Showing 45001 words to 48000 words out of 87333 words

Chapter 16 - Nazir Bok Complete Hausa Novels by Janafty.txt

Advertisement

cikin sanyin murya yace"Hello...Muryan sai tadaki Nusiba sai ta lumshe ido ta lafe kan kujera tace"Assalamu Alaikum..Ya Nazir barka da hutawa"Tafada cikin karya murya tsam Nazir yayi wanda yake kwance shame shame kan gado barci ne yafara daukansa kiran Nusiba ya shigo bai ko duba no din ba yadaga.



""Yauwa..Ya"akayi ne"yafada cikin muryan wanda yatashi daga barci,mirmishi tasaki kan tace"ayyah dama just ince maka munsauka lafiya ne'masha Allah"ya furta kafin yace"plz kidaina kokarin katsemin Abubuwa na masu muhimmaci ba"a kirana ina na kwanta,ok"Yafada yana datse kiran Nusiba tazare wayan tana dariya tace"yaseen ko anjuma sai na kara kira,ko ahaka natakura maka"Tafada tana shekewa dadariya game din na mata dadi.



Sai da takammallah komai nata daya ke batayi girki ba gun Anty taci fentin rama takoshi kana tadawo gida,kayan barcinta ta sanya masu taushi riga da da wando sai da lumtse bisa katifa ta rufe rabin jikinta da blanket kana tajawo wayarta tadokama Ya Nazir lokacin da wayar ke shiga mirmishi ne bisa kan fuskanta.




lokacin kuma Nazir zaune yake kan daya daga cikin kujerun daya ma falon kwanya,laptop ne akan dan wani tebur dake gabansa yadora kafarsa guda daya,hannunsa daya yana kan na"uran Yana sarrafa ta lokaci bayan lokaci yana daukan kofin coffea dinsa dake gefe,ko Riga bai dashi daga shi sai boxer yana hutawan sa wayarsa dake gefe tadau neman agaji da wutsiyar ido yakalleta baisan sadda yace"Oh may God..wannan wace irin mayyah yarinyace"yafada yana wani bata rai,


tana katsewa tasake kira,shareta yayi ya cigaba da aikinsa Nusiba kuwa tayi dariya tace"ai saika dauka" Ganin bata da niyar daina kira yasa yadaga cikin Fushi yace'Are u mad...Kinkira kinga ba"a daga can u stop callin"yafada cikin Fushi shagwabewa tayi tace"Ayyah...Am srry bansan kana wani abu bane"Tafada Tana kara narkemai Tsaki yaja kafin yace"ok baki maSani bama ko"yafada kai tsaye Nusiba tace'eh...Yace"ok...Ya"a akayine aiki ne nakeyi ne"Nusiba tace"Zaka zo wannan week din ne"Tafada cikin nuna kulawa.


Tabe baki yayi yace"Don"t know if possible dai"Yafada cikin halin ko inkula Nusiba tace"Ok inzaka dawon kagayamin plz"Tafada tana neman samai kuka,yanayin jikinsane yafara canja baisan sadda yadauke hannu bisa Na"urar ba yajingina kansa bisa kujera,yana Fadin"infadamiki kikace?dawowata da Rashin dawowata kina da damuwa da hakan ne"yafada cikin sanyin murya Nusiba tasaki dariyan burgewa tace"Niko keda damuwa Ya Nazir miji guda fa kaji ance"Tafada tana yar shesshekan Dariya.


lumshe ido yayi yanajin tsigar jikinsa na tashi yace muryan sa ta sarke"uhmmm meki ke shiryamin ne banyarda dake ba"mirmishi tasaki kan tace"Ba abunda nake shiryama sai Alheri kayarda dani"Nazir yayi shuru yana shafa sumar kansa yace"Naji....sai da safe"yafada da dakewa,Nusiba tace"Tam...Sweet dream karka manta da addu"an barci"tafada kamar Tana gabansa.



Jinjina kai yayi harzata ijiye wayan taji yace"Hey...Tace"Na"am yacigaba da cewa"Ammh kina shigamin lokacin Aiki be carefull Cikin dariyan dake tasomata tace"Yes Sir..."Mirmishi yasubucemishi sai yayi saurin latse kiran yana mamakin kansa daga jiya zuwa yau komai yake kamar bashi ba,yadade zaune yana Tunanin yadda Yar kauyen nan ke mgana ba karya tana da murya,aikin da bai karisa ba kenan ya tattara yakoma bedroom ye shirin barci...



