Showing 6001 words to 9000 words out of 87333 words
Chapter 3 - Nazir Bok Complete Hausa Novels by Janafty.txt
Nazir yayi ya kalla,yadamu ammh kuma yasan ko giyan wake yasa bazai je ba yanzu.
Yana shiga dakin yafada kan makeken bed din yana ajiyar zuciya,runtse idonsa yayi yana so ya tabbatar da ba mafarki yake ba,all dis ya faru dunkule hannunsa yayi ya naushi dayan hannun nasa yana fadi da karfi"No..!domin tuna sanda Nusiba ta sharara masa mari,mikewa yayi yana rangaji ya isa bakin durowan gadon yajawo sai ga kwalayen sigari duka ya kwaso ya zube su saman bed din,shima yayi zaman dirshan kawai ya hau busawa,data kare sai ya yar ya kunnah wata,ahaka har ya karar da kwali ukun dake gabansa,ammh tukukin dake ransa bai gushe ba,kawai sai yayi fatali da sauran,ya mike ya hau cire kayansa yana watsawa aduk inda yaga dama,boxer din sa kawai ya rage ajikinsa sai takalmin dake kafarsa ya bude toilet ya fada cikin wani yanayi.
Shiko bello bayan fitowarsa daga gida yayi ta tambayan mutane Nusiba ammh sai suce basu santa ba,Sanin cewa ita Nusiba babu wanda yasanta cos bama fita take ba balle,tun wajen karfe 11 na safe yake Abu daya,gashi yana neman cin ma karfe biyu 2 bawani lbri mai dadi har yafara sarewa Allah ya hadasa da wani mai faci agefen hanya kamar bazai tambaya sa ba, sai ya tsaya, bayan sungaisa sai bello yace"Don Allah baba tambaya nake'yace"Allah yasa na sani yaro"bello yace"wata yarinya nake neman bayani akanta,wata Nusiba saddiq bunza,tana aiki da freedom radio"Mai faci ya washe baki yace"Allah sarki bawan Allah,ince ko neman aurenta kake"sai bello yace"A"a bani bane nima an sani ne"mai faci yace"Niko na san Nusiba domin abokina jibo,yar kanwarsa ne,shike rikonta"ai bellon najin haka sai ya nemin gefe ya zauna yana fadin"Kasan komai game da ita kenan"Shiko mai faci yazata wani ne keson Nusiba da Auren shine aka turosa bincike kawai sai ya saki baki yakwashe kaf lbrin Nusiba tundaga yarinta har zuwa yau,da duk ukubar data fuskanta agidan mahaifinta,ya gangaro zuwa daukota da Jibo yayi yasata mkranta har zuwa yau,ya kara dacewa"Ai jibo ba abunda yake boyemin domin tun fara aikinsa a masinja muke tare,Aminina saosai,gama gidansa chan,yafada yana nuna gidan su Nusiban,Ai ma cikin jami"ar bayero yake masinjan a office din Mutum nin kirkir nan,Alhaji Adam galadanchi" bello yagyada kai cike da gamsuwa ya mike yana mikama mai dubu daya yace"gashi baba,nagode'girgiza kai yayi yace"A"a yaro bazan amsa ba,ai Nusiba kamar ya take aguri na,karka damu kaji"yayi yayi dashi yaki amsa sai ya hakura yamai godiya ya wuce.
To Haka bello ya kira manaja dake chan yana dakon jira ya fesama sa komai ,manaja yayi mamaki da"a yaji lbrin marikinta masinjane a office din mahaifin Nazir,tabdijam akwai chakwakiya kenen.
Shikuwa Nazir yadade a toilet kan ya fito daure da tawul gaban dressing mirro ya isa kallon fuskarsa yayi yaga yadda tayi ja idanunsa sun kumbura cikin takaichi yake shafa inda ya maru yana jin wani bakin ciki da takaichi yana tsaye ne ammh hoton sadda take shararamasa mari ke dawomai bai san sadda yasaka hannu ya daki madubin ba ya tarwatse.
