Showing 3001 words to 6000 words out of 87333 words
Chapter 2 - Nazir Bok Complete Hausa Novels by Janafty.txt
da safe Fatsima ta Haifi sunkuceciyar yarta sak mahaifiyarta sai dai kawai bata debo hasken uwarta ba sai ta dauko bakin uban,Sanda Saddiq yaji haihuwan Fatsima harda tuntube ya buga saboda Sauri ammh anguwan zoma na fitowa da albishir din Ansamu mace sai da yakwadeta da mari saboda haushi bai yarda ba sai da yashiga ya ganin ma idonsa ko kallon yar baiyi ba yakalli Fatsima yace"Tir da haihuwarki mara amfani me ake da haihuwar diya mace ki haifo namiji shine haihuwa nikam har abada bazan taba farinciki da haihuwarki ba"Daga haka Yasa kai ya fice rai bace haka Dada ma tazo taita mata fada harda cewa mata da gangan ta haifi mace don kawai ta kuntata musu to Ta Allah batata ba dadin Abun ma yanada wata matar wacce zata iya haifamai duk dan dayake so"Itama ta fice Saude kuwa zuwa tayi tatasata tana tsuntsuran dariya tana cewa"Mai cikin da Namiji ashe...."Sai ta kara sa dariya fatsima tana kwance hawaye na zubomata saboda takaichi da bakinciki cikinsu babu wanda yasake lekosu Allah yasa lafiya kalau tahaihu ita da kanta ta rarrafa ta fita tasama kanta ruwan wanka tayi ma yarta tana yi tana kuka yaro tasamu ta aika yaje yagayama yayanta yanajin lbri yazo da Fatsima tafadamasa abunda yafaru sai da yayi kwallah ya kalle ta yace"Karki damu kanwata kisama yarki albarka...Insha Allahu sai Saddiq yayi alfahari da zamowarshi uban mace"Haka Fatsima ta amshi yarta tamata addu"a Allah sarki yaya jibo shine yaita dawainiya da ita yasiyamasata kayan fitar suna ya kawo mata masara yace suyi fate ranar suna yazo da tunkiya aka yanka Yarinya Taci Sunan *NUSIBA*...Yaya jibo shida kanshi yaradama Nusiba suna wanda yan"uwanta da makota suka mata kara akayi taro lpy aka watse.
To bayan suna Nauyi yayima yaya jibo yawa gana Fatsima da yarta ganashi ga kuma mkranta to bayan tayi arba"i kawai sai ta aika makota cewa tana wanki ba laifi ana kawowa in anbiyata tadan saima Nusiba wani Abu,acikin gidan kuwa babu wanda zaice ma matar gidan nan ne domin komai an wareta abunda ta lura dashi yanzu Saude mulki take zubawa ita da uwarta harta Dada sai Abunda tace takeyi domin bayan Haihuwar Fatsima lami taje gidan boka tasa aka asirce Saddiq da uwarsa itakuma fatsima aka maidata baya yarta kuma aka sanyamata bakin jini wanda ko wasa take cikin yara sun dunga hantaran takenan shiyasa ma tadaina fita wasa take nane da uwarta.
Tasowar Nusiba yarinyace mai kokari da hazaka tuntana karamarta take dazuciya da tsiwa yadda ubanta ko kallonta bayayi to itama tunda ta lura babu mai kaunarta sai mamanta shiyasa tana nanike da ita in ba ita ba to kawunta jibo...Shekarar Nusiba shida aduniya saude ta haihu abun mamaki mace ta haifa ammh yadda kikasan ba"a taba musu haihuwa ba yadda yayi barin Naira Dada kuwa nan take wuni daukan ya"ranar suna yarinya taci zubaida bayan ita tahaifi Amira daga ita sai Habiba daga su bata sake haihuwa ba Namijin dai kam har yau Allah bai bashi ba.