Itama Anata bangaren mirmishin tayi kafin taja bargo tana karanto addu"an barci sai da tashafe ko"ina na jikinta kana takara lumtse kanta jikin matashin..



*ASUBA TA GARI NUSNAZ*





  """Da garin Allah ya waye Text  din Nusiba yatadashi sallar asuba tana umartansa yatashi zuwa sallah,ada ko damuwa daduba mssg bayayi ammh yanzu akai akai yake duba wayarsa baisan dalili ba,-Zaka ma Sani ne_

Haka Nusiba ta rike wuta bata barin Nazir yayi sakat da kiran da Text wani lokaci yadauka su dadi wani lokaci suyi tsiya,duk da bai taba kiranta ba ammh tana ganin cigaba,asatin bai samu dawowa ba sai a wannan weeked din Ranar Friday yana bayan mota ilu natukasa suna kan hanyan zuwa kano yajawo wayarsa yaturama Nusiba text .


    *Miss ma Home....Coming...*



Kawai ya Turamata lokacin tana zaune kusa da Ammi suna hira text yashigo Allah yasa wayar na hannunta tana gani ta mike zumbur har Ammi na cewa"ke lafiyan kuwa"tafada tana kallonta Nusiba tanufi Hanyar fita tana Fadin"Bakomai Ammi Abu na bari kan gas"Ammi tahau tafa hannu tana fadin"kujimin shirme shine kike zaune kinyi dagal dake ko"ko jinta Nusiba batayi da gudu tafice sai gida.

Atsakar falonta taci burgi tana haki hijabinta ta kwabe tana tunanin ta ina zata fara wayan hannunta tashiga latsawa chan tasa akunne tace"Ya musty don Allah taimako nake nema"musty dagachan bangaren yace"name fa matar yaya"Nusiba tace"meye best food din ya Nazir"musty yayi dariya yace"Topha matar yaya"Nusiba tace"Don Allah nidai kafadamin ba lokaci"sakwara da miyar agushi taji manshanu"Tanque kawai tace mai takaste kiran.




Da Hanzari tafada kichen tafara fere doyan tadora kana takoma ta daura miyan sauri sauri hanzari take komai kan kace kwabo har ta daka sakwaranta ta nannadeshe cikin wani leda tasanya awani ubansu kula,itakuwa miyar agushi kaza guda ta markade aciki,sai tayi amfani da Ogun cikin lokaci itama da kammallau zobu tayimai Tunda ba lokaci agurguje Tafada wanka wanda Ruwan wanka yaji Turaruka masu kamshi tana Fitowa takalli agogo har 5:09pm cikin hanzari ta isa gaban mirror tashafa lotion dinta hoda kawai tashafa sai jan baki purpple,wardrope dinta ta bude tajawo wata Atamfanta exclusive mai Ruwan purpple da baki doguwar rigace,AShape wacce ta mata dam ajiki mazaunan ta sunfito sunyi das cikin rigar daurin Zahra buhari tasaki abunta bayan ta zubo da gashinta ta baya,tTurare ta fesa sama sama Tafice kichen takarisa ta dunga kwaso abincin tana jerawa bisa dining da,sauri kuma takunna Turaren wuta na Rushi wanda Ammi da kanta tabata tajuya kenan rimot na Hannunta tana kokarin chanza tashar talabijin taji sansanyar muryasa cikin amo damazakunta yana sallama,duk comfident dinta sai taji jikinta yafara rawa takasa waigowa.



  Shiko tundaga haraban gidan kamshin turaren datasanya ya masa maraba tsaye yayi cak yana bin ilayarin bayanta da kallo cikin wani yanayi aransa yana Tunani kila fa ba yarinyar ba sai dai bakuwa akayi.








