Showing 48001 words to 51000 words out of 111817 words

Chapter 17 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf

Advertisement

16 Aug 2025

4060

hanzari ya shige banɗaki ya wanke fiska, bai yi kowa wanka ba
ya zura jallabiyansa ya fito, Mami ta shiga ta samu Banafsha ta idar da sallahn, kamota tayi suka shige
motan Alhaji, shi kuma ya ja sai asibiti, duk da safiya ne amma Allah ya taimakesu da yake asibitin kuɗi ne
kuma babban asibiti ne, likita yayi attending nasu an mata alluran da aka saba mata, aka basu magani
sannan suka juyo gida, suna dawowa kuma ba jimawa jinin ya zo, nan ma ɗin wani ciwon maran ne dan sai
Mami ne ta gyara mata jikinta staff, haka suka wuni cass! Alhaji daman sai Monday zai koma dan haka yana
gida, Mami sai kula take da yarinyarta tana mata addu'an Allah ya yaye mata wannan ciwon maran
jaraban.

Yamma na yi bayan ya Danish ya shirya tafiya ya fito ya staya a waje, nan ma dai shiru har su Umaima suka
kuma wucewa yana wajan, saboda ganinsa Umaima bata yi gigin zuwa gidan su Banafsha ba, ya Danish
gajiya yayi ganin su Umaima suna dawowa an tashe su ma, sai ya ja guntun tsaki ganin babu ita ya shige
motansa yayi tafiyansa ko sauraran abokinsa IB bai yi ba.
Umaima kuwa suna zuwa makaranta nan ma babu Banafsha har aka tashi, cikin damuwa dai Malam Abbo
ya tambayeta ƙawarta ko lafiya bata zo ba, Umaima ta faɗa masa bata sani ba dan bata dubo ta ba, amma
za ta duba ta, amsawa Malam Abbo yayi yana addu'an Allah ya sa lafiya, Umaima suna komawa suka samu
sai lokacin ya Danish zai tafi, shigewa gida suka yi, ta ce sai ya tafi da anjima za ta je ta dubo masoyiyarta.
Sai da suka yi sallahn Magrib sannan Umaima ta samu Ummu ta ce, "Ummu zan je wajan masoyiya
Banafsha, yau kwata-kwata safe da yamma du bata je makaranta ba bansan me ya faru ba."

Jinjina kai Ummu tayi cikin damuwa ta ce, "To Allah ya sa dai ba wani abun ba ne ya faru kuma, wannan
yarinya Allah bata miji nagari inda za ta huta, Allah dai-daita mata lamuran mahaifiyarta."

"Ameen Ummu ba na je, sai na dawo."

"To ki dawo lafiya, ki ce ina gaisheta, idan ba komai ki dawo da wuri saboda Abbaa kada yayi faɗa kin fita
da Magrib, idan kuma wani abun ne ki kwana can zan faɗa masa, Allah muki albarka dukanku ko" faɗin
Ummu.

Umaima ta miƙe tare da cewa, "Ameen Ummuna" ta fice a ɗakin, tana ƙoƙarin fita a ƙofan palourn su ta
jiyo muryan Umma na faɗin, "Ina za ki je da daren nan bayan anyi Magrib? Abbaanku bai hana ku fita da
dare ba?"

Umaima tura baki tayi ta ce, "Na faɗawa Ummu fa, kuma wajan Banafsha zan je ni, yau bata je makaranta
ba kwata-kwata bansan ko bata da lafiya ba."

Wani kallo Umma ta mata ta ce, "Ita wacce kika faɗawa ita ce uwarki ko ubanki? Umaima zan yi mugun
saɓa miki fa, wallahi ki fita a idona na kulle, na ce sannu Uwar Banafsha, ke ce karuwa uwar Banafsha
ƙarshenta kenan, to maza ki juya ki koma ɗakinki, idan kika fita a gidan nan yau ba wanda ya isa ya hanani
karyaki, ba dai kinga Danish ya tafi ba ko? Shi ne za ki stiro da wani hali, kullum na miki magana bakyaji, to
ni nan zan karyaki, wuce ki koma kamun na taso" Umma ta ƙarishe maganan da mugun stawan da sai da
Umaima ta ɗan firgita, tura baki tayi ta wuce ɗakinta tana kuka an hanata dubo Banafsha, Umma kuwa
ƙwafa tayi ta koma ta zauna ta ga ta inda Umaima za ta fita, duk abinda ya faru Ummu ta jiyo amma sai ta
yi shiru, ko ba komai ba'a shiga tsakanin uwa da ƴa, da gaskiyanta ita ce mahaifiyarta ta fi ta iko da
Umaima, jan baki Ummu tayi ta yi shiru akan zuwa gobe Insha Allahu ita da kanta za ta je ta dubo Banafsha
ɗin.