Bambamci kiri kiri Fatsima take gani agidan suna fara tasawa aka sanyasu mkrantan kudi mai tsada ammh ga Nusiba wajen shekara 8, agida bata shiga mkranta dole tasa tafadama yaya jibo shikuma ya yadan hado yazo da kansa yakai wata mkrantan Gwannati tsoho Abdullahi yakaita saboda girmanta yasa aka sata a prim 1, To haka dai Rayuwa ta cigaba da gungura cikin kunci da wahalar rayuwa har Nusiba ta kammallah primary tafada Goverment secondry sch tudun jukun da taimakon mahaifiyarta da kawunta wanda sukeso sai tayi ilimi da karfinsu sukuwa su zubaida mkrantan kudin ake ammh ba'a gane komai zuwa kawai suke basusan komai ba sai kuLa samarin layi.....
Bayan wasu shekaru Har Nausiba ta kammallah secondry sch dinta cikin Nasara da sa"a duk mkrantan gwannati tayi ammh yarinyar akwai kwanya da hazaka tun tana karamarta asanta agidan bata daukan rai ni macece dabata daukan Wulakanci daga wurin kowaye shiyasa kullum Babansu yadawo sai an kai karanta su zubaida shikuma yakira ta yaita zaginta ita da uwarta abun nadamunta sosai shiyasa tsanar babanta ya darsu Aranta itakuwa Dada kwahon zuka tasa akan nusiba sai ta fito da miji to wazata fito dashi itada bata taba saurayi ba ke ko kawa batayi saboda bata da farinjini agun mutane batason dalili ba...Ana haka manemam su zubaida da Amira suka turo akasanya musu rana shikenan shafin gori ya bude Nusiba bata da halin fitowa tsakar gida saude ta dinga yaba mata mgana kenan ita da yayanta Dada kuwa da babanta wlh kamar su kasheta ita abunma yadaina damunta innanta ne ke komawa daki taita kuka,To ahaka dai aka sha bikin su zubaida aka kai kowacce gidan mijinta wanda da bikin saboda yada maganganu ita da innanta ko waje basu fito ba saboda bakincikin Halin Rayuwar dasuke ciki.
To ya rage gida daga ita sai habiba wanda itama ana mganar aurar da itane abubuwa sun dagulema Fatsima domin gorin mutanen anguwa kadai ya isheta banda na cikin gida dole tasa ta fadama yaya jibo wanda yakoma kano da zama bayan ya kammallah fce sa wani yamai hanya yasamu masinja a Buk office din VC Adam galadanchi har yayi aure da matarsa Suwaiba wacce yar nan kano ne a rijiyar zaki take dayaji hankalinsa ya tashi yana dawowa yafarama nusiba cukucukun samun gurbin karatu a Cikin jami"ar Ta bayero wanda da Taimakon VC Adam galadanchi Nusiba Tasamu gurbi a mkranta akabata masscom hakika Abun yayi ma ya jibo dadi wanda saboda murna har ya kasa boyuwa shida suwaiba suka shirya suka zo har gidan suka shaidama Fatsima yakuma fadamata zai dauke Nusiba takoma wurinshi da zama Allah zai rufa asiri Fatsima sai da tayi kuka saboda farincikin domin dauke Nusiba a garin zaria kamar dauke mata wani nauyi ne,koda ya jibo yafadama babanmu zai tafi dani yasamanmun mkrnta ko ajiknsa illa cewa da yayi Wlh daya taimakesa domin ganinta ma bakinciki yake karamai yarinya ta balage agiba ba mashinshini ita kuwa Dada cewa tayi"wani boko za"a dai karuwanci dama ansaba to Allah raka taki gona in ma da Fatsimar zaka hada duk ka hada wlh ka ragemana mugun iri"miemishi kawai yamata baice koMai ba Nusiba tayi kuka dazata rabu da innarta kuma tadaukan mata alqawari zata karatu domin tazo ta kwatarma innanta yanci.
