Showing 21001 words to 24000 words out of 87333 words

Chapter 8 - Nazir Bok Complete Hausa Novels by Janafty.txt

tayi su iso,direba Ammi tabama Umarnim jidan kayan yana Shiga dasu buhun,shinkafa guda biyu,na masara biyu,katan din taliya,macaroni indomie,semo,maggi star kai komai fa kwaline,su inna Saude na tsakar gida sukaga sai shigowa ake da kaya,farkoma dasuka shigo sai da sukace ina ne dakin innar Su Nusiba cikin mamaki suka nunamai yashiga jera kaya,bayan sungama da kaya suka hau shigo da akwati suna jerawa sai dasuka jera goma sha biyu reras kafin su dakata inna saude da Dada kuwa basu gama Farfadowa ba sai da Ammi ta rangwado sallama atsakar gidan Nusiba dake ciki tayi Wuf ta fito aguje tafadamata cikin murna da Farincikki.



Ammi ta rumgume Nusiba tana Fadin"my dota nayi missin dinki sosai"Nusiba tasaki Ammi kafin ta sadda kai tana dariya Hajiya Hafsart na tayata Inna zainaba kuwa kallon banza kawai takema mutane tana tabe baki,Awaje Anty ta baje wata katuwar Tabarma su Ammi suka zauna ana gaisawa,Ammi ta durkusa har kasa tana gaida inna Fatsima saboda girmamawa Ai kan kace kwabo makota suncika gida,daman Inna ta aika musu hoho jama,"a suka cika gida,su Ammi da hajiya hafsart suka zage sukaji abincinsu suka sha ruwa,ita kuwa inna zainaba sai harare,Atsakar gida aka baje kayan wayyo Allah kayane sai iya kallonka wlh zinarai ne kawai da gwalagwalai ke yawo,kaya tun ana kirgawa har aka bata kirga,komai yaji banda tsiya Anty sakin guda kawai takeyi,Ammi tacire key din mota ta dora tace ga kyauta daga uwar ango,gu yasake daukan guda kayan abinci kuma tadora dubu dari biyu tace sako daga uban ango.


Ai tuni gida ya rikice yara kuwa harsu  ruga sun gayoma su zubaida sun bazamo suma agabansu akai komai inna saude kuwa zaman dirshan tayi akasa tana ganin abu kamar mafarki,Anguwa gabadaya ta dauka ankawoma Nusiba akwati harda makulin mota wacce kaf unguwan ba wacce tasamu kwatankwancinta,Dada kuwa washe baki kawai takeyi wai jikarta tayi goshi,ko kunya bata ji.




Nusiba da Rahma suna dakin kofar gida inda suka kaima musty abinci yashiga yaci,suka zauna suna hira,suna zaune ammh sunajin Haniyar dake cikin gida,Inna Fatsima tana gofe tana share kwallah murna wanda ko amafarki batataba zaton yarta zatayi goshi haka,Sai wajen la"asar su Ammi sukayi haramar komawa inna Fatsima tace adauki kudin Dasuka kawo dubu dari abasu,kememe Ammi taki karba dole suka Hakura abun mamaki wai Dada harda rakasu tana washe baki,suna tafiya tace adakinta za"a kai komai sai in Baba yadawo Tukun,su Anty sunso Su Inna tace su barta ai dai duk abunsu zasu dawo dashi tunda kaya dai bana su bane.







inna Saude da ya"yanta kuwa daki suka shige sukayi zugum,Zubaida ce tace"Inna wai bakince kunsamata bakin jini bane,to in hakane miye yajawo wannan"Tafada cike da bakin ciki,Inna saude dake zaune ta rafka tagumi tace"Nima abunda nake Tunani kenan domin lami tabbatarmin da cewa Nusiba ko kare bazai rabeta ba"Tafada tana jaddawa, Inna saude takara cewa"dole ne naje naga lami gobe dole ne kam.





Baba yana dawowa,Dada tatarasa daki tana Nuna masa tana cewa"Kai Abbakar wakaba Auren Yarinyar nan"Tafada tana Nunamasa dimbin kayan dake zube adakin"Shima da kallo yabi kayan kafin yace"Dada kina Nufin duk wa yarinyarnan aka kawo"Dada tace"Harda mota Abbakar wlh nake gayamaka"tafada tana kara yaye zanin gadon data rufe kayan,Baba yayi zuru kawai yana bin uban kayan da kallo,kan yadawo kan kayan abincin yace"Hardasu kenan? Dada tace"eh harda fa kudi"Tafada harda jadaddawa Baba yajuya yana cewa"to Dada komawaye ita tasani nidai na Rabu da kaya,to alhamdulillah"yana gama fadar haka yafice ko ajikinsa Dada kuwa kwana tayi tana mamaki da Tunanin waye Nusiba ta aura ne itafa tashiga rudu.






