Showing 42001 words to 45000 words out of 87333 words
Chapter 15 - Nazir Bok Complete Hausa Novels by Janafty.txt
kike mgana"Anty tace"Na haihu mana ko tawuce Haihuwan ne"Saude tace"kutumar ubanchan wlh to cikin shege ne,yaushe ma mallam din yake kulaki balle har kiyi ciki"Tafada cikin fushi Dada tace'Nima shi nagani kada fa ta gurbatamin zuru"a dabara gurbi"Inna fatsima dawani abu ya tokaremata kirji tadago kai tana kallon Dada tace cikin muryan marasa lafiya"Allah yamin tsari da aikata Abunda kuke zargina akai,tun ina da kurciyana ban lalace ba sai da girma yakamani"Tafada tana zubda kwallah.
"""Nusiba ta mike tana ganin ikon Allah,kawai sai Dada tasa baki tana kwalama Baba,kira wanda ke waje,duk abu da yafaru akunnensa cikin jin Nauyi yafado dakin Dada tace"maza warwaremana wannan lamari so nake katabbatarmin da cikin dake jikin Fatsima bana ka bane"tafada tana tsareshi da ido cikin jin Nauyi yace"Haba Dada meyasa kuke haka,wannan fa ba girmanki bane"ba Dada kadai ba hatta Inna fatsima dasu Nusiba sunyi mamaki da furucin baba.
"""Dada tanuna kanta tace"Abbakar ni kake fadama,haka"tafada tana kallonsa baice komai yasakai zai fice Dada tayi tsalle ta rikomai riga tana cewa" wlh Sai kafadamin uban wannan cikin don Ubanka"Baba yakalli Dada kunya kamar ya nutse yace cikin kunar rai"Dada cikin na ne,shikenan ko? yafada yana mai saurin kwace kansa yafice,salati Dada Imna saude suka saka lokaci daya Anty tabisu dawata dariya kan tace"Kunada aiki Ciki da ubanshi ku taru kuna sallallami"
Inna Saude tadora hannu aka tana Fadin"Na shiga ni saude boka fa yace saboda bakin jinin ta ko rabarta bazai karayi ba,ammh ace gashi har yayi mata ciki"Topha sai kallo yakoma sama Anty da Nusiba Sukabi Saude da kallo Dada kuwa mutuwar tsaye tayi kan tace"Wani bokan kike mgana saude? sai asannan Saude tadawo hayyacinta tagane tabargazan datayi sai ta hau kame kame tana cewa"Boka kuma Dada,Biba nace bakiji bane,wata mgana ce dabam"tana Fadar haka tayi wuf tafice tana raba ido
Anty tayi ajiyar zuciya tace"Komai kasa Allah agaba sai kaga daidai"Tafada kai tsaye,Nusiba tayi ajiyar zuciya tace"Dama Anty akwai asiri har yanzu"Anty tace"kwarai makuwa Nusiba ammh ga dukkan alamu alkadarinsu yafara karyewa"Dada dake tsaye tafice jikinta duk yayi sanyi,itako inna fatsima kanta na kasa ammh azuciyarta godema Allah take ya dafara nuna ma saude karshenta.
Da yammh Ammi takira Nusiba nan take fadamata sunkoma gida,har akabawa innan takara mata yajiki,Ammi tana yanke waya da Nusiba takira Nazir wanda ke zaune aharabar saman gidanshi kundai san ko"ina Nazir yake to upstair ne gurin zaman shi,yana zaune yana hutawa cikin wasu fararen kujeru kiran Ammi ya shigo wayarsa yadauka suka gaisa cikin girmamawa.
.Ammi tace"Nasan Nusiba bata kira ba ko"Tafada tana tambayarsa"gyada kai yayi tare dacewa"Eh...Lafiya Ammi"Tace"lafiya lau mahaifiyartace batajin dadi tun shekarajiya munachan nima yau nadawo,kakira wayarta sai kamata yajiki,kafin kadawo"Nazir yace"Ayyh.zan kira insha Allahu"daganan suka taba hira kafin suyi sallama.
