Showing 93001 words to 96000 words out of 111817 words

Chapter 32 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf

Advertisement

16 Aug 2025

4037

tare da lumshe ido na cikin ƙarfin hali na ce, "ka yi haƙuri da abin da zan faɗa idan zai ɓata maka rai,
amma shi ne iya abinda nake buƙata."
Alhaji murmushi yayi cikin yabawa da hankali irin na Banafsha ya ce, "ina sauraranki Banafsha."

A hankali na ce, "Alhaji dan Allah dan darajan Annabi da ƙur'ani, ka taimaka ka auri Mamina, dan Allah ku
bar irin wannan rayuwan da girmanku, mu yaranku ba ma jin daɗi musamman ma ni, kuma nasan idan su
Majeeder ma za su ji haka ba daɗi zai musu ba, dan Allah Alhaji ku mini wannan alfarman, wallahi shi kaɗai
ne abin da nake buƙata daga gare ka, har ma da Mamina", ina gama magana kuka ya ƙwace mini, amma
na danne sautin kukan dan kada Mamina da ke kitchen ta jiyo muryana.

Alhaji aniyan zuciya ya sauƙe tare da kallona, yana murmushi ya ce, "In Allah ya yarda Banafsha zan auri
Maminki, ke dai ki taya ni da addu'a da kuma shawo kan ta, Maminki ce sai a hankali amma in Allah ya
yarda wannan karon zan dage kin ji, na miki alƙawarin yin abinda bai fi ƙarfina ba, dan haka auren Ramla
bai fi ƙarfina in Allah ya hukunta hakan, kema kuma ina son ki daina saka damuwa a ranki, ki kuma cigaba
da yiwa mahaifiyarki biyayya."

Jinjina kai nayi cikin gamsuwa da maganansa, na gode sosai sannan na shige ɗakina, wanke fiskana nayi,
sannan na buɗe ledan da Alhaji ya bani, kwali ne a ciki, na kuma buɗe wa, ganin wani ranstasten
kyakkyawan system tuni na stala ihu ba shiri, ihun nawa har ya jawo hankalin Mamina ta shigo da sauri a
firgice tana faɗin, "lafiya Banafsha? Menene ya saka ki ihu?"
Cikin farin ciki na nuna mata system da ke hannuna, ita ma da mamaki take bi na da kallo ta ce,
"Banafshaaa ina kika samo computer?"

Ina murmushi na ce, "Alhaji ne ya bani yanzu, wai shi ne kyauta na", ina faɗa na rungume Mami cikin farin
ciki, ina faɗin ta tayani gode masa.

Abubuwan cikin ledan na ƙarisa cirowa, nan kuma wani sarƙa ya faɗo da ɗan kunnensa da zobensa, da
abun hannu, masu shegen kyau da ɗaukan ido, Mami da ke staye, waro idanuwa tayi ta ce, "Gold dai?"

Ai ban staya ba, na fice palourn, amma na samu Alhaji baya palourn yana cikin ɗakinsa, komawa nayi ɗaki
cikin farin ciki, ina kallon kyautan da Alhaji ya mini, sarƙan gold, system, ga kuma wani haɗaɗɗen dogon
riga wan da kana gani kasan ya ci uban kuɗi shi ma, kayan ma dai ka san ba na Nigeria ba ne, farinciki
kaman nayi yaya.
Mami komawa tayi ta ƙarishe aikinta, ta shirya sannan ta shiga ɗakin Alhaji, samunsa tayi yana waya da
yaronsa, murmushi tayi tare da zama a ɗan nesa da shi, har sai da ya gama, ya dubeta yana murmushi ya
nuna mata gefensa, amma Mami sai ta gyaɗa kai kawai, cewa ta yi, "Alhaji sannu da hidima mun gode
Allah saka da alheri."
Murmushi Alhaji yayi ya ce, "Kada ki gode mini Ramla, dan kin cancanci fiye da haka a wajena, kuma duk
wani wan da ya shafe ki zan masa fiye da haka, Ramla soyayya nake miki na tsakani da Allah, ranan na iso
ana cikin yanayi mara daɗi ne shiyasa, amma ke ma ga naki staraban na Egypt ɗin", Alhaji ya faɗa tare da
miƙa wa Mami wani jibgegen leda.

