Showing 81001 words to 84000 words out of 87333 words
Chapter 28 - Nazir Bok Complete Hausa Novels by Janafty.txt
ma"aiki babu kama hannun yaro...Sai bayan isha"i sai gasu aiko Ammi bata musu mgana ta mika musu ya"yansu tana fadin"Kuje...Allah muku albarka ammh yau kam bana auren dasu ku tafi da ya"yanku"tafada tana dariya Suma dariyan suke domin sunsan me sukayi haka suka tattara suka koma gidansu...kamar yaran sunsani suka hanasu sukuni da sundam samu dama suna makale da juna sai wani yahau kuka sai daya kama su taru sutayi hakanam zasu kwasosu Tabasu Nono shi yaja dayana jijjiga itama taja daya sai sunfara barci su lallaba su shimfide kowannensu adan gadonshi suna shirin barin gun sai su tsala ihu atare...Takaichi kamar me gun Nazir don yaso Adarenan Till down ne dmin fa Nusin tasa jiyayi kamar daga leda ya bareta aranar...Ranar da basu samu lokaci ba sai gabda asuba Su Abul sun saka su gaba..Suma suna samun sunyi barci suma barcin sukayi saboda gajiya.
Haka dai Weeked ya kare Kuma yana Tashi Tafiya yace da Matarsa zai Tafi babu wanda yace don me ana gobe zasu Tafi suka je zaria daganan suka biya kaduna gun Gidado chan suka wuni kafin su koma gida...Washegari kuma sukayi sallama da su Ammi suka kama hanyar Abuja..
*SAFE LANDEED NUZNAZ*
*After 5 month*
zuwa wannan lokacin Tuni yan biyu sungirma sunyi wayau suna da wata bakwai kenan da haihuwa..Sunyi bulbul dasu gasu da karambani harsunfara rarrafe..Yaran sunada shiga rai duk wanda ya gansu yayan turawa sak dasu..Asatin suka dawo bikin Mg wanda suka dargargaji biki agidan gwannan amarya tatare a kaduna inda mijinta ke aiki su Nazir kam sunyi rawan gani gun bikin yanmata dayawa sun rola da Nazir ammh ina ba Fuska..Domin Nusiba na makale da mijinta shima yana manne da ita suda yaransu wanda mutane dadama insuka gansu ko basu sansu kawai saboda suke da sha"awa zasu ce don Allah zasu daukesu pic...
Suna dawowa kuma suka fara shirin zuwa kano domin bikin Musty yazo sati mai kamawa ne duk wani shirye shirye angudanar Ammi da ita kanta Aishan suka je Dubai Sukayo siyayyan kayan Aure wanda akamata akwatuna 12 ubansu narke da dukiya Ammi tabama Anty kwangilan gyara Aisha akwai cikin lokaci Anty ta zage tana gyara Aisha gyara na ban mamaki ashashen dai da"akama jidda jere da barin arzki Aisha zata zauna daman Allah yasa Rabontane.
Tun Asatin Nusiba ta bude wutan tafiya Nazir ya hanata dakyar yasaka ranar laraba ilu ya kwashesu sai kano..Shi sai Ranar friday zai Zo..Akwai gida ya rude damurna lokacin har bakin agadez sun iso gida ya cika da kawayen Ammi da abokan arzuka su Abbu kuwa tuni sun sha dauka gun jama"a anyi cikin gida dasu itama tana bangaren Anty inda Aishan ke zama ita da kwayenta Aisha tayi murna da ganin Nusiban ko bakomai ita take gani amatsayin yar"uwanta..Duk sanda Aisha ta tuna da bakincikin babu mahaifiyarta babu yar"uwanta sai tayi kuka ammh kuma tana musu fatan shiriya ne....
