Showing 75001 words to 78000 words out of 87333 words

Chapter 26 - Nazir Bok Complete Hausa Novels by Janafty.txt

Abun ke raina"Inna zainaba tayi dariya tace"indai kina shirye da daukan Fansa...Nasan komai game da iyalan Adamu yanzu hakama yar iskan yarinyan ma ciki gareta"Jidda ta dafe kirji tace"Nusiban..."inna zainaba tace"Kwarai ma kuwa...Kuma yadda labari yazomin mugun son cikin suke"jidda ta yarda fork din dake hannunta tace'Lalle lokacin daukan Fansa yazo mommy wlh yadda yayimin wulakanci sai nayi sanadiyar zubar da cikin wanda nasaan bakincikin haka zai dade aransu bai goge ba"Tafada tana huci.




Inna zainaba ta mike tana Fadin"Nagode yata...Ai kin nuna ni zainabu ni na haifeki..Mazo sawo mayafi yanzu lokacin dazamu isan mata mu lalata musu komai suma mubar musu record din da bazasu taba manta ba"Jidda ta wuce daki fuu...Ta dauko jaka ko mayafin bata dauko ba daga ita sai riga da wandon da suka kamata kanta ko dan kwali babu sai uban attachment.


Takalli inna Zainaba tace"Muje mommy jikina yana mazari nakosa na ganni kan ruwan cikin yarinyarnan ina sukuwa"Inna zainaba itama ta dauko jakanta da mayafi tana fadin"Karki damu yanzu kuwa"Ficewa sukayi jidda tafada wata mota kiran Benz inna zainaba ta bude gaba tashiga suka fice daga gidan mai gadi na musu adawo lafiya.











