Showing 15001 words to 18000 words out of 87333 words

Chapter 6 - Nazir Bok Complete Hausa Novels by Janafty.txt

afalon Abbu na zaune akan kujera,gefensa Musty ne Ammi ke gefe itama gefenta dan lelentane Nazir wanda ke kishingide idanunsa alumshe hira suke ammh shi ko umh,bai ce ba sai in anyi Abun murmusawa ya murmusa,da sallama suka shiga inda kai tsaye Kawu ya isa ga Abbu yamika masa hanu sukai musabaha,kafin ya mikama mustapha,Anty kuwa bayan tagaida Abbu,musty ya gaisheta.



Ammi tace"Suwaiba ina yata? Anty tace"Tana chan na barta yau tadawo agajiyene,wai batajin dadi"Ammi tadafe kirji da sauri tace"Nusiban tawa ce batajin dadi? ta fada da sigar tambaya,musty dake zaune gefe ya mike yana Fadin"Ayyah ma"akaciyar jarida ba lpy banga ta zama ba"

Sallamar Da Nusiba tayi a falon shi ya yadakatar da Musty wanda yace"Tama warke Ammi"Yafada da sigar zolaya Nusiba ta hararesa  Ammi ta mike ta isa ga Nusiba wacce ke sanye da dogon farin hijabi fuskarta tayi fayau,alamun batajin dadi,


Ammi ta rikota tana Fadin"oyoyo my dota,ya jikin,? yanzu suwaiba kecemin baki jin dadi? meke Damunki ne yata? tafada tana taba wuyanta Abbu yace"Ikon Allah fatima,ai kya bari ta zauna ko"yafada yana Dariya Ammi taja hannunta keeee"Bata direta ako"ina na ba sai a kusa da inda Nazir ke zaune ta zaunar da ita tana Fadin"duk na rudeni ne Abbu kasan yadda ni ko patient aka kawo na shiga rudi kenan.


Nazir dake gefen idanunsa alumshe kamar mai bacci,ammh duk Abunda ke Faruwa akunnesa kaf bakin muryoyin dayaji ne yasa yayi lambo don kadama ace Ya gaishesu,Ita kuwa Nusiba bata ko lura da Nazir dake gefen ta ba,Tace"Ammi ciwon kaine kuma nama sha mgani naji sauki"


Ko amafarki yaji wannan muryan yasan mamallakiyar muryan,muryan data zubarmai da darjansa,ta bashi tarihin da ba"a taba bashi ba Arayuwarsa,muryan data daka mai tsawa tafadamai mganganu masu daci wanda inya Tuna yakejin wani kunci Aransa.


Ammi ta mike tana Fadin"yauwa yanzu naji magana,ammh ban yarda ba  saina duba ki da kaina"Tace"To shikenan Ammi kiduba yarki"Abbu yace"Tab muna ganin sonkai mallam jibo,fatima bako kara"Ammi dariya tayi ta mike tana Fadin"eh man mutum da yarsa,kawai asamai ido,kinji taho my dota ki tayani kawo fulakls din mu jera kan dining.



Nusiba ta mike da azama zata wuce,cikin ikon Allah bata lura dama Nazir ba balle kafafunsa farare dake kwance asaman kafet,wanda taci tuntube dasu tasha kasa,gabadaya falon aka dau subuhannallah lokaci daya,shiko Nazir cikin wani bacin Rai ya bude idanunsa caraf ya sauke Ana Nusiba wacce itama tadago taga wani hallitane wannan,zuru yamata ido yanaso yakara tabbatarwa da ita ce ko ba ita bace,fuskar da ko amafarki bazai manta da ita ba.


Nusiba kuwa mutuwar zaune tayi tana kara ware idanunta akanshi,itama so take ta tabbatar shine ko bashi bane,kallon dayakemata ne yasanya tsoro ya shigeta,A fusace Nazir ya mike yana Nunata da Hannu yana Fadin"Kece...Kece..? Amsamin..?yafada cikin tsawa.

.Ammi da Abbu da kawu da Anty da musty sai sukayi mutuwar Zaune Nusiba da jikinta yafara rawa ta fara ja da baya daga zaune,shi ko yana binta yana ta maimaita Abu daya!Kece...Kece..? Yana Fada yana pointing dinta.
















