Showing 105001 words to 108000 words out of 111817 words

Chapter 36 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf

Advertisement

16 Aug 2025

4045

ta gasƙata abinda
kunnenta ke jiyo mata, Alhaji yana murmushi ya ce, "Amaryan Mukhtar a bani aron mintuna biyar kawai,
yanzu zan ƙira ki."
Mami a nata ɓangaren cikin soyayya ta kashe wayan, tana jiransa ya gama abin da yake yi.

Alhaji yana sakar wa Hajiya Sa'adatu murmushi ya ce, "Hajiya ga waje zauna, Uwar gida ran gida daman ina
son yin magana da ke, amma naga kina busy, tun da ga ki to bari mu yi maganan yanzu."

Hajiya Sa'adatu wani irin banzan, malalacin, arnen, ɗan iskan kallo take bin Alhaji da shi, wani irin masifa
ne da bala'i ke cin ta, nuna Alhaji ta yi da yasta rai a ɓace ta ce...


MASU DARAJA HABIBTIES A GIGITA NI DA COMMENT'S NA HAPPY SALLAH, DAN NASAN KUN YI KEWAN
BANAFSHA DA GASKE.


# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735

# ������
# � &
# ���






'YAR KARUWA

Officially




Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)



SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)


TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma ɗaukacin member's namu.


PAGE NAKU NE
Dr seeyath
Habiba Muhammad yusuf
Fatima abubakar wakili
Annomariama

مهللا ىلص و ملس ىلع ديس ان هللوسر SAW





️ 96 _ 100


Hajiya Sa'adatu a hasale cikin ɓacin rai ta ce, "munafuki, algungumi, mara amana, butulu kawai, to me za
ka ce mini bayan abinda idanuwana suka gane mini, da wan da kunnuwana suka jiye mini, Alhaji Mukhtar
ni za ka wulaƙanta? Ni za ka tozarta? Kishiya dai, aure fa, to wallahi baka isa ba, ba'a haifi uwar mai haifa
mini kishiya ba, ni Sa'adatu na fi ƙarfin kishiya, tun wuri ka nistar da hankalinka waje guda ka dena wannan
ɓaɓatun shirmen dan wallahi ban yarda ba, ba zan taɓa yarda ba, shekaru har talatin da ɗori da aurenmu,
sannan sai yanzu rana staka ka stira ƙara aure, wai zaka mini kishiya, to ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa."

Alhaji murmushi yayi, dan ko ɗaya bai ji zafin kalamanta ba, sannan ya stammani fiye da haka ma daga
gareta, tun da ya san masifanta akan kishiya, amma bai zaci abin zai dameta haka ba, tun da dai ya ga ba
wani damuwa ta yi da shi sosai ba.

Hajiya Sa'adatu hargagi ta fara da masifa da bala'i, tun bai ma yi magana ba, ta inda take shiga ba ta ban
take fita ba, faɗi take bai isa ba, kuma za ta dawo masa da kuɗinsa dan bai yi arziƙin da zai mata kishiya ba,
Alhaji dai ko ci kanka bai ce mata ba, murmushi kawai yake yi, yana shiru kaman wanda uwar sa ke masa
faɗa, har ta gama masifan ta kuma koma kuka tana faɗin, "Amanata za ka ci Alhaji? Tozarta ni za ka yi? Me
na kasa maka? Ta ina na gaza? Mene bana maka? Alhaji duk ƙawaye na kowa shi kaɗai a gidansa, amma ni
me na maka za ka mini haka? To wallahi ka ji na rantse baka isa ba Alhaji", tana surutunta tana kukanta har
ta gaji ta fice a ɗakin, tana komawa nata ta fara ƙiran ƙawarta Hajiya Turai, suka haɗa conference call da
Hajiya bushira, nan ta labarta musu abin da ta gani da wan da ta ji, duk abin da ke faruwa a taƙaice ta juye
musu.

