Showing 54001 words to 57000 words out of 111817 words
Chapter 19 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf
kyakkyawan yaro wanda ba zai wuce 14
year's ba ya zo yayi hugging nasa, Bunayd na murmushi ya ce, "Nabeel kai ne ka girma haka?"
Nabeel murmushi yayi kawai ya amshi kayakin Bunayd da ke hannun sojojinsa, suna tafiya suna hira,
Nabeel ya ce, "Yaya zama Soja is not easy gaskiya, ni kawai ka yiwa General magana nima a barni na tafi ko
Spain ɗin ne ko Turkish nima na karanto wani abun."
Bunayd murmushi yayi dai-dai sun shiga palourn gidan, wani corridor suka bi sai ga su gaban wani parta
haɗaɗɗe, shigewa suka yi Nabeel ya dire kayakin a palourn ya ce, "Yaya CAS ɗan gidan General ya dawo,
nidai ka taimaka ka masa magana, nasan idan kai ne ka yi magana zai yarda."
Bunayd ya ce, "tunda ka dawo za mu yi magana letter, yanzu dai bari na huta, sai ka faɗawa su Suhaila su
shirya tafiya Kano, kai ma har da kai, General ya ce duka gida za'a je, ina tunanin Suhail ma may be zuwa
gobe yana hanya."
Sanin Bunayd baya son hayaniya idan ya ce zai huta, sai Nabeel ya fice salun alun, dan ba laifi idan Bunayd
ya so surutu to ko menene biye musu yake yi, Nabeel na ficewa Bunayd ya rage kayan jikinsa a nan palourn
ya kwant dan ya huta, baccin ne bai ɗauke sa da wuri ba, can yayi ɗan guntun staki a fili ya ce, "Kowa yayi
sa'an Mom amma ban da mu, na stani zuwa Kano ba dan kowa ba sai dan ke Mom.." haka ya dinga mitan
surutu shi kaɗai har bacci yayi gaba da shi, Bunayd fa da alaman birgima ne da shi dan kaman zai faɗo daga
kujeran haka yake baccin.
⭐
Banafsha da Maminta suna zaune a palournsu suna hira, sai Banafsha ta dubi Mami ta ce, "Mamina tunda
ba ki saya mini waya ba ki saya mini system to."
Murmushi Mami tayi ta shafa kai na ta ce, "shalelen Mami kada ki damu ko, Allah ya kawo kuɗi Mami za ta
saya miki abinda ya fi system ma balle ƙaramin alhaƙi waya, duk abinda nake yi dan ke nake yi, neman kuɗi
da komai faɗi tashi duk saboda gudalliyan Maminta nake yi, Faɗima ƴar albarka."
Tura baki nayi jin wai Mamina dan ni take komai, yanzu ba abun na ce idan saboda ni take wannan rayuwa
mara fa'idan to ta bari na yafe ba, amma nasan sai ma Mami ta dakani duk da banda lafiya, jan bakina nayi
tare da yin shiru, can na miƙe na ce, "Mami bari na sauya pad."
"To ammatan Maminta a fito lafiya", Mamina ta faɗa tana murmushi, ni kuma na shige ɗakina cikin jin
kunya.
Banafsha na shiga ɗaki bai jima ba sai ga sallaman Abbaa, Mami da fara'a ta amsa tare da masa iso,
wucewa ɗaki tayi ta sako mayafi sannan ta dawo suka gaisa cikin mutunta juna, Abbaa ya tambayi jikin
Banafsha, Mami tana murmushi ta ce, "Da sauƙi sosai ma, yanzu ta tashi ta shiga ɗaki."
Abbaa yana murmushi ya ce, "To Masha Allah! haka ake so."
Palourn sai ya ɗau shiru na mintuna daga Abbaa har Mami ba mai magana,can Mami sai ta miƙe tare da
cewa, "Bari na ƙira maka Faɗiman tunda ta shiga ɗaki ta zauna shiru."