Washegari Monday bayan Umaima ta shirya tafiya makaranta kasancewan Monday ne suna da class na
safe, sai Umma ta fito, mugun kallo ta bita da shi sannan ta ce, "Umaima kina fita ki wuce makaranta, idan
kika kuskura kika bi gidansu yarinyar nan wallahi ranki zai yi mugun ɓaci, bana son shashanci, idan mutuwa
ta yi ma ina ruwanki? Ko akwai wanda aka ce ba zai mutu ba ne?"
Umaima yanzu ma tura baki tayi haka ta fice, tana kallon gidan su Banafsha tana son zuwa amma tana
storon Umma, haka ta wuce ta tafi makaranta, kaman yanda ta yi tsammani kuwa ba ta ga Banafsha a
boko ba har suka gama class nasu wajan ƙarfe huɗu ta dawo gida, nan ma dai ba daman zuwa tana storon
Umma haka ta shige gida, tana shiga kuwa ta samu Umma a palour, wani kallo Umma ta mata ko amsa
gaisuwan da take mata bata yi ba ta ce, "kinje gidan ƙanwar uwartaki ko?"

Umaima girgiza kai tayi ta wuce kawai, Umma ta yi ƙwafa ta ce, "Ya fi miki, ai da kinje wallahi sai na kusa
karyaki, kuma ki gama abinda za kiyi maza ki fito ki shirya ki tafi tahfiz, kuma kika sake kika bi gidansu sai
na miki baki."

Umaima haka ta ci abinci ta yi sallah ta wasta ruwa, sannan ta shirya ta wuce islamiyya, yau ma shiru ba
Banafsha ba alamanta, Malam Abbo duk ya bi ya damu, ga shi yana son ya bata sato guda tukunna ya
kuma komawa, bayan an tashi ya tambayi Umaima lafiya kuwa ko akwai wani abun da ya hana ƙawarta
zuwa makaranta, Umaima kaman za ta yi kuka ta ce bata samu zuwa ba, amma Insha Allah anjuma za ta je.
Malam Abbo cikin damuwa ya ce, "Allah ya kai mu anjuman, ki faɗa mata ina gaidata, na yi kewanta" yana
gama faɗa ya wuce.

Umaima da kallo ta bi Malam Abbo, duk mamaki take yanda ya bi ya damu haka shi ma, duk da dai tasan
masoyiyarta tana da shiga ran duk wanda ya zauna da ita saboda halinta masu kyau, haka Umaima ta juyo
gida ita kaɗai da aka tashi, nan ma Umma ta kuma faɗa mata kada ta kuskura ta ce za ta je gidan su
Banafsha, Umaima ko Ummu bata yi wa magana ba taja bakinta tayi shiru, sai da Abbaa ya dawo wajan
isha'i sannan ta miƙe saɗaf-saɗaf ta tafi sashinsa, da sallama ta shiga.

Abbaa yana murmushi ya amsa mata ya ce, "shigo ko Umaimatun Abbaa."

Umaima shiga tayi ta samu waje ta zauna, gaishe da Abbaa tayi ya amsa, ta amsa sannu da dawowa.

Abbaa ya ce, "Ya aka yi Ummul-khultum kaman akwai magana a bakinki? Wa ya taɓa mini ke?"

Umaima sarkin taɓara, tura baki tayi cikin shagwaɓa ta ce, "Umma ce Abbaa."

Murmushi Abbaa yayi ya girgiza kai dan yasan za'a rina, yana kallonta ya ce, "ya aka yi? Me Ummanki kuma
ta miki?"