Nan fa suka fara famfa ta, akan tabar kuka, indai aure ke to Alhaji bai isa yayi shi ba, za su ɗau mataki, a
take Hajiya Sa'adatu ta share hawayenta, sai da suka gama kiste-kistensu, sannan suka yi sallama, ta bi
lafiyan gado hankali kwance ta yi baccinta.

Alhaji kuwa tana fita ya sauƙe ajiyan zuciya tare da murmusawa, ya ce, "mata ikon Allah, ɗan Adam
kenan", wayansa ya fidda ya ƙira Mami suka ci-gaba da wayansu har dai suka yi sallama.

Hajiya Sa'adatu tun daga washe-gari ta fara binciken ta, a in da Alhaji ke neman aure, amma sam-sam babu
alama dan bata kawo Adamawa a ranta ba, ana tafiya har aka ƙara cinye sati guda, aure saura sati, amma
ba ta in da bata bincika ba, ba labari, ga shi Alhaji ko fita ma baya yi balle ta ga ko wajan matar zai je,
watarana idan ya fita kuma daga ƙarshe wajan abokansa ko kuma business nasa, ganin abu na ƙara
mastowa dan haka yau ma samun Alhaji tayi cikin masifa ta ce, "ƴar gidan uban waye za ka aura Alhaji, da
na bincika duk Kano babu ita ba labarinta, ai nasan ba zai wuce munafurci ne ya hanaka neman aure a
Kano ba saboda kada na sani."

Alhaji murmushi yayi ya ce, "Da kin kwantar da hankalink Sa'adatu, ai kina tambayana zan faɗa miki ba sai
kin bincika ba, da farko dai ina mai baki haƙuri, kin sani shi aure nufi ne na Ubangiji...."

Kamun Alhaji ya ida maganansa, tuni ta tari numfashinsa, ta ce, "Kuma da son ran ka ba."

Murmushi ya kuma sakar mata ya ce, "sosaima Hajiya Sa'adatu, da son rai na zan yi auren nan in Allah ya
yarda, kuma ina addu'a da fatan Allah ya sa na dace na samu wacce za ta kula da ni."

Hajiya a ƙufule ta ce, "Wato ni bana kula da kai? Ai maza daman ku baku da godiyan Allah, musamman a
abin da ya shafi mata, yanzu idan ba butulci ba me na gaza? Me na kasa? A me na tauyeka ko kuma na
rage ka Alhaji."

Zama Alhaji ya gyara tare da numfasawa ya ce, "An zo wajan, ranan kin mini tambayan nan amma baki
bani daman amsawa ba, yanzu kuma ina ƙoƙarin baki amsa sai ga shi kin maimaita, hakan yayi Masha
Allah, da farko Hajiya Sa'adatu ina so ki sani, ba wai faɗa miki a iya me kika gaza zan yi ba, domin a komai
kin rage ni, a komai kin kasa faranta mini balle ki kula da ni, abu mafi muhimmanci shumfiɗana, tsakaninki
da Allah Hajiya yaushe rabon da ki zo gare ni? Idan na nemeki me kike faɗa mini, ba kin gaji ba? Ban taɓa
hanaki kasuwancinki ba duk da yana taimakawa wajan rashin kula da ni, amma ke kin taɓa lura da hakan
balle ki gyara? Ba ruwanki da yaushe zan dawo, ina zan je, kwana nawa zan yi, mai nake buƙata, idan na
dawo ya ina buƙatar ganinki ko da ba za ki bani komai ba, duk babu ruwanki da wannan Sa'adatu, ko ƙarya
na miki?"

Hajiya Sa'adatu cikin ɓacin rai, da rashin son gaskiya ta ce, "Ni ban ce ƙarya ba ne, amma har da ƙari a kai
Alhaji, yanzu tsakani da Allah da girmanka da girmana, sai mun tsaya wani shimfiɗa-shimfiɗa kaman yara,
kuma naga daga ni har kai kowa business yake yi, hakan bai ishe mu ba Alhaji."