Abbaa na maza yayi ya daure saboda Mami sosai ta masa kwarjini, cikin jarumta ta ce, "A'a ƙyaleta ta huta,
daman dai wajanki na zo."
Mami murmushi tayi tare da komawa ta zauna, bata kawo komai a ranta ba ta ce, "Allah ya sa dai ba laifi
na yi ba."
Abbaa murmushi yayi ya ce, "ai kuwa laifi kika yi, irin gungumemen laifin nan, dan ko a kotu ya wuce civil
case sai dai a ƙira sa da criminal case."
Mami ɗan waro ido tayi ta ce, "ahh! Ba sai an kai ga kotu ba ma, haƙuri zan bada, yanzu dai a faɗa mini
laifin nawa na ji sai na bada haƙuri yanda ya kamata" ta faɗa tana murmushi.
Abbaa gyara zama yayi tare da gyaran murya ya ce, "Ai haƙuri ba zai goge wannan laifin ba, saboda
criminal issue ne, sata kika mini irin babban satan nan da idan aka riga aka maka shi sai abinda Allah yayi
kawai."
Mami da bata harbo jirgin abinda Abbaa ke nufi ba, da mamaki ta ce, "haƙuri kuwa ya zama dole na bada,
Allah baka haƙuri Abbaansu, me na sace haka nayi gaggawan dawo da shi?"
Abbaa murmusawa yayi ya ce, "ai sacewan shi ne dai-dai Mamin yara, idan an sace ba'a dawo da shi sai dai
a riƙe da kyau, Mamin yara maganan gaskiya da gaske nake kuma da gaske nazo sannan a shirye, a taimaka
wa bawan Allah a kula mini da zuciyata da aka sace, tun ranan farko da na fara ganinki naji kin kwanta mini
a rai kin mini, kin tafi da imanina, na daure na kusan shekaru goma sha, amma yanzu abin ya fi ƙarfi na a
taimaka mini a tausaya mini, da gaske kuma na zo idan kin amince ko juma'an nan ban ƙi a kawo mini ke
gidana ba, kuma kada ki yi tunanin alaƙanki da Ummul-khultum, domin ban zo ba sai da duk suka amince
suka kuma yarda, dan Allah ki taimaki marayan Allah mai mata biyu, na jima ina dakon soyayyanki Hajiya
Ramla."
Mami tunda Abbaa ya fara magana ta ɗauke wuta na ƴan mintuna, zamowa tayi kaman photo kawai tana
kallonsa ta rasa ma me za ta ce ko me za ta yi, mamaki kawai ya tafi da ita a zaune, kallonsa take kuma ba
ta ko kiftawa, har ya gama magana bata iya mosta laɓɓanta ba balle ta ce wani abu, dan bata san ma me
za ta ce ba.
Abbaa murmushi ya sakarwa Mami ganin ta kafesa da kallo, a hankali ya ce, "Hajiya Ramla ke na ke
saurare."
Mami wani irin dogon ajiyan zuciya ta sauƙe, sai sannan ta kawar da idonta a kan Abbaa, wani irin
murmushi ta saki tare da buɗe baki ta ce...
# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735
#
# &
#
'YAR KARUWA
Officially
Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)
SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)
TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma ɗaukacin member's namu.
PAGE NAKU NE
Ashe zamu ga juna fan's club
Adamsy fan's club
Sarauta's Library
Asmabaffa official novels
Fan's masu Sharhi a wannan groups, Uwar batoorl na godiya, wannan page naku ne.
مهللا ىلص و ملس ىلع ديس ان هللوسر SAW
Ba editing ayi haƙuri da typing errors.
️ 56 _ 60
Mami ta ce, "Alhaji abinda kunnuwana ke jiye mini kana faɗa haka ne ko kuwa mafarki nake?"
Abbaa yana murmushin ya samu karɓuwa ya ce, "ba mafarki kike ba Mamin yara haka abin yake, nine dai
na ce a taimaka mini a tausaya mini kar na mutu da soyayyanki, kuma ko nan da sati kika buƙaci ayi biki to
a shirye nake."
