Showing 57001 words to 60000 words out of 87333 words
Chapter 20 - Nazir Bok Complete Hausa Novels by Janafty.txt
MAMAN UNWAS 4r completing ur Amarzing Special fantastis and educated Novel...TURURUWA...Hakika kin baza dukkan basiranki da hazakarki da fikiranki,cikin kankanin lokaci sakon dakikeson isarwa ya isu ga al"ummah tabbas kin cancanta ajinjina miki domin salonki na daban ne basirarki na Tafiya dani hazakarki na jana salon rubutinki na dadani uwata wlh ke nake kwaikwayo domin salonki na dabam ne dana sauran,.
Ina Rokon Allah yabaki ladan fadarkarwa Kuskuren dake ciki Allah ya yafemiki mukuma yabamu ikon amfani da Abunda ke ciki Ameen Ameen
Tanque momma Tanque 4 the dedication Tanque very much mommah ta💕💕💕💕💕💕```
_*Alhamdulillah naji sauki,ina mika sakon godiyata ga dukkan masoyana wa"inda sukaiyita kirana awaya da wa"inda sukamin sannu ta chart wasu nasamu amsawa wasu kuma bansamu ba,da masu min addu"o"i agroups dadama ina godiya sakallahu fil jannah hakika masoyan janaf nada yawa wanda ambatonsu bazai yuyu agareni ba ammmh kusani kowani bugawan Numfashina kuna Raina,Janaf tana matukar sonka over*_
_Sakon godiyata gareki my Anty sis Naja"art godiyata tayi kadan agareki babu abunda zence sai Allah yasaka miki da gidan Ajannah firdausi janaf dinki tana matukar yinki over tawan_
30/31
"""yana kashe wayar takara nemansa ammh sai taji akashe,tasake gwadawa nan ma amsan dayace akashe Nusiba batasan sanda ta fashe da kuka ba,tayi wurgi da wayan,tafada gado tana kuka,kwana tayi tana kuka saboda yadda tasa rai ga zuwa taga innanta da kaninta da"aka haifamata wanda bata taba mafarki ba.
Koda da Safe kafin tatafi aiki sai da ta gwada nombarsa akashe,sai kawai ta kashe wayarta itama ta tura a drower, dataje gaida Ammi take tambayanta,yaushe zata Tafi,Rasa mezata cemata tayi sai tacemata,jibi zata Tafi,nan Ammi take fadamata gobe zasu ita da Anty saboda yanayin aikinta data bari jibi suntafi.
Dataje gun Aiki ne take fadama Rahma itama tayi murna,Abun takaichi kowa sai tambaya yaushe zata tafi yake,saboda takaichi da an tambayeta sai tayi kwallah,ko wayama da innan nata da wayar kawu sukayi mgana,Fashema da inna kuka tayi tana Fadamata yadda sukayi da Nazir Inna tayi mirmishinta irin na manya tace"To sai me,kiyi hakuri dama banga mezaki zo yi ba,ni lafiyata kalau kinji ki kwantar da Hankali kibi mijinki,ki kuma bi abunda yace"Nusiba dai rai bai so ba ta amsama innan nata.
Washegari tanaji tana gani,Ammi da Anty da Aisha wacce tace zata bisu suka Tafi zaria,suna Tafiya ko aiki ranar bataje ba takoma daki tadinga zabgan kuka Nazir ya bala'in bata mata rai,Sai yammah su Ammi suka dawo da labari mai dadi na uwa da da"suna cikin koshin lafy,Inna zainaba da jidda kuwa cewa sukayi Allah ya tsaresu su tsinta me,Ana fama dakai bama haka ba,mutum tsofai tsofai dashi da haihuwa itakam bada ita ba adawo lafy,kuji fa babu ma wanda yamata tayin zuwa.