Murmushi Alhaji yayi ya jinjina kai, ya ce, "Tabbas nikam hakan bai ishe ni ba, domin na fi buƙatan nistuwa
fiye da kuɗi, tun da Allah ya hore mana ya sa muna da wan da za mu rufawa kan mu asiri ko daga gida
muke, har mu taimaki wasu ma, to kin gaza a ko ina musamman a nan ɓangaren, saboda ke kin sanni yan
da nake ko wani saurayin albarka, bana jin zan girma wa samun nistuwa a shimfiɗa, ki kuma godewa Allah
da rashin kulawanki bai yi tasiri ba, Allah ya taimake ni ya ceceni daga faɗawa hallaka, duk da na kusa
stunduma cikin harkan neman mata, amma albarkacin wannan baiwar Allah da zan aura sai abun ya tsaya,
to ki gode wa Allah ki gode mata."

Hajiya Sa'adatu wani irin malalacin kallo ta ke jifan Alhaji da shi, idanu jajazir ta ce, "Karuwa za ka aura?
Kuma daman da girmanka sai ka bi mata?"

Girgiza kai Alhaji yayi ya ce, "Ba karuwa ba ce, da mutuncinta da ƙimanta da komai, kuma idan Allah ya
yarda aurena zai ƙara suturtata, domin ta fi wasu matan auren da suke kasa kula da mazajensu har su
sanya su fita su nemi matan banza, sannan akan abin da ya zama ƙaddarana ban da wani girma, sannan
akan abin da ya shafi buƙatuna nan ma ni ba kowa bane, na dai godewa Allah da mummunar ƙaddara bata
same ni ba."

Hajiya a hasale ta ce, "Wallahi bata fi ni ba, kuma idan dan wannan ne zan gyara ka bar maganan auren
nan."

Alhaji murmushi yayi ya ce, "Na riga da na faɗa miki ko ta ina kin tauyeni, da iya wannan ne da sauƙi nima
zan iya haƙuri, Sa'adatu kin cire mahaifanki tun da kika haifi Majeeder, ko ƙarya ne?"

Hajiya Sa'adatu idanuwa ta zaro, mamaki take akan ya aka yi Alhaji ya sani, lallai allura ta tono garma.

Murmushi Alhaji ya kuma yi, nan ya faɗa mata yan da aka yi ya sani, dan yasan ba zai wuce mamaki take yi
ba, cewa yayi, "kuma ni ina son haihuwa, Allah ya bani arziƙi alhamdulillahi, da a ce rashin haihuwanki na
Allah da Annabi ne to ban da mastala shi ma, zan haƙura na gode wa Allah da biyun da ya bani, amma ba
na Allah da Annabi bane, ke kika kista abinki, a yanzu ma na gode wa Allah, kuma ina addu'an Allah ya ma
biyun albarka, amma idan da ƙari ina addu'an Allah sa matata ta haifo mini dozen, Sa'adatu wajaje da
yawa kin kasa kaman yan da na faɗa tun farko, Sa'adatu fita kike ki hau jirgi ki yi tafiyanki babu izinina, idan
kin dawo ma ba za ki bani haƙuri ba, kwata-kwata ma bakya tunani da jirgin da motan, duka ƙarfen nasara
ne ba su da tabbatas, za su iya kai ki ga hallaka ba tare da kin nemi yafiyana ba, Sa'adatu kin kasa bawa
yarana tarbiya balle ki kula da su, guda biyun ma, Sa'adatu ba abinda kika sani kuma ya dame ki sai
business naki, ya isheni haka ba zan iya ci-gaba da haƙuri da halinki ba, aure zan ƙara, kuma matar Yar

Adamawa ce, ba a nan Kano take ba, idan kina so ma har da address nata zan baki, domin ko me za ki yi ba
za ta fasa aurena ba, tana so na kaman yanda nake ƙaunarta, Sa'adatu kawai kina zama da nine kina mini
kallon bansan me nake yi ba, saboda shirun da nake yi sai kike tunanin juyani kike yi, to ki sani bana son
tashin hankali ne, domin idan na bari rai na ya ɓaci da ke, to zan ɗau mummunan mataki, dan haka ki
kiyaye kawo duk wani mastala a wannan biki, idan kin so ki zauna lafiya ki kuma gyara halinki, idan kuma
kin so sai ki yi kishiyan hakan, amma ina mai tabbatar miki matakin da zan ɗauka ba zai mana kyau ba ni da
ke", Alhaji na gama magana rai a ɓace ya miƙe ya fice a gidan gaba-ɗaya.

