Showing 72001 words to 75000 words out of 87333 words
Chapter 25 - Nazir Bok Complete Hausa Novels by Janafty.txt
GA NUSI KU KULA DA ITA,ABBU DA AMMI KUYI HAKURI BANI DA ZABI NE.....*
musty nagama karantawa falon yadau salati da kururuwan Inna zainaba wacce tasaki ihu tayi zaman dirshan akasa,Ammi kuwa kujera tasamu tazauna tana maida Numfashi,Abbu ya yi shuru yana Nazarin jidda kan yayi ajiyar zuciya yace",Komai tsanani yana tare da sauki....Aikin gama kuma ya gama"Yafada yana dafa kansa cikin rashin jin dadi hanyar dakinsa ya nufa cikin kunar zuciya kamar walqiya inna zainaba tasha gabansa tana cewa"Dama nasan za"a rina komai yafaru shirinku ne wlh ko kaffara bazan yi da saninka ADAMU Komai yafaru"!ba Abbu kadai hatta su Ammi dasu Musty mganar dafasu lokaci daya Abbu ya dakata yana kallonta yace "Babu illa ko aibu don kin kirani da Adamu domin sunan kenan.."Yafada yana mata yaken dayafi kuka ciwo"Inna zainba tace"Eh kace haka mana Tunda danka yana kasamin Rayuwar yarinya kalli yadda ya maidata shine kuma bai isheshi ba harda sakin wulakanci To wlh baisan wacece ni bane dukkanku sai kunyi nadama"Tafada kai tsaye tana Nuna Abbu wanda yake kallon kasa lokaci daya hawaye sun cika masa ido.
Ammi tace ranta bace"Haba zainaba in hankali ya gushe ai Natsuwa ke nemo sa karki manta wanda ke gabanki fa"Tsaki inna zainaba taja kan tace"Mtseww...Waye ke gabana wanda ya wuce macucu azzalumi wanda baisan hakkin wanda ke kasansa,..."Inna...!"Musty yakira sunanta, Cikin bacin rai da takaichi hawaye lokaci daya yana wankemishi fuskarsa yana zurarowa tadan glass din dake idonsa yafara takowa cikin sanyi yana fadin"Haba inna meysa kike haka Abbu ne fa Abbu ne kike fadama wannan mummunan kalaman"Yafada cikin kuka Aisha ma dake gefe kukan take.
Ammi tace cikin karayan murya"Ina kika kai zumunci da kaunar dake tsakani"Tafada tana kallonta,Cikin fitan hayyaci inna zainaba tace",Shi zumuncin dake tsakani da kaunar taci kutumar ubanta...Sai yanzu kukasan da haka dakuka san kunyi zalumci""Wlh Allah ya isa tsakanina daku bazan taba yafemuku ba",Tafada tana kuka Abbu dake kallon kasa yadago cikin wani yanayi yana kallon inna zainaba"Yace ko alama banyi mamakin Abunda ki ka aikata duba ga yadda kika maida kanki nasani har Abada bazaki taba godemin ba ammh ina so kisani badole na bane zama dake ko yau iyayenmu suka dawo duniya sunsan na rike Amanarki....Ki fice ki barmin gida yanzu nan Zainaba kuma wlh ko Ahanya kika ga Ni adamu kika Nuna kinsanni bazan taba yafe miki ba,kije duniya zata miki hankali"Yafada yana wucewa cikin kunar zuciya.
Inna zainaba tace"Aikin banza to sai me dama uban na karu dashi agidan dadin Abun dai muna da gun zuwa balle amana wulakanci,"Tana gama fadar haka takalli Aisha tace"Ki wuce muje kihadamana kaya..Mu bar musu gidansu"Aisha ta girgiza kai tana fadin"Babu inda zan biki mommy wlh ayau nayi nadamar dakika kasance uwata"inna zainaba tace"Nima wlh nayi nadamar haihuwarki Aisha domin da badon agida na haifeki ba sai nace musanje akamin...badai kinzabi nan to kizauna ina zaune zaki nemi ni",Tafada tana wucewa Musty juyawa kawai yayi ya shige daki Ammi dake zaune ta dukar dakai kawai tana salallami jidda kuwa na takure agefe tana kuka ko Tak batace ba.