Amsa Mami tayi, tana jin kaman ta rungume Alhaji, amma tasan ba zai so haka ba dan yan da yake gudun
abinda zai saɓawa Allah, ita kuma ba za ta masa abin da bai so ba, dan haka cewa tayi, "To ka zo mu karya
rankashidaɗe."

Alhaji miƙewa yayi da murmushi ya bi bayan Mami, ni ma Mami ƙirana ta yi, duk muka karya, na godewa
Alhaji sosai, amma ya nuna ba komai nima ƴar sa ce.

Mami kuwa kayan a Alhaji ya kawo mata, dogayen riguna ne na Egypt masu shegen kyau kusan kala biyar,
sannan da wani haɗaɗɗen waya ta yayi Redmi, ga turaruka, ita ma har da sarƙanta na diamond, da
takalma, sai kuma wasiƙan soyayya da ya jefa a ciki, Mami duk da ba wannan bane karo na farko da Alhaji
ke mata kyauta, amma farinciki kaman ta yi kuka, musamman kalaman da yayi amfani da su a wasiƙan
nasa.

Washe-gari Lahadi, muna zaune da Alhaji da Mami sai aka mana sallama, Alhaji ne ya fita ganin mai
sallaman, gaisawa suka yi, da ya faɗa masa ya zo gaishe da Mami ne sai ya masa iso, tun da ya shigo nake
kallonsa da mamaki, Ya Danish a cikin gidanmu, yau wace rana, amma sai na dake na miƙe na shige ɗakina
ban ce masa ko sannu ba.
Mami cikin fara'a suka gaisa da Ya Danish, ya tambayi jikin Banafsha ta amsa masa da sauƙi, suka gaisa da
Alhaji kuma, sannan ya ajiye ledan da ya kawo da kaya niƙi-niƙi na dubiya, sallama ya yiwa Mami ya tashi
zai tafi, sai Mami ta ce, "Banafshan tana zuwa ko."

Ya Danish a waje ya staya jirana, ni kuma ina ɗakina kwance ina danne-danne a system na(su Banafsha
duniya sabuwa, ƴan gayu ƴan uwan masu nuƙud), Mami shigowa tayi da sallama, tun da na kalleta na tura
baki dan nasan ba zai wuce ta ce naje ba, ai kam hakan ne kuwa, fiska a haɗe ta ce, "kin ga mutum kin
tashi kin gudo ɗaki, ko gaisuwa babu kuma kin san wajanki ya zo ko, to maza kamun na ɓata miki rai ki
tashi ki je waje yana jiranki, kuma idan kika amsa rashin kunya sai na saɓa miki, yarinya hankali sam-sam
babu, wa ya faɗa miki ana wulaƙanta ɗan adam, maza tashi ki wuce", Mami na gama magana ta fice tana
ƙwafa.

Ni kuwa tura baki nayi, sannan na miƙe, mayafi kawai na yafa na fice, fuuu! Haka na wuce su Mami a
palour na yi waje, a cikin haraban gidan mu na tarar da shi, ƙara haɗe fiska nayi sannan na ƙarisa wajan da
ya ke tsaye, ko kallonsa ban yi ba balle ya sa ran zan masa magana.

Ya Danish cikin damuwa ya ce, "dan Allah kiyi haƙuri ki yafe mini, haka nan ki kulani Banafsha, wallahi da
gaske nake son ki, kibar tunanin wani abu, idan kuskuren da na aikata rana ne ma wallahi ba da niya na yi
ba, kuma ko da ace Abbaa ba su iso sun same mu haka ba wallahi ba zan iya ƙeta wa wata mutunci ba
balle kuma ke, ki yi haƙuri."
Tsaki na ja na ce, "Dole ka ce ba da niya ba tun da dole aka saka ka, ka yage mini hijabi, ka haɗa jikinka da
nawa, har da bakinmu ka haɗe, sannan a haka ka ce ba niya? Ka dai ji baiwa ne a jikin sai ka ga gwanda ka
yaudareni ka aure ni ko, to bari kaji ko maza sun ƙare ba abinda zan yi da kai, ballema ina da wanda nake
so, kuma kwanannan za ka ji an yi aurenmu."
Danish ji yayi kaman ta wasta masa ruwan zafi ne a zuciyarsa da wannan kalaman, kaman zai yi kuka ya ce,
"Wallahi sharrin zuciya ne, saboda irin kalaman da kike faɗa mini.."