Ammi dake jera abinci kan dinnig ita da Mero mai aikinta tayi saurin kallon sama kafin ta girgiza kai kawai,mero tace ta karisa kwaso abincin ita kuma ta wuce daki,wayarta ta dauka tana laluban Abbu ammh kuma tana ta ringin ba'a dauka ba,sai ta hakura ta ijiye wayar tana kyafci tace"Nasan kona je bazai saurare ni ba,ammh in ubansane ai ya jisa"Tafada cikin muryan bacin rai.
Shikuwa Nazir haka duk ya yanke kansa da gilas jini na zuba,ammh ko takan haka bai ba,saima komawa dayayi ya zauna kan gado ya zurama agogo ido yana ji kowani dakiki kamar da ransa ake Tafiya,ayanzu akallah anci awannin takwas saura uku kachal,handline dake dakin yajawo ya latsa yasa akunne yace"ka kawomin duka wayoyina"daga haka ya kashe wayar,ilu ya kwaso duka wayoyin ya nufo falon,Babu kowa sai mero suka gaisa cikin mutumci kafin ya haura sama,knoking yayi kafin Nazir yaxo ya bude masa.
Hannunsa na digan jini ya mika hannu ya amshi wayoyin Ilu ya bi hannu da kallo cikin rudewa yace"Oga...Shiiii.."yace yana wani lumshe ido,maida kofar kawai yayi ya kulle ya bar ilu tsaye,cikin sanyin jiki ilu ya sauko yanajin wani iri aransa,yasan halin ogansa wlh bai iya
fushi ba balle anmai Abunda ba"a taba mai ba atarihin rayuwarsa.
Karfe shidda dai dai ta buga daidai da awannin da Nazir ya dibama manaja waya tana gabaan Nazir kiran manaja ya shigo cikin gaggawa yadaga kiran yana fadin"Hop komai yazama ready"manaja yagyada kai kaman yana ganinsa ya shiga ratta famai kaf Abunda Bello ya fadamai game da Nusiba,yana kokarin yagayamai kawun nata ma a office din mahaifinsa yake aiki,ammh ina tuni Nazir ya katse waya
Cikin kunan rai yafurta"gud news...Waya ya shiga dannawa kawai ji nayi yana kwantance anguwansu Nusiba yana bada umarnin anemi mai gidan duk inda yake agayamai gobe da safe yaje ya sallami mutanen dake gidan sauran aikin yasan dai komai" yana katse wayar ya yi wurgi da ita saman gadon yana cijen lebensa na kasa ga hannunsa na ta zuban jini,kawai sai ya bude kofa ya fice daga dakin.
*Janaf*✍
[4/11, 2:11 PM] 0mmer Farouk: *🧑🏻NAZIR🧑🏻*
_*(The journalist)*_
*(Based on luv and Romantic story)*
*Na*
*Janaf ce*✍
*Vote me on WATTPAD:Janafnancy*
© _*INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION*_🖊
*```DIDECATED TO SAHIBA HAFSART HAFNAN```
*```ASSALAMU ALAIKUM,JAMA"A ADUK INDA KUKE WATA YAR SHAWARA CE KO INCE TUNATARWA NAKE TAFE DA ITA,DON ALLAH GOBE ASABAR 16 GA WATAN FEBARERU ZA "AYI ZABEN SHUGABAN KASA DANA YAN MAJALISU,KADA MU KWANTA AGIDA MUCE BABA BUHARI NADA JAMA"A MU FITO MU BAYYANA KANMU MU DANGWALAMA BABA BUHARI KURU"UNMU DOMIN BASHI DAMAN ZARCEWA,MU FITO!MU FITO!MU FITO MU ZABI YANCI MU ZABI,ZAMAN LPY DA TSARO,WATO BABA BUHARI```
*I stand for baba buhari*
~Baba buhari dodar, insha Allahu 4 + 4 sai kayi~
_Kaduna state kuma sai mai Rusau insha Allahu_
6/7
yana fitowa ya gangaro kasa musty kawai ya tarar a falon yana zaune kan dining yana cin Abinci, Kallo daya yamai kawai ya kauda kai musty daya bisa da kallo,kawai sai yaga jini yana zuba yana dubawa sai yaga Hannun Nazir ne,cikin tashin hankaki ya ijiye spoon din Hannunsa yan Fadin,
"Innalillahi,broda Kana bleeding fa a hannunka"fadar haka yayi dai dai shigowar Dr Adam galadanchi wanda direbansa kebi abaya rike da yar jakar briafcase dinsa cikin alaman tabuwa yake kallon Nazir kan yace yana duban musty,
"Shikuma wannan mai yasameshi yaketa zubar jini a hannu"musty yace"Wlh Abbu banda masaniya nima ganinsa nayi ahaka"Ammi ce taji maganganunsu ta fito ganin Abbu sai ta hau mai Sannu da zuwa suna hada ido,da Nazir ta hararesa tana fadin"Ai ka kyauta"tafada tana amsa briefcase ta wuce daki dashi Nazir kuwa shuru kawai yayi baice komai ba basu damu ba cos daman halinsa kenan,jiri ne ya fara dibarsa domin gilas din duk ya yankesa yana ta zubar jini,musty ne ya lura da sauri yazo ya rikesa suka karisa kan kujera ya kwantar dashi firstAid box ya dauko yazo yahau masa dressing din wajen.
