Showing 87001 words to 90000 words out of 111817 words
Chapter 30 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf
Banafsha, su mayu ne sun lashe
mishi zuciya, murmushin yaƙe Mami ta yi ta ce, "Allah ya bawa Maman Kabeer haƙuri, Allah ya huci
zuciyanta, in Allah ya yarda tun da bata so, to Banafsha ba za ta auri Danish ba, in ba dai Allah ya rubuta
hakan a ƙaddaransu ba, to babu yanda muka iya kuma, sai dai addu'a da fatan alkairi, dan haka wannan
ma ba dalili bane da zai sa ka rabu da iyalinka, ka yi haƙuri Abbaan yara, mu mata sai a hankali, haƙuri ake
da mu, kaga Allah bai haɗa jininmu da ita ba shiyasa bata son ma ɗan ta ya auri Banafsha, to nan ma ina
bayanta, saboda maganin bari kada a soma."
Abbaa wani gauron numfashi ya sauƙe cikin ƙara jin haushin Umma akan abin da ta aikata, kallon Mami
yayi a yanayi na tausayi ya ce, "Hajiya Ramla a taimaka mana ni da Yarona, gaba-ɗaya tun da aka yi abin
nan hankalina ya ƙi kwanciya, sannan yaron nan kwata-kwata ma ya ƙi zuwa ma, balle kuma ya san halin
da ake ciki, ya ce sai ya ji labari an yarda ya nemi Fatima sannan zai zo, dan Allah a taimaka mana."
Mami ajiyan zuciya ta sauƙe cikin duba lamarin Maman Kabeer, dan ba za ta yarda Banafsha tayi aure a irin
wannan gida ba, ita ma babba an yi ƙoƙarin kasheta balle kuma Banafsha yarinya, duk da dai yaron na
ƙaunarta(kunsan Mami bata san abin da ke faruwa ba, duka wannan staman stakanin Banafsha da Danish
bata da labari), amma ba za ta iya ba, dan haka duban Abbaa ta yi ta ce, "afuwan Abbaan yara, amma
magana ta gaskiya Faɗima tana da manemi, wanda zuwa yanzu izini kawai yake jira ya turo manyansa a yi
maganan auren su, bai kamata nima duk da ina mace ba, amma na zama mai magana biyu, kuma dai nema
cikin nema ko a addinan ce babu kyau."
Abbaa kallon Mami yake kaman ya ƙwala ihu, ya ce, "sosaima Hajiya Ramla, nema, cikin nema babu kyau,
dan haka in Allah ya yarda zan yi ƙoƙari na basa haƙuri ya nemi wata, amma nima a duba tawa buƙatan,
ina matuƙar ƙaunarki Hajiya Ramla, a taimake ni, idan ban same ki ba akwai mastala babba ma kuwa."
Furucin Abbaa na idan bai sameta ba akwai mastala babba, dariya ya bata, dan haka ta maste dariyanta, ta
murmusa kawai, a ranta mamaki take irin na halin maza, wato manya da yara duk daɗin baki ta cika su,
namiji ya dage da idan bai sameki ba kaza-kaza, amma abu mai wuyan ki amince ne ayi auren, shikkenan
kin zama permanent kuma sai haƙuri, idan ba ki yi sa'a ba baƙin cikin yau daban na gobe daban, to dai
Allah kyauta ya kuma haɗa kowa da sa'ar sa yayi dacen samun na gari, amma sam-sam halin wasu mazan
bai haɗu ba, duk da wasu matan su suke nemawa kan su irin wannan rayuwan, Allah kyauta kawai.
Mami murmushi tayi ta ce, "Alhaji ka yi haƙuri, amma dai ni abinda ya dame ni yanzu shi ne ka dawo da
Maman Kabeer."
Abbaa kallon Mami yayi cikin ido ya ce, "kin tabbata idan ta dawo za ki amince mini ki aure ni?"
Murmusawa Mami tayi ta ce, "ban yi alƙawari ba, sai dai shi Danish zai iya zuwa wajan ita Faɗima, idan sun
dai-daita taga shi ya fi mata, to shikkenan Allah sanya alkairi, dan abin da yaro ke so shi za mu masa."