Shuru yayi yana Tunani,shifa Ammi tatakuramai abunda ko nombar yarinya baidashi,toshi yama kira yace me"Sai wata zuciyar tace karkai haka Nazir itafa takula dakai lokacin dabaka da lafiya,kuma karka manta tana daraja iyayenka fiye dakomai nata,tuna haka yasa ya danna ma musty kira wanda ke zaune cikin office din sa yana duba patient kiran Nazir ya shigo yadauka cikin zumudi yace"broda Nazir brk da yammah"Nazir yace"lazy dr ya kake"Musty yabata rai kamar yana kallonsa yace"kai broda gama fa ninan ina fama da aiki"yafada harda tura baki"
Dariya Nazir yayi kan yace'ok...Dama no din yarinyarnan zakamin sending"Musty yace"wata yarinya kenan broda?Nazir yayi tsaki yace'kana Tambaya nane,wace kake biyemawa kuna isar mutane da surutu agidan Ammi"yafada yana wani bata rai kamar ansa sa dole musty yace yana dariya"Kai broda Anty Nusiban yace yarinya"Nazir yace"just send it to me nace ban bukatar wani zence kuma"Musty yadanne dariyansa yace"Bandashi sai dai bara na tambayi Ammi bazata Rasa ba"Barshi..."Nazir yafurta afusace yana katse kiran.
Dariya musty yayi mai isarsa kan ya turama Nazir nombar Nusiba wanda yasan yakunna shi,shikuwa Nazir yana katse kiran Musty yayi tsaki shikadai yana fadi afili"Ammi wlh kin bani aiki"sai da yakoma cikin falon ne ma yaji shigowar sako yana dubawa yaga nombar,tabe baki kawai yayi bai waiwayi nombar ba sai ma kokarin kunna talabijin dake falon yakeyi.
Nusiba takwabe ta share dakinsu tas tahada da tsakar gidan bayan tagama tazo tadaura musu girki,sai gabda mangariba ta gama wanka tashiga kafin tadauro alwala tazo tayi sallah bayan ta idar da sallan ne tazo tazauna sukaci abinci da Anty sunayi suna hira inna fatsima nagefe zaune lemo ne ahannunta tana sha,ishha"i aka kira yasa suka tashi sukayi,dama Nusiba jiya asibiti bata samu barci ba,shiyasa tana idarwa tasulale kan darduma barcin yafara fizganta taji wayan na tsuwa tajawo ta ko duba wanda ke kiran batayi ba tadauka takara akunni
Cikin muryan wanda yafara barci tace"Assalamu Alaikum"tafada cikin taushin murya Nazir dake kwance kan kujeran dake falonsa yana shan coffea yayi tsam saboda yadda muryan tadakesa rasa mezai ce yayi kawai sai yace"yamai jiki takaraji"yafada cikin dakewa,dan sauran barcin dake idon Nusiba yasaketa da sauri lokaci daya tamike zaune tana kara duba mai kiran,nombace basuna ammh ko amafarki taji wannan muryan tasan me ita,ganin tayi shuru yasa haushin kansa ya ishesa kawai sai yace"Allah yakara Afuwa"Kan tayi wani yunkuri kit yakashe kiran.
Sororo tayi da waya ahannunta tana mamaki wai yau ita Nazir Adam galadanchi yakira yana tambayan jikin Innanta,yau wata ranar sa"ace tabdijam duk da batasamu zarafin mgana ba ammh Abun yabata mamaki,kawai sai tasamu kanta da murmusawa,lokaci daya kuma ta adana nombar nashi cikin wayarta bayan ta rubuta YA NAZIR.
shiko abangaren Nazir yana datse kiran yayi jim yana Tunanin yadda muryan Nusiba tadakeshi lokaci daya kuma tana mai amsa kuwwa akunne cikin wani yanayi,lokaci daya jikinsa ya mutu har bai iya daga dan yatsansa tsikar jikinsa yana tashi yarrr,kara lafewa yayi kan kujera yana jin wani bakon alma"ari nata shiganshi wanda har barci barawo yasaceshi da Tunanin Nusiba
Abunda yabashi mamaki shine koda yatashi da asuba yana cikin Najasa domin mafarki yayi yana saduwa Da Nusiba,har yayi wanka tsarki yadauro alwala al"amarin yadafashi matuka shiba halinsa bane kwanciya yayi mafarkim yana saduwa dawata mace ba,sai dai kawai bukatuwa irinta da Namiji ammh jiya kam mafarkinshi yasha bambam dana koda yaushe.