Abbun kuwa sai da yayi wanka ya sake fitowa falo Har yanzu Nazir din na kwance afalon ammh wannan karon hannunsa nade da bandeji kallonsa Ammi tayi tace"Oh ni fatima wai Nazir wata irin rayuwace kakeso ka maida kanka ne? Tafada tana bin hannunsa da kallo muskutawa yayi yana fadi ahakalin"Ammi bafa da gangan bane, tsautsayi ne"Harara takara sakarmai,zatayi mgana Abbu yawuce yana fadin"To wai meye naki? ina jikinsane? kowa rai yaima dadi baran mai shine fatima"Yafada yana zama kan dinning
Gyada kai tayi ta isa garesa tana Fadin"Hakane kam,Allah dai ya shirya"Abbu ya amsa da Amin yana bin dan nasa da kallo ta gefe,shikadai kawai yagirgiza kai.
wayan da Nazir yayi to bada kowa yayi ba face da ilu,ilu direbansa ne ammh kuma yana taka matsayi mai girma domin wasu al"amuran Nazir din duk shi ke gabatar dasu,akwai dai Amana mai girma atsakaninsu.
Ilu bai sha wahalan gane ma mallakin gidan dasuke Nusiba suke ci ba, domin yawancin gidajen anguwan,nashine yake bada haya,Alhaji ido Anaira koda ilu yajemai dubu dari biyu ya diremai kan yafadi bukatan ogansa,Alhaji ido Naira babu gardama ya amshe kudi yace"Ko ayanzu akeso zai iya koransu meye aciki,Ilu yace"A"a basai yayi gaggawa ba yabari da safe bukata dai kawai ya koresu agidan.
Nusiba kuwa bata tashi ba sai bayan azahar,lokacin har Anty ta kammallah girki,ta zubomata taci takara shan mgani takoma ta kwanta,bata tashi ba sai bayan,la"asar tatashi tayi sallah,taji dan dama dama shiyasa tafito falo sukaita hira da Anty har mangariba ta kawo,suka mike sukayi sallah,saiga kawu yadawo koda Nusiba tamai Sannu dadawowa bata nuna mai wani Abu yafaru ba,Anty ce ma take fadamai tadawo gida da ciwon kai,sannu yamata yace ,zuwa gobe inbata ji dama ba tazo suje asibiti kan ya fita.
****************
Safiyar Talata
Tun safe Nusiba tatashi tayi aikace,aikacenta wanka tashiga bayan ta fito tana zaune adaki tana shafamai,taji kamar hayaniya atsakar gidansu sai ta dan saurara ammh sai taji kamar muryan kawu yana mgana,kafin ta ankara taji an fado falon ana fadin.
"Ku fitar da komai na gidan ku watsa musu waje,ni da gidana ace don zance atashi sai na wani bada notice"
Tsabar rudewa Nusiba tarude wani tsohon hijabinta data wanka dashi ra zura ta fito da sauri,abunda tagani ne yakara tsoratata wasu matasane gardawa wurin subiyar saijiddan kayansu suke suna fita dashi,ga Alhaji ido Anaira na tsaye yana ta masifa Anty na gefe tana kuka,shikuwa kawu rokon Alhaji yake yadan bashi ko kwana dayane ammh kememe yaki.