Abbaa sosai wannan amsa dangane da Danish ya masa daɗi, dan haka ya sa a rai shi ma zai ci-gaba da
zuwa yin magiya, har Allah ya sa ta amince dan abin zai fi ba da armashi.
Bayan sun gama hiransu, sallama suka yi, Abbaa ya tashi yayi tafiyansa, Mami dai duniyan tunani ta faɗa,
juya abubuwa da dama take a ranta, ƙiran wayan da ya shigo mata ne ya kaste mata tunanin, ganin mai
kira sai ta saki murmushi ta ɗauka, cikin zazzaƙar muryanta ta ce, "Alhaji bar ka da war haka."
Alhaji Mukhtar a ɗaya ɓangaren shi ma yana murmushinsa ya ce, "Barka dai masoyiya ta, fatan kina lafiya،
ya kuma yarinyata Banafsha take?"
"Duk muna nan lafiya yallaɓoi, ya ƙasar mutane?" Faɗin Mami.
Alhaji cewa yayi, "Lafiya Alhamdulillahi! Ga mu cikin ta, sai fama nake da kewanki, yanzu badan-badan ba
ai da kuɗin jirgi zan miki ki biyo ni, ko kuma ma na sakoki a gaba mu taho tare, ga shi duk mutanen ƙasar
masu irin kyawunki ne."
Mami cikin ƴar shagwaɓanta ta ce, "To ai ni na ɗauka ma ka dawo, sai naga ba layin Nigeria ba ne, nima
kewanka nake, kwana biyu babu customers, ina ga kore su ka yi da za ka tafi, ga shi dai ni a buƙace nake,
badan-badan ba nima da na biyoka."
Alhaji a nasa ɓangaren dariya yayi, dan yasan watarana Ramla na irin magannan ne da gan-gan dan ya ji
haushi, amma abun da bata sani ba shi ne, wani irin soyayya yake mata wan da ko turmi da taɓarya ya
kalleta da namiji, to ba zai cire masa son ta ba, shi baisan ko dan a cikin irin rayuwan ya san ta bane, amma
shi a haka ma yake mugun ƙaunarta, yana kishinta ba kaɗan ba, amma a yanzu burinsa ya mallaketa sai
yayi kishin yan da ya kamata, sai da ya gama dariya sannan ya ce, "Ko taurarin sun fara yin ƙasa ne mu
godewa Allah, amma dai kar ki damu soon za ki ganni, suprise kawai, ki shirya ganina a ko wanni lokaci
daga yanzu, tun da kina buƙatata ai zuwa ya zama dole, nima a buƙacen nake, wata biyu ba mata, ina
dawowa na bai wa Hajiyata rabonta, zan wuco na zo ke ma na baki naki rabon masoyiya, duk ƙishin sai na
kawar miki, ke dai ki adana mini kan ki kar na zo kuma kin riga da kin kashe ishinki ni ki kasa kashe mini
nawa."
Mami murmushi tayi suka ci-gaba da wayansu cikin soyayya, ka ɗauka mata da miji ne, tuni ma ta mance
da wata maganan da suka yi da Abbaa, sai da suka yi sallama sannan ta ajiye wayan tare da yin murmushi,
wato Alhaji Mukhtar mutum ne, tun ranan da ta yi kuka ya ce ba zai kuma mata maganan aure ba, to bai
kuma ba, sai kawai Mami ta ji ya bata tausayi.
Ɓangaren Alhaji Mukhtar da ya kwashe fin wata biyu a Egypt, suna gama waya da masoyiyarsa ya
murmusa tare da addu'an Allah shirya su ya dawo masa da ita hanya.
Abbaa ko da ya koma ya ƙira Danish akan zai iya zuwa wajan Banafsha, idan ta aminta da soyayyansa
shikkenan sai ayi maganan aure, amma ya faɗa masa bayan shi akwai wani mai nemanta.
Danish duk da ya kwana da sanin Banafsha na da saurayi, amma ya ƙudurcewa ransa sai ya ka da saurayin
nata, shi yanzu ko bin mazan da ya ce tana yi baya gani, wani mugun son ta da ƙaunarta ne yake damunsa,
burinsa kawai ya mallaketa, dan haka tsaff ya shirya wannan satin ya taho Mubi.