Itama abangaren Nusiba babu wanda tafadamawa cewa Nazir yakira,itama gyara kwanciyarta tayi ammh ita mamakin Hakan baibar ranta,har garin Allah yawaye dayake tatashi da Haila,da asuba baba yashigo duba jikin Inna wanda kana kallonsa kasan a tsorace yake ko zama bai yi ba yafice Anty ta girgiza kai kawai aranta tace"insha Allahu saude karshenki yazo.
Da hantsi wajen sha daya na safe sai ga Rahma wanda ko Nusiban batasan da zuwanta ba tayi murna sosai harda ferfesun kayan ciki tayoma Inna tazomata dashi wanda inna taji dadi to balle Nusiba data rasa mezatace mata bata dade dazuwa ba sai ga Ammi ta iso itama,cikin murna Nusiba ta rumgume Ammi tana murna,itama taxo mata da ferfesun kan rago da sinasir da miyar ganye dayaji manshanu.
Rahma da Nusiba suka kule adaka suna hiransu cikin Hiran ne Rahma takalli Nusiba tace"zan baki shawara Nusiba duk da bakison kifadamin mtsalanki,ammh ni daukeki kamar yar"uwata ta jini"Nusiba tace"meye bani son fadamiki Rahma"Rahma ta gyara zama tace"Zaman dakikeyi agidan Aurenki"Nusiba takalli Rahma da mamaki zatayi mgana Rahma ta dakatar da ita da hannu tana cewa"Basai kinmim kaddama ba ammh na fahimci irin zaman dakikeyi dake da mijinki,karfa kimanta namiji kamar jariri yake yadda kika tafiyar dashi haka zai zauna miki"
Nusiba tayi tagumi tace"Kinfi kowa sanin yadda Aurenmu yakansace Rahma kuma dakike wannan mganar bakison waye Nazir din bane"Harara Rahma ta zabgamata kan tace"Nasan waye shi ma,ai duk wulakancin da Namiji da rawan kanshi mace ke gyaramai zama,to kibudi kunnenki da kyau kiji matukar baki mike tsaye ba baza ki taba samun kan Nazir balle ki rama abubuwa da yayi miki,kuma tayaya zaki nunamai mata irinmu sunada daraja da kima adonsa kina zaune shurun guri daya,wai ke dole kina matsayin mace"Tafada ranta bace.
Gyada kai Nusiba tayi tana fadin"Gaskiyane kawata...To yanzu yazanyi"Rahma ta gyara zama tace"yauwa...Kinga da farko dai dole zaki chanza tsarin zamanku zaki fara shigemai inyana gida,yawan yin hot and sexy dreessing inyana gida,lakanta mai yafiso,mai yake batamai rai,bashi girma ki daraja sa fiye da da,kikuma zama baiwa agaresa sai yadda yayi dake ammh duk wa"innan bazasu samu ba Nusiba sai kin cire tsoro"Tafada tana kallonta,cire Tagumi Nusiba tayi kan tace"kina ganin zai fada tarkonmu kuwa Rahma.
Rahma tayi tsaki tace"ke banza ce wlh duk jin kansa kikayi amfani da shawarana nadan lokaci wlh sai Nazir Adam galadanchi yazam miki jaka ko"ina yana manne dake"tafada wit ful comfident,Nusiba tace"da gaske.."Rahma tace"Insha Allahu..Ammh sai kin daure duk wani jizgaki dazai yi ki share kada kiyi fushi kice zaki ja baya,inkikai haka kin lalatamana Aiki"Nusiba tayi tace"Ban insha kawata suka tafa suna dariya atare,ANTY ce ta leko tana cemusu"To sarakan hira sai ku Fito Ammi zata tafi.
Fitowa sukayi Rahma nakara jaddadama Nusiba kudirinsu itakuma Nusiba tamata alqwarin dazaran takoma komai zai fara,Rahma tashirya domin tabi Ammi su koma tare Ammi takalli Nusiba tace"Nazata tare zamu tafi tunda naga inna taji sauki",Nusiba tayi narai da Fuska tace"Kai Ammi da zan yi sati nefa"Ammi tace"ok baruwana kikira mijinki ki tambayeshi "Nusiba tace'Kai Ammi kifadamai mana"Ammi tace"Mijina ne ko mijinki"Tafada tana dariya inna fatsima tace"kibita kikoma dakinki naji sauki"Ammi tace"kyaleta dai tafadama mijinta Allah barshi ko zuwa jibi ne tadwo ita da suwaiba.