Umaima ta ce, "Abbaa wai fa Banafsha ce tun ranan asabar rabona da ita, ranan Lahadi har yau litin
kwata-kwata bata je boko ba, kuma ba ta je tahfiz ba, shi ne nace zan je dubota na faɗawa Ummu, har ta

barni naje kuma ta ce za ta faɗa maka, amma sai Umma ta hanani, kuma ta ce idan na tafi makaranta na bi
gidansu bata yafe mini ba.......", Umaima ta faɗawa Abbaa duk yanda aka yi, kaman za ta yi kuka."

Girgiza kai Abbaa yayi ya ce, "Mai hali ba ya fasa halinsa, Allah ya kyauta, ki yi haƙuri ko, yanzu ki je ki jirani
ina zuwa sai mu shiga gidan nasu tare, Allah ya sa tana lafiya, ki ƙyale Ummanki kar ki ce mata komai, duk
abinda dai ta ce miki kiyi ko kar kiyi, idan bai saɓa addini ba kiji magananta, ita mahaifiyarki ce, kuma sai
an anrabu da iyaye lafiya ake dacewa."
Umaima jinjina kai tayi sannan ta tashi ta fice ta koma cikin gida, Abbaa kuwa wasta ruwa yayi ya saka
jallabiyansa ya feshe jikinsa da turare sannan ya shiga cikin gidan, duk matan sannu suka masa ya amsa,
sannan ya ƙira Umaima ya saka ta a gaba suka fice, suka nufi gidansu Banafsha.


Ɓangaren Banafsha haka ta kwana ranan Lahadi da ciwonta, Mami sai tattalinta take yi, Alhaji ma dai
tausayin yarinyar yake yi, har washe gari Litinin haka suka wuni, Banafsha zuciyanta cike da kewan
Umaimatynta ga shi bata shigo ta duba ta ba, amma ta mata uzuri tasan ba zai wuce ya Danish ba ne ya
hanata zuwa, sai bayan azahar Alhaji ya sallami Mami, bayan ya ajiye mata kuɗi masu yawa dan jinyan
Banafsha, Allah ƙara sauƙi ya mata sannan ya fito ya shige motansa, ya nufi Yola daga nan kuma sai Kano
Kanawan dabo.

Sai da Mami tayi Magrib sannan ta Lallaɓa Banafsha ta yi wankanta da kanta a daddafe ta gyara jikinta
chass da ita, abinci ma da lallami ta ci Mami na bata a baki, ana ƙiran isha'i Mami taje tayi sallah, Banafsha
kuma tana kwance a palourn idanuwanta akan TV amma hankalinta ba ya kan TV, hankalinta na can yana
tunano mata Malam Abbo nata, har Mami ta idar ta fito bata sani ba, sai da ta taɓa ta ta ce, "shalelen
Mami me kike tunani haka?"

Murmushi na sakarwa Mamina na ƙarfin hali na ce, "bakomai Mamina."

Mami ta ce, "Ban yarda ba, amma dai ina son ki daina saka damuwa a ranki, komai na duniya mai wucewa
ne, watarana ciwon nan zai barki kaman ba kiyi ba, Allah dai ya baki miji nagari Banafsha wanda zai kula
mini da ke sosai fiye da ni."

Ajiyan zuciya kawai na sauƙe tuna maganganun Malam Abbo, kawar da tunanin nayi tunda nasan ba mai
yiwuwa bane na ce, "Mamina bansan me ya hana Umaima shigowa ba kwata-kwata, Allah ya sa ita ma
lafiya."

Murmushi Mami tayi ta ce, "Insha Allah! Lafiya lau take, may be wani abun ne, karki damu za ta shigo,
kinsan dai Umaima na ƙaunarki."

Murmushin nima na yi da na tuno Umaima, na yi shiru tare da ɗaura kai na a cinyan Mamina da ta sha
nata wankan muna kallo, ba jimawa kuwa muka jiyo sallamana Umaima, daga ni har Mamina da murmushi
muka amsa, hannuwana na buɗe na ce, "oyoyo Umaimatyna."

Umaima rungumeni ta yi ta ce, "afuwan masoyiya."

Hararanta nayi na ce, "Na janye oyoyon ma fushi nake da ke."

Umaima gaishe da Mami tayi ta ce, "Tare Da Abbaa muke Mami."

Washe baki Mami tayi ta ce, "To shi ne kika bar Abbaan naku a waje Umaima saboda yaranta? Ki ce ya
shigo mana."