Mami murmushin yaƙe wanda ya fi kuka ciwo tayi sannan ta ce, "ka yi haƙuri Alhaji ba wai na ƙi ka bane,
a'a aure ne kawai ba ya gabana har yanzu, wanda nayi a baya ya isheni."
Abbaa cikin damuwa yake kallon Mami ya ce, "Me yasa Hajiya Ramla? Ki faɗa mini gaskiya idan nine ban
miki ba ko kina tunanin wani abu ne akan mata na."
Girgiza kai Mami tayi tana mai iya ƙoƙarinta wajan ganin wannan magana bai sa ta yiwa Abbaa rashin
mutunci ba ta ce, "Ko ɗaya Alhaji, nice kawai ba aure a gabana."
Abbaa ya ce, "Duk ɗan sunna ai ba ya ƙin aure Mamin yara, nasan dole dai kina da wani dalilin naki, Allah
huci zuciyanki amma dai ina sonki, kuma zan baki lokaci dan jiran amsar da za ki bani, yanzu ban ɗauki
wannan a matsayin amsa ba, daganan har wata guda na baki duk ki yi shawara ki yi tunani, duk abinda kika
yanke ki sanar da ni, musamman in maganan bikin ne to sati guda kawai za'a yi Insha Allah sai ki fara shiri
tun kamun ki gama tunanin" Abbaa ya faɗa yana sakar wa Mami murmushi ƙayatacce.
Gululun baƙin ciki ne ya tokare Mami, amma da yake bata son dogon magana sai bata ce wa Abbaa komai
ba, har ya gama iya surutunsa ya fice, sai sannan ta ja wani dogon tsaki a fili ta ce, "Matarka bata ƙyaleni
ba kuma ba ta ƙyale yarinyata ba a haka zan aure ka? Ai ko auren zan yi ina da wanda nake ƙauna, shi ma
ban amince masa ba balle kai, saboda ba auren bane a gabana yanzu, kuma iya shekarun da ka ɗauka kana
dakon soyayyata haka Alhaji Mukhtar ya ɗauka ko na ce fiye da haka, dan tun Banafsha bata yi wayo ba ga
shi har ta zama budurwa, wa ma ya san ko kai naka na yaudara ne kawai, ni yanzu ba aure ne a gabana ba,
aurar da Faɗimatu na shi ne a gabana, Allah kuma ya bata miji nagari..." Haka Mami ta dinga mita da
surutu ita kaɗai kaman wacce ke yi da mutum a gefenta, ko kuma wacce aka kunnata, hhh ko da yake
Abbaa ne ya kunnata tunda ya taɓo mata inda ke mata ƙaiƙayi.
Banafsha da ta shiga ɗaki sanya pad, tun shigowan Abbaa ta ji, da har tana niyan fitowa amma tun daga
kalman Abbaa na Mami ta masa laifi har ya ce criminal case ne, sata ta masa tuni Banafsha ta fahimci me
Abbaa ke nufi, mamaki ne da kuma farinciki suka kuma kama Banafsha san da Abbaa ya furta abinda ke
zuciyansa, duk da a wani gefe tana tuna Umma da Ya Danish, amma abin ba ƙaramin daɗi ya mata ba,
kuma ya ƙara wa Abbaa kima a idonta, Abbaa shekara da shekaru yake maƙwabtaka da Maminta, yasan
abinda take aikatawa amma duk da haka yana sonta, kuma bai yi ƙasa a guiwa ba yau ya sanar mata
sannan a shirye yake da ya aure Mami akan lokaci, su Abbaa na hiransu amma Banafsha ke musu
murmushi ita ɗaya kaman ta buga tsalle, saboda haka kawai ita ta ji Abbaa ya fi kwanta mata akan Alhaji,
musamman da za su zama so close again da Umaimatynta, kuma tunda su Ummu sun amince su shikkenan
ba komai Allah ya sa Mami ma ta amince...
