Showing 12001 words to 15000 words out of 87333 words

Chapter 5 - Nazir Bok Complete Hausa Novels by Janafty.txt

kana cemin forget it"Nazir yaji Ransa ya baci to mezai ce,wacce ta mareshi a freedom,No bazai yuyuba wannan shine kuskurensa na Farko dazai yi.

Cikin Nauyin baki yace"Am srry Abbu kawai tana min kama Da wata ne"Yafada yana mikewa Ammi tayi tsaki tace"shashanci yanzu haka cikin yan"matan sane take kama Da wata"Nusiba ta dago sai da ta takallesa daga yadda ya zuciya tace"Eh man Ammi kila dai kama ce"tafada tana dariya kasa kasa.

Nazir ko yakalli Nusiba lokacin daya haura step din tako sakarmai gwalo nuna kansa yayi alamu,shi tagyada kai tana Dariya,Nazir yayi saurin shigewa daki yana jin takaichi aransa,yadda komai ya juye dashi.

Musty duk yana lura da yadda Nusiba kema Nazir gwalo Abun yadauremai kai,wai mace kema Nazir gwalo dadariya yana tsaye,tabbas akwai lauje cikin Nadi,ko takanshi ba wanda yakara bi don Asan tunda yayi Fushi yashiga ciki shikenan,dininng din suka isa Ammi da Nusiba Suka zubama kowa bakajin karan komai Sai na haduwar cokula da plate.

Nazir yana Shiga daki ya dauki wayarsa da Hanzari ya Dannah wasu lambobi Ilu dake zaune kofar gidansu gun wani mai rake yayi zumbur ya mike yana Fadin"Ogane...Yadaga kiran yana Dauka Nazir yace"Ilu kasan na tsani makaryaci ko? ilu ya amsa cikin rawan murya"Eh yallabai..Me..."Kasan zan iya rabuwa da duk wanda na yarda dashi yamim karya ko'gyada kai kawai ilu keyi jikinsa yafara rawa kai Tsaye Nazir yace"Tambayarka zanyi,kuma wlh inbaka Fadamin gaskiya ba kasan hukuncina"yafada ahasale jikin ilu na Rawa yace"To..To..Yallabai wlh zan fadama gaskiya.

Nazir yace"gud...Wannan yarinyar Tana garin nan kokuwa batanan"ilu yaji cikinsa yabada wani kulukulu...Saboda tsoro cikin in ina yace"Wa...Wata yarinyar....Shout up ur dirty mouth ina tambayanka kana Tambayana"Nazir ya katsesa a fusace ilu yace"kayi hakuri oga bangane wata yarinya kake Nufi ba"Nazir ya hadiye miyau mai zafi kan yace"Dat girl dana baka aiki akanta"ilu dacikinsa ke rugugi da alamu zawo ne yakamasa yace"umh...Uhm...Yallabai don girman Allah kamin aikin gafara"Nazir yace rai bace"answer me yes or No..."ilu ya hadiye wani miyau mai zafi yace"eh tana garin nan kuma Abbun ne ya daukesu rannan,.."Ammh meyasa baka fadamun ba"Nazir ya katsesa cikin daburcewa Ilu yace"Bansan yazaka karbi batun bane yallabai ammh wlh bada gayyah nayi ba"shuru Nazir yayi Saboda takaichi ji yake kamar yajawo ilu ta wayan ya zabgamasa mari,sai kashen wayan Kenan ilu yace"Oga hukuncin fa...Kamin sassauci"tsaki Kawai Nazir yaja ya datse kiran,kan gadon yafada yana jin wani bakinciki,yanzu wannan yarinya ita tayi winning akansa kenan,ta maresa yasa ankoresu,daga karshe sundawo gidansu da zama,yanzu baya da wata hanya ramuwa domin kome yace zaiyi at any time asirinshi zai Tonu kuma dole aji ba"asin meya hadasu,shikuma shine baison aji don wlh mutumcisa ne zai zube.

Ilu kuwa Nazir na kashe waya ya kwaso aguje ya shige gida bai zame ko"ina ba Sai Bayi,domin yana ma
Tunanin yafara awando😂😂😂😂


Bayan sun kammalah cin abincin sun dade suna Hira sai wurin goma Suka musu sallama suka wuce shashensu ammh kawu Abun na Ransa sai da ya titsiye Nusiba kan tafadamai ko me ke tsakaninta Da Nazir,ammh Nusiba tace ita batama sanshi ba saiyau,bawai don ya yarda sai ya kyaleta ammh yafada mata,tabi asannu don Nazir bayada sauki kamar Mustapha.

