Showing 39001 words to 42000 words out of 87333 words
Chapter 14 - Nazir Bok Complete Hausa Novels by Janafty.txt
story)*
*Na*
*JAMEELA UMAR*
_*Janaf*_✍
*Vote me on WATTPAD:Janafnancy*
© _*INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION*_🖊
*```(onward together)
*JUSZ GIVE US A FOLLOW*✔
*```DIDECATED TO SAHIBA HAFSART HAFNAN```
_*Wannan shafin kacokan mallakin all JAMEELA"S over d world ne,shafin yau Namu ne,inkinsan sunan jamila chasisc,jami,jamila ta iya daura zani,jamila ta iya daura Atamfa....To daku nake shafin namune kutaho mutaru mu yagalgalashi son ranmu*_
_ATTENTION:Don Allah masu bina pc suna fadamin wai ka ga yadda zanyi,insaka Nazir ya wulakanta,Nusiba tabashi wuya,yakamu da sonta matsananci,to plx and plz suyi hakuri na farko dai ni nazauna tunfarko na tsara farko da tsakiya da karshen lbarina babu wacce nanemi shawaranta,so ku barni na tsara abuna yadda yake bani jin dadi sam Abunda wasu kemin gaskiya,fatan za"a kiyaye_
*ESHAN AUFANA,KITAHO YAU RANAR TAKICE,SOYAYYAHRKI GARENI SAI DAI INCE MASHA ALLAHU...Tanque 4r luv support and care,janaf relli care abount u*💞
*NOT EDITED*
21/22
"""""Nusiba na cikin kichen taji shigowar mutum cikin falon kuma koda ta leko,babu kowa kawai sai takoma tacigaba da aikinta,fanke takeyi saboda tunda tatashi da safe taji shi take sha"awa shiyasa bayan tatashi tatashi ta kwabashi,shine take soyawa harta kammallah,tazuboshi cikin filet tahado da maltina tazo tazauna afalo tashar Arewa ta latso tana kallo tanacin famkenta ammh kuma sai me,kakarin Amai taketa jiyowa tun tanadaukan Abun wasa har taji abun nakara yawa zumbur ta mike tana raba ido A"a kakari take ji ba ada tafara tsorota ammh daga baya sai tafara ji kamar daga saman Nazir ne takejin Abun.
Tana tsaye ne atsakiyar falon tana raba ido to indaga samanshi ne takeji to ai baya nan,to waye bata gama zencen zuccin ba taji Abun yakara yawa ai da hanzari tafara haura step din babu tsoro ko kadan aranta,kwankwansa kofar falon tahauyi da hanzari ammh sai kawai kofar ta wangale ma"ana abude take,koda tashiga falon bata ganshi ba harta nufi bedroom din kawai taji nishi abayanta tana juyawa taga Nazir kwance cikin amai yana fitar da Nishi kamar shedansa zata dauke,cikin wani firgita da tsoro ta nufeshi tana fadin"Na shiga uku...Ya Nazir"tafada tana dukawa garesa duk da Aman dayayi haka ta tarairayoshi ta aza kanshi bisa cinyarta tana taba wuyansa da taji mugun zafin da sai da tayi saurin cire hannunta,kara yunkurin Aman yake ammmh rashin babu komai acikinsa yasa babu abunda ke fitowa,
Nusiba taji hawaye lokaci daya yawanke mata fuska,saboda ita mutumci mai tsausayi bata so tagama yaro na ciwo balle babba,yau ga Nazir duk jin kansa da matsayinsa yana kwance cikin kazanta,lalle Allah kenan
Rasa yadda zatayi dashi tayi, gashi ya cukwikwiyota,takasa tashi,gashi sunyi dama dama cikin Amai dakyar ta mike tarikemai hannu tana kallonsa yadda idanunsa ke komawa suna lumshewa shi yabata tsoro tasakesa da hanzari tajuya ammh sai me tattausan Hannunshi taji yasaka ya riketa gam,tawaigo da mamaki taga idanunsa arufe yana wani wahalallan Nishi,cikin kuka ta rike nashi hannu tace"Ammi zanje na kiraho Yaya Naxir mukai ka asibiti"Kin sakinta yayi shiyasa takoma tazauna ta aza kanshi bisa cinyarta tama rasa inazata saka kanta gashi bata iya daukansa,
Sundade ahaka dataga babu sarki sai Allah sai ta mike tarikemai hannu tana Fadin"Bara na taimaka maka kakoma bisa gado...Kaga kana cikin najasa fa"bai iyi cemata komai ba tadaddage ta rikosa dakyar domin bazata iyaba shikanshi baida control na jikinsa gabadaya tallafe yake ajikinta shiyasa suna mikewa taku biyu uku taji su sunyi luuu gabadayansu ta runtse ido tasadakar kawai sai tajisu sun lumtsuma bisa kujera tafada saman kanshi yaraf,
Duk da Nazir na halin ciwo duk abunda ke faru yana gani kuma yana ji ammh baida wani halin hanawa,cos yadda aman ya galabaitasa,saurin tashi tayi tana gyara dankwalin dake kanta,saurin sauka kasa tayi tazo da abun shara da moper tahau gyara inda yabata yana kallonta da lumsansun idanunshi ammh cikin ranshi mamaki yadda ko kadan bata nuna kyamartata ba,tana ta aikin amansa,tas ta goge aman tayi mopping din gun.