Hajiya Sa'adatu a maimakon ta yi nadama, ta ɗau niyan gyara halayenta, ta kuma rungumi zuwan Amarya
hannu bibbiyu, sai dai inaa, sam ƙara rikicewa tayi, ko kaɗan bata yi nadaman abubuwan da ta yi wa Alhaji
Mukhtar ba, ba abin da take sai kumfan baki kan cewa ba za ta bari ayi auren nan ba, idan ma ta bari, to ba
za ta bar matar ta zauna ba dole ta koma in da ta fito, Alhaji nata ne ita kaɗai.

Alhaji tun da ya fice rai a ɓace, gidan wani abokinsa ya je, amma sai da ya seta kan sa, dan ba zai sanar da
sirrin gidansa ba, cikin fara'a suka din ga hira, abokin nasa sai zolaya yake masa, wai yanzu ne zai san daɗin
aure, mata biyu duniya ne, idan kana zaune da mata ɗaya ba abin da ka sani tukunna(kun ji munafukan
abokai masu ɓallo mana ruwa).
Alhaji Mukhtar yana tare da abokinsa, ƙiran Bunayd ya shigo wayansa, ɗauka yayi yana murmushi ya ce,
"Air Chief Marshal."

ACM Bunayd a nasa ɓangaren murmusawa yayi ya ce, "Papi Ango ka sha ƙamshi, ya shirye-shirye? Ina
Mom fa, ina hanya zuwa mata danne ƙirji."

Dariya Alhaji yayi ya ce, "Ubanka General, ba mu gayyaceka ba, tun da ka yi naka gudumawan ya isa ba sai
ka zo ba, idan kuma so kake ka zo a stine maka shikkenan, ni ba ruwana."

ACM kiston kansa ya shafa ya ce, "wai da zan kawo lefe ne, da kuma na danne ƙirji, kasan Momsee har da
Mom ta haɗowa wai na faɗan kishiya."

Alhaji dariya yayi ya ce, "Allah shiryeku kai da iyayen naka, yanzu dai maganan lefen nan a bar sa sai an
kawo Amarya washe-gari, amma idan su Maman naku Huraira za su taho bikin za su iya zuwa da na Hajiya,
kai kam ban ce ka zo ba, sai ɗaurin aure mu haɗu a Adamawan."

Waya Alhaji yayi da yaron nasa, kaman ko yaushe cikin soyayya da annashuwa, sai da suka gama suka yi
sallama, ya kashe wayansa ya dubi abokin nasa ya ce, "kana ji na da fitinannen yaron General ko."

Dariya Alhaji Idris yayi ya ce, "Ai ni a rayuwata wannan ɗan gidan General ɗin burgeni yake, ga shi dai idan
aka kallesa kaman an ga burtai a filin yaƙi rai a haɗe, amma mu'amalansa da jama'a, da halayyansa sai ina
jin ina ma yaronane."

Murmushi Alhaji yayi ya ce, "ai Bunayd sai addu'an shiriya kawai, sam fa baya ji, wannan da yaronka ne ma
ba za ka iya masa ba, wannan halinsa sai irin ubansa General ɗin."

Alhaji Idris ya ce, "Amma dai magana kake Alhaji Mukhtar, ai kuma Bunayd da jin magana da biyayya duk
ba wanda aka bar sa a baya, a irin zamanin nan ka samu ɗan uwa irin General Sufyan ya riƙe maka yaro da
amana haka ya masa tarbiya, ai sai ɗaɗɗaya."

Alhaji murmushi yayi tare da sanyawa ƙanin nasa da yaron nasa albarka, sannan ya ce, "Allah dai ya shirya
mana zuria'a ya kuma musu albarka."