Itakuwa Nusiba taki Fadane domin atunaninta in su kawu sukaji Abunda tayi zasuce bata kyauta ba,tunda suna cin arzikisu agurinsu,kuma batason Ammi taji ta mari danta,don tasan bazata ji dadi ba,itakanta bata so marinsa ba shi yaja,don shi ya Fusatata.

Nazir kusan kwana yayi yana saka yadda zaiyi da Nusiba ammh yarasa mafita,Tashinsa kenan ya sauko kasa ya iske Abbu da musty suna beakfsat kowannensu yayi Shirin Fita gaida Abbu yayi ya amsa yana Fadin"Nazirun Ammi an sauko"Bata fuska yayi yana fadin"nifa Abbu basunana Naziru ba,Abbu yace"To yane sunan? Nazir yace"Nazir..."Abbu yace"Af Nazirun kenan...

Musty yakyalkyace dadariya yana Fadin"Kawai broda sai kasamu mata mai Suna Nazira"Nazir ya doka masa harara kawai Sai musty yasaki dariyan dayake boyewa,ai da gudu Nazir ya bisa shiko yayi Hanyar dakin Ammi yana Fadin"Ammi kinganshi ko,Abbu fa yafada"

Ammi da ta fito daga daki taci karo dasu Musty ya biyo abayanta,Ammi ta kalli Nazir dake Hararan mustytace"Kai kuma lafiyarka gotai gotai dakai"bai ce komai ba yajuya yawuce kichen ya bude fridge ya dauko Apple da kankana da Abarba,wanda Ammi ta yankasu kanana tunjiya tasanya afridge saboda yayi Sanyi,yana wani Tura baki ya haye Sama Abbu ya bishi da kallo yana Fadin"Fatima kin sangarta Nazira wlh"Ammi tayi Dariya tana rike baki,Nazir kuwa yanajinsu sai kawai yayi mirmishi yana Fadi afili"No happy place like Home.

inda yasaba zama inyadawo,nan ya bude ya shiga bai zauna ba sai ya isa ga dan dakalin da"akama gun kwalliya ya dora farantin fruit din yadare kai yana sa fork yana ci hankalinsa na kan Farfajiyan gidan a idonsa Abbu ya fito direba yaja sa sukawuce,bayan shi sai Kawu,wanda shima da dan mashin dinshi,tsuru Nazir yamai da ido yana kallonsa wai yagani ko acikin yan"uwansu ne ammh bai gane shiba.

Yana nan zaune gun yana kalle kallensa yana jin Nishadi,kamar ance kalan chan kyar idonsa akan Nusiba data fito daga Shashensu Sanye cikin leshi doguwar riga AShape wanda ta mata das ajiki,tayi Daurin zarah buhari wanda yazauna mata das,dashi ammh sai ta dunkule gashinta ta tusa aciki,ta sanya katon mayafinta ta sakashi akanta,Wata karamar jaka rataye akafadarta.

Shashensu Ammi ta Nufa Hankalinta akwance cikin tafiyanta na natsuwa,Abun mamaki idanu Nazir yasamata yana kallon duk wani motsinta,cikin ikon Allah kamar ance tadaga kanta Sama,caraf ta sauke A Nazir wanda ke Sanye da 3quater black sai farar vest wanda gabadaya muscles dinsa sun bayyana,tsayawa Nusiba tayi ta coge tana kallonsa Dariya ta kamata data tuna yadda jiya yayi muzai muzai yakasa fadan ta shararamai mari,dariya takemai tana Nuna sa,dafari yazata dawani take ammh kuma sai ya lura yarinya shi take Nunawa,cikin mamaki ya yi pointing kansa da small knife din dake Hannunsa,gyada kai Nusiba tayi harda rike kantada hannu biyu tana dagamai Hannu tareda gwalo,Nazir yaji Ransa yayi mugun Baci,kawai yajuya yayo kasa afusace.

Nusiba na ganin Haka tayi Saurin Fadawa Shashen Ammi da Sallama,Musty taci karo dashi Afalon yana gyara zaman nektie dinshi dake Wuyansa,gaisawa sukayi ammh gabadaya kwalliyan Nusiba tatafi Da musty over wanda ya shagala da kallonta,itakuwa Hankalinta na kan,benen tana so taga ta inda dan renin wayau Gayen nan zai Fito.