*Comment*
*Share*
*Vote*
*Janafi*💖
*INTELLIGENT WRITERS ASSO*📝
```{onward together}´´´
*NAZIR*
_*(The journalist)*_
*Based on luv and Romantic story*
*Na*
*JANAF CE*✍
*SADAUKARWA GA SAHIBA HAFSART HAFNAN*
_*HIP...HIP...HIP....HIP.....Happy Birthday To me...Happy Birthday To me...Happy birthday...Happy birthday...To me....Wish my self long life and prosperity Allah Rahmas and khairs...More hankali more basira..More Masoya...More halal money to my bank account..More egg to my indomie..More..More...More...Evertin ya Allah...albarka rayuwa mai dorewa...ya Allah bless my New age...,ALHAMDULILLAH!*_
_Thank yhu all my reletive loves one and Fans..For all ur prayers...Thank yhu so very much...Janaf relli Appriciate my dears one...am srry t wa"inda bansamu ma reply ba suyu hakuri duk nagani kuma ina godiya kwarai Allah bar zumunci janaf na matukar sonka over my lovely fans...#Janaf fans#oneluv_
NOT EDITED⚒
46/47
""""Nusiba ta korema Aisha kewa da rashin yar"uwa domin tashige gaba kan komai..Gata ta hannun damam Amarya kuma matar yaya gareta gata kuma bangaren angoma haka tana da wani mtsayi mai girma,takowani fanni tana taka muhimmiyan Rawa..Komai akayi Musty zai kira Nusiba hakama Aisha..Nusi dai tazama takowa domin hatta Ammi da ita take shawara.
*RANAR DAURIN AURE*
Nazir bai iso kano ba sai Ranar asabar da safe dashi da bash suka zo da zahra..Suna isowa badadewa saiga mg da gidado suma kowanne da matansa,nan suka shiga ciki suka hade da Nusiba anata hidima suko su Abbu Nazir na isowa ya nemesu aka kaimai chan suka koma gida shida su bash suna dan hira kan lokacin Daurin aure.
Musty kuwa da gayyah abokansa a hotel suka yada zango baki ne da kasashe dadama abokan karatunsa da abokan aikinsa kunsam Abun na likotocine to gabadaya gayyah nasu ne...
Aharabar gidan Abbu aka daurama Aisha da musty aure bayan Abbu yayima Aisha wakilci Shikuma wani kawu marigayi Alhaji hasan yayima Musty( Dama Abbu yakirasu yafadamusu dayake daman baida wasu dangi duk sun kare wa"inda suka rike zumunci basu da yawa)Lalle daurin Aure yasamu hallatan manyan mutane kama daga abokan Abbu da yan"uwa masu huldan arziki..daganan Wani kayatattacen Restaurant akaje akayi liyafar arziki,aka ci aka sha kafin kowa ya watse yana ma amarya da angon fata alheri.
Aisha kuwa ana cewa andauramata Aure...Tawani rushe da kuka kukan farinciki ne hade da na bakinciki na tuna yau andauramata aure ammh babu mommy babu Anty jidda sunbiye ma rudin duniya dana shedan,Kuka take bata ko share hawayen Nusiba dasu zahra sunyi lallashi ammh taki yin shuru..Kyaleta sukayi domin sunga alaman kukan ne Rahama gareta.
Komai Tuwona maina akayi domin abun na gidane,Aisha dkyar ta bar kuka ammh idanunan sunyi jawur dasu ammh fa tasha kyau domin shiga kawai take tana fita cikin kayan alfarma baki kuwa sunzo kamar ana barinsu,Rahma ma tazo Yan zaria ma sunzo wato su zubaida wanda Nusiba tace su ranto kudin mota suzo dondai itama ace yau ga nata sunzo..Kuma Ammi taji dadi kwarai da gaske.
Karfe Takwas na dare aka kawo Aisha gaban Ammi tamata Nasiha Ammi dafa kanta kawai tayi tace"Allah ya albarkaci Aurenku Aisha kamar yadda nake shedan mustapha haka zanyi naki..kuyi ta hakuri da biyayyah ga mijinki domin Aljanannanki na karkashin diga diginsa...Tashi kuje Allah yayi Muku albarka...Allah sarki Ammi harda dan hawayenta tare da ita aka dumguma sai gidan dasu Nusiba ke ciki aka yada zango abangaren Aishan...Lalle Masu duniya domin Uban dukiya sai wanda yagani kowa masha Allah kawai yake tare da addu"an zaman lafiya.