*Comment*
*Share*
*Vote*








*Janaf*✍
[4/11, 2:11 PM] 0mmer Farouk: *🧑🏻NAZIR🧑🏻*

     _*(The journalist)*_

*(Based on luv and Romantic story)*

  *Na*

*Janaf ce*✍

*Vote me on WATTPAD:Janafnancy*

© _*INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION*_🖊

*```DIDECATED TO SAHIBA HAFSART HAFNAN```







```Live u life to be fullest,dont let people put u down,be wit someone who cares for u like u do for them,don"t get Red of someone couse of what other people say it's you life.Not them```







12/13




       """Suna fara tafiya suna gabda fita cikin kano,Abbu yazaro wayarsa yakira Hassan wanda ke zaune kusa Da inna zainaba,kiran Abbu ya shigo,yana dauka suka gaisa sama sama yace"Hassan kana gidane? yafada muryansa babu Annuri.

Alhaji Hassan yace"ina gida,Adamu lpy naji muryanka wani iri lafiya kuwa? Abbu yace"Lafiya kalau,don Allah ka shirya yanzu deraba yakawoka muna yan katako munajiranka katahomin da kwalayen minti da huhunan goro"Alhaji Hassan ya mike yana Fadin"Tom shikenan ganin nan tafe" Suka yanke wayar Inna zainaba dake kallonsa tace"Lafiya kuwa? me yayan yace ne? tafada tana kallonsa hanyar bandaki yayi yana Fadin"bansa niba  nidai yace nazo na same yanzu  A yan katako,suna jirana kuma nazomai da minti da goro'"Inna zainaba tace"minti da goro kuma? tafada da sigar tambaya Sai dai bamai bata amsa don tuni megidan nata ya shige toilet,Tunaninta yabata kila Aure yayan zai kara,kai ingaske ne wlh sai tayi rawan Amada saboda Murna.

Agurguje Alhaji Hassan ya shirya direbansa ya daukesa ta kasuwa yafara biyawa aka cika booth din motar da huhunan goro da katan katan din minti da sweet,ako yan katakon ya tarardasu Abbu bai cemai komai ba yace su biyosu Abaya cikin Alhaji Hassan shidai nasa ido don yarasa meke Faruwane.



**************

Nusiba kuwa tana ficewa daga freedom kotakan Abun hawa bata bi tadinga tafiya akasa tana Tafe tana kuka kamar mahaukaciya Nusiba batajin ta tsani kanta ba saiyau,tun da uwarta ta haifata babu wanda yataba cimata mutumci da Nazir yacimata ashe lbrinta kaf yaje ya binciko saboda yacima mutumci A idon Duniya tafetake tana kuka kowani dakika tsanar Nazir na kara ninkuwa Aranta.

Tafiyan nata harda gudu take Hadawa mutane,dadama suna tsayawa tambayanta ko lafiya ammh ko kallo bata binsu dashi tafiyarta kawai takeyu,Koda Nusiba takawo gidan tacanza kammani da kuka da wahala megadi daya ganta sai da yatsorata.

Anty na Falo zaune tayi tagumi kukan Nusiba yafara mata maraba tamike ta sauri,tana duban kofa,Nusiba tashigo da gudu tafada jikin Anty tana Fadin"Anty ban taba jin tsanar kainaba Sai yau,ban taba jin Halin danake ciki yadameni ba Sai yau"Takareshe fada da gunjin kuka,Anty ta rumgumeta tana sharemata Hawaye ammh hawayen Nusiba yaki karewa Nusiba ta rabu da jikin Anty tana Fadin"Kuyi hakuri Anty zan koma gida gaban iyayena domin koda za"a gorantamin baza agorantamin nabar gabansu ba"Tafada tana wucewa daki,cikin sauri Nusiba ke watso kayanta cikin wardrope tana zubewa kan gado tana kuka take Hada kayanta cikin wata trolley tana Fadin"Yayi gaskiya ni Nusiba da bakin jini aka halliceni,domin babu wanda yataba cewa na taba burgesa"tafada cikin Nuna Rauni.