Cikin zafi ya gangaro da bibbiyu yake tako step din ya kariso kenan Saiga Ammi ta Fito daga daki cikin shirin zuwa Asibiti,ganin yadda Nazir yake Nufota yasa tayi bayan Ammi da gudu tana Fadin"Wayyo Ammi kin ganshi ko"Ammi ta waigo tana kallon Nazir wanda idanunsa suka rine saboda bacinrai,tace"Na shiga uku, ni Fatima,shin meke Damunka ne?

Nazir yafurta rai Bace"Ammi wannan yarinya sam bata da kunya,gwalo fa takemin"yafada ransa namasa zafi,Nusiba dake bayan Ammi taleko tana Fadin"La Ammi nida na shigo yanzu a ina ma na gansa balle har na mai gwalo? tafada da sigar mamaki,ammh tana fakaikan idon Ammi takaramai gwalon,Ammi tayi tsaki tace"mtewwww...Yaushe taganga balle tama gwalo,kaga wlh kafita ido na,narufe kasama yarinyarnan ido tunjiya wai metama kane"tafada tana Hararansa Nazir daskarewa yayi kawai yana kallon yadda yarinya tamai dashi wani wawa.


Musty ne yace"Broda yanzu fa ka sauko,itakuma Nusiba shigowarta kenan,banajin naga sanda tamaka gwalo"yafada billhaqqi da gaskiya,Nazir ya juyo ransa bace"Ok nayi karya ko mustapha? Musty yayi saurin cewa"Am srry broda ban fada don inbata maka ba"yafada harda rankwafawa,Ammi tace'Mustapha kuwuce ku Tafi karku makara,my dota adawo lpy'Nusiba ta amsa da"Allah yasa Ammina tafada tana Dariya kasa kasa ganin yadda Nazir yayi wani nuku nuku da fuska.



Musty yace"broda mun Tafi"ko kallonsa Nazir bai yi ba kawai yajuya saboda bakincikin yadda karamar halitta take cazamai kwakwalwa,karamar halittar ma mace,macen yar Africa,kai Never wlh,tunda yarinyarnan Tashiga rayuwarsa yafara damuwa,ada baisan wani abu bacin rai ba,ammh dalilinta yasan yazauna yaita bacin Rai shi kadai.

Saboda takaichi Shi kadai ya wuni cikin daki,sai yammah Ammi tadawo ganin bai sauko ba,sai ta kyalesa tasan Fushi yayi, yammah nayi kuma yakoma gun,dan yana jin dadin iskan gurin,yauma din tare suka dawo suna hira suna,dariya,yana lura da yadda Musty yake wani binta dawani siririn kallo,Abun bai bashi mamaki ba Sai da yaga yadauki jakarta,sun Nufi Shashensu Nusiba,Rike baki yayi yana binsu da kallo Abun mamaki shida baya maida kai kan Abunda bai damesa ba ammh sai gashi yana zaune yana jiran yaga yaushe zasu fito gefe daya kuma yana tsara yadda zai kuntatama yarinyarnan,yadda bayan tagama marinsa kuma tazo ta siye iyayensa wanda sam basuson laifinta,cikin lokaci kadan yasamo solution tsalle yayi yana Fadin"gud...nasan wannan karon i make sure nama Rayuwarta Dameji,cikin Farinciki yakoma dakinsa yayo alwala yatafi massallaci sallar mangarib sai da akayi issha"i yadawo koda yadawo fushi yake shiyasa,ko hirar bai Tsaya ba ya wuce Sama Ammi tabisa da kallo kan Tace"Allah shirye ka Nazir.

Washegari.

Karfe bakwai yasauko cikin shirinsa na shigarsa wato American suit blue and white kafarsa sanye cikin Takalmi rufaffe yar jakar briefcase dinsane makale a hannunsa yafito sanye da waya akunnesa yana Fadin'Kazo gida ka sameni"Daga Haka ya datse kiran Ammi ce keta hadadan hada breafsat ya kalleta yace"Gud mrning Ammi"ta kallesa tace"ka gama Fushin"Tafada tana cigaba da aikinta mirmishi yayi yace"Wazai yi fushi da Amminsa,kawai Ammi ina son kadaicine"Tabe baki kawai Ammi tayi yace"Ammi zan koma Abuja,Sai next week in Allah ya yarda"Dakatawa tana Fadin"tafiya da gaggawa haka"sosa kai yayi yace"Ammi kiran gaggawa na samu but next week zan zo'Fatan Allah ya kiyaye tamai,ya tambayi Abbu tace bai Tashi ba,yace inyatashi tafadamai ya wuce.