*ABUJA*
Tunlokacin da Nazir ya datse kiran ya kashe wayar bai Tuna da bai kunnata ba sai zuwa yammah yana kunnah wa Nusiba yafara laluba ammh akashe tun yana maida Abun wasa,har ya kwana ya wuni ammh yaki samun layinta Tuni hankalinsa ya Tashi kawai sai yakira Ammi lokacin tana Asibiti,bayan sungaisa yake Tambayanta Nusiba Ammi tace"tana nan mana ko wani abu yafaru ne? Nazir yace"No..Ina kiran nombarta tunjiya akashe ne"Ammi tace"To gaskiya bansani ba sai dai inda nakoma nakirata na tambayeta"Sallama sukayi akan haka,ammah kafin Ammi takoma gida yakirata yafi sau uku tana cemai bata koma gida ba,Ana hudu ne tadauka ta cemai"Wai shin hala bazan koma gidan bane,kadameni nace kabari nakoma ko"Dole ya kashe wayan ransa baiso ba.
Sai dare Ammi takoma gida,tana ko komawa yakara kira,tsaki Ammi tayi taba Aisha wayar tace"Takaima Nusiba Nazir keson mgana da ita"Koda Aisha takai mata wayar tana bedroom dinta tana kwance kin karba tayi sai ma cema Aishan tayi tamaida mata wayar taga tata dama wani guri tashige.
Aisha tafita kenan yakara kira sai ita tadauka tafadamai Abunda Nusiban tace tsaki kawai yaja ya kashe wayar ya hau neman Nusiba akayi ko sa"a daidai ta kunna wayar Kiran yashigo sai da takusa katsewa kana tadaga.
"Ajiyar zuciya mai karfi Nazir ya sauke lokacin da Nusiba tadauki kiran,kin mgana tayi shiko shuru yayi yana sauraran bugawan Numfashinta akunnensa,Sai shine yace cikin sanyin murya"bab....Saurin rufe bakinsa yayi kafin yace"Nusi..What all dis? yafada cikin karya murya kawai sai Nusiba tasanyamai kukan shagwaba harda shessheka rudewa Nazir yayi yana fadin"Oh my god...Wai meye haka ne Nusi plz stop zuciyata bazata iya juran jin kukanki ba"yafada cikin nuna kulawa .
Dagatawa tayi tana ajiyar zuciya Nazir yace"Menene..? gayamin..Uhm waye yatabamin ke? yafada da sigar lallashi,Cikin shessheka Nusiba tace"Ba...Kai...Bane?Zaro ido yayi kamar tana gabansa yace'Nikuma?menayi kuma"yafada cikin sangarta tura baki tayi tace"ba...Ba..Kai..bane ka..Kace bazani gun mama ba sai ana gobe suna ba,karka manta nikadai mama ta haifa aduniya sai yanzu da Allah yabata,ko bata bude baki tayi mgana ba kasan tana bukatata kusa da ita tsakani ga Allah fa'"Tafada cikin Damuwa.
Gyada kai yayi kamar tana gabansa yace"Hakane...Gaskiya ban kyauta bako Nusi"Yafada da sigar zolaya yar dariya tayi kan tace"La...Ni bance ba haka ba",Mirmishi yayi yace'iz ok am srry ban kyauta ba dana hanaki zuwa ammh yanzu yaushe zaki tafi?yafada wit serious Tok,Gyara zama tayi dacewa"Ko yau ma ya Nazir kace sai na Tafi",rike baki yayi yana fadin"Ke yarinyarnan kin baci da sangarta pass 7 din ne zan sake ki sakaka kitafi zaria kamar na xare"yafada yana dan dariya.