Rakasu tayi har kofar gida tana daga musu Hannu sai da suka wuce takoma gida,tana tunanin ta ina zata fara,chan zuwa dare wajen karfe 8 nadare tana zaune kan darduma wayace ahannunta sai tayi dialing no din Ya Nazir sai tayi sauri takashe tarasa ta ina zata fara tsoro takeji.
*Comment*
*Share*
*Vote*
*Janaf*💕
[4/11, 2:14 PM] 0mmer Farouk: *🧑🏻NAZIR🧑🏻*
_*(The journalist)*_
*(Based on luv and Romantic story)*
*Na*
*Janaf ce*✍
*Vote me on WATTPAD:Janafnancy*
© _*INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION*_🖊
*```(onward together)
*JUSZ GIVE US A FOLLOW*✔
*```DIDECATED TO SAHIBA HAFSART HAFNAN
_*Mama Hadizata bata da lfy,she need ur prayers,wish u quik recovery momma*_
```D whole page iz dash for u SARDAUNAH u guyz kanada kirki chochai ammh badan Halinka,ba yaseen inbaka daina cemin jalop ba,zansa abika dat kauye a kamamin kai,Abi...Lol Tanque so much sardauna relli Appriciate ur care```
23/24
""""Dakyar tayi shahada ta danah kiran wanda yana shiga takara akunne ammh yadda bugawan ke du!du!haka zuciyarta keyi,harta fidda rai dazai dauka sai taji an dauka ammh anyi shuru.
Nazir dake kwance kan makeken gadonsa daga shi sai dogon wando baki babu riga ajikinsa adaya hannunsa yasaka ya tallabi bayan wuyansa dayakuma yana rike da waya yana,sarrafaata kiran Nusiba yashigo,wanda dama ya ijiye nombar wanda yayi saving da villager girl,yayi mamakin ganin cll dinta shiyasa yaki dauka sai dayagama jan ajinsa sai yadaga yayi shuru.
Nusiba najin saukan Numashinsa akunnenta alamun yanaji sai ta daburce tace cikin in ina"Brk....da...Da dare ya Nazir"tafada harda runtse ido shiko suman kwance yayi saboda yadda takira Ya Nazir din sai da ko ya nizar masa har cikin kwanya.
""Yauwa...Plz who iz on d online"yafada cikin dakewa Nusiba taji gwiwanta yasake ammh sai tace"la...ya Nazir nice fa"Kecea?.....Shinake tambaya"yafada cikin kosawa sai tadake tace"Nice fa Nusiba matarka ashe baka da nombata? tafada asanyaye"Cijen gefen bakinshi yayi kan yac"in jiye nombarki kan mene,kina kirana ne"yafada hankalinsa kwance gyada kai Nusiba tayi kamar tana gabansa yacigaba da cewa
"""ina ijiye nombar dake kirana nakirane bawai kwashe kwashe ba,kingane"yafada haryana dan zaro ido"Nusiba tace"yi hakuri...Ai bansani ba"Tafada da sangarta tsaki yaja aransa yana fadin"one of d probm nadan Nageria kenan Abunda yasani so yake akara tunatar dashi.
Katesta yayi dacewa"iz ok...ya"a kay ne"yafada cikin dakewa Nusiba tace"Dama inaso nadan kara kwana biyu ne harzuwa inna tasamu sauki"tafada cikin sanyi Nazir yayi shuru kan yace"No kiyi zamanki da mahaifiyarki harta warke saboda ni mutum ne dayasan yancin dan Adam so u ar free"yafada harda zakuda kafada
Mgar ta soki Nusiba ammh kuma tunda ita ke neman shiri sai tace"haba kwana biyun dai,inzauna kuma nabarmawa Auren"Tafada kamar zatai mai kuka,lokaci daya yaji jikinsa ya mutu ya furta cikin kasala"Dama kina da Aurene"yar dariya tayi kan tace"Eh man inadashi.