Har bakin mota ta rakasa inda ilu direba ke jiransa fadawa motan,yayi yana satan kallon barayin su Nusiba yana cije baki,ilu cikin tsoro yace"yallabai.....muje FREEDOM RADION"Nazir ya katsesa cikin muryan Jarumta da sadaukantaka,cikin azama ilu yabawa motan nan wuta megadi yabude musu get Suka Fice da gudu.



*TOPHA,KUN HANGO BADAKALAR KO?GA NAZIR YA TAFI FREEDOM,TABBAS BA ALHERI ZAI KAISA BA...Kubiyo ni










*Commet and share*














*Janaf*✍
[4/11, 2:11 PM] 0mmer Farouk: *🧑🏻NAZIR🧑🏻*

     _*(The journalist)*_

*(Based on luv and Romantic story)*

  *Na*

*Janaf ce*✍

*Vote me on WATTPAD:Janafnancy*

© _*INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION*_🖊

*```DIDECATED TO SAHIBA HAFSART HAFNAN```








_*Congratulation!Congratulation!Congratulation NUSIBER UK 4 completing ur Sweetes,Amarzing,educated,special And Adorable Novel,  WATA KADDARA,Hakika kin fadakar,kuma kin wa"anzarta tareda Nishadantarwa,Ina rokon Allah ya yafemiki kurakuran dake ciki,yabamu ikon Amfana da Abunda keciki,ki sani ki kara Sani Ni janaf ina miki son kauna mai dorewa na Har Abada*_



*```dis page goes to u,AUREN FARI FANS,AND JANAF FANS....Walle soyayyanku agareni sai dai Nace Masha Allah,kaunar ku agareni,sai dai Nace ALHAMDULILLAH...Janaf luvs u more and more my habibaties```*





9/10





     """Anty ce ta mike tana Fadin,"Ammi bari in tafi,tunda kin ga danki,kin manta dani"Ammi tamike tana Fadin"Oh..Ni Fatima,Suwaiba wlh Nazir inyazo gida mantawa dakowa nake,kinsan dan" dabaya tareda kai Shiga rai garesa"tafada tana Dariya kan tace tana kallon Nazir daya kishingide kan kujera,idanunsa a lumshe.


"Ga wata sabuwar uwa kayi Nazir,Anty suwaiba,bakasan su ba ko? bayan tafiyarka suka dawo nan da zama"Nazir yadan bude ido cike da kasala yace"Ina yini.."Any ta amsa da cewa"Lpy kaLau Nazir ya Hanya"Alhamdulillah ya bata Amsa daganan ya mike yana kallon Ammi yace.

  "Ammi let me take shower wlh AGajiya nake ji'Ammi tace"Ayyh sannu,dole ka gaji nafa sanka sarkin aiki ne kai ko agogo yashafa maka lpy"takarisa fada tana Dariya,mirmishi yayi ya fara haura step Ammi tace'Mi zan girka ma son? bai juyoba yace"Ammi am ok now...Sai dai zuwa anjuma"yafada yana shigewa ciki.


Ammi tadawo da kallonta kan Anty tana fadin"Kinganshi ko suwaiba,haka yake,komai Nashi dabam,ne Mustapha ya fishi son mutane"Anty tayi mirmishi tace"Ayyah kinsan wasu haka Allah ke halittarsu"

Daganan suka cigaba da hirarsu Ammi na bata lbrin hallayan Nazir da yadda yake Tafiyar da Rayuwarsa,Anty dai ta Fahimci Nazir yafi soyuwa Azuciyar Ammi.


•••••••••

Nusiba na zaune a recording room dinsu suna hira Da Rahma wayarta dake jaka tadauki kara,da hanzari ta cirota wanda ta ganine yana kirane,yasata sakin mirmishi tadaga tana Fadin"Allah taimaki likitan idanu"Musty daga chan bangaren da hannunsa daya ke kan sitiyari daya kuma ya makala akunne yace"Amin..Tare dake yar jaridan Najeria"Atare suka sheke dadariya kan musty yace"Kin tashi aiki ne? Nusiba tace"Yanzu nake son Tashi"Musty yace"Ok kijira in biyo mu koma gida,dama kinga tare muka zo ko? Nusiba tace"Naki wayon karda Kace ina saka aiki fa"


Musty yayi mirmishi yana Fadin"Hmmm tuni nakoma direban Hajiya aie"da sauri Nusiba tace"Wata Hajiyar? da alamar Tambaya musty ya kashe murya yace"Hajiya Nusiba mana"Hannu Nusiba ta sa baki tana Dariya kan ta datse wayan,Rahma dake zaune tayi kasake tana kallon Nusiba,sai Da ta gama wayar ta hau tattara kayanta Rahma tace.


