Showing 1 words to 3000 words out of 111817 words
Chapter 1 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf
í ½í±„'YAR KARUWAí ½í±„í ½í²…
Officially
í µí¹®
Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)
í µí·˜í µí·˜
مهللا ىلص Ùˆ ملس ىلع ديس ان هللوسر SAW í ½í¶¤í ¾í´
Ina mai godiya ga Allah da ya bani iko da daman fara wannan sabon littafin nawa mai suna 'YAR KARUWA,
Allah sa mu kammala lafiya, duk abinda ya ke ba dai-dai ba a ciki Allah ya yafemu duka, ni mai rubutawa da
ku masu karatu, FAN'S ina matuƙar ƙamnarku, Uwar batoorl na mugun yinku irin sosai ɗin nan, masu
daraja habibties.í ¾íµ°
SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)
TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma É—aukacin member's namu.
PAGE NA FARKO DA KU ZAN FARA KAMAN YANDA NA YI ALƘAWARI.
Masoyiya Bealkysou
Ummu Adeel tawan
í ¼íµ¿ï¸ 1 _ 5
Matashiyar yarinya ce zuƙeƙiya fara, farinta dai-dai, 'yar kimanin shekaru 20 da haihuwa, durƙushe take
akan guiwowinta ta yi kneel-down a gaban wata mata wacce ko ba'a faÉ—a ba kasan mahaifiyarta ce duba
da kaman da suke yi da kuma maganganun da matashiyar budurwan ke yi.
Cikin tsananin kuka mai nuni da stagwaran taƙaici da kuma tsaban damuwan da take ke ciki ta ce, "Haba
Mami na, Mami dan Allah dan Annabi ba dan ni ba, kuma ba dan halina ba ki bar wannan rayuwa, Mami
kina zubar da mutuncin kanki kina zubar da na 'yar ki, Mami da girmanki kina rayuwa irin ta yara ƙanana
marassa tunani ko mafaɗi, Mami ke fa ya kamata ki stawatar mini idan kinga ina ƙoƙarin sanya kai na a irin
wannan lalatacciyar rayuwan, amma fa Mami ke da kanki kike yi ba ma ni É—in ba, haba Mami na ina iliminki
da tunaninki kika zaɓa mana wannan rayuwa irin ta jahilai...."
Maganan dake baki na ne ya maƙale a maƙoshi na, sakamakon wani azababben marin da Mami na ta kifa
mini, miƙewa tayi tsaye tana huci ranta a ɓace kaman ko da yaushe idan hakan ya faru tsakaninmu,
idanuwanta ta zuba mini tare da cewa, "BANAFSHA har rashin kunyar ki da fistaranki sun kai haka? Ina
mahaifiyarki kina sokamun baƙaƙen magana, ni kike faɗawa ina rayuwa irin ta jahilai? Ni kike ƙira jahila
Banafsha? Irin tarbiyyan da na miki kenan ki nunawa duniya ni ma kin renani balle wasu? Banafsha ni kike
faɗa wa haka?" Mami ta ƙarishe maganan cikin stananin ɓacin ran da har idonta na ƙoƙarin sauya kala.
Cikin kukan da ya zamo mini jiki dan in da sabo na saba, sai na ce, "Allah ya huci zuciyanki Mami na,
amma wuyana bai yi ƙwarin da zai sa nayi suɓutan harshe a kan mahaifiya ta ba, koma menene ke ɗin uwa
ce a gare ni kuma ko ya kike ke mahaifiyata ce, amma ina mai haÉ—a ki da Allah da Manzon sa Mami kiji
tausayin rayuwata kibar wannan lalatacciyar rayuwan, munanan maganganun da mutane ke jifa na da shi
tun baya damuna har ya fara mini ciwo, Mamina dan Allah kiji tausayin maraici na ki daina wannan
rayuwan ko dan ni Mami, wallahi duk inda naje suna É—aya ake qira na da shi manya da yara, duk inda na
wuce sai ace ga 'YAR KARUWA! Mami tun ana faɗa a ɓoye har takai mutum zai staya a gabana ya ce mini
hakan kuma ba ni da yacce zan yi, dan girman Allah Mami kiji tausayi na kibar wannan rayuwa mai cike da
kunyan duniya da lahira, Mami ki tuna fa akwai mutuwa fa, kuma ba mu san yaushe, a ina, a wanne hali, ta
yaya za ta riske mu ba, dan Allah Mamina ki daina kinji" na ƙarishe maganana cikin sigan tausayi ina share
hawaye mai É—umin gaske da ke bin kunci na.