Dariya takamata tanayi tana Rufe baki,shima dariyan yake kadan yanajin nishadi aransa naganin dariyan Nusiba dakatar da ita yayi dacewa"Ki bari first in d mrnin sai kiyi sammakon tafiya kinji don"t wrry nima dana dawo i promise u zanzo har zaria nama mama barka"rufe baki Nusiba tayi tana jin farincikinta yadadu tace"Da gaske ya Nazir...Da gaske zaka gidanmu kagaida mamata"Tafada cikin nuna zallan murna
Sai tsausayinta yakamashi baisan sadda yace mata'Insha Allahu daman in da niyyan zuwa sai kuma ga wannan,kozaki bari nadawo ne mutafi tare"Saurin cewa tayi "A"a inkadawon mazo taren ammh yanzu kam ban yarda ba"Shagwabemata yayi wai sai tabari yadawo dariya tahaumai tana Fadin"Duk Ammi ta bataka da shagwaba ko"dariya yayi yana bata lbrin abunda yafaru shida Ammi dazu daya dameta da kira ,dariya Nusiba ke ke kyatatawa Nazir na biyemata basu ankara ba sai da sukaji kiran sallan asuba hira tayi dadi basu sani ba,Nazir ne yace"Nusi kamar fa sallah naji ana kira,tana duba agogo taga 4:30 ai sai ta dafe kai tace"Da gaske ko ya Nazir kiran sallah asuba ne.
Ai kashe waya kawai Nazir yana mamakin yadda ya iya kwana yana waya da mace wanda dadin muryan Nusiba da shaukin soyayyanta yadinga jansa baisani ba,wanka yafada tare da dauro alwala ya wuce masallaci.
Itakuwa Nusiba bata sallah sai tamaida kai kawai ta kwanta tana tuna hiransu tana mirmishi ita kadai Abun yana sata nishadi matuka,koda ba son juna suke ba zaman lafyan dasukeyi yafimata dadi.
Gari na wayewa karfe 7:00 Na safe tagama duka shirinta sai ga musty ya shigo da kaya niki niki aledoji yace sako ne daga ya nazir yace akawomata,cike da mamaki take bude kayan ledan farko kayan baby boy ne universal hadaddu wanda haduwarsu tawuce misali,kala goma,da sabulai da lotion na jarirai,sai dayan ledan Atamfofine guda takwas da leshi biyu masu tsada da garari harda kudi dubu hamsim Musty yabata yace duk ya Nazir yace akawo mata,baki bude ta amsa,tana mamaki daki takoma ta dauki waya takira Ya Nazir yana dauka yace mata"Kin isa ne? cikin sanyin murya tace"Tanque so much ya Nazir bansan.....Shiiiii....Komai yayi ko"Yafada yana katseta gyada kai tayi tana cewa"Yayi Allah kara budi,mirmishi yayi mata kan yace"Zan shiga dakin labaru inkin Tafi Safe landeed dear"Daga haka yakatse kiran yana murmusawa koba komai hallayan nusiba na burgesa bata raina alheri ko kadan ne.
Nusiba haka ta kwashi kaya takaima kawu da Anty hardasu Ammi suka gani sukasa albarka ita Anty suka tafi Ammi tace sai ranar suna xata zo gun aikinta kuwa dama tuni tafadama manaja kiransa kawai tayi takara fadamai ya amince yamata fatan dawowa lafy direban su Ammi yakaisu har kofar gida yara suka shiga da ihu suna murnan ga Nusiba nan kayansu aka fara shiga dasu kafin su su shigo,gidan ko cike da makota ana ta dama kunun Kanwa Da Dada sukaci karo wacce harda Rumgumo Nusiba tana Fadin"Yar jikalle kin taho"Abun sai yazama wani bambarankwai daga ita har Anty da kallo suka bita na mamaki basu gama mamaki ba sai da suka karisa dakin inna Fatsima Dada tashigo tana musu maraba ita ta shimfida musu tabarma ta kawomusu ruwa ta zauna tana musu sannu da hanya sudai kawai da ido nake binta saboda mamaki harta fice Nusiba ta kasa hakuri sai da tace"Inna ina fa cike da mamaki naga Dada nata rawan jiki akanki damu gabadaya ne"
mirmishi inna Fatsima tayi kan tace"Hoho Nusiba baki da hakuri sam,daman Abunda aka gina shi ba bisa Allah ba ai baya harko lokacin rushewar komai ne yazo"Inna Tafada tana gyada kai Nusiba tasowa tayi tana zama kusa da inna Jaririn tadauka wanda keta sharan barci Abinshi takuramai ido lokaci daya kaunarsa tagama ratsa ko"ina ajikinta rumgumesa tayi tana fitar da kwallan farinciki.