_am srry say bazaku jini ba gobe ba da jibi ba sai dai zuwa sunday ko monday cos zanshiga sch hop bazakuyi fushi wlh Abubuwan ne sai slow...Tanque love u all_





*Comment*
*Share*
Vote*






*Amula bea*💕
[4/11, 2:14 PM] 0mmer Farouk: *🧑🏻NAZIR🧑🏻*

     _*(The journalist)*_

*(Based on luv and Romantic story)*

  *Na*

*Janaf ce*✍

*Vote me on WATTPAD:Janafnancy*



© _*INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION*_🖊




*```DIDECATED TO SAHIBA HAFSART HAFNAN```




_Sakon gaisuwata gareku tareda jinjina mai dimbin yawa ga wa"innan gidaje masu tarin albarka,gidajene da"ake tattauna alhairai dadama,NAZIR na matukar godiya ga soyayyar ku garesa,hakama NUSNAZ Tana miko jinjina bisa shawarwarinku gareta tace ince muku one love_💞💞


*DALA NOVEL GROUP1&2*
*FEEDOHM NOBELLA*
*AUREN FARI FANS*
*ZAUREN MAI DAMBU*
ZAHRA AND PINKEEY NOVELS*
*UMMYN YUSRA NOVELS*
*JANAF NOVELLA*
*SO KO WAHALA FANS*
*FATALWAR MIJINA FANS*
*YARIMA SUHAIL1&2*
*WRITERS NOVELS FANS*
*MHIZ HAFNAN"S NOVELS*
*ZAUREN MAI DAMBU*
*TAKWACEN MIJI FANS1&2*
*INTRLLIGENT WRITERS FANS*
*AUFANA TRUE FANS*
*RUDANI FANS GROUP*
*PURE MOMENT FANS*
*WANI MATSAYI FANS*
*BILLY S FARI NOVELS*
*INTELLIGEN WRITERS FANS*
*NAZIR FANS1&2*
*ZANGON KASA*
*AYSHA SADA MACHIKA NOVELS*

*Etc suna da yawa,godiyata agareku bazata yanke Ba tanque so much for u luv support and care*



_*D whole page iz dash for u my bestie SA"ADA ALKALI D TSAFE...ki shana ki huta kiyi yadda kika ga dama shi mallakinkine sai kinga dama kiba wani yakaranta,janaf relli Appriate Allah yabar kauna da zumunci mai dorewa*_







24/25







       """"Ajikinta taji cewa yana kallonta,jikinta yafara rawa,takasa waigowa,shikuwa cikin wani yanayi yake dire idanunasa ako"ina na jikinta yakasa yadauke idanunsa akanta,itakuwa dakyar tayi karfin halin ijiye remot din tajuyo cikin wani slow motion fuskarta dauke dawani kayatattacen murmishi karaf idanunsu suka sarke ana juna kallonta yake daga karkashin ziciyarshi itama haka,kuma lokaci daya zuciyoyinsu ke bugawa fat!Fat!




      Tafiya tafarayi zata isa garesa ammh in yalura jikinta rawa yakeyi sai da tazo gab dashi kana yayi saurin kauda kansa zai raba ta gefenta ya wuce,caraf ta rike yar jakar briefcase dinsa tace cikin sanyin murya"sannu da zuwa"tafada tana kallonsa kai tsaye,sakarmata jakar yayi kawai batare daya kalleta ba.

kallonsa tayi taga yana kallon gefe sai ta murmusa tace"zauna mana kana tsaye"tafada kai tsaye,kamar wani wawa kuwa yasamu daya daga cikin kujerun falon yazauna yana dora kafa daya kan daya yana girgizata ijiye jakar tayi kan center table din dake tsakiyar falon tanufi kichen cikin takunta na sanyi kowani gefe na jikinta na motawa binta yayi da kallo harta shiga kichen din,ajiyar zuciya yasauke yana lumahe ido lokaci daya dashafa sumar kansa,cikin wani yanayin dashi kadai yasani.

   Tana shiga tabude fridge tadaukomai Ruwa mai sanyi,da kofi tadora kan wani kyakyawan karamin farantin tafito tana taku daya bayan daya,harta kariso gun,idanunsa alumshe suke tsiyayamai ruwan tayi tamikamai tana Fadin"Ga ruwa ya Nazir..Nasan kasha hanya"tafada tana kallonsa,shiko sai dayagama shankamshinsa kana yabude lumsassun idanunsa yasaukesu akanta langwabe kai tayi tace cikin shagwaba"plz ka amsa mana"Kallon cikin idanunta yayi kan yamika hannu ya amsa cikin kasala,yasa kofin abaki ammh still yana kallon kwayan idanunta ammh sai kuma data kallesa cikin ido sai ya janye idamunsa.