Nusiba taji jikinta yafara rawa tama kasa daga kafafunta dakyar tayi karfin Halin karasawa kusa da kawu tana fadi cikin rawan,
"Kawu...Ka...Kawu,mekefaruwa ne,naga Ana fitar mana da kaya? kawu ya jiyo yana kallonta idanunsa yayi ja ya riko hannunta yana fadin"Bansani ba!bansani ba Nusiba kawai nema haka naga sunzo wai mu barmasa gidansa yanzu nan"Nusiba taji hawaye sun wankemata ido takalli Alhaji ido Anaira tace.
"Haba bawan Allah,haka ake Rayuwa don ka mallaki abu,sai akace kayima wanda suke karkashinka wulakanci?tafada tana kallonsa idanunta na tafasa,Alhaji ido Anaira ya kalleta yace"Ke yarinya ki iya bakinki,kinga nima umarni aka bani na sallame ku,mganan daga samane,tun wuri in kuna so ku tsira da mutumci wlh kufice daga gidan nan"
kawu Da Nusiba suka kalli juna cikin firgici kawu yace"Ni...Waye yasa akoreni ni jibo? bana shiga harkan kowa fa"yafada muryansa tayi Rauni,Alhaji ido Anaira yace"oho!nima nace ma aikowa akayi, bansa kowaye ba"Nusiba da tunda Alhaji ido Anaira ya furta haka taji gwiwanta yasaki,kardai ace gayen nan ne na jiya? to waye? shine ma,don babu wanda suka taba samun sabani in bashi ba,ta tuna kalaman manaja dana Rahma alokaci daya,ai batasan sadda ta durkushe tana kuka mai cin rai ba.
Kawu ya dafata yana Fadin"Tashi,tashi daina kuka,ku hada kayan sawan mu,dake da suwaiba bari naje gun habu naji yadda za"ayi"daga haka ya fice,Anty ce tazo tatada ita suka fice,sukuwa matasan nan cikin lokaci suka gama yi musu waje da kaya kaf,suka jibgemusu awaje Alhaji ya mika musu katon kwado suka garkame gida,
mutane kuwa duk da sassafe ne sunfara cincirondo suna kallo Nusiba durkushe take kawai tana kuka tana tsausayama kawunta,domin duk itace silan komai,nan da nan tsanar Nazir ya darsu aranta tanaji inda zata ganshi babu abunda zai hana in an bata wuka bata kasheshi ba,Anty ce keta hadamusu kayan sawansu wuri daya tanayi tana hawaye.
Shikuwa kawu jibo,gun abokinsa yaje habu mai faci yake fadamai,habu yabiyosa cikin tashin hankali dadamuwa koda yazo yaga yadda akayomusu fatali da kaya sai da yayi musu kwallah,Kawu jibo yace"Su Nusiba su hada kayansu wuri daya suzo zai kaisu tasha yasasu amotar zarai,shi zai tsaya yayi buga buganshi ya gani ko zai saman musu gun dazasu zauna,kayan kuma aka saka yara suka dauka suka na kaiwa gidan Habu mai faci,kowa ya janjanta cikin tsautsaya domin daman Shi talaka baida tacewa tunda bai Dashi.
Duk wannan Abunda ke Faruwa a idon ilu direba,domin Nazir ya umarcesa ya tabbarta da sunbar gida ya kuma ya bisu ko"ina suka je ya tabbatar da basu samu matsugunni agarin kano ba,yana cikin wata mota baka camry wanda tasha tintec babu mai ganinsu sabida Tsausayi Sai Da Yayi musu kwallah,yaji dama bashi oga yabawa wannan aikin ba,kawai saboda zalunci karaba mutane da muhallinsu don kawai ka tona musu asiri,wlh yayi Tir da hallayan ogansa Na rashin yafiya.
yana cikin mota suka zo suka wucesa zuwa bakin titi,Nusiba kuwa Fuskar tasha kuka,duk ta kode Anty ma haka,kawu ne kadai ke karfin hali,shima ilu sai da yaga sun isa bakin titi kana yabiyosu ya paka gefe yana kallonsu,kokarin tsaida musu Abun hawa yakeyi Saiga wata bakar jeef tazo ta wucesu harta gota su tadawo da baya ta tsaya daidai gurinsu.