Nazir ko da Abokansa ba wanda yasaka matarsa a ido ko su Abbu dasuka gaji suka fara kuka,da yaita kiran wayanta ba"a picking aikamata yayi tazo ammh taki zuwa dole yaran yabada aka kaimata,su kansu bash kowa nason ganin matansa ammh ba dama hidima ta boyesu...Suko suna shashen amarya suna bidirinsu sunma manta da wasu miji...Suko sun shaka aiko basu gama shaka ba sai da dare yayi bash yakira Zahra tace mai suyi hakuri su kwanta sukan suna shashen amarya...Galala yayi da baki kafin ya kwashe wayar yana gayamusu Tsaki Nazir yayi kan yace"Shikuma musty ya kwana a ina..."Oho bash ya bashi amsa kira wayan zai kara yi Nazir yace"No leave demm...Wlh da gangan sukayi just mu manta dasu zamu hadu gobe aie"Sunyi Na"am da mganansa daganan ficewa sukayi suka shiga gari sai chan dare suka dawo...Suko su Nusiba Musty suka kira suka sai ya kawo musu kazan amarcinsu ba yadda ya iya hakanan ya baro abokananshi ya je ya siyo musu bankararrun kaza,da madarar hollandia ya kawomusu suka amsa suna dariya suna fadin sune yan"matan amarya domin yau hatta mazajen nasu yar sai gobe zasu maido su dariya shima yaita yi yana jin nishadi aransa na yau yatashi daga gwauro yakoma ango..Wayyo Abun yamai Dadi sosai.
Washegari tun Wuri su zahra da Ramlart da surayyah suka shirya domin sanin da wuri zasu koma mh bayan sunma Aisha dan gyare gyare bangaren Ammi suka fara zuwa Nusiba tabawa su Abbu Nono don Ammi ta wurga masu ta gudu..Aiko makalemata sukayi sai da tatafi dasu..Shashenta suka Nufa suna shiga suka iske mazajennasu a falo zaune kowanne yayi gayu cikin shigan wani boyel black ne mai sharashara dukkansu dinki iri daya..Kowanne makale da waya akunne..Bash ne yafara cewa'Kai baby..Kibari kada ki rikitani"Yafada yana wani narkewa Shiko mg makale murya yayi yace"Dear...Wlh jiya muna rabuwa naji duk ba dadi how i wish kina kusa dani"Yafada harda lumshe ido shiko Gidado cewa yayi yana kara rike waya"Wlh kece farinciki Thank yhu for yesterday bby"Yafada yana dariya shiko uban gayyan killer smile ya saki kan yadora kafa kan daya ya dora waya bisa kunni yana wani cijen lebensa na kasa yace cikin husky voice dinsa" u already know..Ni Nazir naki ne kinsan Allah my Noor kinsa Wlh naji ina son aurenmu yazo soon"Yafada yana shafa gemunsa yana yar dariya.
Kallon kallon Suka farayi tsakaninsu kafin kafin Nusiba ta musu alama da ido salin alim kowacce Ta nufi mijinta murmishi kwance abisa fuskarta...Nusiba kuwa kusa da Nazir da ijiye Su Abbu batai wata wata ba tajawo cushion din kujera tahau makama Nazir haka suma su Zahra suka hau makasu suko suna dariyan shakiyanci...Sai da suka gaji kodan kansa kana suka hakura suka koma gefe suna maida Numfashi,Kowanne rumgume matarsa yayi yana fadin yayi missin dinta..Nan suka lalace da shakiyanci kan suyi shirin Tafiya..Sunje sunma Ammi da Abbu sallama kan kowanne yaja matarsa yakara gaba cike da kewa.