Inna zainaba tahada kayansu kaf takira megadi ya fitar musu dashi mai napep tabada umarnin ya samota sai ko gashi ko kallon Ammi da Aisha batayi ba wanda suke mata magiyan kartayi haka,Jidda ta taimakama suka mike kan takalli Ammi tace"Fatima yau dai burinki yacika sai kisa aruwa akasa kisha"Tana gama fadar haka tafice ita da jidda suka shiga napep yaja suka tafi tana ma gidan kallon karshe,Aisha taji zuciyarta tayi rauni kawai sai fada jikin Ammi tana kuka Ammi na rarrashinta nan da nan xazzabi ya rufeta Ammi ne takaita daki tabata mgani ta kwantar da ita.
Koda Ammi takoma daki tasamu Abbu na shirin fita ko ajikinsa duk da yana kokarin boye damuwarsa ammh kallo daya zakamai kafahimci cewa yana cikin damuwa,Ammi takalli Abbu dayake shirin ficewa tace"Kayi hakuri Abbun mustapha komai zai wuce'!Kallonta yayi kan ya murmusa yana fadin"Ah...Aike zanba hakuri Fatima donke ne akafi batamawa"Daga haka kawai ya fice tabishi da ido kwallah tazubomata tayi saurin sharewa.
*************
Nazir kuwa Su jidda na tafiya ba dadewa shima yayi shirinsa Airport ya kira yana tambayan ko akwai flight dazai tashi zuwa lagos sai akayi sa"a akwai wanda zai tashi nan da awa daya,bash yama waya yazo yakaisa Airport din duk yadda Bash yaso jin maike damun Nazir ammh yaki fadamai haka yarakasa har jirgin ya tashi.
. Daya sauka a lagos bai Tashi zuwa london ba sai awashegari ya dira chan wanda azahirin gaskiya ransa ajagule yake yazabi yin nesa da gidane don yasamu kwanciyar hankali da Natsuwar zuciya.
*Comment*
*Share*
*Vote*
*JANAF*💕
*INTELLIGENT WRITERS ASSO*📝
```{onward together}´´´
*NAZIR*
_*(The journalist)*_
*Based on luv and Romantic story*
*Na*
*JANAF CE*✍
*SADAUKARWA GA SAHIBA HAFSART HAFNAN*
_Wannan shafin nakune don jin dadinku...Sis Dala...,Mman Ummi my Takwara...,Ummikursoom...,Juwairriya rogo...,Sanah...,Hanah...,Asiya....,Maman Abdulmalik...,maman Nusi...,Baby Matazu...,Aisha matazu...,Habiba m shehu...,Oum Ahmed...,Maman Noor...,Maman Amira...,Amacatering....,Maman sayeed...,Maman musa...,Kai kuna dayawa wanda lissafoku sai na cika wannan shafn bangama ba...,ammh ina so kusani kowanni bugawan Numfashina kuna Raina...,janaf fans..Oneluv*_
EDITED BY:HAFNAN💞
40/41
"""""Nusiba duk batasan wainar da"ake toyawaba sai da yammah datazo gaida Ammi ta iske Ammi wani iri ga Aisha kwance ba lafiya ammh kuma tana kuka,cikin rudu ta tambayi Ammi,nan ko take warwaremata komai.
Cikin tashin hankali mara misaltuwa Nusiba ta mike dafe da kirji ta Furta "Saki uku Ammi? Cikin tashin hankaLi Ammi tadaga mata kai"Nusiba ta Sulale takoma ta zauna batasan dalili ba kawai taji hawaye suna suntiri a idanunta tasan bana komai bane sai na tsausayin Abbu da Ammi.