Ranar Alhamis

Fitowarsa kenan daga dakin lbru kiran Abbu yashigo wayarsa,cikin mamaki yadaga Abbu yace cikin kakkausan murya"Duk Abunda kakeyi ka ijiye kataho kano yanzu ina son ganinka"Yana gama Fadarhaka ya datse kiran,bai kawo komai Aransa ba,Ammh Abunda yabashi mamaki koda safe kafin yashiga dakin lbrai sun Hadu da bash,suna Haduwa yahau cewa"Angon yar africa"Nazir yaji yana fada ammh shi atunaninsa badashi yake ba shiyasa yakallesa kawai ya tabe baki,shiko bash dariya yaita tsuntsurawa yana dukuwa yana dagowa,Sanin Halin Bash na dariyan rashin dalili yasa ya masa banza bai Tankashi ba.



Suna daukan Hanya ya Fadama ilu cewa,kano zasu cikin lokaci suka fita daga Abuja suka dauki Hanya.


cikin lokaci suka isa,cikin azama da sassarfa ya shiga falon da Sallama,Ammi ne da Abbu ne zaune suna cin Fruit wanda ke cikin wani Faranti yana shigowa da sallama suka amsa,da suna dariyane ammh yana shigowa suka chanza Fuska kusa dasu ya isa yadurkusa yana gaishesu kin amsawa sukayi Abbu yagyara zama yace"Sannu ishasshe ko ince angon mai bakinjini"Yafada yana kallonsa.



Shiko Nazir yaji abunda Abbu yace ammh atunaninsa badashi yake ba shiyasa yayi masa shuru,Ammi tace"Mgana fa Abbu ke maka kayi shuru ko muma zaka kaimu freedom din ka yayatamu mara mutumci"Tafada ta hasala,cikin matukar mamaki Nazir yadago yana kallon iyayensa shifa bai gane inda suka dosa ba,bakinsa ya motsa yace"Abbu ban...Bangane abunda kuke mgana akai ba"Abbu ya sakin mai dakuwa yace"kaci uwaka daba ka gane muke Nufi ba,mungode da cimana mutumci daka je kayi,don ba Nusiba kacimawa ba mu kacimawa"Ammi ta amshe dacewa"yaci ma kansa dai,domin iyalansa ya tonama asiri aie"Tafada Tana Hararansa.



Nazir yayi tsam yana so ya tattara bayanan,domin shifa ya manta ma yayi wani Abu ammh jin sun ambaci freedom kuma suna ambaton wani Suna dabai gama ganewa ba yasa yadan fara dagowa,to a ina su Ammi sukaji zakuda kafada yay yace"Kuyi hakuri Abbu da Ammi'Abbu ya tabe baki yace"Kai ke da hakuri domin ina farin cikin shaida maka aranar daka cima mata mutumci amtsayin mai bakinjini to Aranar aka daura maka aure da ita"Abbu yafada wit full comfident.


Nazir dake zaune yazubama Abbu ido yana maimata maganganun nasa akwakwalwarsa abu daya kemasa yawo akwanya" *An daura maka aure da ita* Kafin yagama hada maganan zufa ta ketomai cikim Razana ya zare ido yace"What dawa aka Dauramin Aure Abbu.?

















*Comment,share and vote*




*Mubjam*✍
[4/11, 2:11 PM] 0mmer Farouk: *🧑🏻NAZIR🧑🏻*

     _*(The journalist)*_

*(Based on luv and Romantic story)*

  *Na*

*Janaf ce*✍

*Vote me on WATTPAD:Janafnancy*

© _*INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION*_🖊
    ` ``{Onward together}


*```DIDECATED TO SAHIBA HAFSART HAFNAN```




_*I dedicated dis page to u,Mmmansaddiq,mman Khadija,mman Amira,Name see,Fadila talba,Lashmizy,Teema bby,mematjj,Amina,maman shukura,maman Abdulmalik,Sanah,maman Noor,My Fadi maman Tanimu,u Dala naki dabam ne, kursum,safiyya,my maneesha,cwt ramlart,kanwata Fati Umar,kuna da yawa wlh innace zan ambaceku,sai na karar da duk page din baku kare ba,ammh duk wanda baiji sunanshi ba inaso kusani ni Janaf ina tare daku akowani Babin da Rayuwa zata budemin*_