Ɓangaren su Banafsha sun duƙufa akan karatunu musabaƙan da za su yi, gaba ɗaya yanzu ko Malam Abbo
sai ya dage yake samun lokacinta, ga shi tsakaninta da Maminta indai ta mata maganan aure to ranan sai
Mami ta saka ta kuka, ita ta dage sai Mami ta yi aure ita ma, ko kuwa ta koma wa danginta, sannan za ta yi
aure, Mami kuma bata amince da ko ɗaya ba, ta dai dage sai Banafsha ɗin ta yi aure.
Mami bata faɗa wa Banafsha zuwan Abbaa ba, sannan bata mata maganan Danish ba, ta bar ta dai, idan
ya mata ta ji tana son sa, to da kanta za ta yi maganan wanda take so tsakanin shi da Malam Aliyu.
Umma tana can zaune a prison har yanzu ba'a fara case nata ba, ko da Mami ta je station ɗin ma akan ta
yafe mata a ƙyaleta, amma nunawa suka yi ai case ya riga da ya koma court, kuma ba daman janye ƙara,
kuma yanzu a ƙarƙashin ma'aikatan prison take ba ma'aikatan station ba, dole haka Mami ta dawo ba dan
ta so ba, yaya babba ko da yaji labari jinjinawa haƙuri irin na Mami yayi, Umaima ma sai ji tayi ta ƙara
ƙaunar Mami, Ya Mus'ab ma har da godiya ya yiwa Mami dan sun san yanzu abin zai zo da sauƙi, tun da ta
ce ta yafe, ko a court ne to abin da sauƙi.
Banafsha da ta ji wai Mami ta yafe wa Umma, sai ta samu Mami ta ce, "Mamina me yasa ba za ki bari a
hukuntata ba? Yunƙurin kashe ki fa ta yi, kisa fa Mami, da yanzu na zama marainiya ban da kowa."
Murmushi Mami ta yi ta ce, "Innallaha ma'assabirin! Allah na tare da mai haƙuri Banafsha, yafe mata da
nayi, sai kiga nima Allah ya dubi wasu laifukana ya yafe mini, ya kuma shirya ni ya dai-daita lamurana,
Banafsha ita komai a duniya ƴar haƙuri ce idan ɗan Adam ya gane."
Kallon Mamina nayi na ce, "haƙuri Mami? Shikkenan ta yi a banza? Ni fa duk da Umman Umaimata ce
amma ya kamata a hukuntata, dan wasu masu irin wannan yunƙurin su hankalta, tun da an ce gani ga
wane ya isa wane storon Allah."
Murmushi Mami ta kuma yi ta ce, "Ba na yafe mata saboda wasu su ji daɗin aikatawa bane, a'a na yafe
mata ne saboda waɗanda aka wa laifi irin nawa ko fin nawa, su ji daɗin yin yafiya da nufin su ma Allah ya
yafe musu wani yanki na zunubansu, Banafsha akwai wani kissa daga Manzon Allah SAW kan cewa,
watarana a gaban Allah ranan tashin ƙiyama, akwai wani mutum da za'a tattara ladansa a biya bashuka,
zalunci, munafurci, ha'inci da sauran su, duk za'a biya haƙƙonƙin jama'a da ya ci, da ladan ayyukansa na
alkairi, sai ya zamana dai-dai da ƙwayan zarra ba shi da lada ko guda, to ana cikin haka kuma wani
mutumin zai ƙara ɓullowa ya faɗawa Allah, ai shi ma yana bin wannan mutumin bashi dan haka asaka shi
ya biya sa, idan Allah ya ce wa wannan mutumi mai laifukan ya ji abinda wannan ya faɗa, sai ya kama
murmushi, ko da Allah ya tambayi dalilin murmushin nasa, sai ya ce ai gani yayi bai da lada ko ƙwayan
zarra, duk ladan an biya jama'a da shi, yanzu ba shi da komai sai zunubi, Allah ya kuma duban mai kawo
ƙara ya ce kai ma ka ji abinda ya faɗa ai ba shi da lada, sai mai kawo ƙara ya ce, in mutumi mai laifin bai da
lada, to ai shi yana da zunubi, dan haka a ɗiba, zunubinsa gwargwadon haƙƙinsa da ke kan mutumi mai