*Comment*
Share*
*Vote*






*Janaf*💕
*INTELLIGENT WRITERS ASSO*📝

```{onward together}´´´

*NAZIR*
_*(The journalist)*_

*Based on luv and Romantic story*

 
*Na*   

*JANAF CE*✍

*_SADAUKARWA GA SAHIBA HAFSAT HAFNAN*_



_*Labari,Tsarawa da Rubutawa,Jamila janaf*_


_*Tantancewa,shiryawa da Bada Umarni Hafsart Hafnan*_





NOT EDITED⚒


42/43

    """Kiransa yayi sundan dade suna mgana kan ya nufi gun motan...Ilu naganin haka ya taso ya budemai suka fice daga asibitin...

  Kai tsaye address din da Cp ya rubutomasa na inda aka sakaya su jidda suka nufa,suna isa dpo da ganshi yafito ya taryi Nazir domin mai girma Cp yamai waya,bayan shigansu office din Dpo ya jawo fayel dinsu inna zainaba yana kara karantama Nazir lafikansu girgiza kai kawai Nazir yake bai yi mgana ba Dpo yace"Ranka yadade kotu yakamata mika ku fa...Domin ta"addanci yayi yawa rai biyu suka Nema alokaci daya'Tsuru Nazir yamai da ido kan ya muskuta yace"No Need...Yallabai kudai kawai kuci gaba da horasu horo mai tsanani wanda sai sun amsa laifinsu da kansu"Gyada kai Dpo yayi kan yace"Ai suna cin ubansu domin daya yarinya sam bata da kunya...Ai da kabari an mika ku kotu..Alkali ya tura yan iska gidan kaso ko na wata biyar ne"mirmishi Nazir yaya dan cizen lebensa umarni yabada afito masa da su jidda.

  Tawaya DPO yabada umarnin akawo su jidda,sun cigaba da tattaunawa kafin ya shigo dasu inna zainaba ce agaba duk ta fige ta lalace sai ido daya zazzago sai jidda dake bayanta tana wani tafiyan sanyi akwai chimaka yar sandan nan ta ingizota har sai da tafadi gaban Nazir tana Fadin"Shege...Wane zaka ma yanga"Nazir dake zaune yadago yana karemusu kallo inna zainaba na ganinsa tahau rawan jiki ta fashe da kuka tana cewa"Dama nafada muku munada gata..Kuma nasan wlh kwananku yakare tunda dana ya iso gun nan"Tafada tana kallon DPO wanda yake aikamata da dariyan mugunta inna zainaba kallon Nazir tayi tana fadin"Gasunan bamu musu komai suka kamomu suna ta dukkanmu...Kaci. uban yan iska"Tafada tana nuna chimaka...

  Daure fuska Nazir yayi kamar baitaba dariya ba yace"Karki sake...Am not ur son..Am Nazir Adam galadanci by Name...Shakikin da ga VC Adam galadanci...Wanda baki hada komai dashi so be carefull"Ai ba inna zainaba hatta jidda jikinta rawa yakamayi suka bi juna da kallo..Nazir kallon jidda yakeyi yana jin wani turirina Fitowa daga kasan zuciyarsa sai kokari yake yana kokawa da Numfashinsa kada yakaima shegiya Naushi,ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe ido kan ya kalli DPO yace"Kucigaba da aikin ku...Kada ku manta babu cin abinci balle walwala mai dadi beat dem very well...Rai biyu suka so kashewo so plz yallabai make dem suffer don Allah"Yafada yana hada hannuwa,Dariya DPO yayi kan yace"Karma kaji komai...Ai dan sanda ba"a gayamai duka ko horo"Mikewa yayi bayan ya bashi hannu sun yi musabaha Kafin Nazir ya ciro kudi dami daya ya ijiyemai kan Tebur yasakai ya fice inna zainaba na ihu tana kiransa ko waige haka aka ingiza keyersu aka mayar jidda ce keda sauran baki aiko chimaka tasamu Nama ta nadi banza sai da tadaina motsi inna zainaba na gefe ba halin mgana yanzu kam tama rasa mafita ta tabbatar da Tunda Nazir yasaka akakamasu ai shikenan sungama yawo kuma.

   *After 2 Days*

    Alhandulillah Acikin kwana biyun Nusiba tasamu sauki..Tunda hartana cin abinci kuma tabar tsoratan datakeyi,ansaka mata jinin duka leda biyun da"aka diba,kuma komai Normal, sai dai Tunda tafara samun sauki Nusiba bata mgana ko gaisheta akayi da jiki da kai take amsawa,Shikanshi uban gayyan ko yayi mgana bata cemai komai dakuma ya mtsamata ta fashemai da kuka Abun ya fara damunshi yama likitan dake kula da ita mgana kan rashin mganan da batayi yazo ya kara dubata ya tabbatarmai da cewa babu wani mtsala sai da in itace bata ra"ayin mganan yanzu.

  Abbu kuwa Tun awashegari sukayi mgana da megadin gidan Su Jidda yafadai yan sanda sunzo sun tafi dasu..Abbu yace shikenan zai bincika,bayan yanke wayar ne yayi Nazari ko shakka babu Da hannun Nazir akamasu domin shurunsa bayana Nufin ya hakura bane...Abbu baida Tuninin yin wani Abu akai ShiYasa Abbu ya watsar da Abun ya Nuna ma Nazir kamar baisan komai ba....Domin bayason yakasance mai dakushe dukkan motsin Nazir.