Tuni baki suka watse yan zaria ma sunkoma cike murnan karban da"akayi musu dare nayi Musty yadauko Aisha suka zo gun Abbu yayi musu Nasiha sosai Allah sarki musty har shashen su Nazir suka shiga suka durkusa musty yace'broda kasamana albarka kuma kamana fada kasan ku kundade a harkan"rankwashi Nazir ya sakarmai akai yana Fadin"yaushe ka zama mara kunya mustpha sa"ankane neni"Sosa kai ya hau yi kafin ya shagwabe yana fadin"Kai broda wlh da zafi"Dariya Nusiba da Aisha suka sanya harara Nazir ya makamai kan yace"Wato kayi aure shine kake neman hada kai dani ko...To yaro karyanka domin inbaka manta ba baban yan"biyu nake kuma nan da 9month zan zama baban yan"uku"Yafada yana wani hade rai..Dariya suka kwashe dashi gabadaya Nusiba ta sakarmai harara tana Fadin"See ur mouth..Wazai kara haifan fiye da daya..Yaseen dayan ma ina jin tsoro"Dariya suka kara sakamata kan Nazir yayi musu Nasiha kan su zauna lafiya su Nazir fa anyi hankali harda Ma Musty fadan yayi koyi dasu don su Ammi basu taba jin kansu ba...Su suka rakasu har bakin bangarensu kana suka koma nasu.
Musty dai Da Aisha bayan gudanar da ciye da tandetande suka gudanar sallar godiya ga Allah..Tare da addu"o"i abubuwan dasuka biyo baya masu dadi ne domin musty ya maida Aisha cikakkakiyan Mace bayan Tarin gumurzun da"aka sha,tasha albarka dagodiya mai yawa...Tare da godema Allah daya tsaremai Eshansa..
*After 6 month*
Bude kofar office din akayi lokaci daya dashigowa...Sanye yake da suit black and white,sai rigar likitocin dake jikinsa Da siririn glass din daya karamasa kyau over...Kallonta yake tazaune kan kujera sanye dawani material black and red..Jan mayafine nade ajikinta fuskarta tayi fayau da ita..Nufanta yayi yana Fadin'Am so srry...My Esha na jima ko"Baki ta tura kan tace"Ni..Ni...Kafin ta karisa ya kariso kusa da ita ya rumgume yana fadin"I miss u my esha..Kina raina aikine yamin yawa kema kinsani"Kara rumgumesa tayi kan tace'Nasani mijina abun alfaharina wanda bayason damuwata..Allah nake roko ya taimakeka akan dukkan Aikinka kazamo wani jigo gareni ka kuremin rashin uwa kazama makwafin yar"uwa agareni...Wlh.."harshensa ya tura cikin bakinta shiyadakatar da ita,sumbatarta yake cikin shauki itama ta tallafeshi suna farantama juna rai..Sunfi minti goma ahaka kan yaxare harshensa cikin kasala yana kallonta yace"Shiii...Yafada yana zagaye hannunshi kan lebenta"Babu godiya tsakaninmu my Esha Na tabbatar Da Allah ya haliccemu don juna ne...Ina sonki kuma zancigaba da sonki har karshen Numfashina"yafada yana shafa cikinta yana mata mirmishi itama tana maidamai kan tayi mgana yaduka ya sumbaci cikin yana fadin"Ya bby na ya ke"Ta lumshe ido tace"yana lafiya sai kewan Dadynsa yake"Dariya yayi kan yace yana mikewa"Ok..Kar yadamu yau Daddynsa zai gana dashi..Hop maman baby bazata ma baban Bby kuka ba ko"Jin haka yasa ta mike ta diddira kafa ta bishi da gudu yafada tiolet yana dariya itama dariyan tayi takoma ta zauna tana ayyana Abubuwa dadama...Wai ita Aisha ce tazama cikakakkiyan matar aure harda ciki na tsawon wata hudu...Tasamu dukkan Fatinciki takowani Fanni..Ya musty mutum ne abun so ga kowa...Wanda yasan darajan kansa da wanda ke karkashinsa wlh da badon kar ace tayi sonkai ba sai tace Tafi kowacce mace sa"a Aduniya..Hawaye ya zubomata data Tunani mahaifiyarta da yar"uwanta ko awani hali suke ciki oho..Kwanaki da ya musty yaga nadamu har daukanta yayi suka je gidansu ammh Abun mamaki wasu suka tarar agidan..Gidan ma da badon sunmai mugun sani ba dkyar suka gane shine saboda yadda yaji gyara yadawo kamar ba shi ba har ciki suka shiga matar gidan ta tabbatar musu dacewaa"basu dade dadawo ba daga lagos suke suma siyan gidan megidanta sun tambayeta su Jidda ammh ta fadamusu cewa itakam basu iske kowa ciki ba"Haka suka fito jiki asanyaye kamar marasa lafiya amota kuwa kuka taitayi kamar musty yaita lallashinta Abunda sai da yajamata zazzabi...Tun lokacin damuwa yaki barinta tana kokarin dannewa ne.