"Ameen", faɗin Alhaji Idris yana dariya, ya ce, "Wato shi Bunayd har da wata hidima yayi, ah lallai
mahaifiyarsa ta sani zai gane kurensa."

Alhaji tuni ya mance da wani damuwan da Hajiya Sa'adatu ta cusa masa, hira suka din ga yi da Alhaji Idris
abokinsa, suna dariya, rabi da kwatan hiran akan Bunayd ne da kuma batun auren Alhaji, har Alhaji Idris ke
faɗin da yana da yarinya mace babba to da ya bai wa, Bunayd aurenta.

Safiya ta yi ta wuce, dare ya zo ya mamayeta, sannan gari ya waye, a haka ake tafiya yau da gobe har dai
aka shiga satin biki, in da yau Alhamis, mutanen Lagos suka tattaro gaba-ɗaya har General da yaronsa,
Suhail da Nabeel ma duk sun zo, an kamo hanyan Kano da su, kayan lefe ma duka an taho da shi, na
Amarya da na Mom.
Jirginsu ya sauƙa da wuri, in da motoci suka zo jidansu, komai na gama zama ready, motoci suka ɗau
hanyan Railway estate, suna isa kuma a ƙofan sashin General da yake a gyare a kimste suka ya da zango,
ma'aikatan ne suka jidi akwatunan suka shiga da su ciki.

Sai da suka sha ruwa suka huta, sannan Momsee ta sa ma'aikatan suka ɗau iya na Mom suka yi part nata
da shi, ita kuma Momsee ta bi su a baya.

Da sallama suka shiga sashin Alhaji, Mom na hakimce a kujera da ƙawayenta, ba wanda ma yayi gigin amsa
sallaman, ma'aikatan dai suna ajiyewa suka juya abin su, Momsee ce ta ƙarisa ta samu waje ta zauna,
ganin duk babu wanda ya bi ta da kallon rashin kirki balle na arziƙi, a hankali ta ɗaga musu gaisuwa, nan
ma shiru ba wan da ya ce komai.
Momsee miƙewa tayi tare da cewa, "To Hajiya ga kayan faɗan kishiya, muna fata da addu'an Allah baku
zaman lafiya da zaman haƙuri", tana gama faɗa ta fice abinta, bata staya sauran ko A daga bakinsu ba.

Hajiya bushira ce ta ja wani dogon tsaki ta ce, "shegen iyayi, shishshigi shiga abin da bai shafe ka ba da
Ghana-most-go."

Mom ta ce, "Munafuka ba, wai ita ga ta tagari, tun da ita ƴar uwarsu ce, auren dangi ne, shi ne za ta dinga
yi wa mutane shishshigi."

Hajiya Turai murmusawa tayi tare da mikewa ta buɗe akwatuna, zaro ido tayi ta kama baki ganin irin arnun
kayan da ke ciki, dan ko lokacin auren Hajiya Sa'adatu ai ba'a saka mata irin haka a lefe ba, nan baƙin ciki
ya rufeta, amma sai ta yabi kayan, Hajiya bushira ma jefa bakinta tayi suka dinga kallon kaya suna koɗawa.

Mom kuwa haushin su take ji kaman ta shaƙe su, ko abu ɗaya bai burgeta ba, haushin komai take ji, ƙarshe
cewa tayi su tattara kayan a gabanta ko ta cunna masa wuta, a haka suka sa masu aiki suka kai ɗakin Mom,
tana faɗin bata so, duk wacce ta ga abin da ya mata a ciki ta ɗauka, ita bata son kayan.

Hajiya Turai ta ce, "To wannan shegun kayan wa ke na faɗan kishiya, wa kuma ya san ita munafukar
Amaryan taki wani irin ƴan banza kaya aka mata, cigaba suka yi da hura Hajiya Sa'adatu, ita kuma sai
karɓan iska take, ta cika ta baste ta yi fam kaman wacce ta ji yist, tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login