   ""Ki wai bangane miki ba fa kwana biyu,are u in luv? Nusiba ta juyo tana kallon Rahma kan tace"Meye luv? wani kalan gwanjo ne,kokuwa wani sabon yadi ne dayafito kwanan nan"Tafada Hankalinta kwance,Rahma ta rike baki tace"Bansani ba yar Renin Hammata kawai"Nusiba ta kyalkyace da dariya tana Fadin"Bana Riga ba,yar Air kawai,ai kece dawata mgana,yo ai atsarin Nusiba babu soyayyar Da wani da Namiji"Rahma ta kalleta cike da mamaki kan tace"Meyasa? kefa bani fa gane inda kika dosa Nusiba,kwata kwata baki daukeni a yar"uwa ba"



Nusiba tace"Kinji ki da wata mgana,kawai hirar ce bata zoba..Kinga zan fada miki komai ammh sai gobe kinga yanzu yaya musty na jirana"Rahma tace"Hmmm...Allah yasa,to shi wai gayen nan dake kawoki waye? ko shine mustyn"Nusiba ta yi dariya kan tace"Hoho ni na hadu da yar jarida yau,shine mana broda na ne"



Rahma tayi shuru bata ce komai ba,ammh aranta tana mamakin yadda Nusiba tace wannan hadadden gayen dan"uwanta ne,to bata ce ba,domin tun haduwarsu Nusiba bata yarda tasan komai akanta ba,ammh ita har gidan su taje,komai babu Abunda take boyemata.

Nusiba ta rataya jakarta tazo kusa da Rahma ta dafata tana Fadin"Haba kawalliya mai remon jaba,ki manta kawai wlh zan fadamiki komai,kawata nidin ne nacika zurfin ciki"Rahma tace"Babu damuwa,kin dai dau alqawari ko"Gyada kai Nusiba tayi tana wucewa tace"Sai gobe yar rigima,tafada tana ficewa.


Tana Fitowa ta iske manaja na gaisawa Da musty tana zuwa,Musty yace ma "manaja ai ma gatanan,Manaja yabi Nusiba da kallon mamaki domin yadan rasa jinsa da ganinsa na dan lokaci,kafin yayi mgana Nusiba ta bude mota ta shiga tana Fadin"Yallabai sai gobe,daman ina son ganin ka goben"musty yabashi Hannu sukayi musabaha yafada mota suka fice.



Manaja yayi zuru yana Fadi Aransa"To wai meyake Faruwa ne? meya Hada Nusiba Da kanin Nazir Adam galadanchi,? kodai saurayinta ne? tab yafada yana rike haba yace"Akwai mgana kuwa"yadade tsaye yana jimami kafin ya wuce yakoma office.







Nazir tunda yahau Sama bai sauko ba Sai bayan la"asar wanka yayi ya sanya  jallabiya baka mai gajeren Hannu,kasa ya sauko falon tsit bakowa,buruntu yaji akichen sai ya nufi chan abakin kichen din yatsaya yana Fadin"Ammi na ina kike shige sai nemanki nake"Ammi dake tsaye akichen suna aiki dasu mero ta waigo tana Fadin"Ina nan Dan Ammi..Favourite dinka nake maka"Mirmishi yayi yana Fadin"Wow...dat why i love u my Ammi,"Tace tana Dariya"Me too my son.



Juyawa yana Fadin"Ammi yau Abbu sai jamana Rai yake yaki dawowa?Ammi tace"yo shima ya ramane,kwana nawa yana dawowa da wuri baka zoba'bai bata amsa ba ya isa ga fridge ya dauki lemonsa na squach yasake haurawa sama,wata kofa ya bude sai ga wani guri wanda ya kawatu da wasu fulawoyi masu kyau da sha"awa,anyi round dinsu,daga tsakiya kuma wani dan lilo ne yana reto agurin kai tsaye ya isa ga liken ya haye yana daga roban lemon abakinsa baifi minti goma da zama ba aka bude get,yana daga inda yake yana kallon komai dake Faruwa  afarfajiyan gidan.