Ammi ta kalleta tace"Ki bar kuka dota,Dama komai kika ga tafaru da sanin Allah...Kidai kawai kima mijinki addu"an Allah yadawo dashi lafiya"Gyada kai Nusiba tayi tana sharan hawaye kan tace"Ammh Ammi ya Nazir bai kyauta ba Abunda yayi,kome jidda tamai baikamata yayimata saki har uku ba sakin da Allah bayaso"Tafada cikin nuna damuwa,Ajiyar zuciya Ammi ta saki kan takalli Nusiba tace"hakane ammh nasan dan zaman dakikayi Da Nazir kin fahimci shi kaifi dayane,yaro ne mai biyayyah da gudun zuciya duk Abunda ya faru munbarsa akaddara na dama chan ba abokin xamanta bane"Kallon Ammi Nusiba take tana jinjina dattako da soyayyah irinta da da mahaifiya,share hawayenta kawai tayi ammh Abun yadameta ainun.
Nan takai dare har Abbu yadawo shima din dai hakuri ya bata to ita mai zata ce,banda hakuri Aisha kuma sai da Musty yakai aka dubata aka rubuta mata mgani kana suka dawo,Nasiha Abbu yaitamata kan tayi hakuri da rayuwa kuma tacigaba dama mahaifiyart addu"a ita da yar"Uwanta,to wazai iya chanza kaddaran Allah.
•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°
""Inna Zainaba kuwa gidansu dai databari suka koma dayske dama key din gidan na hannunta,duk da bakowa ammh akwai maigadi yana kula da gidan,shikanshi yayi mamakin dawowarta don tun barinta gidan bata kara lekowa ba.
Shiga da kayansu tayi cikin gidan kawai tadauki jidda suka yi asibiti wasa wasa sai da aka ba jidda agado saboda tadaku fa ba karya ga jikinta duk ya none Garkuwa Hospital din dai takaita kuma Dr Hisham din ya amsheta har yana masifa dayaji abunda yafaru bakin inna zainaba wai sai ya shigar da karan Nazir kotu bisa dukan rashn hankalin dayayi ma jidda Inna zainaba ta kwabesa domin tasani duk haukan Dr Hishan Nazir yafishi hauka,da kafa agwannati tasan tsab zaisa adauresa har igiya tayi rara,dama gashi ya gano plan dinsu.
Sai da jidda takwana uku aka sallameta Dr Hisham yaita dawainniya dasu don so yake jidda ta warke suka koma ruwa don tunda tayi aure basu hadu ba,Inna zainaba yan aiki ta dauka har guda biyu saboda daga ita har jidda baza su iya aiki ba,dama gadon su na dukiyar mijinta Alhaji Hassan Babu ko sisi hannun Abbun yana gun yan kasuwan dayake har dasu suna cigaba da juya musu to Inna zainaba ta nemosu tace kowanne yahada dukiyarsu yadawo mata dashi,dama tuni dukiyarta tabi ruwa kawayenta da diyan banza sunciye duk abanza.
Nusiba kuwa tashiga halin damuwa kullum cikin gwada kiran lambar Nazir take akashe ta rame saboda zullumi gashi kwanakin tarasa gane kanta da zaran yammah tayi sai zazzabi da ciwon kai ga kasala yanzu bata iya tsinanama kanta komai gashi yanzu ta tsani wanka sai tayi kwana uku da kaya daya,ko abinci inba wainan fulawa ba bata iya cin komai ga yawan barci da mutuwan jiki,gabadaya ta kazance ta kazanta gidanta inba Aisha bace tashigo ko Rahma intazo suke dan gyaramata gidan ba wlh haka zata wuni barci ko wainar fulawan ma Anty takai aikamawa ta mata ko gidansu Ammi su mero suyimata Ko Ammi taga ta chanza data tambayets meke damunta sai tayi shuru,to ita Ammi duk tadauka rashin Nazir ne hakuri kawai taita bata,to ita kanta Nusiba ta lakanta hakan da rashin Nazir kusa da ita.
*After 2 month*
kwanci Tashi babu wuya agun Allah gashi har Nazir yayi wata biyu babu shi babu dalilinsa Musty har london din yaje chan ma"akatansu ammh babu wani lbri domin sunce hutu yadauka na karshen shekara,Abuja ma shuru babu shi Abbu yace"Su kwantar da Hankalinsu ko"ina Nazir yake zai dawo da yardan Allah.