   Satin Nusiba daya asibiti suka dawo gida...Suna dawowa Nusiba tadinga kuka ita gida za"a kaita. Kuka bana wasa ba domin da farko Nazir Tafarama rigiman kuma ranar ne tafarko data faramai mgana da yadauka wasane saida yaga ta hau kuka baji bagani,Ammi yaje yadamawa Ammi kuma ta goyi bayanta,Abbu ma dayaji bai musa ba yace Nazir ya barta da tatafi gidan saboda hankalinta ya kwanta,Babu yadda Nazir ya iya washegari yana ji yana gani Anty da Ammi suka kwashi Nusiba da uban kayanta direba yatafi kaisu zaria.

   Tabbas Su inna zainaba sun anmasa ma jikinsu domin asatin dayan dasukayi ahannun hukuma sun fadama aya zakinta,domin daga DPO Har Ma"akatan dake karshinsa basu da Imani domin arana ma sau daya ake basu abinci kullum kuma duka kamar sunsamu jakai...Gwanda inna Zainaba da yake ita akwai tsoro to bata sha wuyansu ba sai da yunwa da zaman wuri daya,ita kuwa jidda tuni suka chanzamata kammani,ta rame ta lalace lokaci daya suka amsa laifunsu suna ganin tabbas sunkusa mutuwa,Waya DPO Yama Nazir yace yazo nan yasameshi.

   Lokacin Da Nazir yazo aka fito dasu jidda yayaba da yadda sukaci Ubansu,sai gashi Sun zube suna kuka suna ban Hakuri Nazir ya yarda asakesu ammh sai da akayi rubutu cewa ko kofar gidan Abbu wata cikinsu tataka wlh sai taje gidan  yari...Nan Nazir din ya Yatafi ya barsu suka tarkata su sukayi waje dasu Su jidda Abun tsausayi,Inna zainaba ne ma tayi kokarin sama musu Abun hawa suka Tafi gida.Jidda kuka kawai takeyi kamar me Tarasa kukan me take,kukan kaicho da Rayuwarta take kona Kaicho da rashin Samun uwata gari.








*********   ***********   ********



     Dalindalilai Sai Ga Nazir har tsakar dakin inna Fatsima yana Sanye  da shadda Gezner mai Ruwan kasa,sai hularsa zannah bukar,takalminsa Ruffaffe sawu ciki,yana sukuye dakai yana gaisheta cikin girmamawa Dada kuwa ta zage sai hidima dashi take tana Tsokanansa,Nusiba dake sanye da doguwar riga ta Atamfa anyi mata dinki buba,ga dan ciknta daya bayyana tadan kumbura,kuma tayi duhu,kusan dai Nusin bata wanka.

  Ita tamikamai Muhd Nasir yadaukeshi ammh halinshi na kan Nusiba yana karemata kallo...Lura da hakan yasa Inna Fatsima ficewa ta basu waje...Bayan takarbi danta wanda Nazir ya ijiemata Dubu ashirin...Tsam ya mike ya isa ga Nusiba baiyi wata wata ya rumgmeta kam har tana dan ihu saboda yadda ya kamkameta Itama luf tayi akan kirjinsa tana ajiyar zuciya don tayi missin din mijinta.


Dago da kanta yayi yana kallonta,itama shi take kallo...Itama shi take kallo cikin shauki ganin yadda yake lumshe ido yasa tasan meyake Nufi,Harshenta ta dora kan lebenshi bayan ta budemai bakin,cikn azama da rawan jiki Nazir ya cafki Bakinta bayan ya lalubo harshenta ya shiga kissing dinta in a romantic way...Cikin zafi Zafi yake aikamata da sakonnin itama tana maidamai martani,tsayuwa ta garersu sai gasu zube kan gadon inna fatsima🙈🙈
Ganin Nazir na neman wuce gona da iri ne Yasa Nusiba saurin Janye jikinta tana maida hannu doguwar riganta da Nazir ya ciremata.




Cikin wani hali Nazir yadago yana binta da kallo Kan yayi mgana ta rigasa da cewa"Nan fa ba gidanmu Kano bane fa"Tafada tana Nuna masa kofa...Dauke kai yayi kawai yana maida Numfashi kan ya mike akasalance yana Fadin"Ki shirya muje Hotel Nusi...Nakai limint din da bazan iya hakura ba"Kallonsa tayi shima ita yake kallo,Tsam ta mike domin idanunsa kadai ya nunamata Halin da Mijinta ke ciki.

Hijabi Ta sanyo Kan Taje tafadama Su Inna Nazir zai Tafi...Nan suka zo sukayi sallama ya zube musu kudi duk da basu hadu da baba ammh yace agaisheshi sai ya kara dawowa...Ilu ne dama ya kawosa suna shiga mota yace ma ilu ya kaisu daya daga cikin Hotel din Zaria...Shagalinku Hotel ya kaisu agurguje Nazir ya kama musu daki koda suka kai ga dakin jikin Nazir rawa yake yafara fita daga hayyacinsa Nusiban ce tayi kokarin Taimakamishi..Hakika Nusiba ta gurzu domin kaf bashin da Nazir ke binta sai da ya famshe bayan nan sai Da yakara kafin suyi wanka sufito su maidata gida karfe Shidda na yammh suka ijiyeta da nikin nikin kayan makulashe da suka shiga shagalinku store......shi kuma ya Wuce Abuja..,










_manage dis...Ina busy ne wlh,love u janaf fans#One love#_








*Comment*
*Vote*
*Share*











*Janaf*💖
*INTELLIGENT WRITERS ASSO*📝