Course din da"a ka bata yayimata dai dai ko banza zatayi amfani da damarta ta yar jarida tayaki masu hali irin na Abbanta komawar Nusiba kano ta bude sabuwar Rayuwa domin kawu da Anty wlh goyatane kadai basayi saboda gata komai suka samu ita saboda dai su cire mata damuwa tafara karatunta cikin sa"a da nasara bata wahalar da kanta wurin shigema kowa ba saboda tasani bakin jini gareta ita kadai ke rayuwarta itadai kawai tasamu cikar burinta.
AFTER 4YEARS
Nusiba ta kammallah karatunta cikin nasara da taimakon kawunta daya zama jigonta tun bayan zuwanta kano sau daya taje zaria wanda tayi nadamar zuwa domin innata tazama kamar tsohuwa saboda wahala wanki da surfe shine sana"arta take samun rufin asiri shikuwa babansu arziki yaci uban nada ammh Nusiba da uwarta ko kwabonsa ba suci zuwan da tayi Dada tacemata tsohuwar kilaki taji kunya dai ga kannenta nan da ya"ya ye har biyu itakuwa ta zauna yawon duniya Abun yamata ciwo harta maida mata tace"Eh kilakin ai ko banza za"a kira sunan danki ace shine uban kilaki kekuma aki raki a kakar kilaki kinga kenan kike kika haifi kilakin da kanki"Ai nan na danan Dada Tahau kuka babanmu nadawo tafadamai karya da gaskiya yazo har kan gadon innata yamin dukan da sai da nakwana biyiu ban iya tashi ba Innata da kanta ta hadamin kayana da kudin mota takaini har tasha ta kalleni tana kuka tace"Nusiba ki kije don Allah karki sake dawowa in ma gani na kike sonyi in nasamu lokaci zan zo muga juna....Kikoma gun yaya jibo da izinin lahi Rayuwarki bazata tagayyaraba albarkata tana bibiyanki aduk inda kike...Kije Allah yama Rayuwarki Albarka ammh kuma yata kowani hali kika samu kanki ki zama mai biyayya ammh kada kizama wawiya ataka ki kizama mai kwatarma kanki yanci ako'ina kika tsinci kanki"Fatsima kuka Nusiba kuka haka suka rabu cike da kewa Allah sarki Rayuwa kenan.
Tundaga lokacin bata kara zuwa ba tamaida hankalinta akaratunta tayi bautar kasarta ta gama lpy duk wanda ysan Nusiba to yasanta rayuwarta ira daya takeyi ko"ina ko taje saboda sanin yadda take da bakin jini sai ya kasance Anty ne da kawu abokan hirarta da sha"wararta ako'ina suda basu taba haihuwa ba Tafi shekara da amsan result dinta ammh babu wani mgana aiki tanema tanema ammh shuru kakeji shikanshi kawun yana ta ma kokari duk inda yasan za"a samu yana kaimata takardunta ammh babu Nasara to sai Allah yakaita Freedom shima din kamar baza"a dauketa ba sai daga baya kuma suka dauketa akan zasu fara gudanar da sabon shiri manaja ya fadamata dukkan sharaddan Nazir ammh saboda kagare take da neman aiki shiysa ta amsa da rawan jiki...