Anty itama da hawaye ke gangaromata ta share tana Fadin"Haba Nusiba,don Allah kiyi hakuri ki dakata daTafiyar nan"ina Nusiba tariga da zuciyarta ta kekashe tana gama hada kayan tarufe trolley tajawota tana Fadin"Kibawa kawu hakuri Anty banda zabi ne,ai dai duk bakin jini uwata bazata gujeni ba ko'tafada idanunta na zubar kwallah.

Anty tana tsaye Nusiba tazo ta wuce,Anty ta bita da sauri tana rokonta ta dawo har farfajiyan gidan Anty dataga Abun yafi karfinta sai ta hau kwalama Ammi ke kira wacce ke chan zaune afalo Tana sharan kwallah cin mutumcin da Nazir yama Nusiba musty na gefenta dafe dakai shi kadai yasan Abunda ke Damunta.

Jin kiran da Anty ke yine yasa suka yo waje atare cikin firgici,ganin yadda Anty ke jan Akwatin Nusiba tana rokonta kar tata tafi,shi yabasu amsa tambayan dasuke so suyi cikin sauri Ammi ta isa ga Nusiba ta rumgume Nusiba tana cewa'"ina zaki? eye...bazaki tafi ba ba inda zaki Nusiba Sai dai Shi kada yadawomana gida,domin kinfiyema shi"Tafada kwallah na ziraromata,Shuru Nusiba tayi tana kallon Ammi na kuka,to ita mai zatayi Uwar data haifeshima kuka take dashi to ita awa,tana dagowa suka hada ido da musty wanda ke tsaye idanunsa sun kada sunyi ja,sundade suna kalan juna kan yakauda  kai cikin kunci da takaichi,Ammi ta riko Hannun Nusiba ita kuma Anty ta riko Akwatin suka Nufa shashen Ammi tana rarrashin Nusiba.


*NAZIR*

yana fitowa cikin tsantsan murna da Farinciki wanda tunda Abun yafaru sai yau yaji wasai,tabbas yaga yadda kammanin Nusiba ya canza sabida kuka,yasani wannan shine Abu na karshe atozartaka cikin jama"a yafi komai ciwo da muni,Ransa kal Suka nufi Abuja wanda time by time yana Sakin murmushi shi kadai,wato Abu yamai Dadi,Yasani yanzu yarigaya dayama rayuwarta Damegi wanda ko Sunanshi taji an ambata sai jikinta yadau kyarma.



*ZARIA*

   ""Da kwatancen kawu jibo suka iso kofar gidanmu wanda lokacin wajen sha daya na Safe ne wurin babu hayaniya kawu shi yashiga gidan da kanshi Inna Fatsima dake tsakar gida tana surfe Taji sallaman kawu kamar amafarki cikin mamaki da murna take amsawa,shima cikin murna yake karisowa.

Inna tace"Yaya kaine Tafe? tafada tana rike Haba"Mirmishi yasakarmata kan yace"eh fati tafiyarce babu shiri,ina fatan megidan naki na nan"Ta amsa da yananan"kawu yace"yi masa mgana tare na....Amun mgana gani ai lafiya"Baba ya katse Kawu da cewa Haka,Kawu ya bashi Hannu Wulakance ya amsa yana Fadin"Gani ina fatan ba shegiyar yarinyarnan bace kadawomin da ita ba ko? yafada yana kalllonsa inna fatsima taji hawaye ya kawomata,wai haryaushene Megida zai koma kallon Nusiba amtsayin ya"kamar kowa.


Mirmushi Kawu yayi yana Cewa"Ko daya bansani ba dai ammh bakine sukace na rakosu gun ka"Baba yayi kasake kan yace"Baki daga ina? kawu yajuya yace"kafito ka gansu mana "yana gama fadar haka ya wuce,baba yabi bayansa buguzun bugunzun yana fadin"bari naje inma wani abun ta tafka wlh saita tatsaya muku chan ku kadai"yafice yana fitowa tundaga nesa ya hangi Abbu da Alhaji Hassan suna jingine jikin mota,kodaga yanayinsu da suturun dake jikinsu uba uba tsalatsalan motocin dasuka zo dashi yasa baba ya isa wurinsu cikin rawan jiki yana gaishesu kamar zai kifa,Abbu yabasa hannu sukayi musabaha kafin Alhaji Hassan yamikasa.