Direban ne ya fito da sauri ya budema na baya ya fito cikin Sauri yana Fadin"Kamar mallam jibo nake gani"?kawu yayi Saurin rakwafawa yana Fadin"Brka da safiya yallabai,nine wlh"Ya bashi Amsa
Yace"Lpy naganku anan cikin wani yanayi,ga wasu na kuka?kawu jibo yace"Ranka yadade wlh me gidan danake ciki ne,kawai yazo yace yanzu yanzu yakeson mu barmai gida,to shine yasa aka fitoma na da kayan ya rufe gidan"Girgiza kai yayi yace"Ashh...Abu baiyi dadi ba mutane basu da ragowa sam,yanzu ina kuka nufa? Kawu yace"Zaria zan tura su iyalan nawa,nikuma in dan yi buga bugana koza"a samu inda zamu raba"yafada da girmamawa,Jim yayi kafin yace"baza"ayi haka ba mallam jibo,ku shigo mota muje gun zama bazai garara ba"yafada yana bude gidan gaba yashiga,mamaki yahana kawu mgana nan da nan yaji kwallah tatahomai yayi saurin, sharewa yace su Nusiba su shiga sallama sukayi da habu mai faci kan shima ya bisu ya shiga baya inda su Anty suke.
Direbane yace"yallabai ina muka Nufa? mu koma gida"ya basa amsa direba yagyada kai Suka wuce.
Ilu dake zaune ya daskare kawai in ba idonsa ke gizo ba kamar VC ADAM GALADANCHI NE ya dauki Su Nusiba fa,tabdijam akwai Daru kenan,bai gama mamaki ba wayan Nazir ya katsesa yana dauka ya katsesa da cewa"Komai yayi ko? yafada cikin muryan yanga,ilu ya gyada kai yace"eh yallabai gani ma zan dawo domin na gansu sun Nufi tasha sun hau motar zaria"yasamu kansa da sharara masa karya.
Nazir dake kwance bayan wata mota kirar camry yace"Gud job...Kana ina ne? ilu yace"na fito daga zoom road din"Nazir yace"cikin kasaita"ka tsaya nan,mu zo,Abuja zamu koma"daganan ya datse kiran yana wani killer smile yace afili"yes...!
*Commet and share*
*Janaf*✍
[4/11, 2:11 PM] 0mmer Farouk: *🧑🏻NAZIR🧑🏻*
_*(The journalist)*_
*(Based on luv and Romantic story)*
*Na*
*Janaf ce*✍
*Vote me on WATTPAD:Janafnancy*
© _*INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION*_🖊
*```DIDECATED TO SAHIBA HAFSART HAFNAN```
_*Ina kike my swt Anty,kanwar uwa abokiyar wasa,wannan kyautar page gareki gabadaya keda ahalinki*_
*```Anty salamatu muhd Ba"are,dake da megidan naki,Unku fodio Sunusi Gumbi,da ya"yan naku,Aliyu Fodio S G,Umar Fodio SG,Muhammed Gidado Fodio SG Sai Fatima Fodio SG(Hibba)```
```Miss u so much```😰
7/8
"""Tunda suka shigo anguwar Nusiba tabar kuka takoma ba idonta Abinci,domin tundaga farkon anguwa tafahimci anguwace tamasu dashi,kokuma kososhi a gwannati.
Bata gama mamaki ba sai da taga an zuba hon awani tamgamemen gida wanda tsaruwanshi,kamar akasar turai,ai Nusiba bata kara Raina kanta ba sai da suka sulala parking space din,haka take bin ko"ina da kallo cikin nuna zallan kauyanci,dole ta nuna don duk a iya tsawon Rayuwarta bata taba ganin gidan daya tafi da ita ba irin wannan.
ashe kallonta na tafe domin,sai da sauko daga motar tana karema,Harabar gidan kallo,tabbas ba shakka Naira na inda take ba abunda yafi daukan,hankalinta irin tsararrun motocin dake pake a harabar gidan masu kyau da tsari birjit kamar ma bamasu hawa,tana chan gurin kalle kallenta har Su kawu sukayi gaba bata fargaba sai da taji kawu na mata mgana.