laifin, a ƙara masa akan nasa zunuban, Allah zai ƙara kallon mutumi mai laifin ya faɗa masa ya ji abinda
mai ƙaransa ya faɗa, sai mutumin yayi murmushi ya ce ya ji ya amince, sai Allah ya sa a nuna wa mai laifin
yan da jahannama ta ke, idan ya kalli jahannama sai hankalinsa ya tashi, daga dariya ya koma kuka, idan
Allah ya tambayesa yana dariya kuma mai yasa ya koma kuka tun da ya yarda, mutumi mai laifin cikin
tsananin kuka da tashin hankali zai faɗawa Allah yana son yayi magana da wannan mai ƙaran nasa, to Allah
zai basu wata farfajiya su magantu, wannan mai laifin yana kuka zai haɗa mai ƙaransa Allah da Annabi ya
taimaka ya yafe masa, idan ya ce a ƙara masa zunubinsa zai ƙara masa azaba ne, kuma idan yana da
zunubai da yawa to shi ma ba zai hanasa shiga wutan ba, dan haka sai wannan mai ƙaran ya yafe masa, su
koma gaban Allah mutumi mai ƙaran ya faɗawa Allah ya yafe ma mutumi mai laifin, idan Allah ya tambayi
dalili sai ya faɗa masa ai shi ma yana da zunubi, dan ya ce a ƙarawa wani zunubinsa ba zai hanasa shiga
wuta ba, kawai ya yafe, sai yayi haƙuri, to saboda wannan yafiyan da ya yiwa mutumi mai laifin ya kuma
haƙura, sai Allah ya yafe musu duka ya saka su a aljanna, saboda Allah ya ce yana ƙaunar masu haƙuri, to
sai Sahabbai suke mamakin yan da ake wannan al'amari duka a gaban Allah, Manzon Allah SAW ya faɗa
musu abinda ake nufi da wannan al'amari shi ne haƙuri, Allah na tare da mai haƙuri, Allah na son mai
haƙuri, Allah yana sakawa ga mai haƙuri, saboda Allah shi ne ahkamul hakeemin, shi ya fi kowa iya
hukunci..."
Tun da Mamina ta fara wannan bayani na stura mata idanuwana ko kiftawa bana yi, har sai da ta kai aya,
sannan na sauƙe ajiyan zuciya tare da lumshe ido na ce, "To Allah ba da lada Mamina, Allah kuma ya
yafemu baki ɗaya, Mami amma dan Allah me yasa kika kasa haƙuri da danginki? In kuma ke ce kika musu
laifi me ya sa ba za ki je, ki basu haƙuri ba tare da nusar da su fa'idan haƙuri da yafiya ya za su miki, Mami
shi kuma mahaifina me ya miki? Ina yake? Mamina dan Allah dan darajan Annabi SAW ki taimaka ki amsa
mini waɗannan tambayoyin."
Mami murmushi tayi tare da ƙarisa wa da salati Manzon Allah SAW, ta ce, "Insha Allah Banafsha zan ba ki
duk amsoshin tambayoyinki amma ba yanzu ba, kuma ba yau ba, ban faɗa rana na amma na kusa sanar da
ke komai kin ji, ki yi haƙuri ki ƙara haƙuri."
Kwantawa nayi a jikin Mamina ban kuma cewa komai ba, wannan mutumin da muka haɗu da shi a asibiti
ne ya faɗo mini a rai, tura baki nayi lokaci guda kuma na murmusa, tuno abinda ya faru, Mamina kallona ta
ce, "Lafiya da murmushi haka gudalliyan Maminta."
Murmushi nayi ba ɓoyel-ɓoyel na ce, "Mami bansan me ya same ni ba lokacin da kika yi rashin lafiyan nan,
amma gaba ɗaya na zama kaman parrot a surutu, wannan Soja da Abbaa ya faɗa miki shi ya biya kuɗin
komai, Allah haka kawai na dinga masa masifa na rasa me ya sa, sai kuma yanzu abin nake tunawa, ni da
ba halina ba, meyasa na masa haka oho، kuma fa bai biye mini ba, ce mini kawai yayi idiot" na ƙarishe
maganan ina tura baki.