Fita tayi tasake dawowo tana zuwa,ta tsaya gabansa tace"Ammh kayan jikinka sun baci"tafada tana kallonsa shiko motsawa sai takarisa ta jawo kafarsa ta ciremai sawo cikin dake kafarsa da safa,kana ta tattara briafcase dinsa da wayoyinsa tashigamai bedroom dashi,karo na farko data fara shiga,komai tsaf tsaf kamar mace duk da tasan shi baison kazanta ammh batazata har ciki yana gyarawa ba.
Nazir na kwance Nusiba ta taimakamai ta ciremai coat din dake jikinsa data ciki ta cire mai wandom tabarshi daga shi sai vest da boxes wanda karfin hali tayi kawai tanayi tana kauda kai,shiko duk da baida lafiya haushin kanshi yakeji yazauna yarinya karama na sarrafashi yadda taga dama,ammh dayayi kokarin motsawa sai yakasa,kayan tashiga dasu tiolet tajikasu cikin bucket kana ta zubo wani ruwn sanyi awani karamin baho tazo tazauna akasa tamatso tawul din dake ciki tahau shafamai bisa jiki.
Nazir yabude jajayen idanunsa lokaci daya da rike tawul din yana kallonta,cikin karfin hali Nusiba tace'jikin kane yayi zafi,hakan zai sa kaji dadi"bata jira cewarsa ba ta amshi tawul din tacigabada da mammatsamai ajikinsa na tsawon lokaci,har zafin ya sauka kana tabarshi,kuma ba laifi yaji dadin jikin nasa haka,komawa tiolet tayi tazage ta wankemai kayan daya bata,kana ta wanke toilet kar dashi kafim ta fito.
Koda tazo har yasamu barci,ajiyar zuciya ta sauke tana bin saukan Numfashinsa da ido duk da haka cikin wahala,ficewa tayi tareda jawomai kofar,hijabinta kawai tadauka tafice zuwa gidansu Ammi koda tashiga su meero kawai tagani suna aiki a kichen ta tambayesu Ammi sukace bata fito ba yau.
Zama tayi kan kujera tana jiran fitowan Ammi tadade zaune har shabiyu tagota Ammi bata fito ba,sai ga musty yafito yana Hammah alamun shima tashin shi kenan,da mamaki yake kallon Nusiba kafin yakariso cikin muryan barci yace"matar yaya lafiya kuwa? kike zaune ke kadai? yafada cikin mamaki Nusiba da fuskanta ke cikin damuwa tace'lafiya kalau...Ammh ya Nazir ne yadawo bashi da lfy"
Musty yazaro ido yace"broda Nazir din"yafada cikin tsoro kan tasamu zarafin mgana Sukaji Ammi dake fitowa daga daki tana fadin"waye ba lpy kuma? Musty yace yana kallonta"Ammi wai kinji broda ne baida Lafiya'zaro ido Ammi tayi cikin kaduwa tace"Nazir din yaushe yadawo"Tafada tana kallon Nusiba.