   Mikewa tayi tarataya yar briefcase dinsa tanufi dakinsa tana taka step din yana binta da idanu har tabace masa ajiyar zuciya yasaki kan yace afili"what wrong wit me ne"inajin son kallo yarinyan, kwayan idanunta in nakalleta suna sani cikin wani yanayi..Why? ya tambayi kansa ammh yagaragara gano amsa.

Tashi yayi yabita saman yashiga bedroom din kenan yaganta tana gyaramai gadonsa kallonta yayi kan yawani hade rai"ke...Wai naga sai wani  shisshigemin kike nasaki ne"yafada fuskarsa adaure,Nusiba ta murmusa tace"baka sakani ba,ammh ai aikina ne ko"tafada tana sakarmai ido sai kuma yakasa mgana yakarisa bakin gadon ya ijiye wayarsa.

  tsayawa tayi hannunta sarke akirjinta tana kallonsa yana zama bakin gado kokarin cire takalmin sawu ciki dake kafarsa yakeyi,da hanzari takarisa taduka tafadora hannunta kan Nashi tana Fadin"let me help u"tafada fuskarta ba alaman wasa,hannunshi yayi saurin jayewa yana binta da kallo ammh ita taki bari takallesa tana ciremai takalman taciremai socks sai ta mike kai tsaye tasa hannu tafara zaremai jaket din dake jikinsa ta ijiye kan Gado hannu tasanya tafara ballemai botiran rigar dake cikinsa,so yake so hada ido ammh taki bari saboda tasan gwaleta zaiyi,baigama mamaki ba yaga harta vest din jikinsa tazaremai,taciremai belt taja dogon wondon dake jikinsa,tabarshi daga shi sai boxers kauda kai tayi zata wuce tace"Ruwan wanka fa yana jiranka atiolet"tana fada tajuya zata wuce yayi saurin damko hannunta cikin zafin nama yadawo da ita harsaida tabugi kafadansa tajuyo takallesa da manyan idanunta.

  Nazir fuskarsa babu Annuri ko kadan yace"baki gama aikinki ba malama"yafada harda waremata ido kallonsa tayi da mamaki kan tace"wani aiki kenan"?Tafada still tana kallonsa,mirmishin mugunta yayi kan yayi pointing din boxers din sa yana cewa"kinbar wannan madam,oya up him"kunya takama Nusiba tayi saurin sadda kai tana kokarin kwace hannunta,ammh rikon ba daya ba.

Gefen bakinsa ya ciza yace cikin dakewa"kefa nake jira malama"Nusiba ta runtse ido tanajin kunyan duniya takamata itafa wlh Don Rahma tacene ammh ita maizai kaita ma,gani yayi bata da niyar yin abunda yace kawai sai yarike hannunta da hannu daya hannu daya kuma yana kokarin zame wando,wani kara Nusiba tasaki tana runtse idonta tace cikin rawan murya"plz ya Nazir don...Allah kabari"tafada kamar zatau kuka,banza da ita yay ,ganin haka yasa ta daddage ta turesa yafada kan gado tayi wuf tafice hartana tuntube.

   Nazir kuwa dariya ta subucemai yadinga kyatakyatawa kamar mahaukaci yafada afili"gobe kisake kiran mai alewa baki da kudi,villager girl ji yadda tafita hayyacinta just don zata ganni niked mtswww yayi tsaki yana fadawa tiolet din.



Nusiba bata ci burki ako"ina ba sai a Tsakar falonta tafada kujera tana maida Numfashi kamar wacce tayi gudun famfalaki,Afili ta furta"lalle Namiji baida kunya,sam baisan ko kayan dana ciremai ba,karfin hali bane"tafada hannunta dafe akirji gyara zama tayi tana maida hankalinta kan talabijin itakadai take sakin mirmushi in tatuna Abunda yafaru.


  Shiko yana shiga tiolet din yaga tahadamai ruwa cikin bath yana shiga sai yasaki siririn ajiyar zuciya saboda yadda kamshin ruwan yadakimai hanci yadade zaune cikin ruwan kafin yayi wanka yafito daure da tawul daya akansa yana gogewa daya yadaureshi akugunsa,mai yasha tareda body spry wardrope dinsa yabude barayin kananan kayansa yaciro wani wando truser da wata riga ta kamfanin Armani daga sama anyi rubutu dabakin shudi *Giant* sumar kansa yataje fuskarsa tana wani kyalli saukowa yayi yana takunsa na takama Nusiba batama kula dashi ba saida yaratso falon kusa da ita yazo kamar zai fadamata kawai sai yadau remot yanufi kujeran dake fuskantata yazauna yadora kafa daya kan daya yana girgizawa,Tashar aljazira yakamo Ko inda take bai kalle ba.