Abbu yakallesa yace"Gunka muka zo ina fatan babu mtsala"Baba jiki na rawa yace"babu..babu Alhaji bara na daukomama tabarma mu zauna daga can"yafada yana juyawa cikin rawan jiki dukkansu da kallo suka bisa.


Yana shiga gidan yahau kwalama Fatsima kira,asukwane tafito jiki na rawa saboda tasan wannan kiran ba Alheri bane"Kallonta yayi yana Fadin"Kawo tabarma mai kyau Fatsima wlh manyan mutane ne sukazo"Shekesheke Fatsima ke kallonsa yau kuma mallam ita yake cewa takawoma baki tabarma,juyawa tayi takoma Daki tadaukomai Tabarma ta mikamai,ya amsa yana Fadin"Sa ruwa a filet da kufuna Fatsima zan Aiko a amsa"yafice da sauri kamar zai kifa.


Inna fatsima ta rike baki tace"oh ni fatsima meye mallam yagani yake ta rawan kafane",ganin bata da amsa shiyasa ta kama aikinta.


Cikin rawan jiki ya shimfida tabarman jikin bishiyar dalbejiyan dake bakin kofar gida,cikin Natsuwa suka zauna aka kara gaisawa Abbu ya kalli Baba cikin Natsuwa yace"Munzo nan ne muna neman Aure awurinka"Ba baba kadai ba Hatta kawu sai da ya razana Alhaji Hassan kuwa gyara zama yayi yana ganin Abun al"ajabi.

Baba yace cikin rawan murya"Wa...Wata yarinyar tawa kuma Alhaji"Kai tsaye Abbu yace"Yarka Nusiba Da mallam jibo yake riko"Baba yace"To...To....Abbu yace"Ina neman ma Dana Nazir Aurenta indai zaka bashi"cikin mamaki dukkansu kebin Abbu da kallo shiko yakima kallon barayinsu.

Baba yace"masha Allahu,Alhaji wlh na baku halak malak"Abbu yace"to masha Allahu Hassan akwai kudi Ahannunka"Alhaji yace"eh akwai yana fitowa dawasu bandir din yan dubu dubu ya ijiye atsakiya Abbu yace"To kamika sadakin danka da Hannunka"Alhaji hasan baida tacewa illa ya gyara zama yace"To nawa zamu biya? Baba ya amsa da cewa"Kubada talatin Alhaji ya isa",Abbu yamirmishi yace"Hassan basu dari,Allah sa ma Auren albarka,nan da nan kuwa ya kirga dubu dari cur ya mika ma Baba,baba ya amsa cikin ikon Allah ya mika ma kawu yana Fadin"Kai yakamata karike kudin tukun na"


Abbu yace"to Alhamdulillahi naji dadi ammh ina neman alfarman mu kammallah neman Auren yau din nan"Baba yace"bangane Nufinka ba Alhaji"Abbu yayi gyaran murya yace"Don Allah kaje yanzu kasanarma wanda yazama dole,so nake nakoma gida bayan an daura auren"Guri yadau shuru kawu da Alhaji Hassan suka zurama Abbu ido.


Baba ya mike yana Fadin"To to masha Allahu dama meza"a jira tunda sadakin ya kammallah bari na shiga gida na fito saimu karisa nan Massallacin Albani nan ake daura musu Aure"Abbu yace"To babu Damuwa.



Baba da hanzari ya shiga cikin guda,yana kwalama Saude kira,Saude tafito daga daki tana Fadin"Megida lafiya kakemin wannan kiran"Baba yace'miko min babban Rigata,Daurin Aure zani"Saude tace"Daurin Aure megida darana tsaka"Baba yace"Eh..Gyara ki gani jirana akeyi ya tureta ya shige dakin da sauri inna Fatsima dake wanki atsakar gida tana jinsu Aranta tana maimaita daurin Aure kuma?

Yana futowa Sabe da babban riga sai ga Dada tafito daga shashenta tana Fadin"Hayaniyar mu nake ji haka Abbakar'Baba yace"Dada yau dai Zan daura auren yarinyarnan kowa ma yahuta,"Dada tace"wata yarinya kuma"Baba yawani bata rai yace yana Nuna Inna fatsima da baki yace"Diyar wanchan mana datake chan tana watsewarta agari'"Dada da Saude suka hada bakin suna Fadin"wani dan Asaran ne zai kwasa"Baba yace yanabin Hanyar waje"Wama yasani nidai baza"a rabani da kaya ba Dada,koma dan mafiyane chan ta matsemata"