*Wannan shine silan komai*
comment
Share
Vote
*Janaf*✍
[4/11, 2:11 PM] 0mmer Farouk: *🧑🏻NAZIR🧑🏻*
_*(The journalist)*_
*(Based on luv and Romantic story)*
*Na*
*Janaf ce*✍
*Vote me on WATTPAD:Janafnancy*
_*INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION*_
*DIDECATED TO SAHIBA HAFSART HAFNAN*
_*Ina godiya masoyana a duk inda kuke duka duka pages uku kadai nayi ammh naga zallan soyayyah...Ina matukar godiya da soyayyanku ina so kusani a duk inda nike ni janaf ina sonku*_
```Har naji kunya matuka ace sai yanzu zan baku kyautar pages...Meemartjj marubuciyar SO KO WAHALA...Dake Safiyyah Aliyu wakili marubuciyar MASAUKIN SO....Kudin nawane tunkan nafara amsa kaina a marubuciya ku makotanane na gida da waje ina godiya sosai da duk kan kulawarku ga wannan page din kyauta na baku kuyi yadda kukaga dama shi```
5/6
Cak suka tsaya ammh sukansu jikinsa rawa yakeyi duk da suna kokarin boyewa,Nazir yayi taku daya biyu yasanya hannu ya zare bakin gilashin dake idanunsa yadago idonsa ya sauke kan ma"aikatan dasuka zagaye gurin ai yana dagowa naga kowanne yafara darewa idanunsa na kallah sai da naja baya saboda yadda naga kyawawan idanunsa sun rikide sunkoma jawur kamar barkonu wasu jiyoyi duk sun fito a saman kansa ba kyan gani tsaye yake kawai yana fidda wani huci kamar tsohon zaki taku yafarayi yana nufar inda manaja yake wanda tunda yayi zaman yan bori bai kara tashi ba ganin Nazir ya nufosa ai sai yaji kamar fitsarin dayaketa makalewa ne yafara zubowa, sai da yazo kusa dashi ya sanya hannu kamar zai kaimai naushi kawai sai ji kake tus..!ya Naushi wata randan flower dake bayan manaja ya furta cikin tsawa da fushi"Who is she...? Ai ba manaja kadai ba hatta Rahma sai da ta kamkame Nusiba tana fadin"Kinji ko Nusiba me ya kaiki? kinsan wa kika mara kuwa?"Nusiba ta saki Rahama tana cewa"Sanin ko shi waye bai dameni ba,Rahma nidai bazan bari don yana takama da kudi ba ya banzatar da kima ta ya mace ba" tana fadar haka ta wuce ta zauna fuskanta ba alaman tsoro, Rahma tabita da kallo mahaukaciya domin duk wacce tayi abunda Nusiba tayi to kila bata cikin hayyancintane.
Manaja kuwa yana dagowa suka hada ido da Nazir wanda yazubamasa jajayen idanunsa cikin kyarma da rawan baki manaja yace"Ba...Ban...Bam sani ba yallabai sunan...."shout up yafada da karfi naman kirjinsa na wani jida yace cikin muryan bacin rai"awa goma na baka ka bincikomim wacece ita dawa take takama da har zata iya daga hannu ta mari NAZIR FREEKING ADAM GALADANCHI" yana gama fadar haka ya wuce da sassarfa ya nufi mota da hanzari ilu ya budemasa sai da ya shiga kana yace"All abount her nakeso..10 hours kada kawuce koda da kika dayane,nan da kafin yammah nakeson na nuna ma yarinyarnan waye Nazir"Yana gama fada ilu ya maida kofa ya rufe yashiga bangaren direba yaja, suka fice da gudu suma gound din nashi shiga motan sukayi suka rufamusu baya,ai manaja dake zaune baisan sadda ya mike da hanzari ya nausa office din su Nasiba yana fadin",Nusiba kin san ko me kika aikatama Rayuwarki kuwa? What of all dis Nusiba"Nusiba dake zaune ta mike tana fadin"Haba yallabai wai ya kuke son kuga laifinane,shi bakuganin nasa zarafina fa kawai yaso yaci haka kurum me na mai"Manaja ya dafe kai yace"Nusiba komai ya miki bai kamata ki maresa ba wlh inajin tsoro saboda nasan Nazir bazai taba kyaleki ba"Nusiba tadanyi jim tsoro yafara shiganta tace"Babu abunda ya yamin ni ga Allah na dogara"cike da mamaki manaja ke kallonta kafin yayi mgana ta rigasa da cewa"yallabai Amun afuwa in koma gida wlh banda lpy ciwon kai ke damuna"gyada mata kai kawai yayi yama kasa mgana Sallama tama Rahama tafice suka bita da kallon, karshe domin dukkansu babu wanda yasa ran kara ganinta...Topha
tana fitowa abun yabata mamaki yadda aketa kallonta data waigo kuma akauda kai sai abun yakara bata tsoro,da sauri ta tsaida mai napep ta shiga tana waige waige jikinta bai bata ba tana tsoron karfa yasa asaceta,data shiga uku bata da kowa daga kawu sai Allah.