Haka ko akayi kwatsam Ranar wata alhamis da misalin karfe hudu na yammah Musty na asibiti kawai kamar amafarki yaji wayarsa naneman agaji,yana dubawa yaga sunan broda Nazir baro baro ya bayyana akan fuskar wayarsa cikin Zumudi da Rawan jiki ya daga kiran yana Fadin"Broda Nazir.."Lazy Doc..Bar wannan surutu kazo Mallam Aminu international Airport ka daukeni"!Daga haka ya yanke kiran Ai musty cikin azama da murna ya fice daga asibitin da gudu kamar zai tashi sama.
Yana isa filin jirgin yahango dan"uwan nasa cikin wasu haddadun Suit masu ruwan toka na kamfanin DKNY...Ya matse wuyansa da Tie kafansa sanye cikin rufaffan Takalmi na kamfani Rado,kallo daya zakamai ka fahimci hutu da jin dadi sun zauna mai fuskarsa tayi fayau da ita sajensa yana kwance luf gwanin ban sha"awa,kashin kansa yasha gyara ya kwanta yana fitar da sheki,ammh Daga kallansa zaka fahimci Ramarsa domin har dan wuyansa ya bayyana.
Da gudu Musty ya isa ya rumgume dan"wansa yana fidda da Annurin murna shima Nazir din Rumgumesa yayi back yana buga bayansa cikin kauna da kewa,Musty shi dauki jakar Nazir ta kaya suka isa mota,suka shiga suka fice daga Airport dim bakin musty yaki rufuwa Shiko Nazir mirmishi kawai yakeyi yana kada kai cikin nuna shima tsantsan Murna.tun amota Musty ya labartama Nazir yadda komai ya gudana da Nazir yaji cin mutumcin Da inna zainaba taima Abbu.Sai dayaji kwallah takawomai yanajin kamar yayi kuka saboda tsausayin Abbu.
Ammi na Zaune afalo Aisha na kankaremata farce,Musty ya shigo da ihu hannusa rike da jaka yana kwalama Ammi kira"Ammi ta mike afirgice tana cewa"Lafiyanka ko mustapha"Tafada hankalinta atashe,Cikin murna ya karisa yana Fadin"Ammi...Broda yadawo wlh"Harara Ammi ta sakarmai kan tace,"Karyan banza..."Kan tarufe baki Nazir ya sawo kai Falon da sallamansa cikin muryansa mai cike da Haiba.
Ammi Ta tsuramai ido lokaci daya idonta suka ciko da kwallah,Cikin hanzari,yakarisa kusa da Ammi ya rumgumota yana fadin"I miss u Ammi..."Yafada yana kamkameta Ammi ta rumgumesa kawai kwallah idonta sun gangaro,Tace cikin kuka"Miss u too...Son"Dagota yayi jin tana kuka hawayenta ya sharemata kafin yasaka gwiwoyinsa akasa yana Fadin"Am very srry...Ammi...Gani nadawo gareku"Yafada yana rike hannunta tadashi Ammi tayi tana Fadin"Bakamana komai ba Nazir komai ya faru rubuttace ne daga Allah"Kara rumgume juna sukayi Aisha da musty na gefe suna dariyan Ammi da Nazir ana cikin haka sai ga Abbu yau yadawo da wuri cikin mamaki yake bin Nazir da kallo Musty ya yi gyaran murya Nazir da Ammi suka juyo suka ga Abbu.