Tunanin Banafsha na Allah sa Maminta ta amince ne ya staya, sakamakon jin amsan da Mami ke bawa
Abbaa, saurin runste ido Banafsha tayi tana jin kaman ita ake sokawa wani abu mara daɗi a kirjinta,
gaskiyan Abbaa ne da ya ce duk ɗan Sunna ba ya ƙin aure, kuma a ganin Banafsha ko yana da dalili duk da
haka ƙin aure bai kamace sa ba, saboda yanda aka same shi ta Sunna, to bai kamata a ce shi ma bai da
wannan burin na samar da wasu ta Sunna ba, menene mastalan Mami kam? Allah ya hore mata baiwan
kyawun jiki, fiska, hali da na zuciya, sannan uwa uba abinda wasu sai sun haɗa da boka da malam suke
samu, to ita Allah ya hore mata a sauƙi wato farinjini, Mami na da jama'a sosai-sosai, amma Banafsha har
yau ta rasa ne ya sa mahaifiyarta ta zaɓi wannan rayuwan, dole tana buƙatan amsa, dole tana buƙatan jin
labarin wacece Maminta, asalinta, ƴan uwanta, mijin da take ikirarin ta yi auren farko ta gama, da duk
komai ma dangance da tarihin rayuwan baya na Mami, a hankali Banafsha ta lumshe ido ta ce, "Duk a ina
zan samo waɗannan amsoshin ya Rabbi, ka iya mini da kanka ya Hayyu ya Ƙayyum" ta faɗa kaman za ta
fashe da kuka(ni uwar batoorl na ce ni ke da amsoshin Banafshaty, ki biya kiji komai a_z).
Banafsha dai-daita nistuwanta tayi yanda Mami ba za ta gane ta ji abinda suka tattauna da Abbaa ba, ta
shiga palourn da sallama, jikin Mami ta koma ta kwanta tana cewa, "Mamina kaman muryan mutun na ji,
amma kamun na fito ban ga kowa ba ke ɗaya."
Mami taɓe baki tayi ta ce, "Eh! Abbanku ne ya zo tambayan ya jikinki, na faɗa masa da sauƙi, zan ƙira ki
kuma ya ce sauri yake, idan kin ji sauƙi sai ki shiga gidan ki gaishe sa ko."
Jinjina kai na yi a zahiri, a zuciyata kuwa mamakin Mamina nake, mamakin gaske ma kuwa, wato Mami ba
za ta ma faɗa mini ba, ana cewa yaran fari abokanan shawara ne kuma ƙawaye amma banda Mamina,
musamman a irin wannan magana, uhmn to Alhamdulillahi!, Duk da nasan maganan da ta yi ɗazu da ɗan
gaskiyanta na Umma bata ƙyaleta ba kuma ba ta ƙyale ni ba, amma wannan ba hujja ba ne, ko ni da ya
Danish yayi ƙoƙarin ƙeta mini mutunci na so mata auren Abbaa balle ita da bata san da wannan ba ma,
kuma Mami in za ta duba da kyau ni a ganina auren Abbaa ya fi mata auran Alhaji, tana son Alhaji kam
amma wani lokacin abinda muke so ba shi ne alkairi a gare mu ba, sannan tana maganan aurar da ni, a
muna zaune haka ba namiji shi ne take tunanin wasu za su zo neman aurena wajanta tana mace? Ai babu
mai aurar mara uba, ana dai auran wacce/wanda ba su da uwa amma banda marassa uba, saboda da uba
ake ado ba rigar aro ba, ni sai yanzu ma Malam Abbo ya faɗo mini a rai, Mamina bata nadama a irin
wannan rayuwan ina na isa na yi maganan aure, shiyasa ma ni ban saka wa rai na zan yi aure ba, tunda
haka Mamina ta zaɓa sai mu zauna duka haka, niyan nayi shiru nayi mu je a haka a bansan abinda ke tafiya
ba, amma zuciyata ta ƙi ƙyaleni nayi shiru, numfasa nayi a hankali kaman munafuka na ce, "Mamina me
yasa kike yi yin haka?" Na faɗa kaman zan yi kuka.