Sukuwa ilu yana daidaita mota kan kwalta yabata wuta ammh sai me yarasa ina suka nufa kuma yana tsoron yin mgana asauke akansa kawai da sunkai round abount sai yayi newton ya kara komawa Nazir dake baya abun mamaki hannunsa dafe da kunci ya lura da zagayen da ilu keyi dashi yace cikin tsawa"Zagayen me kake dani ilu"ilu ya tsorata cikin dakiya yace"Yallabai to ina muka nufa? Abuja?Abuja..? ya maimaita kafin yace cikin sanyin murya" inkoma Abuja batare dana Dau mataki game da yarinyarnan ba, kake nufi? Ilu ya girgiza kai yakafin yayi mgana yarigasa da cewa"muje gida kawai"yafada cikin wani irin yanayi wanda saida ilu ya waiga yana kallonsa,shikuma ya kwantar da kansa abayan kujera idanunsa a lumshe suke ammh hannunsa na dafe da kuncinsa.
Shikuwa manaja yana komawa office dinsa,yakasa zaune ya kasa tsaye, yamarasa ta ina zai fara,kan waya ya jawo ya nemo wani abokinsa bello wanda anguwansu daya da Nusiban.
Bayan sungama gaisawa,manaja yace cikin damuwa"Bello wani taimako zakamim don Allah"Bello yace"Haba mutumina sai ka ma rokeni"Kawai ka fada, indai ina da halin yimaka shi zan maka"Manaja yace"Wata yarinya nakeson kayo min bincikenta,komai da komai daya dangaceta"
Bello yayi dariya yace"shege nawa wato ka hango wata,zakama madam kishiya ko? manaja yayi dariyan yake yace"bello bafa wasa nake ba,kataimaka min nan da awa goma nakeson komai ya kammallah"Bello yace"tom babu komai,bani cikakken sunanta da adireshinta"Manaja yace"kaji kuma fa wlh bansan adireshinta ba kawai dai nasan anguwanku daya tafara aiki damu satin daya gabata"cikakken sunanta ya bashi,inda bellon yamai alqawarin cewa zai yi iya kokarinsa yaga ya bincikomai.
Afirgice Nusiba ta shigo gidan,Anty na kichen taji shigowarta ta fito tana rike baki,tace"Lpy kika dawo yanzu? Nusiba ta yamutsa fuska tace"Anty kaina ne ya dameni da ciwo wlh"Anty tace"Ashsh!sannu Allah ya sauwake,ki shiga daki saman mirror zakiga panadon kidauka kisha,inaga rashin hutun da baki samune kwana biyu"tafada da alamar tsausayawa.
Nusiba ta shiga daki tana rangaji sai da tadauko panadol din,tasha kana tazo ta kwanta tana sake sake duk da tsoro na cinta,bai hanata cewa a fili ba"shi ba Allah bane,balle yamin wani abu"daganan barci yayi awon gaba da ita.
Cikin mintina sha biyar suka isa bakin wani tamgamemen gidan, sukayi hon megadi ya budemusu suka sulala cikin parking space ilu ya fito jikinsa na rawa ya budemasa suma bodygourd din nasa fitowa sukayi suka jeru suna jiran fitowarsa ,sai da ya bata lokaci kafin ya fito abun mamaki da ban dariya,hannunsa na hagu na dafe da kuncinsa ya fito,da sassarfa ya kama hanyar falon sukuma ko tak baice musu ba,kuma ba wanda ya motsa.