Tare suka fito daga office din Hannunsu sakale da na juna haka ake binsu da kallo domin inda sabo sunsaba don Dr Mustapha mayen esha ne ko ina suna tare da jun...Motarsu suka suka fice daga asibitin...Tafe suke suna hiransu ta masoya Daidai Aminu Road sai gawata mata tazo tsallakawa digon hijabi ajikinta har kasa da kullin leda baka ahannunta sauri kawai take kamar bata gani kawai tafado titi sukuma sunkawo gab...Jikake..Kuuuuu...karan taka burgi Allah ya kyauta ammh duk da haka sai da motar ta bangajeta tafadi gefe ledan ya zube...Da sauri Aisha musty suka fito suna salati da mutanen dake gun Saurin rikota Aisha tayi tana mata sannu har yanzu basu ga fuskarta saboda bata dagoba shiko musty kokarin tattara dan garin rogon daya zube yakeyi Aisha ta rikota tana Fadin"!Sannu baiwar Allah...Muje asibiti"Tafada tana son ganin Fuskarta jikin matan yafara rawa ko amafarki bazata manta da wannan muryan ba..Cikin kasala da rauni tadago Fuskarta karaf sai ana Aisha da karfi taja baya tana Fadi da karfi
JIDDA...tafada jikinta nawara...Musty dake gefe ya yarda abunda ke hannunsa ya tsurama wcce ke tsaye ido cikin mamaki da jimami...Yafurta ahankali JIDDA....Yafada da son Tabbatarwa domin shifa wacce ke gabansa batamai kama da jidda yar gayu ba wata yamutsantsan tsohuwa yagani wacce wahala ya tsufar da ita......
.
*Comment*
*Share*
*Vote*
*janafi*💖
_*JANAF*_✍
*DAGA* _*INTELLIGENT WRITERS ASSO*_📝
*NAZIR*
_*(D Journalist)*_
_Based on luv and Romantic story_
*Dedicated to u my Sahiba HAFSAT HAFNAN*💞
*DEDICATED TO:ZUMUT@ NOVELL@ AND BENEFICIAL WRITERS FANS...THANK YHU ALL JANAF RELLI APPRICIATE*
NOT EDITED⚒
47/48
""""Cikin sauri Jidda tajuya idanunta sunciko da hawaye ta fara Tafiya da hanzari Aisha Da Musty suka take mata baya suna kwalamata kira..Mutanen dasuka dan Taru suka bisu da kallon mamaki..Ganin jidda taki tsayawa gudu kawai takeyi tana kuka Yasa musty yayi saurin shan gabanta yana Fadin"Jidda..Meye haka mune kike gudu kuma? yafada yana kallonta Jidda ta dago idanunta da sukayi jajir ta saukesu kan musty kan tace cikin wata raunanniyan murya.