Mamina zama tayi ta dubeni tare da cewa, "Maganar da nake faÉ—a miki a kullum ita ce zan ci-gaba
da faÉ—a miki Banafsha, ni ba karuwanci nake yi ba sana'a nake yi, wanda kuma da wannan sana'a na siya
gida na kai ki makaranta, cinki, shanki, suturanki, maganinki, da komai naki har kika kawo i zuwa yanzu da
kuÉ—in sana'ar nan nake miki, me yasa kema za ki bi ta faÉ—in jama'a ba za ki fahimci mahaifiyarki ba? In na
zauna bana komai kina ga akwai mai kula da mu? Akwai mai É—aukan nauyin karantunki, cinki ko shanki ko
suturanki? Ko da ace aikatau muka je gidan mutane to tabbas nasan za'a nemi lalata mini ke ko wulaƙanta
mu, wanda ni kuma ba zan jure hakan ba, akan abu ya same ki gwanda ko duniya ne su taru a kaina su ce
komai ma sannan sunan da ake ce miki 'YAR KARUWA ya bar damunki in baki fahimci mahaifiyarki ba babu
mai fahimtarta Banafsha, ki dubi rayuwan yanzu da idon basira da kyau, ko bara na ce zan yi dan na kula da
ke to fa tabbas za'a nemi lalata miki rayuwa ko kuma ni É—in, Banafsha duk da ke yarinya ce, amma a
wannan shekarun naki ya kamata ki fahimci rayuwa da kyau."
Kallon Mamina nayi da idanuwana da kullum cikin zubar hawaye suke na ce, "Wallahil Azeem Mami na
gwammaci muyi rayuwan aikatau akan irin wannan rayuwa, na kuma zaɓi muyi rayuwan bara akan
wannan rayuwa, Mamina gwanda na zama 'yar talla mu yi sana'anmu ko na rufawa kai asiri ne ya fi mini
akan wannan rayuwan, sannan lalata rayuwata ba wanda yake da ikon hakan in har Allah bai ƙaddara
hakan ba to babu wanda ya isa tunda kina min addu'a, kuma Allah zai kare ni dan addu'an bakin mahaifiya
ba a maida shi, dan Allah Mamina ki daina, wallahi Mami akwai mutane na gari da yawa a rayuwa masu yi
dan Allah ba tare da zalunci ba, nifa Mami ko baran kika turani zanyi na nemo mana abinda za muci karatu
ko wani sutura na haƙura da su, mutuncinki da nawa su ne abun da nafi buƙata, wannan suna da ake faɗa
mini yana sa zuciyata tana mini zafi sosai-sosai Mamina, dan Allah inma ba za mu yi wani aikin ba mubar
garin nan mu koma wajan 'yan uwanki ko na mahaifi na ne kinji.....", wannan karon ba mari ne ya maƙalar
da sauran maganan dake baki na ba domin kuwa Mamina rufe ni tayi da duka ko ta ina kaman an aiko ta,
da ƙyar aka shigo aka karɓe ni.
Maman ƙawata Umaima ce ta shigo ta karɓe ni ta riƙe hannuna muka tafi gidanta wanda ya ke gidan su
babbar ƙawata kuma Aminiyata wacce banda kamarta.