Nazir na ganin Abbu kawai sai ya durkusa yafara frogjumb, yana zagaye falon hannunsa akunnensa,Haba mezasuyi inba dariya ba Abbu da kansa yakamosa ya rumgume yana dariya ganin haka yasa musty ma yayi joining dinsu,shima suka rumgume Abbu,Abbu yana fadin"Na yafemaka Nazir dama ban kullace ka ba...Allah yayima Rayuwarku albarka gabadayanku"Suka amsa da Amin cikin jin dadi,
Duk budirn da ake Nusiba bata sani ba,tana gidanta kwance tana barci wunin ranar bata tsinana komai ba,Shiko Nazir yadan dade gidansu Ammi kafin musty ya rakosa,da sallau megadi suka tsayawa gaisawa shiko musty ya shigo falon yana kwalama,Nusiba kira wacce ke bedroom tana kwance duk da ba barci take ba ammh kasala ta sarketa ko hannunta takasa dagawa,Tana kwancen taji musy ta kwalamata kira dakyar ta iya mikewa sanye take dawata blue din doguwar riga kwananta uku ajikinta batayi wanka ba duk tayi wani iri kamar ba Nusiba ba.
Fitowa tayi tana yamutsa fuska kallonta musty yake yana mamakin yadda Nusiba haka duk tawani lalace,Musty yace"Matar yaya...Wai don Allah meke damunki ne"Zama tayi kan kujera tana cewa"Wama yasani nidai wlh nasan banda lafiya komai na jikina baya min Dadi"Kafin yayi mgana Nazir ya sawo kai falon Turarensa na Deen yabude falon,Nusiba na kwance taji sallaman Nazir kamar amafarki lokaci daya da kamshin turaransa,tana kwance daga inda take takasa tashi,Nazir ya tako har tsakiyar falon yana zubama Nusiba ido yana so ya gane wai shin Nusin sa ce takoma kamar mai yin kuli kuli.
Kuri sukama juna da ido kafin Nusiba Tabude baki tace cikin rawan murya"Ya Nazir..."Tafada hawaye na zubomata jin muryanta yasa Nazir ya karisa da sassafar ya isa gareta ganin haka yasa ta yunkura ta mike yana isowa baiyi wata wata ba yayi mata wani wawan rumguma Yana sakin ajiyar zuciya ita kuwa Nusiba kuka kawai tasaki tanayi harda jiniya ga matsan da Nazir yayi mata,ga kuma kamshin turaran Nazir Daya dameta yafara tashinmata zuciya.
Nazir yadago yana kallonta harshensa yakai kan fuskarta yana sharemata hawaye ammh kamar kara bulbulosu ake,musty ko tunda yaga anyi wani rumguma ya fice yana dariya.
Nazir kallon Nusiba kawai yake yana mamaki bai gama mamaki ba sai da yakara kallon Falon duk yayi kura,Kara rumgmota yayi itakuma tana zillewa saboda aman daya tasomata Nazir yana kallon kwayan idonta yayi yana cewa"Nusi...meyafaru dake haka kin rame komai naki ya chanza..Kinyi ciwo ne"!Yafada yana zare dankwalin kanta Yaga yadda kan yayi cuducudu yawani hade guri daya zaiyi mgana kenan kawai Nusiba tafara kelaya Amai ta wankemai jiki riketa yayi cikin mamaki yana kuma mata sannu.
Amai take har taduke saboda wuya,aman ma bakomai sai ruwa tana gamawa Nazir ya sunkuce Nusiba sai toilet,shima kwabewan yayi ya shiga mata wanka itakuwa gabadaya karfinta ya kare tas..Yayi mata wanka ya nadota atawul,yazo shi ya shiryata cikin riga da sikat na atamfa yasanyamata hijabi,shima kayansa ya chanza ,zuwa riga da wando,cak yadauketa,sai mota Ya zuba hon mai megadi ya bude musu get suka fice.
Sai bayan sun isa cikin iyali hop din kana Nazir yama Ammi waya yake fadamata kana yace Ta tura Aisha gidansu tadan gyara,Ammi hankalinta ya tashi ainin tace zata biyosu Ammh Nazir ya hana suna zuwa aka bata gado aka sanya mata drip,aka dibi jininta da Fitsarinta...,Nan da nan barci yasuri Nusiba dayake an mata allurai barci.