_Nagode sosai da wa"inda suka kirani sukamin yajiki mussaman Aisha ta pmlv da ke Aisha ta Janaf&Hafnan novel ina godiya sosai da yarda kuka nuna kulawanku Akaina,Allah yabar zumunci da kauna,mai dorewa ko yanzu ma ina bukatar addu"anku domin banajin dadi_





```I love u  more Than u will ever know.You have made me the happiest women on earth,i hope to be ur wife someday...I LOVE U....mubjam```💔💔



13/14



     """Musty yace"Ammi mekuma ya Faru"Ammi ta kariso tana fadin"komai ma ya faru musty Abbu na hanya mu jiraceshi"Musty yamaida kai kan kujera kawai baice komai ba.

Ammi takalli Nusiba dake Zaune akasa tasaka kanta atsakanin cinyoyinta Ammi tadafata tadago tana kallonta hawaye yana diga bisa kuncinta,Ammi tasanya Hannu tasharemata hawaye tana cewa"Har Abada kuka yakare Nusiba,kidaina kuka hakan kidaukeni amatsayin Mahaifiya ba mahaifiyar Nazir ba"Nusiba batace komai sai yada kai datayi kanciyar Ammi tana zubar kwallah,Ammi tana Shafa kanta tace"harga Allah Nusiba sonki nake tsakani da Allah,kallon yata nake miki"Nusiba tace"Nima Wlh Ammi ina sonki kuma ina miki kallon mahaifiyatace'

Ammi tace"To in hakane ki share hawayenki kibar kuka,tuni Abbu yakammallah komai wlh sai Nazir yaduka da kanshi yanemi afuwarki",Nusiba ta kalli Ammi,cike da mamaki Ammi tagyada kai tace"Belive me my dota,"Cikin sauri Nusiba ta gyada kai tana kara kwantar da kanta acinyar Ammi.

Da la"asar su Abbu suka dawo daga chan Alhaji yayi sallama dasu ya wuce gida,Abbu basu shigo ba saida suka tsaya sukayi la"asar kana,cike da Farinciki Ammi ta isa ga Abbu batai wata wata ba kawai takaimai rumgume tana Fadin"Brka dadawo jarumin mijin Fatima,uban tagwayen maza"Tafada tana sakin mirmishi,Abbu ya rumgumeta yana Fadin"yaushe rabon da Amin haka tunda,yaranchan suka kwace ki shikenan"yafada yana kallonta.

Musty dake kokarin fitowa daga daki,yayi Saurin komawa,da baya itakuwa Nusiba dake kichen tadauko kulolin Abinci zata dinning itama takoma da baya tana Rufe baki,duk Abbu ya gansu ammh sai ya basar,suna rumgume da juna suka Nufi Dakinsu Musty yafito yana rike baki Aransa yace"Tab..Lalke Abbu da Ammi..Kun kusa korarmu agidan nan kuwa"ficewa yayi zuwa massallaci.

Itakuwa Nusiba sai da tabata lokaci kafin tafito,tajera Abincin kan dinning tana kammallahwa tazari hijabinta tafice takoma shashensu koda suka Hadu da kawu baimata wani jawabi ba kuma baimata mganar komai ba,shiyasa itama tashige daki tana kukan zucci don Abun na mukurkusanta.

Tana kwance Anty ta leko tace"Tataso Abbu yana kiranta,haka tatashi tana rangaji tabi bayan Anty koda suka isa Falon Sun iske Ammi da Abbu zaune kan kujera musty na zaune agefe,sai kawu dake gefe zaune,suna shigowa Abbu yasa baki yaKira Nusiba yace tazo kusa dashi,ba musu ta isa kusa da Ammi ta zauna,Abbu ne yayi gyaran murya yafara mgana.

  "To Alhamdulillah da farko kafin ince komai zan fara mika hakurinmu ne gareka mallam jibo dake Nusiba,kan Abunda mara jin yaron nan ya aikata,wlh bada yawunmu bane sam,bamu da masaniya kan...."Ash Alhaji basai ka rantse wlh in akwai wanda zai bada shedar ka nine na farko,wlh babu komai sha"anin yara ne"kawu jibo yakatse Abbu dacewa haka.