```{onward together}´´´

*NAZIR*
_*(The journalist)*_

*Based on luv and Romantic story*

 
*Na*   

*JANAF CE*✍

*SADAUKARWA GA SAHIBA HAFSART HAFNAN*


_*D whole page is dash for u...AISHA ALTO..Writer of...SANA"ACE...Tanque sis 4r luv support and care...and tanque for been their For me Sisi....Can"t love u less dear*_




NOT EDITED⚒

43/44


     """Koda Nusiba tadawo ba wanda yamata mgaan dadewarta itama kuma bata ma kowa ba,Dada ce ke zolayanta dacewa mijin nan nata baturene ko ba indiye Nusiba na dariya tace "Kodai kina ciki ne dada sai kidaura damarar zaman kishi dani"Dada na  dariya tace"Ah akai kasuwa...Sai da Baba yadawo ne yaji labarin zuwan mijin Nusiba yayi takaichin Rashin ganin surikinsa ammh yasani inda rabo zasu hadu...

•°•°•°••°•°•°•°

  Komawarsu inna zainaba gida bana ce ga hakikanin me zuciyarsu ke kullawa ba ammh har zuwa yanzu basuyi wani yunkuri ba domin bayan jinyan jikinsu dasukayi ko kofar gida basu leka ba Dr Hisham ne ke zuwa kuma shima..Bai kirata ba itama bata nemeshi ba,abunda bata sani ba shine suna hannun hukuma Dr Hisham yazo megadi yamai bayani..Tunda yji haka yakama kansa saboda bayaso bala"in dasuka jawo ya shafesa saboda shikanshi yana tarin da laifuffuka.

  Jidda jikinta yayi mata sanyi sosai domin tagane Rayuwa dan adam bai komai bane..Itako inna zainaba ko ajikinta domin ta dukiyatake Jidda bata da sani taga Inna zainaba na jawo zawarawanta har falo suna zance data mata mgana sai tace Aure zatayi jidda tadade tana kallonta kwallah fal idanunta,Tace"Mommy..Aure kuma"Inna zainaba tace"Kwarai ko nawuce Aure ne"Girgiza kai jidda tayi kan tace"Baki wuce ba Mommy..But inkikayi Aure ni dawa zan zauna"Harara Inna zainaba ta zabgamata kan tace"Ohon miki,nidai saboda ke bazan fasa raya sunnar ma"aiki ba"Daga haka ta fesa turare ta rataya gyade tafice dama kwalliya tasameta tanayi...Nan jidda ta sulale tana kukan bakinciki Da Nadama mara amfani.


  Alhaji Basiru shine ke zuwa gun Inna zainaba amtsayin wanda zai aureta,Alhaji basira mugum mayaudarine Tunda yaji labarin irin dukiyar da inna zainaba ta mallaka ita da yayanta ya lashi takobin sai ya karbe komai dake hannunta shiyasa yazomata shima a mtsayin dan kasuwa wanda ke da shgo da motoci daga kwatano zuwa nan kano...Nan da nan Inna zainaba ta yarda shi da kusan Fitan rabo..To yana nan yana hada yadda zai yasheta yayi gaba domin matansa hudu kuma babu wacce zai saka balle har ya aureta.



Wannan kenan.



Nusiba ta cigaba da renon cikin adakn mahaifiyarta,cikinta na wata na biyar tafara zuwa awo nan asibitin ABU Dake Tudun wadan zaria Tunda Tariga ta yanke hukunci anan zata haihu ko zata koma kano...Nazir yasao yayi gaddama Ammi ta dakatar dashi akan ya rabu da ita sai ta haihu ta dawo,..Nazir yace ma Ammi"Haba Ammi gabadaya renon cikin achan zatayi shikenan"Yafada rai babu dadi Ammi ko kallonsa Ammi batai ba tace"Har haifansa ma achan zatayi bama Renon cikn ba,to dole yanaji yana gani ya zuramata ido itama ta zama alallaba.Sai da in Abunshi ya tsungolusa yazo zarian yadauketa suje hotel ysamu natsuwa kana yadawo da ita ko Kano yanzu Abbu sundai ganinsa.