Matar da ta shigo ta karɓeni wacce muke ƙira da Ummu, kallona tayi ta ce "BANAFSHA wai me yasa kike
son yawan yin sa'insa da Maminki ne da har yake kai da ga miki irin wannan dukan ne? Yanzu ba dan Allah
yayi fitowa na ba kin san halinta za ta iya miki rauni, Banafsha kin girma fa yanzu ba da bane kin zama
budurwa duka bai kama ce ki ba kiwa mahaifiyarki biyayya ki kuma yi haƙuri komai zai wuce kiyi ta
addu'a."
Cikin tsananin kuka da ciwon da jikina ke mun na dukan da Mamina ta mini ina sheshsheqa da muryana
da ta fara dishewa na ce, "Um..mu yaa..yaa.. yaya zan.. yi? Ummu, Maa..mi na, Ummu me yasa sai ni?
Wan.....nann ra..yuwa..n akwai...ciwo mahaifiyar mutum ta dinga kule-kulen mazaje daban-daban, Ummu
kiji fa sunan da ake qira na da shi a anguwan nan 'YAR KARUWA! Ummu hakan akwai daÉ—i? Ummu ya
zanyi da rayuwa ta? Ya ake so nayi? ina ake son na saka kai na? Ko sai na mutu kowa hankalinsa zai
kwanta?" Na faɗa ina ƙara fashewa da mastanancin kukan da zuwa yanzu sautin ma ba ya fita.
Ummu kallona tayi cikin sigan rarrà shi ta ce, "komai na duniya mai wucewa ne Banafsha, ke dai ki ci-gaba
da addu'an Allah ya kawo miki miji na gari kiyi aurenki wanda nake fata zuwa wannan lokacin Allah yasa
komai ya wuce."
Cikin kuka na ce, "Ummu wa zai yi aure? Wa zai aure ni? Ina 'YAR KARUWA wa zai auri yarinyar da uwarta
ke lalatacciyar rayuwa? A'a Ummu karki faɗa min abinda ni da kai na nasan ba zai taɓa faruwa ba, kuma
nima ba zan yaudari kai na ba, nasani ni da aure har na mutu sai dai a lahira idan ana yi, zan zauna da
Mamina na dinga addu'an Allah gyara mana rayuwanmu ya shirya min uwata, amma ba zan taɓa yin aure
ba dan nasan ba mai aure na, kuma ko an aure ni za'a goranta mini."
Ummu murmushi tayi wanda hakan ya ɗan sauƙaƙa mini abinda ke damuna a zuciyata, dan sosai nake jin
Ummu a rai tamkar mahaifiya ta, Ummu ta ce, "Banafsha ki rubuta ki ajiye ni Ummul-khultum na ce za kiyi
aure in Allah ya yarda, kuma aure ne irin wanda ba ko wacce yarinya ke dacen yi ba sai wacce Allah ya
ƙaddarawa hakan, za kiyi aure in Allah ya yarda wanda mijinki na tabbata zai sanya ki mance kin ma taɓa
shiga wannan halin quncin rayuwa, duk bawan da ƙaddara ta stananta a rayuwarsa to tabbas gaba kaɗan
idan da rayuwa zai riske alkairi mara misaltuwa, to ina so kema ki É—auka hakan, duk da akan jarabawan
rayuwa da wani ke ciki to naki ba komai bane, kuma bawan da Allah ke jarraba shi Allah ke so, kibar
wannan tunanin in Allah ya yarda za ki yi aure."
Kallon Ummu nayi idanuwana har yanzun da burbushin ƙwalla na ce, "Ummu nasan da haka, amma babu
mai aure na ina 'YAR KARUWA! sannan ko da nayi auren to Ummu tabbas wulaƙantaccen rayuwa zan yi
dan kuwa zan zama tamkar mujiya ko saniyar ware yacce ake nuni dani yanzu haka can ma za'a yi, za'a
dinga gorantamini a ce ni Ƴar karuwa ce a dinga wulaƙantani, Ummu ni ko kaɗan ma bana ƙaunar maza,
Ummu na tsani maza gani nake kowa irin halin sa kenan bin mata."