Ammi tafurta cikin takaichi"Wlh sam yaron nan ba halina ya biyo ba,kuma ba halin Abbun bane,bansan ina yasamu mugun halinsa ba"tafada tana nuna takaichinta,Kawu yace"Babu komai hajiya don Allah karkusa Abun aranku"

Abbu yace"yo ai angama mgana domin shine ya tabbata mai bakinjini...Yata kiyi hakuri nariga dana yanke Hukunci,domin kinga fitar da mukayi to Aurenki mukaje muka Daura"Nusiba tadago da sauri tana kallon Abbu,Abbu yakalleta yace"Tabbas ke yanzu kina mtsayin matar Nazir na"Dafe kai Nusiba tayi kafin tafashe da kuka,Anty da musty suka kalli juna cikin al"ajabi

Nusiba tace cikin kuka"Abbu mai bakin jinin ka auramasa? da gaskene inada bakinjini domin babu mai sona daga inna ta sai kawu Da Anty,sai ku wlh bayanku ko mahaifina baya sona"Tafada tana kara fashewa da kuKa,Ammi ta riketa tana lallashi

Abbu yace"Ashsh..kidaina cewa haka,yaza"ayi mahaifinki yace bayasonki? yafada da alamar tambaya kawu yace"Da gaske ne Alhaji Nusiba tana cikin jarabtan Rayuwa,nan yashiga warware musu kaf lbrin Nusiba wanda kan yagama Ammi da musty sunata share kwallah Abbu yace"Allahu Akbar,wlh Allah ne yazabeki Nusiba Allah yasani bani na zabeki ba"Yafada cikin tsausayawa yana kallon Nusiba dake kuka da Hannu Abbu yace tazo kusa Dashi tatashi ta isa gabanshi ta durkusa dafa kanta yayi yana Fadin"Ki karbi karambanin dana miki Nusiba namiki Alkwarin Rayuwa mai inganci kuma da yardan Allah sai mahaifinki yacireki cikin ya mafi daraja acikin ya"yanshi"Nusiba tagyada kai Hawaye na kwaranyomata tace"waceni naki amsan Auren nan Abbu? kune fa gatana ko mahaifina bai damu dani ba,wlh na amince zanyi biyayyah ga mijina har karshen Numfashina"Tafada cikin Raunin murya Ammi tataso tazo ta tagota ta Rumgumeta tana sharemata Hawaye tace"Wlh mumana sonki Nusiba mu na bukatarki kimun alqawarin kwantar da hankalinki domin muba makiyanmu kunya"Nusiba tadago itama tana Share mata Hawaye tace"Na miki alqawarin baki dukkan goyan bayana na amsa na amsa Ammi da hannu bibbiyu kuwa"Tafada tana mata mirmishi.

Nusiba ta nufi gun kawu ta durkusa tana Fadin"Bansan dawani kalma zan gode maka ba kawu,ka....Bari Nusiba bari,karki godemin domin kedin yatace halak malak"Kawu ya fada yana dafa kanta yace"Allah nake roko yama Rayuwarki albarka ya daukaki ya Albarkaci Rayuwarki yata"Gabadaya suka amsa da Amin.

Nusiba kuka take bana wasa ba Anty da Ammi suka rumgumeta suna sharemata hawaye,Kawu yace"gobe Suwaiba zata rakata takoma gida zuwa Ranar tarewar"Abbu yace"Hakan yayi daidai muma zamu gabatar danamu shirye shirye insha Allahu Aurenku alheri ne"Aka amsa Da Amin cikin fahimtar juna taron ya Tashi ammh Ammi taroki alfarman abarmata Nusiba takwana awurinta nan kuwa aka barma Ammi Nusiba tana ta karfafamata gwiwa,Musty kuwa Abbu hakuri yabashi yace"babu komai Ai shida Broda duk dayane"




**********

Alhaji Hassan kuwa na komawa gida,ya iske Inna zainaba zaune ita da jidda da Aisha suna hira ya shigo sannu da zuwa sukayimai ya amsa yana Shiga ciki,tashi tayi tabishi ciki yana cire babban rigansa Inna zainaba tashigo tana Fadin"Alhaji wai ina kuka jene"tundazu shuru kodai da gaske hasashen danayi yazama  gaskiya ne"Tafada tana zama gefen gado,Kallonta yayi kafin yace"Wani hasashe kenan kika yi"Kai tsaye tace"Na yaya yakara Aure mana"Dariya yayi kafin yace"gaskiya zainaba baki da kyau,ke yanzu murna kikeyi don kina zaton an ma Fatima kishiya"Yafada da mamaki kwabe fuska tayi kan tace"yo dole mana,me ake da irin mayu"Tsaki yaja kan yace"Mtsewww..To baki hasaso daidai ba don Nazir aka daurama Aure"Wani irin Hautsilawa inna zainaba tayi ta diro daga gadon hannunta Dafe da kirji tace"Wani Nazir din? tafada idonta Awaje.