Nusiba tarasa mezata tace sai tace"bai dade dawowa ba Ammi yanashigowa sai Amai",Ai kan ta rufe baki musty da Ammi na rigen rigen ficewa sai dai tabibayansu da sassarfa suke tafiyan cikin hanzari suka haura saman,inda tabarshi nan suka iskeshi yana barci cikin tsausayi suke binshi da kallo musty yace"Ammi nidai da wayau na broda bai taba ciwo ba"Ammi tayi ajiyar zuciya tace'gaskiya nima ko yana yaro baida yawan ciwo,nidai daya girma banta ganina ba"tafada tana zama gefensa lokaci daya tana shafa kansa,
Musty yakalli Nusiba yace"meyasha ne hala"Nusiba tace"baici komai ba gaskiya"Waya yafito da ita yana cema Ammi bari nakira doctor Auwal yazo yadubasa"Ammi tace"yauwa hakan ma yafi,kiransa yayi yace gayi nan zuwa.
Suna tsaye jugum jugum sai ga Abbu yakira wayan musty yana tambayansa yafadamasa suna gidan broda yadawo baida lafiya,iya rudewa Abbu yayi karku manta,shine dan gaban goshinsu,lokaci daya Dr Auwal da Abbu suka shigo falon,kuma lokacin Nazir ya farka Ammi tana mai sannu idanunsa alumshe yake kallo kowa yana son mikewa ammh baida karfi sai yakoma yakwanta ammh yadamke Hannun Ammi.
Suka gaisa da Dr Auwal kafin yafara dubasa kallonsa yayi kafin yace"jounalist kana zama da yunwa ko'gyada kai kawai Nazir yayi kan ya furta cikin wani yanayi'bakina bayamin dadi Doc...Kuma cikina yana ciwo..So..Sosai"yafada yana dafe cikin kallonsa yayi kan yakalli su Ammi yace"plz Ammi kuyi hakuri kubamu guri"ba musu kuwa suka fice suka sauka falo,suka zauna kowa kagani yayi tagumi,Nusiba kowa gefe ta rakube cike da alhini duk da basa shiri da Nazir ammh ciwo yawuce komai
Suna ficewa Dr Auwal yataimakasa yatashi zaune ya jingina da kujera kafin yace"wai mtsalar damukayi mgana dakai har yanzu baka samu mafita ba"idanunsa na lumshe yace"dsame problem ne doc,harda Amai fa nai tayi dis time"yafada awahale,Dr Auwal yace"Ulcer ce takamaka sakamakon rashin cin abinci dabakayi ammh ciwon cikin ka yana danasaba da problem dinka na farko,yakamata by now kasaman ma kanka mafita gaskiya domin illah nebabba sperm yadinga tarummaka amara"yafada yana kallonsa yamutsa fuska Nazir yayi kan yace"Allah ya tsareni dana hada shimfida da wannan yarinyar doc,kabar mganannan"Dr Auwal yamurmusa yace"to ka kara Aure mana"Nazir yayi saurin bude ido yana cewa"What...Haba Dr kasan ko waye ni? mata basa cikin tsarina,dayan ma yana kare da ita balle na auro wata"yafada yana numfarfashi maidashi baya Dr.Auwal yayi yana Fadin"Maida wukar man,Abbu kawai zan fadama mtsalarka"Nazir yace"Kadade baka fadamai ba,kadai san akwai amana mai girma atsakaninmu ko,"yafada yana kallonsa Dr.Auwal yamurmusa kawai bai ce komai yanata hada allura wanda sai da sukasha daka kan Nazir yayarda akayimai ,bedroom yakamasa suka shiga yabude dan kit din dayazo da kayan aiki yakwantar dashi yasanya masa drip saboda rashin karfin jikin dabaida shi,sai da yakammallah komai yahada kayansa kan yakallesa yace"last time kenen dazamu kara irin wannan mganan wlh inbaka yi amfani da shawarata ba,zan tara su Abbu na fadamusu"yana fadar haka yafice shiko Nazir lumshe ido kawai yayi.