"dole na guje ku ya Musty bandace dazama acikinku..Ni zunibi ne wlh ni bala"i ce Ku tafi don girman Allah kubarni"Tafada tana kara fashewa da kuka Aisha dake gefe tana kuka ta riko jidda tana Fadin"Haba Anty jidda..Kidaina cewa haka komai xaki zama kidin jininmu ce wlh Rana batata ba fitowa ban Tunaku ba keda mommy"tafada tana Rumgume Jidda tana Fadin"'Anty jidda ina mommy...ina kuka shige mun nemeku har mungaji"Kuka Jidda kawai tasaka Aisha na Rumgume da ita,ammh ita takasa rumgumanta back
Ganin Sun fara kokarin Tara jama"a yasa Musty yace"Ku muje mota ma karisa kun tara jama'a fa"Aisha ce tariko Hannun jidda ammh taki binsu sai ta turje,Musty yakalleta yace"Wai meye haka ne"Jidda tayi mirmishin karfin Hali tace tana kallon Aisha"Bandace da binku ba..Kar ku manta Abunda muka aikata gareku..Aisha kinmanta duk tsanar...Shiiii..Aisha tace tana dora hannunta kan bakin jidda kawai taja hannunta sai gun mota ita ta bude mota ta sakata abaya ita kuma takoma gaba Musty ya shiga ya tada motan sukayi gaba.
Sunfara Tafiya Ammh Jidda kuka kawai takeyi hakama Aisha..baice musu komai ba illa kada kai kawai yakeyi Aisha ce tajuyo ga jidda tace"Anty jidda ina mommy...?Tafada hawaye yana zubomata kara fashewa da kuka Jidda tayi kamar wacce ake yankawa Aisha ta tsananta kukanta kan tace"Tana ina..Don Allah karki cemin wani Abu yasamu mommy'"Tafada tana kuka.
Dagowa jidda tayi tana kallon Aisha kawai hawaye yana zuba batare datayi mgana ba,Musty ne ya katsesu da cewa"Jidda ina muka Nufa? kallonsa tayi murya shake tace'!muje kawai.."Bai kara mgana ba saida suka kai Dawakin Tofa kana jidda tace su tsaya abakin titi ya Faka motar Musty yayi suka Fito jidda bata musu mgana ba tawuce tafara tafiya ta dumfari wani lungu suma basuyi mgana ba suka bita..fita chan lungun shiga chan sai gasu ga wani kango wanda daga gani yayi shekara goma dafara ginasa ba"a karasa ba Abun mamaki ciki suka ga jidda ta shige Aisha takalli musty shima ita yake kallo..binta sukayi gidan yana da girma daki bayan daki suke binta ammh dole sai da suka toshe hanci saboda warin kashin alma"jirai duk sun bata guri.
Basu tsinke da al"amarin ba sai Jidda ta tsaya cikin wani daki wanda babu komai ciki sai ciyayi daya cika gun suna shiga wani wari ya ziyarci hancinsu sai da suka kara Dade hanci Jidda tajuyo tana kuka tace"Kince ina mommy ko..? To ga mommy ga yadda Rayuwa tajuya momy ga yadda Allah ya maidata g yadda Rudin Duniya da Rudin shedan ya maidata kinga yadda Allah ya maida ta ko Aisha"Jidda tafada tana kuka tana Nuna wani wata yamutsatsan Tsohuwa,kwance duk ta rame ta lalace tayi fitsari harda kashi akwance domin wani wari ne ke busowa bakinta ya karkace miyau yana zuba aciki.
Musty Da Aisha suka bi inda Jidda taNuna musu da kall lokaci daya suka ja baya domin ganin Fuskar inna zainaba wacce ta zagwanye ta rame ta lalace,Dafe kirji Aisha tayi jikinta narawa ta daga hanni tana Nuna inna zainaba dake kwance akasa Cikin Najasa da kazanta halittarta duk ya canza...Tace"Mo..Mo..Mmmy.."Tafada bakinta da harshenta na Rawa shima musty Duk jarumtarsa sai da ya girgiza shima cikin mamaki da al"ajabi yace"Inna kece kika dawo haka...Innalillahi wa"inna Alaihirraju"un..."Yafada yana jin gwiwowinsa sunyi sanyi.
Inna zainaba dake kwance take jin surutu ta dago karkaceccen bakinta tana fadin"Waye..Waye..Nan jidda ce"Tafada Daba Daba wanda