Umaima miƙewa tayi ta fice, tana murmushi ta ce, "Abba ka shigo inji Maminmu."

Abbaa na murmushi ya biyo Umaima da sallama suka shigo, duk amsawa muka yi, na miƙe daga kwanciyan
da nayi ina murna na ce, "Sannu da shigowa Abbaanmu."

Murmushi shi ma Abbaa yayi ya ce, "Sannu Faɗima."

Mamina da mayafinta ita ma ta yiwa Abbaa sannu da shigowa ya amsa yana fara'a bayan ya zauna, gaishe
da Abbaa nayi ya amsa, sannan na miƙe cikin dauriya, muka shige ɗakina da Umaima muka bar Abbaa da
Mamina a palourn.

Muna shiga ɗaki Umaima ta ce, "ki yafe mini masoyiya, na yi kewanki sosai."

Murmushi na sakar mata na ce, "Nima haka Umaimatyna, wallahi kekam marana ke ciwo tun ranan asabar
da dare shiyasa, kuma nasan ba zai wuce ya Danish ne ya hanaki shigowa ba, bakomai wallahi, ya karatu?
Fatan dai ba'a ba da assignment ko presentation ba? Tahfiz ma normal ko?"

Umaima murmushi tayi ta ce, "Nasan ai babu dalili ba za ki ƙi zuwa makaranta ba, mayyar karatu, kina
fama da kanki kina tambayan wani presentation ɗin buhun uba, ni fa na stani presentation ɗin nan wallahi,
amma normal ba'a ba da komai ba, tahfiz ma lafiya, Malam Abbo ya ce na ce yana gaisheki kuma yayi
kewanki" ta faɗa tana kyalkyalewa da dariya.
Murmushin yaƙe kawai nayi a nawa ɓangaren na ce, "Masha Allah! Ina amsawa, amma tunda ya Danish ya
koma jiya Sunday, me ya hanaki shigowa da safe yau Monday?"

Tura baki Umaima tayi ta faɗa mini yanda suka yi da Umma, murmushi kawai na kuma yi na ce, "Allah ya
kyauta, bakomai, Allah raba mu da su lafiya."

"Ameen masoyiya Banafsha" faɗin Umaima tana kwanciya a kan gadon."

Wani abu na faɗa mini na faɗawa Umaima yanda muka yi da Malam Abbo, amma wani abu na ce mini a'a,
sai kawai na ƙyale nayi shiru, nima kwanciyan nayi, muna hiranmu da yake ciwon maran da sauƙi.

Mamina bayan mun shige ɗaki sai ta kawo wa Abbaa ruwa, bayan ya sha suka gaisa, ya ce, "kwana biyu
bana ganin giftawan Faɗima fatan dai lafiya?"

Mami ta ce, "Lafiya Alhamdulillahi Abbaansu, dama bata ji dad'i bane amma da sauƙi."

"To Masha Allah! Haka ake so, Allah ƙara afuwa, Umaima duk ta bi ta ishi mutane da rigima shi ne nace
bari mu taho tare ma."

Mami dariya ta ɗan yi ta ce, "Yaran nan ai rigimansu ya fi ƙarfinsu, ita Banafsha ma tana kwance tana fama
amma sai mita take wai Umaima bata shigo ba yanzu ma mun gama maganan kenan sai ga sallamanta."

Abbaa murmushi yayi ya ce, "Masha Allah! Ai haka ake so, Allah ƙara haɗa kawunansu, kinga sai a bar miki
su ki haɗa duka biyu."

Mami ta ce, "Waii! Wane ni, ai Ummu ba za ta bar mini yarinyarta ba, da dai za'a ce a haɗa mata su ne ita
za ta yarda."

Dariya Abbaa yayi suka ɗan taɓa hira da Mami sosai da yake daman can sun ɗan mutunci, Abbaa mutum
ne da bai da damuwa sam-sam, da yayi tunanin baje wa Mami sirrin ƙalbinsa amma sai ya fasa ya bari
zuwa gobe, tunda yanzu dubiyan Banafsha suka zo.