Inna Fatsima ta kalleta ita kwallan tashare aboye tana cewa"Kibar kukan nan hakan zuwan yaron nan duniya shi yafitar da Abunda ke boye"Anty tace'Meyafaru ne mufa kinsamu aduhu"Inna Fatsima tace"tun bayan bayyana cikin nan Abubuwa suka fara daidaita kodaman tunkan cikin aboye yake shigowa dakina batare da sanin Saude ba ko Dada nidai nadage da addu"a kawai to bayan cikin ya bayyana hankali saude yayi matukar tashi,nasani tayi nata kokarin domin ganin bayan cikin nan Allah bai bata sa"a ba kulawa ta ko"ina ina fuskanta duk da wani lokacin babanki yana dan shakkan Saude,Ranar dana Fara Nakuda Saude batanan Dada ce kadai itazo ta tsaya akaina wanda ban dauki lokaci mai tsawo ba na haifi kaninki tun yazo duniya ya cancara ihu,daidai lokacin da Saude tasawo kai gidan bata gasgata ba sai da tafado dakin na ta iske Dada ta dagasa tana murna da Farinciki,lokaci daya kuma da shigowar Abban Nusiba bayan Dada ta Aikamai yazo,Saude hannu tadora akanta tana kururuwa da ihu tana Fadin"Boka ya fadamata itace zata Haifi mgaji acikin gidan sai gashi komai na kwabeta,lokaci daya taita warware abunda suka kulla ida uwarta harda Asirin dasuka miki na bakin jini da wanda suka min na farraku tsakanina da Babanki.
Nusiba ta zaro ido tana fadin"Inna harda ni suka ma asirin"inna ta gyada kai tana cewa"Ammh Allah ya nuna musu iyakarsu domin ai tana gani kikayi aure kuma kika kere mata sa"a"Anty tace"Wannan haka domin Mijin Nusiba kadai Abun muradin kowacce macece balle a gangaro dattako na iyayensa"Inna tace"Tabbas nima nagani kodaga karamci da girmamawa irin na mahaifiyarsa da mahaifinsa duk da bantaba ganin surikin nawa ba na yarda na amince dan"uwana bai miki zabin banza"Tafada tana kallon Nusiba wacce tadukar dakai tana tsiyayar hawaye na tuna halin Rayuwarta na baya.
Anty tace"To ya sauden ta kare domin ga duk alamun komai ya kare mata"Inna tacigaba da cewa"Nan da nan Dada tashiga tsinemata da zaginta tana kuka da idonta tana rokona gafara shiko babanki gyada kai kawai yayi kafin yace"Allah na gode maka dabakasa Fatima ta gujeni ba,ke kuma bazan ce miki komai kije duniya ta isheki riga da wando,nan tafice tana kirarin kozatayi yawo tsirara wlh sai taga bayana dani da Abunda na haifa to tafiyar ba dadewa sai ga uwarta tazo tasamu Dada da tijara wanda dalilin haka yasa Dada tasa Babanki yasaki Sauden saki daya kunji yadda komai ya gudana.
Anty ta jinjina kai kantace"Allah Abun godiya komai yayi farko zaiyi karshe insha Allahu babu Abunda zata iya yi Allah ya fita"Nusiba ta share hawayenta tana Fadin"Ashe itace dalilin dayasa nakasa samun soyayyah mahaifina ta tsawon lokaci,nakasa sakewa cikin yan"uwana da kawayena ba...Wlh tsakanina da Saude sai Allah ya isa"Takareshe ta hasala inna Fatsima tace"Ki yafemata domin inda ba da umarnin sa ba da haka bai faru ba,kibarta da wanda yayi ta shiyasan maganinta.