Cigaba da rarrashina Ummu tayi har
Ƙawata Umaima ta shigo ta same mu a haka, ganina kawai da tayi ta fahimci me ke faruwa dan ta sani
tabbas labarin gizo baya wuce na ƙoƙi, dan kusan aikin kenan kullum ni da Mamina, idan ba'a yi da safe ba
za'a yi da yamma.
Cikin yanayi na rarrà shi ta ƙira sunana ta ce, "Masoyiya Banafshaty."
Jin sunan da ta qira ni da shi sai da na ɗan murmusa dan kuwa Allah ya gani ni da Umaima ba ƙaramin
ƙaunar junan mu muke ba, duk irin halayyan mahaifiyata da yacce ake yama-ɗiɗi da ni a gari hakan bai
dame ta ba ko kaɗan dan Allah take ƙaunata nima dan Allah nake ƙaunarta, duk gidansu suna ƙaunata illa
iyaka yayansu É—aya da ko giftawa nayi sai yaja staki in kuma ya ganni da Umaima to ranan sai tasha na jaki
idan dai ba wai Ummu na gida bane ta gani ta hanasa, gaba É—aya ya staneni shi da mahaifiyarsa, ba iya su
ba kowa a anguwar kallona yake da laifin mahaifiyata kowa ɗauramun laifin da ban taɓa kusantan shi ba
yake yi, in ka cire wannan gida to ba gidan da nake shiga a anguwan mu, kuma bayan Umaima ba ni da
wata ƙawa ko a makaranta.
Cikin sigan wasa na harari Umaima na ce "Ba wata Masoyiya atou kar ki yaudare ni, kin tashi kin kama
hanya kin tafi aiken Ummu ke kaÉ—ai wato salon asa miki albarkan ke kaÉ—ai ba, irin ba amanan nan, shi ne
za ki wani ce mini masoyiya to na ƙi", na juya ga Ummu nace "Ummuna ai dai tare za ki raba mana
albarkan ko?"
Ummu na murmushi ta ce, "Dai-dai wa dai-da ma kuwa Banafsha 'yar Ummu."
Murmushi nayi, ƙawata Umaima ta riƙe hannuna ta jani har cikin ɗakin su ta zaunar da ni a bakin gado ta
ta ce, "Wai yanzu ke ni za ki cewa yaudara amma dai kinsan ƙaunar da nake miki na amanane ko?"
Kukan da nake dannewa ne ya samu nasaran kuɓucemun, sai kawai na rungume Umaima ina kuka mai cin
zuciya.
Hankalinta ya tashi ita ma a take idanuwanta suka kawo ruwa sai hawaye kuma, bubbuga bayana take yi
cikin sigan rarrashi ta ke cewa "Kiyi haƙuri haka dan Allah masoyiya, kukan da kike yi yana yawa ko so kike
hawayenki ya ƙare ne? dan Allah kibar kukan nan bana so please Banafshaty."
Cikin kukan na ce, "Umaima ya zan yi da rayuwa ta? Ya ake so nayi ne? Ni ji nake mutuwa ma tafi mini
wannan ƙazantaccen rayuwan, dan Allah ace uwarka ta rasa abun yi sai karuwanci kuma a haka Mami ke
cewa sana'a ce wai dama karuwanci sana'a ne? Mami ta ce bata so aci mutunci na ko a lalata mini tarbiya
shi ya hanata zama haka ta kama wannan sana'a dan Allah wannan shi ne soyayya Umaima? Ta kwaɓar da
mutuncinta sannan ta kwaɓar da nawa, shi fa mutunci Madara ne, a abinda Mamina ke yi wa zai ganta da
mutunci idan ba ni da ya zamo mini dole ba?" duk cikin mastanancin kuka nake wannan magana wanda i
zuwa yanzu kai na mugun sara mini yake yi kaman na cire kan na huta.
Umaima ta ce "Banafshaty dan Allah ki yi haƙuri haka nan, ni dai mu ci gaba da addu'a komai zai wuce kin
ji, kuma Mami na sonki fiye da yanda take faɗa ma dan Allah kiyi haƙuri kina addu'a kina kau da kai kinji"
ta faÉ—a tana sharemun hawayena.