Sai da suka ɗan ɗau lokaci sannan Abbaa yayi ƙiran Umaima ta zo su koma, amma rigima ta saka ita za ta
kwana, ba musu Abbaa ya ce su kwana lafiya ya juya yayi tafiyansa bayan sun yi sai da safe da Mami,
Umaima da farinciki suka fito da Banafsha suna kallo duka da Mami har dare tayi suka wuce suka kwanta,
Mami ma tayi nata ɗakin ta kira Alhajinta suna wayansu cikin soyayya tana masa sannu da hanya dan ya
koma gida.

Abbaa yana komawa dai Umma sai zubawa bayansa ido ta ke ta ga ɓullowan Umaima amma shiru,
daganan ya fahimci inda suka je, wato Umaima faɗawa mahaifinta tayi shi ne suka je tare, daman mai
neman kuka ne aka jefe sa da kashin akuya, ya ce zai auro karuwa ga shi ya samu daman zuwa zance ma
dan cin fuska, ƙwafa Umma ta yi ta ce, "Idan na kamaki Umaima sai ɗan buzunki."
Ummu kuwa ta tambayi ina Umaima ya faɗa mata ya baro ta gidansu Faɗima, Ummu ta tambayi ya jikin
nata, ya amsa da sauƙi, ta ce ita ma gobe za ta je dubo ta, Abbaa ya ce, "Ba damuwa Allah ya kai mu, Kinga
sai ki raka ni zance mu dai-daita, tasan da amincewnki, dan inaga idan ba ki ce kin amince ba, zai yi wuya
ta yarda saboda kar ta ci amanan ƙawance."
Dariya Ummu tayi ta ce, "Allah ya kai mu Abbaansu."

Sai da safe ya yiwa Ummu ya wuce ɗakin Umma da yake ita ce da girki.


Washe-gari da safe Umaima daga gidan Mami ta shirya ta je tahfiz, bayan anyi karatu an tashi Malam Abbo
ya kuma tambayanta, ta faɗa masa bata jin daɗi ne amma da sauƙi, hamdala yayi tare da yi mata addu'an
samun sauƙi, sai yanzu hankalinsa ya kwanta, kuma yana kan lissafi sati guda ranan asabar nayi zai koma
ya kuma jin hukuncin da ta yanke, Umaima kuwa tana dawowa ta kuma shiryawa daga gidan Mami ta
wuce school ta saka uniform na Banafsha, ko da ta dawo bata tafi gida ba har sai da Ummu ta shigo, bayan
sun gaisa da Mami ta tambayi jikin Banafsha Mami ta amsa da sauƙi, sannan ta saka Umaima a gaba suka
koma gida, bata haɗu da Umma ba daga nan ta shirya ta koma tahfiz na yamma.

Abbaa yau ma bayan ya dawo ya shirya tsaff ya nufi gidan Mami dan ya sanar da ita abinda ke ransa.


Alhaji Mukhtar ya koma gida lafiya, ya samu Hajiya ta tafi Dubai akan business nata, gaba-ɗaya ya ji ba
daɗi amma yayi haƙuri yana addu'an Allah sa ta gyara halinta, Allah kuma ya mallaka masa Ramla.

Yana zaune a palourn sama yana ayyukansa a system nasa, Majeeder ta shigo da sallama, amsawa yayi
yana murmushi ya ce, "zauna Maman babanta."

Majeeder zama tayi ta gaishe da Alhaji sannan cikin shagwaɓa ta ce, "Papi ni wallahi na gaji, gida kullum
shiru, dan Allah nima a mayar da ni gidan Affa General."

Alhaji barin abinda yake yi yayi ya shafa kanta tare da kamo hannunta ta zauna a kusa da shi, yana
murmushi ya ce, "Mai jiddan babanta kina so idan kika tafi na zauna ni ɗaya ne nima? Kina son damuwa ya
yiwa babanki yawa? Ke nake gani a gidan nan naji sanyi a rai na, ki yi haƙuri ko, in Allah ya yarda komai zai
wuce, na kusa kawo miki Aunty da kuma ƙawa abokiyar hira, ba dai kina son ƙawa ba?"
Gyaɗa kai Majeeder tayo ta ce, "Eh Papi ina so."

Murmushi yayi ya ce, "yauwá na kusa kawo miki ƙawa, kuma auntynki har da ƙanne za ta haifa muku,
Mami za ki dinga ƙiranta ma, ƙawarki kuma sunanta Faɗima amma ana ce mata Banafsha, ita ma ta sanki,
kuma tana son ƙawance da ke, su ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login