Nan sukai ta tattaunawa,Ammi takira Taji ko sun isa sukace sun isa lafy,kawu ma yakira akaba inna suka dade suna mgana yana kara jadaddamata data kara dakewa da addu"a,Sai gashi Dada har kasa tana rokon Nusiba data yafemata,rumgumeta Nusiba tana jin wani farinciki karo na farko da ta san dadin jikin kakanta,Da daddare ma haka Baba yakirata dakinshi yanata bata hakuri wanda sai da Nusiba tayi kuka,saboda Farinciki sai gashi sundade suna hira da baba yana tambayanta game da gidan Aurenta nan take fadamai ma tana aiki yaita samata albarka tare da mata Nasihan ta rike Aurenta da amana takuma yi ma mijinta da biyayyah.
Ranar kwanan farinciki Nusiba tayi wanda ta manta da Ya Nazir sai da safe suka kwama,domin tasamu mussd cll din sa dayawa data kirasa kin dagawa yayi sai da tura masa text kana yakirata,kin mgana yayi sai da tayi tamishi shagwaba tana narkemai kana ya hakura,ammh yace sai ya rama in yadawo,Sai gashi har inna Fatsima Nusiba taba taita mishi godiya,Kunya takama Nazir yaji duk ya tsargu kansa ace dan wannan hidiman ji yadda inna take mai godiya tare da sa albarka ransa yayi fari yaji duk ma mai yama Nusiba da ahalinta bai fadi ba.
Gurin yammah sai ga Rahma tazo ita da Ummanta wanda Nusiba ma batasan da zuwanta ba Rumgume juna sukayi suna murna,Inna fatsima ma taji dadin zuwan Maman Rahma wacce takawoma innan yajin jego cike dawani botiki, nan sukaita hira itakuwa Nusiba takoma yar kakanta domin komai Dada tasamu Nusiba shiyasa Nusiban ta tattara rahma suka koma dakin Dada suka yada zango.
Ranar suna yaro yaci sunan MUHAMMED NASIR Wanda sunan kakansu ne,Raguna biyu baba ya yanka,girke girke kuwa sai wanda ya gani,tuwon shinkafa,shinkafa jalop,alale waina Ammi kuwa dazata zo tazo da sinasir da miyar ganye wacce taji kashin rago da manshani masha Allah,drinks kuwa Nusiba ta bada kudi aka sauke harda ruwa saboda masu bukata,inna Fatsima kuwa shiga kawai take tana Fita cikin rantsatsun kaya na alfarma domin itama Ammi da ledoji guda tazo na Abun arziki ita Abbu sai wanda yagani Nusiba ba ba"a barta abaya ba shiga kawai take tana fita,Su zubaida Da Amira sai da sukazo ganin gulma akwai ,zuciyarsu takusa bugawa saboda bakin ciki wanda ba wanda yasan Tafiyarsu suka koma suka kaima lami rahoto wanda takeji kamar tayi tsuntsuwa taje tashake innan da dan duka su mutu,lami ce ta tai taushanta kafin tahakura,su ko zubaida hassada yacikasu domin sunga yadda Nusiba takoma wata hajiya da ita,ko kallo ma bata ishesu ba kamar bata sansu ba.
Haka akayi taro aka tashi lafy,Ammi Aranar takoma,washegari Rahma da mamanta suka koma,Da Nusiba taso tashare kafa baba ya warkatata dayan washegarin tabi Anty suka koma cike da kewan kaninta Nasir wanda tashaku dashi matuka.
Da Farinciki Nusiba tadawo domin ita ayanzu bata dawani damuwa Aranta komai yana Tafiya daidai game da aikinta ma masha Allahu domin shirunsu ta ko"ina yana da farinjini bangaren Nazir ma komai na tafiya normal domin yanzu wuni sukeyi waya da juna in daya baiji daya to bafa sukuni Nazir har mamakin kansa yake yadda Rayuwarsa tachanza cikin lokaci wai shine yake zama yana Tunanin mace har ya bata lokacin wurin yimata waya yana zagewa gurin gayamata kalamai masu kwantar da hankali yana biyemata tana mai shagwabanta,duk Nazir bai fahimci cewa he fall in love ba shi atunanin sa kawai ya shaku da ita ne.