Cikin mamaki yake kallonta kan yace"Wani Nazir kika Sani,kinga ni banda lokacin shashankinki,agajiye nake"Yana gama Fadar haka yafada toilet.

Asukwane inna zainaba tayi Falo tana Fadin"Ni Fatima zata cima mutumci"jidda ta mike tana Fadin"momy meye Faru kuma? daga shiganki gun Dad"Inna zainaba tace"Wai Nazir yayi Aure jidda"Tafada hannunta na dafe a kirjinta,jidda tayi dariya tace"kai momy wlh kinsa gabana yafadi,broda Nazir din zaiyi aure baki ji bane"tafada tana komawa kan kujera,inna zainaba tace"da gaske ne don yanzu Abbanku ke Fadamun
,Kin manta Abunda nagama Fada miki"Ai da hanzari jidda tafado daga kan kujera tana Fadin"momy are u serious"tafada da nuna rauni Inna zainaba tazauna akasa tace"bansani ba jidda ammh Abbanku bazaimin karya ba"Ai jidda hannu tadora akai takwala kara wanda sai da ma"aikatan gidan suka bayyana arude Alhaji Hassan da fitowarsa wanka kenan yafito yana mamakin rashin kan jidda.

Ihu take tana Fadin"nashiga uku mommy wlh bazan iya rayuwa ba broda Nazir,ke kikamin alqawarin zama tauraruwa agurinsa,gashi yanzu wata ta rigani'tafada tana birgima akasa dariya ta kama Aisha tashiga kyalkyatawa,Alhaji Hassan ne yace ma"aikatan sukoma bakin aikinsu,suna wucewa yakalli jidda yace"Kunci uwaki,sakarya kawai ashe har yanzu baki yi Hankali bako"yafada yana nunata da Hannu kafin yacigaba da cewa"wlh kifita daga ido,tashi kibama mutane wuri shashasha,ahaka ne Nazir din zai soki,na tabbata ko mustapha wlh bazai soki ba don kowa Abu mai kyau yakeso"yafada yana nuna bacin Ransa.

Tashi jidda tayi tana kuka tashige daki,inna zainaba tabishi da wani kallo tana cewa"Ai nadade da sanin tuni fatima tabaka kasha Aruwa"ko kallonta baiyi ba,don inda Sabo wlh yasaba da Halin zainab.

Inna zainaba tajuyo takalli Aisha dake Dariya tace"Anya ke yata ce tacikina kuwa"tafada tana kallonta,shuru tamata kan tacigaba dacewa"Wlh badon agida na Haifeki ba dasai nace musanye aka min"Aisha tace"mommy bawanda ya miki musanye,kawai bambamci Ra"ayi muke daku,kai wlh na taya broda murna"tafada tana kara Sa dariya,takaichi ya kume inna zainaba ta dauki filon kujera tajefamata tana Fadin"kekam kinyi asara wlh nabarma Fatima ke,tunda na lura kema tawanke tabaki kinsha kamar yadda tabawa Abbanku"tashi tayi ta wuce Dakin jidda Fuu wacce take chan tana kuka kamar mahaukaciya.



Washegari

Tun karfe bakwai na Safe su Nusiba suka Shirya ita da Anty,domin wucewa zaria,kayanta kaf tadura abooth din motar Da Abbu yasa direba yakai su har gida,NusibaTaso takira Rahma ammh saita bari ta isa,manaja kuwa tace bata da tabbas din zata koma aiki dasu,domin yanzu fa Rayuwarta tana Hannun nan wanda ya tsanetane sai yadda yayi da ita.


Sallama sukayi Ammi tace sai sunzo kawo lefe musty har bakin mota Yarakosu,hatta da Abbu yayi Rakiya motarsu tafice suna daga musu Hannu.