Saurin dakatar da shi nayi na ce, "nake faɗa maka ko kake jifana da su? Ko ka mance ka ce mini ƴar iska mai
bin maza? Ko ka mance cewan da ka yi bana da abin da za ka taɓa? A haka ka yi kokarin ƙeta mini mutunci
ka kuma zo yanzu da niyan aurena wai a faɗanka, duk ka mance abin da ka faɗa ne? Ta ina naga abinda za
ka taɓa? Sannan ka ƙirani da mara tarbiya, shashasha ƴar iska, ka sanya hannunka a jikina kuma da sunan
duka, ban da duk waɗannan ma abu mafi muni da na stana a duniya, sunan da bana son sa bana ƙaunarsa,
sunan da yake ƙaddara ga rayuwata, ka ƙira ni da shi Danish, ƳAR KARUWA MARA TARBIYA, ka faɗa mini,

sannan a haka kake tunanin na so ka har na aureka? To tabbas ka yi wa kanka ƙarya, dan na staneka! Na
staneka! Na staneka! Bana ƙaunarka bana son ka, bana son kallonka, ko mai irin sunanka bana ƙauna, kai
ka sa na stani maza na stani aure, amma Alhamdulillahi yanzu da nayi gwanina mai ilimi da sanin ya
kamata to naji ina son aure kuma zan aure sa."
Ya Danish runste ido yayi kaman wan da aka kikkifawa mari, guiwansa ya saka a ƙasa ya ce, "Duk abinda
kika faɗa ba sharri na faɗe su kuma na yi su, baki ƙara komai ba sai ma ragewa da kika yi, kuma nasan na yi
ba dai-dai ba, ban kyauta ba, bayan haka uwata ta yiwa mahaifiyarki illa, dan Allah da Manzonsa ki yafe
mini, dan darajan Annabi ki yafe mini, duk abin da na miki kuma idan ba ki manta ba, babu wanda baki
rama ba a take ma kuwa, sannan ga shi Allah ya ɗaura mini soyayyanki, ki yi haƙuri Banafsha, ina sonki ina
ƙaunanki dan Allah, ko da baki aure ni yanzu ba, zan zauna dakon jiranki har idan Allah ya sa ke rabona ce,
to mijin zai bar mini ke ko kuwa zai mutu na aureki."

Jikinane yayi sanyi saboda yan da ya haɗa ni da Allah da Annabi, wan da ya halicce ni da kuma wan da aka
halicci dubiya baki ɗaya saboda shi, Allah ya wuce komai ya wuce abin wasa, sannan kana ɗan Adam bai
kamata a ce ka yi abu dan Allah ko Annabi ka ƙi yi ba, sannan na tuna maganan Mamina na ranan akan
haƙuri, dan haka ajiyan zuciya na sauƙe tare da faɗin, "Na yafe maka duniya da lahira, komai kuma ya
wuce, amma dai ka sani ina da wan da nake so, kuma in Allah ya yarda idan ya aure ni mutuwanma tare da
shi zan yi", ina gama faɗan haka na juya na shige gida.

Ya Danish ajiyan zuciya ya sauƙe jin na yafe masa, sai ya ji wani abu mai nauyi ya sauƙa masa a zuciya,
domin kuwa tun ranan da yayi ƙoƙarin ƙeta mata mutunci shikkenan abin yake damunsa, tun da yasan nan
gaba shi ma uba zai zama.

Ni kuwa ina shiga gida na wuce ɗakina, ko ta kan ledan da Mami ta nuna mini ban bi ba.