  Nusiba ta kallesa da mamaki aranta tace"kaji dashi kuma"gyara zama tayi tace"Ammh...Ya Nazir"tafada cikin zakin murya ko dagowa baiyi ba illa idanu daya sakarmata tace"nace dinner fa iz ready"yamutsa fuska yayi kamar bazai yi mgana ba har ta fidda rai sai chan taji yace"cemiki akayi da yunwa nadawo"yafada hankalinsa kwance, Galala Nusiba tayi tana kallonsa kan talamgwabe kai tace"plz karkace A"a wlh best food dinka nayi maka"tafada hartana hada hannuwanta kallonta yayi cikin ido yabude baki zaiyi mgana takatseshi dacewa"plz...Kaji"baisan sadda yace"iz ok zanci"tafi tayi kafin tamike tana cewa"Thank u "Dinner din tawuce tana rawan jiki da ido yabita,yana ayyana abubuwa aranshi.


   Sake dawowa tayi ta tsaya gabansa,tana cewa"Kataso muje kaci abincin don Allah"tafada tana tsaye kansa,bude ido yayi yana cewa"oh my god wai ke meke damunki ne"yafada yana kureta da ido,kafin yacigaba da cewa"komai kice sai kin tasani ni danki ne"yafada cikin fushi.

  Juyawa tayi dariya naneman kubcemata tace"Allah baka hakuri"tafada tana wucewa sai daya gama jan ajinsa kana yataso yazo gun dinning din tana tsaye tana ganin yazo tayi saurin jawomamai kujera zama yayi yana wani cika yana batsewa kular miyan tafara budewa kamshi miyar data dakesa sai da ya lumshe ido sakwara biyu tasanyamai takuma zubamai ferfesun kan ragon,tsaye tayi akansa shikuma yakalleta yace'ki tashimin aka,kada ki shanyemin jini"yafada ba alamun wasa atare dashi dariya tayi harda rufe baki kan tawuce falo kallonta yayi yana fadi afili,Funny girl


  Abu kamar wasa sai ga Nazir ya share sakwara nan har biyu yashare ferfesu yana shirin shanye zubo bai lura ba,sai da ya ga babu space kana yadakata daidai ko ana kiran mangarib,sama yahaura aransa ya mamakin yadda yar kauyen nan ta iya tsara hadadden abuncin irin haka wanda duk yawon duniyansa bai taba cin sakwaran dayajishi komai zam ba irin na yau ba,alwala yadauro ya sauko da Nusiba Yaci karo zata shiga daki adawo lafy tamai,duk da bai amsa mata ba yaji dadi sai yakada kai yafice,zuwa tayi taduba kan dining din suman tsaye tayi ganin yadda yaci abinci rike baki tana mamaki sosai kafin kuma tayi dariyan jin dadi koda bai yaba ba tasan yaji dadi.

Daki takoma itama tayo alwala tazo ta kabarta sallah,shikuwa sai da aka sallame sallama,sun fito kenan Abbu yaganshi,cikin mamaki Abbu yace"Mallam Naziru yaushe agari kuma? Yafada yana dafa kafadansa mirmishi yayi yana Fadin"dazun nan Abbu,yanzu nake shirin shiga mu gaisa"Abbu yarike masa hannu yana cewa"lalle Naziru danwaken zagaye ko"yafada yana dariya kawu ne yace"a"a Ba danwaken zagaye bane Alhaji"Dariya sukayi dukkansu Shikuma Nazir ya murmusa tare suka rankaya zuwa gidan,Kawu dai gida yawuce,Ammi tayi mamakin ganin Nazir kan tace"Abbu ina kasamoshi haka daga sama"Abbu yace yana jawo hannunsa "Nima a massalaci na gansa"Nazir ya isa ga Ammi yana Rumgumota yace"miss u Ammi"Ammi ta bubbuga bayansa tana Fadin"miss u too my son"Abbu yakallesu kan ya wuce yana cewa"Muna ganin sonkai muda ba"ayi missing dinmu ba,bari mukama kanmu"yafada yana shigewa ciki dariya Ammi da Nazir suka saka.