   Cikinta Nada wata Shidda Zahran Bash ta haihu da Namiji..Wanda Nazir da kanshi yazo yadauketa suka zo Abuja ya yadata gidan Bash wanda basu taba tsammanin zai kawota ba duba da batajin dadi..Ramlart ma matar mg ta iso harta shi mg yazo gidado ma yazo wanda bikinsa yakusa Taruwa sukayi suka dinga chakar Nazir wanda Nusiba ke karemai...Nazir dariya kawai yake yana fadin"Yauwa yar aljannah...Cimun uban yan iska da kyau"Dariya suka sheke dashi gabadaya suma su zahran na karema mazajensu Da Nazir yaga zasu takurasu sai ya dauki Nusiba chak ya shige dakin da"a ka sauke su..Yana musu gwalo suko suka bishi ihu...Ranar Suna yaro yaci sunan NAZIR BASHIR....Tabbas Abun ya farantama Nazir rai..Kudi tsaba dubu dari biyu ya mallakama yaron bayan ya mallakama bash sabuwar mota prado mai tsada da yarari itako uwar jego kaya tasha kamar za"a bude shago suma su mg ba"a barsu abaya ba sunyi rawan gani ba shakka anyi komai cikin kudi da wata..Taro ya tashi lafiya baki sunkoma gidajensu lafiya.

  Nusiba sai da Nazir ya riketa ta kara kwanaki kana yasaka ilu ya maidota gida,duk yanzu Nusiba ta rage zama babu wanka takanyi ko da ba kullum ba,kuma rage son jikinta sai sai jarabar kwadayi kamar mayyah wai abinci yanzu tadawo ci arobar almajirai datasaka kuka sai da Dada da kanta da amshi roban wani almajiri tabashi kudi ya siya wata aka zubama Nusiba Wainar fulawanta aciki shikenan ita tasamu kwano in ba aciki ba..To bazata taba cin abinci ako"ina ba.








   *BAYAN WATA BIYU*

  Cikin Nasiba na wata na takwas labarin Rasuwar Saude da uwarta lami ya iskesu sun rasu sakamakon hadarin mota suna hanyar dawowa daga chadi..Gun neman asiri sai an farraka inna da Fatsima da yarta sunkasa yarda duk zakaran da Allah ya nufa da chara sai yayi...Kuma hassada gamai rabo taki ce..Sunyi yawo gidan bokaye sai amshe musu kudi ake ba nasara shine suka ji lbrin wanna bokan Sukatafi sun amaso mganin suna hanyan dawowa Daf tabi takansu ta taka babu wanda ya rayu a motar...

  Hakika inna Fatsima taji mutuwar saude duk da irin zaman dasukayi ammh bata taba kullanta ba...Ta yafemata har Abada Inna fatsima da Nusiba da Dada suka shirya suka tafi gidan gaisuwan...Wayyo Abun tsausayi nan Nusiba taga yadda yan"uwanta suka koma sun mauje sun lalace kamar tsofaffi ko wa"inda suka shekara suna daka...Sai da tayi musiu kwallah suma kunya tahanasu ma mata mgana to yau ga yadda rayuwa Ta nuna musu duk wanda ya rike Allah bazai tabe ba yau ga inna fatsima da yarta...Su kuma ga yadda Rayuwarsu takoma babu saude ba lami..Sukuma ga yadda rayuwa takoma dasu don dukkansu ba wacce tayi sa"ar mijin aure.

  Har akayi bakwai Nusiba na zuwa kullum sai taje musu da abinci itace take shigema yan"uwanta ganin suna baya da ita...ammh ita tana kokarin Nuna musu komai ya wuce domin kaf duniya bata da wasu yan"uwan da suka wucesa haka suka durkusa suna rokonta gafara suna kuka,rumgume su tayi itama tana kuka domin bata taba samun kyakyawan alaka da yan"uwanta ba tunda tazo duniya.

