sai gidajen mai tatashi da guda hudu,akwai shanaye dasuke kiwo akauye garke tatashi da rabin kargen shanu da rabin na awaki,washe baki kawai takeyi taga kudi,Abbh kallonta kawai yake yana mamaki,kallon Abbu yayi yace"Meyasa zaka biyemata Adam,karka manta nima danike megidanta hakuri nake da ita,meyasa kai bazakayi ba"Kallonsa Abbu yayi da bakinciki Fal Ransa yace"Menace Hassan wlh bance komai ba,hakkintane tanda daman Amsa komai nata har Abada tana nan amtsayin kanwata"Yafada yananuna masa babu komai,Ammh chan kasan Ransu kunshe da takaichi.
Alhaji Hassan saboda bakinciki marin tane kadai baiyi ba saboda Fada ammh tace"Ai daman Hakkinta ne tuntuni yakamata,ta amshi kayanta ko"Ganin tayi nisa yasa ya tattarata yasa mata ido,jidda kuwa tafi kowa murna don Tashin Farko tayi Sabuwar mota Camry ta kamfanin toyota,bayan tamfatsetsiyar waya data siyamata Ammh Aisha kuwa ko tsinke ba"a siyamata ba ance yar bakinciki ce,sudai nasu ido ne domin komai yayi Farko zaiyi karshe.
Ammi Hajiya Hafsart,(Sahibata)takira kawartace yar kasuwace ta karshe wacce kaf Nageria asan da ita gurin Hada kayan Aure zata hadama mutum komai da komai saidai tamaka bill katuramata ta banki,kiranta kawai tayi tafadamata size din takalmin Nusiba dana inner wears dinta tace nan da zuwa jibi takeso komai yayi ready seti takeso guda guda sha biyu takeso masu tsada da garari,Hajiya Hafsart ta tabbatarma Da Ammi bazata bata kunya ba,balle tasan cewa babban zuru"ace fa mai ji da komai.
Nusiba takira Rahma waya tafadamata komai tace tahadata da Ummanta tamata bayani,Umma ta yarda da mganan Nusiba tayimata alqwarin gobe Rahaman zata taho,Gari na wayewa Rahma ta shirya tawuce bayan tabiya freedom tadauki excuse nacewa Tafiya takamata Manaja yaso ya tambayeta Nusiba ammh kuma yanajin kunya shiyasa ya kyaleta,domin yasan shine silar komai.
Rahma na sauka Akwangila takira Nusiba tafadamata kwantance tama dan mashin din daya dauko Rahman cikin ikon Allah kuwa yasan garin sai gashi ya kawota har tukur tukur din Nusiba tazo tatafi da ita,Inna Saude tayi matukar mamaki data ga wata wai kawar Nusiba,wacce sukama Asirin bakinjini itace har tayi kawa,Nusiba taita ina tasaka Da Rahma ita da innanta,sai dare bayan sun Samu lokaci Nusiba,ta kwashe kaf tarihin Rayuwarta Tafadama Rahma Harda halin data ke ciki yanzu,Rumgume ta kawai Rahma tayi tana fitar da kwallah tace"Ban duba Nusiba ammh Tabbas *NAZIR* shine mabudin Hasken Rayuwarki,shawarata agareki Shine sai kinzama mai Hakuri kin jajirce kuma bana so ki watsama Abbu da Ammi kasa a ido"Haka dai Rahma taita bawa Nusiba baki,itakuwa Nusiba jinta kawai take arantana Fadin batasan waye Nazir bane shiyasa.
Bash kuwa tuni yake gudanar da duk wani shirye shiryen sa musty yakira yace ya taimakamusu da hoton Amarya,in yana dashi,musty kuwa daman yataba daukan Nusiba awaya yako turama Bash ta wsop Bash yaga Nusiba wacce ya tabbatar bata da makusa tako"ina kaiwa yayi aka hada hotun na Nusiba da na Nazir akayi editing wlh ka gansu sai kace tare suka dauka,sauran abokansu kuwa Muhamed Gaddafi,da muhammed Gidado wanda childfriend din Nazir ne sukazo kuma suka dunke da bash wanda sukazama su hudu kenan,abokaine na sosai wa"inda suka shaku dukkansu suna da bambamcin Ra"ayi gurin Nazir da duk ciki shine yafita daman.
Muhammed Gidado dasuke cema mg shima dan jaridane dayake aiki da gidan Radion Nagarta dake maraban jos,yana da matar aura daya mai Suna Ramlart suna zaune a anguwan Sarki akaduna,sai muhammed gaddafi da ya kansance dane ga mataimakin gwannah jahar kano Dr Gaddafi zailani shi ma"aikacine a NNPC dake kaduna,baya da mata sai dai budurwansa wacce ta kasance bafullatan nan yolace tana aiki da kamfanin sadarwa ta mtn agarin.
Tawaya suke tattauna yadda komai zai gudana,sunyi alqawarin hallata Ranar alhamis sai sukarisa shirya komai da komai.
Ranar laraba Hajiya Hafsart ta iso da kayan alfarma masu kyau da tsada wanda tsayawa fadan kyawun kayan wlh bata baki ne masu karatu nabarku ku kimanta adadin kyawu tareda dimbim Nairan da"aka zubama Nusiba Ammi kiran Nusiba tayi tace gasunan tafe,zasu kawo lefe,Nusiba taji Abun kamar almara nan take Fadamasu inna Da Anty nan da nan suka mike aka Fara shirin Tarbansu.
Ammi ce da ita da hajiya Hafsart sai inna zainaba datazo ganin kwakwaf direban dayakai Su Nusiba shi yayi gaba dauke da akwatunan ayayinda dayan motan musty ke jan su Ammi,sai wata bus dake bayansu cike da kayan Abinci iri iri.
inna Saude Da Dada sukaga anata hada hada ga kaji an yanka wanda inna Fatsima ke kiwo ne aka yanka,sai jallop din Taliya da"aka musu daidai Ruwa dai dai gurji,Koda azahar