Nazir yagyara kwanciya yana cewa"Au kina dashi? nadauka baki dashi ne don naga ko agidan bawani abu kike min ba"Sai daya fada haka kuma yaji haushin kanshi harda marin kuncinsa,Nusiba tarike baki cikin zolaya tace"La...Dama kana so namaka wani abu baka taba cewa ba"Tafada tana rufe baki,Nazir yace cikin dakewa"Inace Tunkan kiyi Aure kinsan hakkokin mata kan mijinta ko? "yafada da alamar tambaya bai bari tace wani abu yace"tom wani karin bayani kike Nema,kinga kincinyemin lokacina"Yana gama fadar haka kit yakashe kiran.
Sororo Nusiba tayi da wayar ahannunta tana mamakin abunda yakwana tsakaninta da Nazir,ashe yana da saukin kai mutane ne basu sani ba,itakadai take tuna hiransu tana mirmishi shigowar Inna fatsima dakin ne yasa tadawo hayyacinta,wanda tafita waje shan iska,Cemata tayi Ya Nazir yakira yamata yajiki tafita,ammh yace agaisheta,inna Fatsima tace"Tana amsawa,Lalle Nusiba kin iya sharota😂😂😂
Shima Nazir abangarensu haushin kansa yakamasa yadda yaga yabata lokacinsa wurin wannan yarinyar wanda shi atsarinshi baya doguwar waya,ammh sai gashi ya lalace yana waya da ita,ammh akasan ransa wasai yakeji yar hiran dasukayi wanda Da Abun yakwana Aransa yakasa gane kansa.
Gari na wayewa around 7 Nusiba tasake kiran Nazir tabashi 2miss baiyi picking ba sai ta turamai Text
_Slm hop u wk up Naurish and glossly...Ok enjoy ur mrnin coffea……Ur wife NusNaz_
Lokacin da messg din yashiga yana dakin labarai yana labarun karfe bakwai cikin ratsatsan Turancinsa sai da ya fito kana yaduba wayar lokacim dayaga messg din yana tsayene bakin motarsa Kara bin Messg yayi yana karantawa abunda yafi daukan hankalinsa shine *NUZNAZ* Wanda harsaida mirmishi yasubucemai bash dake tahowa ya tsuramai ido yana kallonsa har yakariso bai sani ba sai da yadaki kafadansa yana cewa"Mutumi mekasamu ne...Kake wani killer smiller haka"Yafada yana kuresa da ido,Tsaki Nazir yaja kan ya juya yace"In ruwanka dan sa"ido"yafada yana hararansa.
Bash yayi dariya yace""Kanka akeji kuma"yafada yana wucewa da harara Nazir yabisa kafin yafada mota wanda dama already ilu yana ciki,suka fice daga gidan talabijin din.
Har yammah shuru Nusiba bata ga reply din Nazir ba balle tasa ran kira,wanda dama bata kawo ba,sai itama ta share kawai,shiko Nazir dama koda yagani bai yi wani tunanin maida martani ba,ammh lokaci bayan lokaci yakan duba messg din wanda yakasa goguwa aransa kai haddacce kowani harafi yayi daga ciki,wanda yarasa dalili.
washegari Tana idar da sallah Subahi tajawo wayarta tasake turamai message.
_Salam,gud mrnin ya Nazir,how was ur night hop iz full of happines and fantatic dream...yau zan koma kano,ur Wife NazNuz_
Tana gama Turamai tahau shirya kayanta Anty suwaiba ma tana nata shirin suna Haka sai ga baba bayan sun gaisheshi ne yakalli inna yace"ya jikin naki"yafada da kulawa Inna fatsima tace cikin kunya"Da sauki Alhamdulillah"Baba yace"To masha Allah yafada yana kallo Nusiba dake Tura kaya ajaka yace"Ke yaushe zaki koma dakinki ne"yafada yana tsareta da ido.
Cikin mamaki,tadago tana kallo baba dama Baba yadamu da itada har zai tambayeta yaushe zata koma,lalle wannan zuwan taga canje canje acikin gidansu hakan yananuna mata cewa alkadarin inna Saude yafara karyewa cikin girmamawa tace"yau dama zan koma baba"Tafada harda Rusunawa"Baba ya gyada kai yace"yauwa gwara kuyi haraba harda ke Suwaiba kada kuma muzama mutanen banza'yafada cike da dattako.