Alhaji dai ya kasa haƙuri sai da ya yiwa Mami magana Danish, faɗa masa komai ta yi bata ɓoye masa ba,
har da akasin da suka samu da mahaifiyar sa, da kuma son ta da Abbaa ke yi, Alhaji ya ji kishi jin wani na
son Mami har ga yaronsa ba son Banafsha, sai ya ji ina ma shi da yaronsa ne za su mallaki Mami da ƴar ta,
amma dai Alhaji sai ya ɓoye bai nuna ba, addu'a yayi kawai da fatan alkairi.
Ya Danish a ranan da yamma-yamma ya koma wajan aikinsa, cike da ɗimbin soyayyan Banafsha,
musamman ma da ta ce ta yafe masa.

Bayan sallahn isha'i kuma sai ga Malam Abbo, Alhaji da yake ya sheda sa shi kam, gaisawa suka yi, suka
gaisa da Mami sannan suka bamu waje, sai da na ɗan shafa kwalli da man baki sannan na fito, cikin fara'a
muka gaisa da Malam Abbo, nan ya fara baza hajar soyayyansa yanda ya saba, kalamai masu shiga jini da
jijiya, su tsaga ƙashi da ɓargo su kai maka har ƙwaƙwalwanka, gaskiya wan da ya ce ustazai ba su iya
soyayya ba sai wa'azi to gaskiya yayi kuskuren fahimta, gaba-ɗaya Malam Abbo idan yana kalamansa tafiya
yake da tunanina.

Malam Abbo ya jima sannan ya mini sallama ya tafi, ni kuwa na shige ɗakina cikin dimbin tunanin Malam
Abbo da soyayyar sa da nake ji yana kama ni.


Washe-gari Litinin, Alhaji sai da ya ajiye ni a makaranta sannan ya wuce zai koma gidansa, wannan karon
bai jima ba saboda yana da shungulla, ina makaranta Malam Abbo ya zo suka gaisa da Mami ya faɗa mata
batun tafiyanmu Yola musabaƙa, Mami ta yarje ba komai bayan ta musu addu'an nasara, da kuma roƙon a
kula musu da yara, kada a ci amanan iyayen yara a ɓata musu tarbiyya.
Bayan na dawo makaranta, Mami ta faɗa mini, sai lokacin ma na tuna nikam, na faɗa mata ai muma an
faɗa mana na sha'afa ne, murmushi kawai Mami ta yi ta ce, "je ki wasta ruwa ki ci abinci, idan kun dawo
makaranta zuwa anjima za mu yi magana ko."

Amsawa nayi na miƙe n shige ɗakina, ruwa na watsa sannan na ci abinci na yi sallah, shirin tahfiz kuma na
yi, sallama na yiwa Mami na fice muka tafi tare da Umaimata.

Bayan mun je mun dawo, zuwa dare muna zaune da Mamina ta dubeni ta ce, "Banafsha!"

Da murmushi a fiskana na ce, "na'am Mamina."

Ajiyan zuciya Mami ta sauƙe ta ce, "Banafsha na sadaukar miki da abubuwa da dama a rayuwata, tun kina
ciki har zuwan ki duniya, ban taɓa gajiya ba kuma bana fatan gajiya watarana indai zan sa ki farin ciki, kaza
bata taka ɗan ta saboda bata son sa, a'a saboda tarbiyya take haka, nasani kina da tarbiyyan da na baki
dai-dai gwargwado, kina jin maganata kuma kina kiyaye ɓacin rai ba, Banafsha ina da dalilin ƙin aure,
amma kuma dalilin nawa bai kai naki ba na yan da kike so nayi aure, Allah ya ce ko iyayene idan suna ba
dai-dai ba ka faɗa musu gaskiya, dan haka zan yi abin da kike so, nasan ke ma ba ƙin abinda nake so kike yi
ba, zan yi aure da yardan Allah, zan kuma baki labarin dangina kaman yan da na faɗa, zuwa gaba kuma zan
kai ki gare su, aure dai yanzu zan yi, labari kuma zan baki shi ne a matsayin kyautan bikinki, dan haka idan
kin amince kin turo miji to kin shirya jin labarin Maminki."

Ajiyan zuciya na sauƙe cikin sanyin jiki na ce, "Mami Allah nima ina son ki kuma zan iya sadaukar da komai
saboda ke da farincikinki, ki yi haƙuri ki yafe ni idan na ɓata miki."