*****************
wannan karon sai da yayi 4weeks kana Yazo weeked Ranar daya tashi zuwa,Ranar monday ce babu wanda yasan zai dawo domin ko Aranar ma da safe sunyi waya ammh bai ce ba mata yana tafe ba harta shirya tatafi gun aiki,wajen 11:00am ya shigo koda yazo inna zainaba kadai ya tarar agidan sai jidda wacce tana ganin sa tafara wani yauki ko zama baiyi ba ya wuce gidansu Jidda taso ta bishi inna zainaba ta mata alama da ido da karta bishi ranta baiso ba,tahakura.
Wanka yayi kafin ya sauko falon kichen ya nufa yadauko ruwa yazo falo yana zauna,tun zama na mai dadi har yagaji da zama waya yadauko yana ta kiran Nusiba batayi picking, ba ransa yabaci sosai yabata kusan missd call hudu ammh no respond yana kara na biyar din Rahma tadauka lokacin jakar Nusiban yana office dinsu taga anata kira shiyasa tadauka.
Rahma tace"Hello...."Nazir yaji ba muryan Nusiban bace yasa yace"plz who iz on d line"Rahma ta cire wayar akunne tana kara kallon wanda ke kira baki ta rike kan tace"ina wuni..Rahma ce"yamutsa fuska yayi kan yace"ok..Ina ita mai wayar"Rahma tace"Tana dakin gabatar da shiri ne"Shiri...?Nazir ya maimaita kan yace"Shirin me kuma ita dawa ne? Rahma bata kawo komai ba tace"Shirin Freedom takuce,Ita Da Nura Dabo"Kutmar ubanchan Nazir yafada aransa kan ya katse wayan mikewa yayi yana maimata Nusiba na chan na shiri da wani gardi shiyasa taki daukan call dinshi.
Azafafe yahaura sama kaya ya sanya riga da wando na kamfanin Armani,makullin mota yazara yafito cikin takun isa fuskar nan babu Annuri yafada mota,sallau namai mgana ko jinsa baiyi ba,yana tafe ahanya yana turituri shi kadai kamar ance ya kunna radio motan yana ko kunnawa muryan Nusiba tadakeshi sanda take cewa" _Ai yakamata wannan azumin akada ma Nura Dabo kidan gwaranci saboda tazuran cinka yayi yawa_
Dariya yayi yana Fadin" _Harda kema ko Hajiya Nusiba to kedin yaushe kikayi balle har kisama wani ido_
Nusiba tace" *To ai masu saurare suka aiko da tambayar yaushe zakayi Aure shine nafada musu gaskiya ko ka....*
Radion motan Nazir yadaka da hannusa wanda sai da yafashe sabida zafin kishi dana zuciya jiyake kamar zuciysrsa zata fashe saboda kishi lokaci daya halittarsa ya canja idanunsa suka chanza launi jiyoyin kansa suka mike radam,kirjinsa na cida saboda kunnuwansa suna mai amo da muryan Nusibansa da wani gardi hartana mai dariya da mirmishi.
Cikin gudun ganganci ya shiga gidan radion wanda mutane dadama suna mamakin wani mara hankali ne,ko gama parking din motan baiyi ba yafito cikin bacin rai gadan gadan ya nufi cikin gidan kallo daya zakamai kafahimci tsatsan bacin ran daya ke ciki.
Manaja na zaune labari yazo mai jiki na rawa ya fito daga office dinsa domin yasan zuwan Nazir wuri wlh ba alheri ba ne....
*Comment*
*Share*
*Vote*
*Janaf*
[4/11, 2:15 PM] 0mmer Farouk: *INTELLIGENT WRITERS ASSO*📝
```{onward together}
*NAZIR*
_*(The journalist)*_
*Based on luv and Romantic story*
*Na*
*JANAF CE*✍
*SADAUKARWA GA SAHIBA HAFSART HAFNAN*
_*Attention:Gaskiya banajin dadin yadda wasu sukemin ba, haba karfa ku manta nima fa dan adam ce inada nawa sabgogin rayuwa gashi banda ishasshiyan