VC Adam galadanchi ne akan gaba yayi sallama acikin falon,musty ne ke tsaye cikin shirinsa na zuwa asibiti harda rigar likitocinsa ,ya kalli Abban nasa cikin mamaki zai yi mgana kenan,sai yaga Kawu jibo yashigo da Anty bayansa Sai Nusiba tana ta zuba kauyanci baki sake.
Abbu yace yana kallon musty"Kai mustapha kiran min Amminku"Yafada yana fadin"Bismilan ku,ku zauna don Allah"Dukkansu akasa suka zauna suna bin tsararran falon da kallo ita kuwa Nusiba wanda aka kira da mustapha dake bi da kallo,kamar tasan fuskan nan awani guri bata dawo daga tunaninta ba Ammi tasawo kai Falon tana Fadin"Abbu lafiya kadawo kuma? Alhalin yanzu ka fita"
Tafada tana karisowa falo karaf idonta akan Nusiba wacce ke kallon inda taji mganan suna hala ido,suka sakarma juna mirmishi lokaci daya.
Abbu yace yana gyara zama"Kedai bari Fatima ina tafe ne da baki"tace tana zama gefensa"Allah Sarki sannunku da zuwa"Kawu ya amsa yana gaisheta,ta amsa da sakin fuska idanunta nakan Nusiba,Anty tadago suka gaisa,kana Nusiba ta gaisheta,mikamata hannu tana fadin"Zo nan yata,Abbu ina kasamomana yar budurwa mai kyau haka"Tafada tana dariya.
Nusiba tatashi a kunyace ta isa ga Ammi tana dukar dakai,Zata zauna akasa Ammi tayi saurin zaunar da ita kusa da ita,tana fadin"A"a zauna kusa dani,yata kinsan ni uwar maza ce,to duk inda naga budurwan mace sha"awa take bani"
Abbu yayi dariya yana fadin"To gashi Allah ya baki ai"Yafada yana yawaita dariyarsa,kafin yafara koramata jawabin komai tagumi ta zabga tana fadin"kaji ko,wlh wasu mutanen sam basu da imani,ita Rayuwa babu lamani"Abbu yace"Ai haka wasu suke,babu komai ai mallam jibo mun dade muna aiki tare,yanzu shine nake tunanin Mustapha yakaisu gidana dake zoo road.
Ammi tayi saurin cewa"A"a Abbu don Allah kabarsu anan gidan don Allah"Tafada hartana dangwabe kai Dariya Abbu yayi,yana kallon mallam jibo yace"Kaji mallam jibo,shin zaku zauna damu? Zama na Amanar juna"
kawu yadago hawaye yacika idanunsa yace"Yallabai bamu dace da zama daku ba,dadai an barmu...."Meyasa zaka ce haka mallam jibo? baku son zama damu ne"Ammi ta katsesu tacigaba da cewa"Anzama daya fa muma,mutane ne kamar ku,don Allah ku zauna damu wlh ganin farko na muku kuka shiga Raina,don Allah"Tafada tana rikema Nusiba Hannu.
Kawu yayi saurin cewa"Mun yarda hajiya,wlh mun yarda kun wuce mtsayin komai agurin mu,muda zaku taimakamawa,mungode Allah ya saka da Alheri,Allah kara girma"yafada kwallah tana zubomai Abbu yace"Ashh..Mallam jibo meye kuma Abun kuka? don Allah bari.
Anty itama tana ta godiya Ammi tace"Babu komai wlh,ni wata alfarma ma nake nema? Anty tace cikin mamaki"Wata alfarma hajiya? Ammi tace tana dafa Nusiba"Diyarki zaki bani,nikuma na baki mustapha,gashi nan tsaye"tafada tana Nuna mustapha dake tsaye Hannunsa akirji,Anty tayi mirmishi tace"Ah!Babu komai na baki ita,nikuma na dauki dana Mustapha"Tafada tana kallonsa.
Mirmishi yayi yana Fadin"Ammi yan ubanci za"a Nuna min yau"Ammi tace"Eh din ga mamarka can,ni kaga yata nan"Tafada tana dago kan Nusiba data sunne kai tana mirmishi .
Musty yace"To shikenan Ammi,nima ai nayi Sabuwar uwa ko"Yafada yana kallonta wacce ta amsa tana mirmishi,Abbu dake tsaye dadi acika ransa ganin iyalansa cikin farinciki mikewa yayi yana