Zama yayi kan kujera suna kara gaisawa da Ammi sai ga Musty ya shigo cike da murna ya isa ga dan"uwansa ya rumgumesa yana cewa"oyoyo broda yaushe kadawo'Nazir ya rumgumesa yana Fadin"lazy doctor ya aiki"Bata rai musty yayi kan yace"Kai broda sai fa yanzu nadawo daga aiki"yafada kamar zaiyi kuka Dariya Ammi tasaka kan tace"rabu dashi zolayarka yake ammh yasan ko aiki kafishi"Nazir yace"Haba Ammi wannan layaulayau din ne yafini"Ammi tace"Ah yafimaka mana shifa in yafita tun safe sai iwar haka yake dawowa,"Nazir ya tura baki yace cikin kunkuni"ni kuma sai weeked nake samun sukuni fa Ammi"Ammi tamike ta wuce tana cewa"bari natafi gun mijina inna biye muku haka zan lalace gurin raban gaddamanku"shigewa daki tayi tana dariya.


   musty shima karisawa daki yayi domin yayi wanka,Nazir aka bari afalo yana kishingide yana hutawa,Harsaida musty yayi wanka yashirya ya fito kan yace"broda gidanka zani najira kane"Ko kallonsa Nazir baiyi ba sai kara gyara kwanciya dayayi yace"dama tare muke zuwa"yafada hankalinsa kwance tabe baki Musty yayi kan yace yana wucewa"Ah daga tambaya",yafada yana dariya girgiza kai Nazir yayi kan yace" Allah ya shiryeka.


  Nusiba bayan tagama sallah zama tayi tana azkar har aka kira issha"i tatashi tayi kana ta shiga wanka koda tafito simple makeup tayi,tasanya wata doguwar mai roba,pick colour sai wata hula data sanya, falo tadawo taso taci sakwaran ammh kuma sai taji indomie take son ci,shiyasa tashiga kichen tadora tajefe kwai aciki tadafa tazubo a filet kenan Tafito musty yayi sallama ya shigo da fara"a suka gaisa kan yazauna yana Fadin"Matar yaya ina fatan anyi mana sakwaran"Harara ta sakarmai kan yace"Kai akamawa dakake tambaya"Musty yace"Ah kanin miji mana"gyada kai Nusiba tayi kan tace"Gaskiya ne su kanin miji manya"dariya Musty ya yi kan ya mike yanufi dinning yana Fadin"kinga inada ma nayi"batamai mgana ba ya isa ga dinning din yazubama kansa yahau lodawa yanayi yana jinjinama Nusiba saboda gaskiya girkin yayi dadi.


   Sai da yakammallah kana yadawo falon yana Fadin"matar yaya kin yi mkrantar home management ne hala"yafada yana zama ,dariya tana samai filon kujera tace"bari namaka waigo kar ka fado,atare sukasa dariya dai dai lokacin da Nazir yakawo tsakiyar falon ta gefen ido ya kallesu lokaci daya kuma Annurinsa ya dauke ganin yadda suke dararraku babu wacce tabashi haushi sai Nusiba,.


  Musty ne yace"ah broda yanzu ka shigo kenan"inkunce tak to ya tanka zama yayi kawai ya maida hankalinsa kan talabijin ammh akasan ransa hankalinsa na gun su musty.

  Musty yace"matar yaya kinsan shekaranjiya na saurari shirinki,kai wlh kin na kokari sosai matuka,duk labarin danikeji ya wuce yadda naji"Nusiba tace"Da gaske,karfa kasa kaina ya fashe"Musty yace"ai yafashen matar yaya,ko"ina zencenki ake musamman shirin dakuke da Nura dabo"Nusiba tace"Freedom takuce,ai ya karbu sosai wlh "

  Nazir dawani Abu ya tokaresa masa awuya wato ma yarinyarnan Tasamu sake dama wani gardi take gudanar da shirin har ana labarinsu agari,nan da nan yaji ransa yabaci baisan sadda yadaka musu tsawa ba dacewa"Shoutup stupit..."Yafada ransa bace musty yakalli Nazir yaga yadda yake Turiri sai yakama bakinsa.

  Nazir yacigaba dacewa"Chacha kubaku gajiyane,kun dameni da hayaniyarku na banza,plz ku bani space am beging u"yafada har yana hada hannu,musty da Nusiba suka kalli juna lokaci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login