Har dare Ammi taji shuru kawai sai ta Musty yadaukesu ita da Aisha yakai asibitin sun iske Nusiba ta farka Har Nazir na bata ayaba tana amsa da dakyar shigowarsu daidai da shigowar likita yaba Nazir hannu yana mika mishi farar takarda yace"Congratulation sir...matarka tana dauke da cikinka har na tsawon wata hudu...both of dem they are in good health"Da wani irin murna Nazir ya rike hannu likita yana Fadin"Thank sir...Thank very much"Yana gama fadar haka ya suri Nusiba yana juyawa da ita afalon cikin murna,Ammi ne ta dakatar dashi damai tsawa haka ya ijiyeta yana kallonta yana fadin"Nagode Nusiba nagode da wannan babban kyauta Allah yayi miki albarka"
Ammi tace,"Cikin murna ashe dota juna biyu ne ya maida ke haka...Kai nifa nayi toshewar basira da bangane ba"Dariya musty da Aisha suka kwashe dashi Ammi ta harareshi tana Fadin"wuce dai kazama tuzuru wlh ba Aure"Sosa kai musty yahau yi yana kallon Aisha Nusiba na kallonsa tana yar dariya kan tace"In tona ko kar na tona..."Tafada da muryan ciwo,Sauri musty yace"A"a matar yaya ba yanzu ba kibari in lokaci yayi zan fada da bakina"Nazir yace"Kai gulman meye kuka kulla kuma"Ammi tace"Meye naka,in tayi wari maji"Dariya dakin yadauka cike da farinciki.
Nan suka raba dare kana akabar Ammi da Aisha gun Nusiba sukuma su Nazir suka koma gida,sai washegari aka sallami Nusiba tadawo gida,wanda Anty batanan tatafi gidansu sai aranar tadawo,takeji kowa yaji samuwar cikin nusiba murna yake haka Abbu ma dayaji,sai jinyar Nusiba takoma hannun mutane da yawa ba uban gayyah ba Ammi ba ba musty ba Aisha ba,ba Anty ba kowa kulawa yake bata,Rahma ma nan take wunin mata.
Sati daya jikinta ya warware Nazir yakoma fama,domin Nusiba bata kaunar wanka sai yayi da gaske take yarda yayi mata kuma abincinta kenan wainar fulawa da yaji tun Nazir na hanawa har ya hakura Yasa mata ido,gashi cikinta bayason kamshin turaransa shiyasa dole yadaina sawa gashi bata kaunar ya rabeta Abu fa yayi ma Nazir yawa duk da kafin yadawo daga london sai yaje aka dubasa aka tabbatar da baida kowacce cuta kana hankalinsa ya kwanta.
Sati biyu yayi,yayi musu shirin komawa ammh Ammi tace"Bazai yuyu yatafi da Nusiba ba cos tana ji da kanta hakanan babu yarda Nazir zai yi yanaji yana gani yatafi yabar Nusiba wacce ko ajikinta murna take mai sata yin wanka zai tafi,shi wlh lamarinta ma dariya yake bashi,Yana Tafiya takoma gidan Ammi tatare tana zuba shagwabanta yadda taga dama,wanka ko bamai sata dole sai in Ammi taga tayi kwanaki ne zata mtsamata tayi,tana tura baki tana komai zatashiga tayi.
*INA LABARIN INNA ZAINABA DA YARTA JIDDA*
Duniya Sabuwa ita Tabudema inna zainaba da jidda don kaf dukiyarsu Wanda alhakin ke hannunsu sun damkata shi ahannunta,to kusan giyan kudi tuni suka dibi inna zainaba tafara famtawa agari ita da jidda tahadu da kawayen banza suka fara huremata kunne,ita kuwa jidda ruwa takoma tsumdum duk da da farko jikinta yayi sanyi kodaga sakin da Nazir yayi mata ammh inna zainaba tanuna mata har yanzu tana da dama,kuma dama ga Dr Hisham na sintiri badon tasoba ta biyema Dr Hisham suka koma Ruwa.
Yau suna zaune dukkansu afalo ita da jidda Tuffa suke ci inna zainaba takalli Jidda tace"Baki ce komai ba kan mganar dana miki ko kin hakura ne"Jidd ta kalli inna zainaba tace'Na hakura.."Tab ai wlh mommy yadda tabon dukansa bai bace min haka