Achan Falo kuwa Dr Auwal cema su Abbu yayi ulcer ce takama Nazir ammh yayimai allura yasamasa drip zuwa amjuma zai dawo,godiya su Ammi suka mai kan yayi musu sallama yafice,sake komawa sukayi saman wanda Nusiba taki binsu,domin kada tatakurasu daki takoma tashiga wanka domin itama warin Aman take.
Nazir yanajinsu suna ta mgana ammh yayi kamar yana barci saboda baison tambaya yasan halin Ammi intahau mai tambayan meyasa meyasa,har saiya gaji,wunin ranar dai nan suka lalace,Ammi da kanta tayima Nazir fenten wake da alaiyahu da hanta tatasashi tana bashi abaki,Nusiba kuwa sai dai ta leko tadubashi tadan zauna sai takoma daki,saboda taga ga Ammi ga Musty ga Abbu ai sun isa jinya,sai yammah Dr.Auwal yadawo yaciremai ruwan yasake mai alluran ba laifi jikin nashi yayi sauki har yarama sallolinsa da"ake binsa duk da musty yarikesa ya je bayin.
Dr Auwal dai kwararan likitane abangare dadama,likitansu ne batun yau ba,kuma aboki ne ga Nazir domin tare sukayi primary sch dinsu,tunwani ciwon ciki da Nazir yayi yaje gun Dr Auwal yadubasa yace mai mace yake bukata ammh Nazir ya ture mganan,gab da aurensu da Nusiba ma ciwon cikin yakara tasarmai,bayan Auren nasu ma Dr Auwal kamar zai ari baki akan Nazir yaje ga matarsa ammah yace Allah ya tsaresa,babu wanda yasani daga shi sai Dr.Auwal ne suka sani kuma yahanasa yafadama kowa.
Cikin kwana biyun nan Nusiba taga wani abu wai shi gata domin kaf Ammi da musty suka tare bangaresu suna jinyan Nazir wanda yake kara lamgwabewa kamar wata mace,itadai nata tashiga da safe tamai yajiki,ya amsa kamar baiso sai kuma abinci datake kokari yi safe da yammah,bata shishigemai itadaman don Allah tayi kuma Allah yabata lada,kawu ma Anty kullum sai sun shiga sun dubashi Safe da yammah ada musty yace yadinga kwana dashi ammh Abbu yace kul ga maidakinsa meye nawani sai musty yakwana dashi,hakanan take zuwa duk dare,tana kwana abun takaichi akasa take kwana shiko yahaye gado Abunsa,kuma ko kanzil bai hadasu iyaka tana sanya alarm awayarta uku nayi zata tashi tahau sallah,kuma duk yanajin sanda take tashi komai akan idonsa kawai nunamata yake baisani ba,asuba nayi zata tashi tayi komawarta daki,ahaka har yayi Sati agida wanda har bash sai da yazo yadubashi kuma ko so daya baitaba kallon Nusiba yagodemata bisa kokarin datayi akanshi ba duk da don Allah tayi ammh ai da dadi ayaba maka,ammh mutumin nan ko shiga tayi gaisheshi sai aidon su Ammi yake amsawa wlh inbasu ko kallonta baiyi itako aranta tace wlh yayi da ya"saboda shi har excuse tadauka agun aiki
Batama san yatafi ba sai datashiga gaida Ammi taji suna waya tana mai Allah kiyaye hanya,tare da fadan yakula da cin abinci,tabe baki tayi tace"ummh tagaida Assha"cikin ranta.
*Comment*
*Share*
*Vote*
*Janaf*✍
[4/11, 2:14 PM] 0mmer Farouk: *🧑🏻NAZIR🧑🏻*
_*(The journalist)*_
*(Based on luv and Romantic story)*
*Na*
*Janaf ce*✍
*Vote me on WATTPAD:Janafnancy*
© _*INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION*_🖊
*```(onward together)
*JUSZ GIVE US A FOLLOW*✔
*```DIDECATED TO SAHIBA HAFSART HAFNAN```
*NOT EDITED*
22/23
*Abuja*
*MAFARIN KOMAI*
""""Nazir ne kwance akan makeken gadonsa wuraran sha biyu dawani abu ne nadare,dakin yayi duhu sosai domin babu fitila balle dumlight na barci,labulayan windunan bedroom din ke kadawa hasken farinwatan daya haske gari alamar watan taraba tsakiya kenan shike dan shigowa yana haskaka dakin lokaci bayan lokaci.