Dada tace"Tabdijam...lalle kam kiowaani mai tsautsayin ne banjimai Dadi ba ankwashi Sauran Titi"Saude ta karbe da cewa"Yo kika sani Dada ko abokin shashancin natane suka gaji da watsewar tasu shine za"ayi Aure"Dada tace'kuma Fa hakane saude don ba dan arzikin da zai auri wacce tazama uwar mata agida"inna fatsima dake duke  tana tsiyayar hawaye tsam ta mike tashige daki dariya saude suka sheke dashi ita da Dada harda tafawa,Inna fatsima tazauna bakin gado tana maimata zancen dataji wanda takasa ganeshi ammh komeye kenan zata ji gun yaya Aie.




Yana fitiwa yaci karo da makocinsa mallam sale yamai mgana suka sguga mota sai massallacin Albani suna zuwa kuwa ana hada hadan Yin sallar Azahar Suma alwala sukayi suka bi jam"i bayan ankammallah Sallah baba ya mtsa ga liman wanda *Mallam musa sahabi* wanda shine yabada sallar yana mai bayani yafalala furkarsa yana Fadin"Masha Allahu to bari mu sanar,nan da nan kuwa akayi sanarwa a lasifika cewa mutane su tsaya zasu Daura Aure,cikin abun da baifi dakika ashirin ba dubban mutane suka shaida Daurin Aure NAZIR ADAM GALADANCHI DA NUSIBA SADDIQ BUNZA Akan Sadakin dubu dari lakadan ba ajalan ba,Alhaji Hassan shi yayima Nazir waliyi ayayinda liman ya karbi na Nusiba.





Cikin Farinciki daurin Auren yatashi daganan kuma gida suka maida Baba bayan an sauke duka goron da kwalayen minti,Ayayinda Abbu yace"cikin Satin nan za"a kawo lefe,yana so zuwa ranar jumma"a Nusiba zata tare"Shidai baba komai akace sai ya amsa babu gardama,Kawu ya shiga gidan yana shiga dakin Innata ta mike tunkan tayi mgana kawu yace"Nasan mezaki ce ammh karma kice komai Domin komai kikaji to Tabbas Alherine"Inna Fatsima tace"Aure fa Yaya yace zai daurama Nusiba"Kawu yace"eh..An ma daura karki damu zan dawo tareda Nusiban da suwaiba komai kenan zakiji"


Dada da Saude kuwa kusan suman tsaye sukayi lokacin da Baba ya tsaya gaban kwalayen mintin ya dora dubu darin yana gaya musu sadakin Nusiba ne"Dada tace cikin rawan murya"kai Abbakar duk wannan natane"Ya amsa da eh kuma sunce zuwa sati mai zuwa zata tare"yana gama Fadar haka ya dauki kudin yana Fadin"Dada ashiga dashi dakin ki,anjuma zanzo muyi mgana"daga haka ya fice,saude da Dada sukayi tsum atsaye suna mamakin dimbin kayan da"akace duk na Nusiba wanda kaf cikin ya,"yan gidan ba wacce aka taba kawowa kwatankwansa.


Cikin Aminci da farinciki sukayi Sallama su Abbu suka jiya suka koma kano,Tun Ahanya Abbu ya tura Ammi da text yana cemata" * NAZIR YAZAMA MIJIN MAI BAKIN JINI FATIMA*


Ammi kuwa naganin sakon ta rangwada guda tana Fadin"Kamin Dadi Sadaukin Uba,Musty da Nusiba dake zaune gefe suka bita da kallon mamaki.











*nagaji walle,manage diz ban jin dadi*









*comment*
Share*
*vote*












*Janaf*✍
[4/11, 2:11 PM] 0mmer Farouk: *🧑🏻NAZIR🧑🏻*

     _*(The journalist)*_

*(Based on luv and Romantic story)*

  *Na*

*Janaf ce*✍

*Vote me on WATTPAD:Janafnancy*

© _*INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION*_🖊

*```DIDECATED TO SAHIBA HAFSART HAFNAN```







_i Dedicated dis page to u,Guyz NAZIR FANS1&2,JANAF FANS,WANI MATSAYI FANS,and u AUREN FARI FANS....wlh soyayyarku agareni mai girma ce,kusani janaf tana muku tsaftatacciyar soyayyah mara karewa_