Murmushi Mami tayi ta ce, "Ya isa haka Banafsha, yanzu dai ke ce ƙawar Maminki, ke ce mahaifiyar
Maminki, kuma mahaifin Maminki, ƙanwata, yayata, yarinyata kuma komai na, dan haka sai ki bawa Mami
shawara wa ya kamata ta aura tsakanin Abbaanku da Alhaji", Mami ta ƙarishe maganan tana murmushi.

Wani farinciki ne ya lulluɓeni, tun ba'a je ko ina ba, na fara ganin sakamakon haƙuri da kuma jarrabawan
rayuwa da na shiga, Mamina ke mini wannan magana, lallai uwa-uwace, bai ma kamata mutum ya haɗa
soyayyan mahaifiya da na kowa ba a duniya, cikin ƙaunan Mamina na ce, "Mami tsakani da Allah da farko
Abbaa nake so ki aura, amma yanzu na fi son ki aure Alhaji."
"Saboda me kika so na auri Abbaa kuma kika fasa, Sannan saboda me kika ƙi Alhaji yanzu kuma shi kike so
Maminki ta aura."

Murmushi nayi na ce, "Mami da farko na ga ƙoƙarin Abbaa ne na stawon shekaru yasan irin rayuwan da
kike yi amma yake dakon soyayyanki har zuwa yanzu da ya faɗa miki shiyasa na so ki aure sa dan gani ga
Umaima ta, amma kuma da wannan abu faru sai hankalina bai kwanta da hakan ba, Abbaa ya saki Umma
kuma saboda ke yana son aurenki, to bana son kema ya miki haka nan gaba, sannan kar Umma ta kashe
mini Mamina."

Murmushi Mami tayi ta ce, "Sayyada Faɗima, ina jinki shi kuma Alhaji fa."

"Uhmñ! Mami haushinsa nake ji saboda yan da yake zuwa gidannan yayi kwanaki, kuma da aurensa da
yaransa, yana ta ɗawainiya da mu wataƙila baya yi wa matansa da yaransa, shi ne bana so dan kada ya
aureki ya miki haka, amma yanzu na fahimci ba haka bane, da gaske Alhaji yake son ki, dan Allah Mamina
ki amince ki aure sa, wallahi ko ba za ki kai ni wajan dangin babana ba to na yarda ya bayar da aurena."
Mami jinjina kai ta yi ta ce, "Madalla da yarinya ta mai halin manya, tunanin nesa da kuma nazartan
rayuwa, Allah miki albarka Banafsha, naji shawaranki kuma na ɗauka indai hakan zai saka ki farin ciki,
amma kuma zan cigaba da neman zaɓin Allah, kema ina son ki dage da addu'a da istihara duka, tsakanin
Aliyu da Danish Allah zaɓa miki mafi alkairi, idan dukan su ma ba alkairi bane, to Allah baki nagari wan da
ya fi su, saboda duk halin da kuke ciki da Danish na sani, ina kallonki ne kawai da ido, to ki dena ki bari
bana so, ba kyau wulaƙanta mutum dan ya ce yana son ka, aya ce guda a ƙur'ani mai girma cikin Suratul
baƙara da ya ce, "ASA AN TUKRAHU SHAI'AN WA HUWA KHAIRUN LAKUM, WA ASA AN TUHIBBU SHAI'AM

WA HUWA SHARRUN LAKUM" dan haka ina son ki cire stanan kowa a ranki ki yi addu'an alkairi kawai, Allah
miki albarka ya tabbatar mana da alkairi."

Da, "Ameen" na amsa cikin gamsuwa da maganan Mamina.


Haka rayuwa ta din ga tafiya Umma har yanzu tana kulle kuma tukunna ba'a fara shari'anta ba, amma dai
an kai Court ɗin, kuma ana ƙoƙarin farawa.

Ɓangare na kaman yanda Mami ta mini faɗa to naji, addu'a nake na neman zaɓin Allah, idan Ya Danish ya
zo ba hantara ba komai zan kulasa amma dai ba dan ina jin son sa a rai na ba, Malam Abbo ma duka ina
kula shi.

Ɓangaren Mamina ma ta cigaba da addu'a, kuma zuwa yanzu Alhajin ne take jin ya kwanta mata a rai, dan
haka ba ɓata lokaci ta fara shiri tana gyaran jikinta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login