Mami kallona tayi ta ce, "Me nayi Banafshan Mami?"
Gyara kwanciya nayi a cinyan Mamina na ce, "Dan Allah ki yi haƙuri Mami idan abinda zan faɗa zai ɓata
miki rai, gaskiya ce komin ɗacinta faɗansa yana da kyau, Mami me ya sa za ki ce ba aure a gabanki? Mami
me yasa kike nunawa mahaliccinki ba za ki cika sunnan ma'aikinsa Annabi SAW ba, Mami duk mace ko
namiji da suka kai aure suka mutu ba aure fa Allah ma tausayinsu yake, Mamina nasan kin sani aure ni'ima
ne kuma rahama ne, Mami Allah ya azurtaki da farinjini wanda wasu ma sai sun nema da kuɗi sun saɓa ma
Allah sannan suke samu, Mami har yanzu taurarinki suna haskawa ba su disashe ba, me yasa ba za ki yi
aure ba tun yana binki, kamun ya zo yana guje miki kina bin sa, Mami a haka akwai mai aure na ban da uba
ina ƴar mace? Mami...." Maganan baki nane ya maƙale sakamakon wani irin stawan da Mamina ta daka
mini, wanda ya sa na miƙe zaune babu shiri a rikice.
"Banafshaaaa!!!!" Haka Mamina ta ƙira sunana a stawa ce.
Tura baki nayi tare da runste ido na inma duka na Mami za tayi sai dai ta kashe ni, amma sai na faɗa mata
gaskiya, ci-gaba nayi da magana ba ruwana da hucin da Mamina take yi, cewa nayi, "Mami ranan Alhaji ya
ce miki Amaryansa kika ɓata rai, ya ce za ki haifa mini ƙanne kika yi fushi, Mami yau ina ji Abbaanmu ya ce
zai aure ki nan ma kika ce ke ba aure bane a gabanki, Mami menene damuwanki dan Allah? Mami ya kike
so a miki, duk da Alhaji mutum ne da yake rayuwan da bai dace da ke ba amma ya nuna yana ƙaunanki a
haka, kuma zai aure ki, akwai soyayyan da ta fi wannan? Abbaa ya san ki shekara da shekaru, ya san duk
abinda kike da wanda kike aikatawa na ba dai-dai ba amma hakan bai dame sa ba, bai hana sa ƙaunanki
ba, yana sonki ya danne zuciyarsa, yanzu ya kasa haƙuri kuma ya furta miki kin ce ba haka ba ya kike so
Mami? Wani irin masoyi kike son samu sai ki kawo maganan aure a starinki? Mami kina tuna mutuwa
kuwa? Kina tuna za mu mutu ba tare da mun san yanzu ne ko anjuma ko kuma yaushe ba? Mami ita fa
mutuwa ba ta alert a ko wane yanayi za ta ɗauke ka idan lokacinka yayi, Mamina kowa burinsa da fatansa
ƙarshensa ya fi farkonsa kyau ya kuma gama da duniya lafiya yana mai imani mumini amintacce, Mami ke
me yasa bakya fatan hakan? Mami dan Allah ki yi aure, wallahi idan ba za ki yi aure ba to kibar cewa aurar
da ni ne damuwanki kuma burinki, sabida babu mai aure na a wajan mace, kuma ko akwai ma to ba auran
zan yi ba, ba zan jure a goranta mini ina gidan mahaifiyata a ƙira ni da ƴar karuwa, sannan a ce nayi aure a
goranta mini a ƙira ni da ƴar mace ba, Mami kina da dangi, kuma nasan ina da uba tunda mutum ba ya
haifan yaro shi ɗaya, amma duk kin rabamu da su kin guje su kin wastar da su saboda me Mami? Ni