Lumshe ido nayi nace "Umaima in dai wannan ce soyayya to tirr! da soyayya, Allah wadaran soyayya,
bana son soyayya, bana ƙaunar soyayya, na tsani soyayyan, Umaima ko na kau da kai kan baya kauduwa
domin muddin ina gida wani zai zo wajanta to sai naji zuciyata na tafarfasa zuciya ta kaman ana wastamun
ruwan zafi zuciyata kaman ana ƙonemun ita, ji nake kaman na kashe kaina na huta, wallahi ba dan kisan
kai zunubi ne babba ba da na jima da kashe kai na dan da wannan rayuwa gwanda na mutu na huta,
Umaima imagine wai har YA DANISH shiima zai ce mun 'YAR KARUWA, stana da cin mutuncin ya wuce
mutanen waje ya koma har kan mutanen gida suna min wannan wacce iriyar rayuwa ce?"
Fashewa nayi da kuka mai ciwo tuno abinda ya faru É—azu sai na ce, "Umaima kinsan me ya faru É—azu?"
Girgiza kai tayi tana hawaye dan maganan ya Danish ya mata ciwo ita ma sai ta ce, "Banafshaty kar ma ki
faÉ—a min me ya faru kinji, yacce kike shanyewa ki shanye kawai, saboda ciki ba dan tuwo kawai aka yi sa ba
ki yi haƙuri za ki ga riban haƙurin da muke cewa kiyi kullum da yardan Allah, babu jimawa za ki ga
sakamakon Ubangiji akan jarabtar da ya miki."
Hannunta na riƙo ina hawaye na ce "A'a Umaima, ko kaɗan wani abun ba zai riƙu a ciki ba dan riƙuwan sa
tabbas masifa ne, haÉ—iye wani abun to barazana ce ga lafiyan mutum, kaman kai ne ka samu guba ka cusa
a cikinka kuma ka ƙi zuwa asibiti a baka taimako, Umaima idan ban faɗa miki ba bazan ji sanyi a rai na ba
wallahi ba abinda zan ɓoye miki a rayuwata indai bai kauce sirrin da Allah ya ce ya zama sirri na ba, wanda
wannan nasan babu shi a kai na nikam, Umaima wai É—azu fa ina kwance a É—aki na ina bita haddan da ya
rage mana kawai naga mutum ya faÉ—o mini É—aki daga shi sai É—an gajeren wando, wai yana tambaya ta ina
Mami na ta tafi a hannu yake sauri yake" kuka nake sosai nace "Umaima kiji fa wai har ni ya ke gayawa
wannan magana, to wallahi idan ita Uwata na haƙura ban ɗau mataki ba dan Uwata ce to su na kusa fara
É—aukan mataki a kansu in ta kama in kashe mutum in yaso nima a kashe ni, yaro ya zo babba ya zo dattijo
ya zo stoho ya zo, Mami har da wanda ta kusa haifa take kulawa wannan wacce rayuwa ce? Haka da safe
wani saurayi ya fito É—akinta ina stugunne ina aiki kawai naji an zame mini É—an-kwali É—an iska wai gashina
na burgesa irin na mamata", kuka nake sosai idan na tuna wasu abubuwan.
Ƙawata Umaima rarrà shi na ta ci-gaba da yi kawai dan ita ma abun sosai yake damun ta, ba ɓata lokaci
zazzaɓi ya rufe ni ruf-ruf nan take na fara tari wanda nake ji tamkar zuciyata zan amayo dan azaban da
nake ji a ƙirji na, hawaye nake ina tarin, wanda hakan ya storita Umaima, cikin ruɗewa ta fice ta ƙira
Ummu suka shigo tare, Ummu ma ta ruÉ—e amma duk da haka ta mini faÉ—a na daina saka damuwa a rai na,
sai da ta gyara mini kwanciyana ta lulluɓe ni sannan ta fice dan ta ɗauko mini magani, Umaima kuma tana
zaune a gefe na tana aikin jero mini sannu tana hawaye.
Ganin tarin yaƙi stayawa