Shafa kai na Mami tayi tare da sakin murmushi ta ce, "Allah ya amsa albarka ya saka masa da alkairi, ga shi
ko sunansa ba mu sani ba, wannan su ne masu yin abu dan Allah, fisabilillahi, ke kuma Allah shirya mini ke,
ai daman Banafsha bakya ji, kin cika stiwa da manyance."
Tura baki nayi, muka ci-gaba da hiranmu da Mamina tana shafa kai na, gaba-ɗaya hasaso wannan bawan
Allah kyakkyawan soja nake ina murmushi, har ban sani ba bacci yayi gaba da ni.
Danish kuwa tun da ya zo ya ji labarin abin da ya faru, ba ƙaramin damuwa yayi ba, musamman da ya
kasance shi ne sanadin komai, haƙuri ya bai wa yaya babba, bayan ya masa faɗa sosai, tare suka shirya
suka tafi wajan Umma, amma da ƙyar aka bar su suka kalleta, nan ma sai da Danish ya bada kuɗi masu
yawa na cin hanci.
Duk maganan da suke yi Umma ko ƙala bata ce musu ba, bayan amsa gaisuwansu da ta yi, tambayan
Umaima tayi da kuma matar yaya babba ko ta haihu, bayan sun bata amsa shiru ta ƙara yi, gaba-ɗaya sai
tausayin mahaifiyarsu ya rufe su, ta zama abin tausayi ta rame ta yi baƙi, shiru ta musu har lokacin su ya
cika, suka tashi za su tafi, sannan Umma ta buɗe baki ta ce, "idan yayi ku kawo mini Autana Umaima na
gan ta."
Cikin tausayin Umma, yaya babba ya ce, "Insha Allah Umma za'a kawo miki ita."
Ficewa suka yi suka tafi, daga nan kuma suka ci-gaba da tattaunawa akan yan da za su yi Ummansu ta fito.
Gaba-ɗaya mun zama busy a maganan makaranta, ko kaɗan duk ƙoƙarin Ya Danish na ganin ya samu
daman stayuwa da ni ta ƙi samuwa, har ya cinye weekend nasa, yau Sunday zai koma, dan haka yau ya
dage komin dare to kamun ya koma sai ya haɗu da ni.
Ni da Umaima mun je tahfiz na yamma, mun dawo, muka yi wa junanmu sallama, ta shige gidansu nima na
wuce namu, kai na a ƙasa ina sakin murmushi ni kaɗai, saboda hiran Soja muka gana yanzu da Umaima, ba
tare da na kula ba na ji nayi karo da mutum na yi baya zan faɗi, sai aka riƙo hannuna, idanuwana a lumshe
nayi hamdala sannan na buɗe su na ɗago ina faɗin, "Na gode....", maganan baki nane ya maƙale ganin
wanda na yi karo da shi, kuma ya riƙe ni ban faɗi ba.
Haɗe fiska nayi na ce, "Allah ya isa na, hannuna da ka taɓa."
Maimakon na ga ya ɓata rai, ya fara ci mini mutunci yan da ya saba, sai naga saɓanin haka, murmushi yake
sakar mini tare da faɗin, "Afuwan gimbiyata."
Ƙara kallonsa nayi dan na tabbatar da shi ya faɗi abin da kunnena ya jiye mini, murmushi ya sakar mini
tare da ɗaga gira guda.
"Hmmn!" Na faɗa tare da jan dogon staki, fiskana a haɗe na ce, "let me have my way."
Murmushi yayi ya ce, "faɗa da hausa gimbiya."
Wani bansan harara na aika masa da shi, sannan na ce idan ya na yiwa Allah da Manzonsa ya bar mana
ƙofan gidan mu.
Ya Danish ko a jikinsa, ya ce, "Nima ya zama gidanmu ai, please Beb ki saurare ni, da farko ku yi haƙuri da
abin da Umma ta yi, duk nine na ja, amma dan Allah a yafe mata, ki