  Ita taja su suka je gida suka nemi gafaran baba da Dada uwa uba inna Fatsima wanda Ta rumgume tana share musu hawaye tace"Har Abada ni mahaifiyarku  ce..Ta nuna Nusiba tace ita kuma yar uwanku ce baku da kamarta"Haka dai Baba ya tarasu yaita musu Nasiha banda kuka ba"a Abunda sukeyi suna mai Nadama da Da danasani mara amfani.









_*Rayuwa kenan...Wlh mu kama Allah domin shine maganin kowani damuwa..Kunga karshen Saude da yayanta duk hassandansu ga inna Fatsima da yarta gashi ta kare Saude tabar duniya batare data Tuban ma Allah ba...Sukuma su Zubaida sunyi Nadama lokacin da komai ya tsaya musu,yanzu basu da wacce Tafi NUSIBA..."*_



_Darasin dake ciki yafara fita daga wannan page har karshe...Ngd sosai onelove Janaf fans_













*Comment*
*Share*
*Vote*






*Janafi*✍
*INTELLIGENT WRITERS ASSO*📝

```{onward together}´´´

*NAZIR*
_*(The journalist)*_

*Based on luv and Romantic story*

 
*Na*   

*JANAF CE*✍

*SADAUKARWA GA SAHIBA HAFSART HAFNAN*







_*I Dedicated dis page to u MAMAN WEEDAD..Writer of ALJAZEERA...Kina kashemu da salonki fa...Thank yhu so much sis...Onelove*_🤘




NOT EDITED⚒




44/45

   """Wannan karon Da Nazir yazo Baba ya bude wuta kan cewa Nusiba tashirya tabi mijinta takoma dakinta baiga amfanin zamanta ba,jin haka yasa Nusiba fashewa da kuka tanayi harda shessheka kan ita bazata ba agida takeson ta haihuwa ganin haka yasa Nazir saurin cewa baba"A"a Baba don Allah kubarta tahaihu anan Da Amincewata Baba"Yafada yana dukar dakai kamar salihi

  Baba yace"Dole zata koma saboda banga dalilin dawowarta nan ba...Tawuce ta bika kutafi tare"Ganin Baba ya dage yasa Nazir ya marairaice yana rokon Baba kan ya bar Nusiba harta haihu...Tsoronsa Allah kada Nusiba tafadi dalinlin dawowarta gida..Dakyar Baba ya Amince Nusiba ta zauna har Tahaihun.



  Sannu Sannu kwana nesa gashi har Cikin Nusiba ya shiga watan haihuwansa harma yana neman gotawa haihuwa shuru,tun an kammallah soyayyah kayan baby da mamansu domin akwatu seti hudu Ammi ta kawo biyu na baby biyu na maman baby bayan kaf abunda za"a bukata kama daga baho botikai da sauransa kan su sabulai kuwa sai wanda ya gani kayan arziki kam masha Allah..Lokacin da su zubaida suka gani kwallah ta taru a idanunsu yau ina inna Saude Tazo taga yarda Nusiba Allah ya azurtata lalle komai kake kokarin zama arayuwa to ka tsarkake zuciyarka kuma ka rike Allah.



  Wata Ranar alhamis Tun safe Nusiba tatashi da Nakuda tun Tana daurewa harta dai Inna tagane taje tafadama Dada..Ba bata lokaci Baba ya samo musu mota suka Nufi asibiti..Suna zuwa inda take awo karamar ABU suka turasu CHIKA..suna zuwa aka amsheta suka shiga da ita ammh kuma sai me kadai Nakuda gadangadan ammh haihu shuru Tun Nusiba na iya Nishi harta kasa karfinta yakare.

  Inna Dake Gida ita tadauki wayar Nusiba da"ake ta kira Ammi ce take fadamata halin da"ake ciki Ammi cikn tashn hankali ta aikama Anty Abbu kawai takira awaya tafadamai shima cikin nuna damuwa yai mata fatan sauka lafiya...Ammi da Anty da Aisha suka shirya agurguje direba ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login