```There was atime when throught that i just couldn't go on....```
And thats when you walked in to my life,and filled it with so much love and happiness...Eversince then you have become a special since,then you have be come a special part of life...Assalamu Alaikum janaf💕💕💕








11/12




     """Fitarsa ba dadewa Nusiba ta fito daga shashensu cikin shigar doguwar rigar baya baka,ta yane kanta da bakin dankwalin fuskarta tayi fayau wanda hoda kawai ta sanya da kwalli sai liptick,yau din tatashi duk zuciyarta babu dadi sakamakon,mafarkin datayi akan Innata data gani cikin wani Rami mai zurfi tana miko mata Hannu tazo ta ciro ta,ita kuwa da azama ta isa gareta,ta jefamata igiya,tarike ta fara jawota Ammh Abun mamaki ko rabi batayi ba,itama taji an zo an ingizata ciki,ana ta babbagan dariya mara dadi batasan ko wanene ba kawai Taga ya zuromusu igiya da ita da innanta Suka kama,ya jawosu suka fit,suna fitowa mutumin yajuya yafara tafiya itakuma,sai ta kwalamai kira ya waigo kenan ammh bata ganin Fuskarsa,fuskar ta fara bayyana ne,taji an kwala kiran Assalatu,cikin Razana da damuwa ta farka,daga barcin tadade zaune tana Saka tana warwara game da mafarkinta,nan da nan Taji ganin innatan ya bijiromata tayi kudirin zata tambaya agun Aiki gobe taje taga innanta bazata iya Sukuni ba inba ta ganta ba.



Jikinta duk asanyaye ta shirya tanaji kamar kartaje ko"ina ga yawan Faduwan gaba wanda tun Safe takeyinshi,ahaka dai Tashirya tama Kawu Da Anty Sallama tafito,kai tsaye ta nufi Shashen Ammi,ta Iske Ammi Afalo suka gaisa.


Ammi ta kalleta tace"Dota,meke damunki? naganki kin canza"Nusiba tayi mirmishin yake,tace"wlh Ammi haka kurum najini yau,bansan meke damuna ba"Ammi tace"Ayyah,yau da gobe ne dota...Kita maimaita HASBUNALLAHI WANI"IMAL WAKIL"Nusiba tace"To Ammi ngd.


Fitowar Musty shi ya katsesu shima cikin Shirin Fita,agurguje yace ma Ammi"Ammi ni na wuce"Ammi tace"Oh ni Fati..Breakfast kamar na girka kashi..Kowa ya fito sai dai ya wuce"Dariya Nusiba Da Musty sukayi Nusiba tace"ayyah Ammi,muje ni naci,don bazan bari yayi kwantai ba"Tafada tana Nufar Dinning din,musty Da Ammi suka rufamata baya.



Sai da suka karya kana Suka ma Ammi sallama Suka fice,ko amota haka Musty yaita tambayan Nusiba meke Damunta ya ganta so silent,cemai Tayi bakomai dole ya kyaleta bawai Don ya yarda ba.




Hon Ilu ya zuba abakin get din freedom aka wangale get ilu ya sulala motar ciki yasamu guri yapakata,yana kokarin Fitowa yazo ya bude mai Murfin mota,Abun mamaki Nazir da kansa ya bude motar yafito kuma bai tsaya jiran komai ba,yafara takawa cikin Isa ya nufin cikin gidan jaridar wanda ilu yayi haa!da baki yana bin Nazir da kallon mamaki,bashi kadai ba kowa yagansa sai ya rike baki,baima Nuna suna ganinsa ba Tafiyarsa kawai yakeyi.



Office din Manaja Ya tura ya shiga manaja dake zaune ya mike cike Da mamaki yana kallon Nazir,ai bai gama mamaki ba Sai da ya kariso fuskarsa cike da mirmushi ya mika masa Hannu yana Fadin"Brka Da safiya manajan Freedom Radio"Tsoro da firgici suka Hana manaja mikamasa Hannu Nazir yasaki kyatattace mirmishi yana Fadin"Baka musabaha ne kuma yau? Manaja yamika masa hannu ammh fa yana rawa bakinsa ma nayi yace"A"a yallabai...Umhm...Ina karba mana"Nazir yace"Olright...Yana zama kan kujeran dake fuskantan manaja yana Fadin"Plz hv a sit"Yafada ya Nunama manaja gun zama.



Kamar wani gaula yakoma ya zauna yana ayyana wani mugun Abun Nazir ya shiryomai,domin banza dai bata kai zomo kasuwa,Nazir yadade shuru kafin yakalli Manaja yace"Meye Sunan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login