Motar musty ne ta shigo,tundaga chan ya hango kamar mace agaban motan,ammh yabarshi idonsane ke gizo,kauda kai yayi ammh kuma baisan dalili ba yakara maidawa kansu,lokacin sun fito daga motar musty na mata mgana tana mirmishi,bayanta yake gani tajuya tana facing din musty,sanye da riga da sikat na atamfa ta sanya katon mayafi,Nazir dake zaune ya kura musu ido Aransa yana ayyana,yaushe mustapha ya zama dan,iska yana kawo mata har gida.


Cikin mamaki ya kallensu har Tawuce ta nufi shashensu shikuma musty ya nufa cikin falo,fuskarsa na bayyana Annuri,Nazir ya kauda kai yana Tabe baki yace Aransa"Lalle Mustapha duka duka yaushe ya girma,balle har ya dinga lekema mata"chan kuma ya tabe baki ya maida kansa yadan daga sama yana shilli da kafafunsa kamar yaro.



Sai da aka kira mangariba ya sauko daga gurin alwala yayi adakinsa kafin ya sauko Falo da musty yaci karo shima fitowarsa kenan daga daki zashi massallaci ya nufeshi yana Fadin"wlcm big broda,tundazu na dawo Ammi tace kadawo,"Rumgumesa yayi,Nazir ya yi huging nasa back yana Fadin"Lazy doctor i miss u'Dariya Musty yayi yana wani makakewa yace"Kai broda ni wlh ba lazy doctor bane"


Abbu ne ya Sawo kai Falon yana Fadin"Yau kuma Antuna da gida kenan? yafada yana kallonsu dagudu kamar kananan yara suka Nufa Abbun suka fadamai suka rumgume,Abbu ya rumgumesu yana Fadin"Kai zafa ku karyama Fatima mijinta"Ammi da fitowarta kenan daga daki tace"Ai kuwa baku isa ba,ku karyamin dan mijina,kowannenku ya tashi matarsa zai dauko,tsaleliya nikuma ku barni da jinya"dariya sukayi gabadayansu musty ne yace"Kai Ammi ai yaci keda Abbu ku barmana ko"Dungurinsa Nazir yayi yana Fadin"Baka Da kunya ko"yafada yana wani sosa kai,dungurin Abbu yakaimasa akai,yana Fadin"See u kai kunyan gareka.


Dariya suka kara shekewa dashi Nazir kuwa murmusawa yayi Abbu yace bari inyi alwala muje massallaci yau gida zai yi albarka,Fatima ki aikama su mallam jibo su zo muyi dinner tare"Ammi tace"Yanzu kuwa Abbun Mustpha,"Abbu yace"Eh naji ki rike Nazirun daman ai shine daidai dake"yafada yana kallon Nazir din dayayi tsaye hannu harde a kirji.



Tare suka fita massallaci nan kusa da gidan ne achan suka hadu da mallam jibo suka gaisa,yaga Nazir wanda daman yataba ganinsa sau biyu yazo gun mahaifinsa,hannu ya basa sukai musabaha,Nazir ko ya tambaya suwaye su Mallam jibo baiyi ba,cos baida damuwa da hakan.

Nusiba kuwa Musty na ijiyeta tashige shashen ta iske Anty na zaune afalo tana kallo agajiye ta dawo,shiyasa tana ma Anty sannu tashige ciki tayo wanka,tazo tafada kan gado ba barci take ba,ammh kuma jikintane a sanyaye ga faduwar gaba datakeyi lokaci bayan lokaci,tana nan kwance har akayi mangariba da issha'i ko motsi ta kasa,kuma dama tana Fashin sallah,Anty ce ta leko take Fadamata zasu shashen su Ammi sun aiko su zo.


Nusiba ta yamutsa  fuska tace"Anty kuje wlh banajin Dadin jikina ne'Anty tace"Ayyah Sannu dadai kin lallaba,kinzo munje don kinsan In Ammi bata ganki ba bazata ji dadi ba,kuma ma babban dansu fa yadawo yau"Takareshe Fada da rike haba Nusiba ta runtse ido tayi shuru kawai,ganin haka yasa Anty ficewa tabarta koda kawu ya tambayeta sai Anty tace tana zuwa,saboda tasan tana cewa bata jin dadi yanzu,zai rasa natsuwarsa.



Koda suka isa sun iske su duka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login