Achan tsakiyar gadon na hango Mutum zaune dirshan daga shi sai gajeran wando,wanda yadan mateshi babu ko riga ajikinsa,abun mamaki hayaki ne ya turnike inda yake lura da yadda yake zukan sigari cikin zafin nama dakuma kwarewa bata kai ga karewa sai yasakata cikin wani bakin farantin dake gabansa cikin lokaci yayi ma kwalaye har uku aiki kuma zuciyarsa bata daina zafi ba,da kafa yasa yashuru faranti yatafi kasa yakife,saukowa yayi daga kan gadon yazo ya isa ga makunni yakunna lantarki dakin.
haske yagauraye ko"ina gaban makeken madubin dake dakin ya isa yana kallon kansa yadda ya yamutse hannu yasa saman gashinsa yana yamutsawa lokaci daya yana fadi"Why? da karfi kamar wani zararre idanunsa sunyi jawur sun canja kama,kwatakwata yarasa meke damunsa,domin tunda yadawo Abuja wani bakon al"amari yake faruwadashi,badama yazo kwanciya daya runtse ido yarinyarnan yake gani durkushe gabansa tana kuka sanda baida lafiya,daya bude kuma yasake rufewa saigakara haskota sanda tarikesa suka fada kan kujera,abun ban Haushi duk sanda ya tuna gun sai yaji tsigar jikinsa ya tashi,akullum cikin dakinsa baida aiki sai sama wuri daya ido saboda gani yake kamar zai ganta kwance agun kamar yadda take kwanciya achan kano.
Tun yana daukan Abun a wacce tayimai hidima sanda baida lafiya,domin tabbas yasan tayi kokari wacce taita hidima da amansa,wanda inshine yadda yakeda kyamkyami wlh bama zai iya ba,but ammh lamarin naneman fita hankalin awannan dare shine dare na hudu dakullum yakwanta baida abun Tunani sai ita abun yafara damunshi,ada in abu yadameshi daya sha sigari zaiji wasai ammh wannan karo Abun yaci tura don ko kwali nawa zai karar wlh sai dai in barci barawo ya sacesa ammh yadinga Abu daya kenan.
yadade tsaye gaban miro yana kallan kansa kafin ya furta afili"Anya yarinyarnan ba asiri tamin ba"Yafada yana rike hannunsa da dayan hannu,tsaki yaja daga baya kan yace"No never insha Allahu bazan taba fadawa tarkonta ba inaga dai hakan yanada nasaba da kula dani datayi ina ciwo"kokarin yake zuciyarsa ta yarda da hakan duk da gefe daya haushin kansa yakeji yadda yake neman susucewa kan dat villager girl.
*KANO*
Sati daya kenan da komawar Nazir,Nusiba tana gun aikinta Aranar kawu yakirata yace"tadawo gida yanzu babanta yamai waya kan inna fatsima bata da lafiya har anyi addmitting dinta a hopt"cikin rudewa Nusiba tafadama manaja ta nufo gida cikin tashin hankali koda tazo kawu yayi kokarin ya kwantar mata da hankali nacewa jikin da sauki ammh Nusiba tagaza fahimta,ita gani take kamar innanta ta rasu ne ake boyemata,kuka take share share shiyasa Abbu yace Ammi tabita su Tafi ita da Anty su zasu zo daga baya
Haka ko akayi direba yakwashesu sai zaria A MUSLIM SPECIALIST HOSPITAL dake danmagaji aka bata gado shiyasa chan suka wuce direct, Nusiba hankalinta bai kwanta ba sai da taga innanta na nan da Ranta ammh abunda yabata haushi babu wanda ke gunta sai ita kadai kamar mayyah kuma babu wani kula da ake bata,shiyasa suna zuwa Ammi taga likitan sukayi mgana aka fara chanza ma Ammi daki aka maidata Aminity,dama ko dasuka zo tana barci ne sai da za"a canja mata daki ta Farko taji dadin ganinsu taitayi musu murmishi.