.Anty suwaiba tace cikin kulawa"Hakane yanzu ma shiri mukeyi ai,tunda taji sauki"Baba yadan jima adakin kafin yafice sai gashi yana cema Nusiba inzasu wuce tamai mgana,dukkansu cikin mamaki suke kallo juna,Nusiba ta zube tana kai kanta kasa tana sujjuda cikin Nuna godiyarta ga Allah,Anty suwaiba tace"kara godema Allah Nusiba,tabbas Allah Abun godiya.
Tafada cikin murna,Nusiba nadagowa ta isa ga inna Fatsima ta Rumgumeta idanunta naFitar da kwallah,Inna Fatsima ta zareta tana cewa"Ya isa Allah zaki godemawa domin da yardanshi komai yafaru"Tafada tana sharema Nusiba kwallah,nan da nan suka gama shirinsu koda Karfe 10Am duk sun kammallah shirinsu Abun mamaki sai gashi Baba yabasu buhun wake dana shinkafa buhu bibbiyu yace kawu biyu inkaima Surukai na biyu murna ta sanya saida nayi kwallah Saude na kallo ammh bata da tacewa Dada ma batayi mgana ba domin itama abun yafara sakinta.
Tashan Napep suka dauka har Saman gada inda suka shiga motar kano suka dau hanya.Nusiba farincikinta yakasa boyuwa shiyaasa tadauki damarar Amfani da shawaran Rahama kodan Nazir yazo hannu shiyasa takara bude jakarta nakamfani Gucci taciro wayarta Text nakara Turamai.
_am on my way...Care_
Tana Turamai tamaida wayar jaka,shiko Nazir tunda garin Allah yawaye bayan yadawo sallar subahi yakoma barci bai farka ba sai after 11 cikin kasala yatashi jiyake jikinsa yasaki wanka yashiga koda yafito,falo yafito ya nufi fridge yadauko Ruwa nan yazauna yakunna Tashar CNN yana kallo bai Tashi daga nan ba sai da aka kira sallar azahar yafita massallaci,sai da yadwo yahaura sama yadauko wayan nasa ya tararda missd call din Ammi dana mg ammh kuma sai messg din dake yawo asaman wayar yadauki Hankalinsa cikin rawan jiki yabude sai yaci karo da sakon Nusiba na farko dana biyu,gefen gado yanema yazauna yana ayyana me yarinyar nan take Nufi kintatan lokacin yayi yaga yanzu in lafiya lafiyan yasan yanzu sun isa gida sai kawai yasamu kansa da Turamata da Reply.
*Safe landeed*
bayan ya Turamata kuma sai yakamajin Haushin kanshi don me ya turamata tsaki yaja ammh fa akasan Ransa dadi yakeji zuciyarsa ke rayamasa cewa yabita yaga ina gudun ruwanta yake.
Itakuwa Nusiba lokacin da Text din yashigomata sun dade da isa,bata dade da barowa gidan su Ammi ba,takaimusu sakon baba wanda Ammi sunata godiya,Allah sarki ko kogi yana son kari,taji shigowar text ammh bata taba kawowa Nazir bane shiyasa bata bi takai ba,sai da tayi wanka tasaka wani riga da sikat yan kanti black and white kan babu dankwali tadaure da band kichen tafara isa ta dauko maltina tataho falo sai da tazauna kana tajawo wayarta harsai da takira inna tafadamata sun isa suka dan Taba hira kana sukayi sallama,latse latsenta takeyi kamar achan tashiga ma"adanar sakon ni kawai taga Ya Nazir arow nayawo asama ai da rawan jiki tabude text din duk babu yawa short ne ammh Abun yabata mamaki matuka bata zata abun zai zo mata da sauki haka ba l,ihun murna tasaka tana Fadin"yes....Komai yana Tafiya daidai,Rahma ta latso cikin rawan jiki take labarta mata komai,
Rahma tace cikin murna"Kinji ko...Kawata wlh dama nasani kekika saka wasa da Tuni anwuce gurin,yanzu kinsan me nake so dake"Nusiba tace"A"a sai kin Fada"Rahma tace"Ki kirasa yanzu kice kun isa lafiya tare damai barka da Rana"Nusiba tace"To kawata yadda kikace"Tafada tana datse kiran.
Shi ta dokama kira,cikin ikon Allah ta yanke bai dauka ba,sai tasake kira shima tana gabda yankewa yadauka