Koda shadaya tayi sun isa zaria,mota na pakawa kofar gidan,gaban Nusiba yahau bugawa Anty taita karfafamata gwiwa Anty tafara fitowa kana Nusiba wacce ke Sanye hijabi kar kasa idanunta sun kumbura saboda kukan data sha,Baba kuwa na kofar gida shida wani makocinsu,yaran dake wasa akofar gidan susuka dinga kwasanmusu kaya suna Shiga dasu,daganan sukayi sallama da direba yakoma,tundaga nesa baban ke kallonta so yake yatabbatar itace ko ba itace bace,jiki asanyaye ta kariso ta zube kasa bakinta na rawa tace"San...Sannunku baba",tafada kanta akasa Baba yace"yauwa ammh ban shedeki ba yan"nan"yafada bilhaqii da gaskiya Nusiba tadago tana kallon Baba hawaye tacika mata ido kan tace"Baba Nusiba ce fa"Baba yagyara tsayuwa yana Fadin"TO..to kece,yo mai yadawo dake,ai dakin tsaya chan tunda chan din zaki zauna"Hawayen ta suka gangaro kawai sai ta mike ta wuce ciki,Anty kuwa saboda Haushi ko kallonshi batayi ba tabi bayan Nusiba.

Nusiba nazuwa zaure tashare hawayenta kan tashiga da Sallamanta Dada da Inna Saude suna tsakar gida sun kurama kofar shigowa ido tana shigowa suka hau salati Dada tace"Yo ashe dai gaskiyan yaran nan itace"tafada idonta kur akan Nusiba itakuwa Nusiba kallo daya ta musu tace"Sannunku su Inna"Tana Fadar haka tafada dakinsu tana Fadin"Innata..Tafada da karfi inna Fatsima dake zaune gefen dan gadon kaban dake dakin tamike,cikin wani gudu Nusiba tafada jikinta lokaci daya da fashewa da kuka Inna Fatsima ta rumgumeta itama hawayen sun kawo mata tana Fadin"Kinga ko,meye na kuka kuma"Tafada tana shafa kanta.


Dagowa Nusiba tayi tana karema Innan nata kallo yadda takoma kamar tsohuwa yar shekara tamanim hawaye suka kara zuboma tace"Innanmu kice kika koma haka? kece? tafada tana *Zubar kwallah NA AZIZA IDIRIS GOMBE* Inna Fatsima tasanya gefen zaninta tana Sharemata Hawaye tace"Duk farinciki yacikani tunsanda yara suka Fara shigowa da kayanki...Shine zaki rusamin shi da kuka Nusiba"girgiza kai Tayi Inna fatsima tacigaba dacewa"To kibar kuka kinji,kinmanta ada ke kike sharemin hawayena in ina kuka"tafada tana jan kumatunta,dariya Nusiba tayi tana kara rumgumeta tace"nayi kewarki Innata tafada da farinciki amuryanta.


Anty dake tsaye agefe sai da tagoge kwallah,tadade tsaye tunbayan data wanke su Dada da mgana tace"eh alqawarin Allah ne ya cika,biki ne yakarato dole yarinya tadawo gidan ubanta tayi bankwanan karshe"Dada tace"Ke yar kanzaki karki zageni,yo meye bamu Sani ba,Auren da sai da aka gama lalacewa tukun"Anty tayi tsaki tace"shine daidai Ai a lalace kuma dawo ayi auren,ai wlh sai bakinciki ya kasheku domin Indai Cigaban Nusibane kucigaba da zura ido,tsuffin banza kawai"Tana gama Fadar haka tashige ta barsu da kumfam baki.

Inna Fatsima taji kunya tayi saurin raba Nusiba da jikinta tashiga yima Anty maraba ,tabarma ta shimfida mata kafin takawomata Ruwa,itakuwa Nusiba Tsalle tayi Tafada kan gadon tana Fadin"i miss u,cikin Farinciki da murna,makota wa"inda ke shiri da inna Fatsima sai shigowa suke yima Nusiba barka da zuwa dayake Sunga dama sunbata kwalin minti daya da huhun gora guda daya,duk uban kayan da"aka kawo batace komai ba ta amsa ta kulla tadinga aikawa makota tana cewa na daurin Auren Nusiba ne Biki kuma Ranar jumma"a cikin farinciki.Domin tunda yaya yace"Tayi fatan Alheri Nusiba tasamu miji na Nuna ma Sa"a.




Nusiba wuni sukayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login