Ammh Abunda yaba Nusiba mamaki yadda innanta taiwani fari goshinta yana kalli gakomai taci sai ta amayar dashi,dayake direba sukabawa kudi ya siyomusu kayan tea da kayan fruit harda abinci domin daga gidan su Nusiba ko kare basu gani ba,Ammi ma Abun yadauremata kai tafara zargin wani abu shiyasa likitan dazai dubata da dare yana zuwa take tambayanshi meke damunta sai dayagama duba folder ta kana yayi ma su Ammi bayanin cewa"Cikine na tsawon wata uku da kwanaki ke wahalar da ita,sai maleria data ke dashi"galala sukayi suna kallonsa Ammi ce ta furta!"Allahu Akbar Allah kenan,tafada tana jinjina kai,Nusiba dake zaune ta tsurama Innanta ido tana ayyana yadda lamarin Aure yake,tab yanzu ahaka lalle kada kayi shishshigi yanzu ina inna saude take sanda haka Tafaru,Lalle kada mutum yadinga ja da lamarin Allah.
Anan Asibitin suka kwana tareda Ammi wanda Nusiba tayi tayi Ammi tazo takaita gida takwana gobe tadawo ammh Ammi tace"ba inda zata sai dai ita taje,"Dole Nusiba tarabu da Ammi,ammh Ammi takara samun matsayi mafi girma atare da ita,washegari inna fatsima tatashi jikin nata da sauki tunda aman yayi sauki kuma har taci abinci,daga ko gida babu wanda suka gani abincinma siya sukayi,suna nan har azahar sai gasu Abbu da kawu da musty sunzo da kayan dubiya abunda yadanganci kayan karin jini lemoku dadai sauransu,dazasu tafi Abbu dubu hamsim yabawa Inna fatsima musty ko 10 thousaund Nusiba taita godiya dazasu tafi Ammi tabisu tace zuwa jibi zata dawo,akabarta ita da Anty to wajen la"asar likita yazo yadubata yayi discharging dinsu Nusiba bata jira kowa ba taje tabiya komai ta sissiyo magungunan da"aka Rubuta mata,fita tayi tayo musu tashar Napep tazo ta daukesu sai gida.
Sai dai kawai aka gansu kwatsam lokacin Da Nusiba tariko Hannun innanta sun iske baba Atsakar gida shida Dada kamar mgana suke,suna shigowa Dada tace"Au kun dawo yanzu fa nakema Abbakar mgana xuwa duboku"Ko kallonta bawanda yayi sai ma ita innan Fatsiman ce tace"komai daman sai Allah yayi"daga haka tayi shuru,dada kuwa kallon Nusiba kawai take yarda takoma wata yargayu da ita.
Anty tashimfidama inna tabarma atsakar dakin tazauna kenan sai ga saude tafado daki tana gaishe da innan tana nan sai ga Dada tashigo tana wani gyara zence,wai wlh sauden ma batajin dadi,ita kuma jikin tsufa,Nusiba dake zaune gefe tana latsa waya ta murmusa kawai batace komai ba Anty tace"yo ai bakomai kunsan Haihuwa mai Rana mu bagashi damukaji mun taho ba,ai kinji ana ba"a jin dadi Dada naka bai kwanta ciwo bane"tafada kai tsaye tana barema inna ayaban dake hannunta,kuma tana gani dada tasa rai Aranta tace"Sai dai ki mutu.
Dada tasan mgana Suwaiba tayaba mata shiyasa tace"wai meke damunta ne nga tayiwani yi fari fat da ita"murmishin jin dadi Anty tayi kan tace"Au Baban Nusiba bai sanar muku bako? wlh Juna biyu ne da ita,kinsan Shi Rabonka baya wuceka ko a ina yake,duk ko tuggu mutum sai dai yaga karshensa"Tafada tana kallon Saude wacce tamike dafe da kirji lokaci daya da Dada suka Furta juna biyu? Suna zare ido ,ita kuwa inna Fatsima kunyace takamata ta sadda kai kasa.
Anty tace"kwarai...juna biyu kuwa"Dada tace baki na rawa"Ke wai wani juna biyun