Ko sallama bai yi ba yasaka kai falon,Wanda musty ke zaune,kan daya daga cikin kujerun dasuka ma falon kwanya waya yake dannawa gefensa Aisha ce zaune taci kwalliya suna hira,gafe daya kuma jidda ce zaune tadora kafa daya kan daya tana taunan cimgam,taci uban makeup kamar wacce zata gasan kyau,adaya gefen ko,inna zainaba ce ta baje kan kafet,gabanta filet din ferfesun naman kaji diba kawai take ba saurarawa.
Ko kallonsu baiyi ba hannunsa dafe da kuncinsa ya kama hanyar haurawa sama gabadayansu suka zubamai ido,suna kallonsa da mamaki jidda ce ta mike tana wani takun yanga ta sha gabansa tana fadin"wlcm broda Nazir"cak ya tsaya kafin yadago idanunsa jawur ya sauke akanta,saurin ja da baya tayi data ga yanayinsa sai dai me ta makara domin shi Nazir rikide mishi tayi takoma mai Nusiba.
Ja da baya takeyi yana biyota kafin su musty su mike yasanya hannu ya damki wuyanta yana fadin"i will kill u"
Inna zainaba dake zaune tayi wuf ta mike a fusace ta isa garesu tana rike Nazir tana fadin"sakarta don ubanka"tafada cikin fusata yayinda datake kokarin bambare hanunsa ajikin jidda wacce idanunta suka firfito saboda wahala.
Hayaniyar da Ammi taji ne ya fito da ita daga kichen,ammh sai me Abunda taci karo dashi ne ya sata daskarewa a tsaye tace cikin tsawa"NAZIR..!tafada da karfi ammh ko waigowa bai yi ba,sai da yaga tana neman sumewa kana ya jefar da ita kanta yaje,ya bugi kujera sai jini,inna zainaba ta dago tana kallonsa tace"Kaniyarka nace"Nace kaniyarka!kashemin ya' zaka yi? Kokuwa soyayyah haukane? in baka sonta ai sai ka fadamata bawai ka shaketa zaka kashe ba"Tafada kamar zata dakesa
Ko kallonta baiyi ba yafara haura step da bibbiyu yake hawa cikin zafin nama harya danganta da dakinsa yashiga ya bugo kofa ji kake gam!
Musty ya kalli Ammi yace"Ammi Meya samu broda ne? ban taba ganinsa cikin wannan yanayin ba"
Ammi tanufi gun jidda tana fadin"ban sani ba musty!koma meye ai sai ya bi ahankali ko? tafada tana riko jidda dake dafe da kanta,inna zainaba tace"dakata!Ammi ta tsaya tana kallonta,inna zainaba tace"karki kuskura ki tabamin ya"Komai ya faru da sanin ki bakar munafuka kawai"
Ammi taja baya tana fadin"Haba zainab, kan me zan ce Nazir ya daki jidda? Inna zainaba tayi tsaki"mteswww dadin Abundai ba"a chanzama tuwo suna,duk abun mutum wlh mu din munzama dolen mutum,kuma aure in nace dole ayi wlh ke baki isa ki hana ba"tafada tana harararta.
Sai kawai Ammi ta juya takoma kichen din Ranta na kuna,Aisha tace takama jidda su wuce,Musty dake tsaye yace"inna ki bari in mata dressing din gurin plz"Harara ta zabgamai tana"dallah gafara chan, dan neman solobiyo ai kana ganin sadda yakusa kashemin ita,me kayi? tafada tana tsaresa da ido,sunkuyar dakai yayi yana fadin"yi hakuri inna"tsaki taja kawai tace"Aisha wuce muje,yayan ai zai dawo gidan"
Haka ta tallabeta suka fice,musty yakoma ya zauna yana ayyana abubuwa dadama Aransa,saman dakin da