Showing 75001 words to 78000 words out of 111817 words

Chapter 26 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf

Advertisement

16 Aug 2025

4044

tsakanimu, mastayinsa da kiman
da nake basa kullum ƙaruwa yake yi, Malam Abbo ya iya soyayya yan da ko wacce mace za ta buƙata,
kuma yana ƙoƙarin mini nasiha da tunatar da ni rayuwa, alhamdulillahi sai fatan alkairi stakaninmu.

Har aka cinye wannan hutun ƙarshen makon Ya Danish bai zo weekend ba, muka shiga wani satin wanda a
wannan weekend ɗin wa'adin da Abbaa ya ba su zai cika, da kuma wa'adin da ya bai wa Mamina na ta yi
tunani, har juma'a ta yi ba Ya Danish ba alamansa, dan haka Abbaa waya ya ɗaga ya ƙirasa, sai da ya
sollesa tass sannan ya faɗa masa ya zo ko ransa yayi mugun ɓacuwa, ba shiri ya Danish ya shirya ya kamo
hanyan zuwa.

Da ya ke Umaima ta yi zazzaɓi kwana biyu, sai Mami ta shirya da yamma bayan an yi la'asar ta shiga gidan
su Ummu, da sallama ta shigo gidan, ta samu Ummu zaune a palour tare da Ya Farooq, cikin fara'a ya
Farooq ya gaishe da Mami ta amsa, sannan suka gaisa da Ummu, tana murmushi ta ce, "Mamin yara sai
yau aka samu daman leƙo gidan namu."
Murmushi Mami ma tayi ta ce, "ai gidan naku ne yana neman fin ƙarfin shiga na, yanzu ma dai yarinyata
na zo dubawa da jiki shiyasa."

Dariya Ummu ta yi ta ce, "Mu da muke addu'an a shigo din-din-din, ina wanda ya isa ya ce ba za ki shigo
ba."

Yaƙe kawai Mami tayi ta ce, "Ina yarinyar tawa?"

Ummu ta ce, "ai Umaima ta ji sauƙi Mamin yara, ina ga tana sallah ne ma, da yanzu kin gan ta..." Ummu
bata gama rufe baki ba sai ga Umaima ta fito tana murmushi, ta buɗe baki ta ce, "Mamina ayoyoo, sannu
da shigowa..."

Umaima bata gama magana ba, ta stinkayo muryan Umma na faɗin, "kika ƙara faɗan wani kalma ran ki zai
ɓaci, wuce ki koma ciki, shashashan yarinya kawai.

Daga Ummu har Mami da Ya Farooq duk da kallo suka bi Umma, Umaima rau-rau ta yi da idanuwanta
kaman za ta yi kuka, wani kallon Umma ta jefe ta da shi ta ce, "koma ciki na ce."

Umaima juyawa tayi ta koma ciki, Ya Farooq dai da mamaki yake kallon Umma, ƙarshe tashuwa yayi ya fice
dan baison ganin abin kunya.

Mami murmushi tayi kaman ba komai ta ce, "Umma Kabeer barka da yamma, ya jikin Umaiman?"

Wani irin kallon banza, kallon stana Umma ya jefawa Mami tare da sakin dogon tsaki ta ce, "Munafuka
kawai, wato kin biyo mu har gida ki ƙwace mijin namu, amma tun da yake ke ɗin ƴar bariki ce dole ki lauye
da duba yarinyata, to ba'a buƙatan gaisuwan an yafe miki, tashi ki fice mana a gida, ƴar ƙwace kawai."

Mami murmushi ta kuma yi ta miƙe tare da kallon Ummu ta ce, "Ummun su sai anjimanku, Allah ƙara
sauƙi."

Ummu nauyayyan ajiyan zuciya ta sauƙe ta ce, "ki yi haƙuri Mamin yara, ke kuma Maman Kabeer gaskiya
abin da kike yi bai kamata ba."

Umma a hasale ta hayayyaƙo wa Ummu ta ce, "To babbar munafuka algunguma, an faɗa miki duk abinda
ke faruwa ban sani ba ne? Wallahi can ya ƙare miki a maste-mastinki, ƙarya kike a auro wata balle ki samu
daman haɗe kai da wata a gidan nan."

Murmushi Ummu ta yi ta girgiza kai tare da cewa, "shi dai kishi ba hauka ba ne, dan haka kisan me ke fita a
bakinki, kada ki ga ina miki shiru, ba storonki nake ji ba, gudun tashin hankali nake yi, kuma Insha Allah sai
ya aurota."

Umma na ƙoƙarin yin magana sai Mami ta yi saurin taran numfashinta ta ce, "Dan Allah kuyi haƙuri
dukanku, in Allah ya yarda ma ba abin da zai haɗa ni da mijinku balle wannan tashin hankali ta faru, kuma
ni ban shigo dan haɗa ku faɗa ba, dubiya na zo yi kuma na yi zan tafi Allah ƙara sauki" Mami na gama
magana ta juya ta fice a gidan, cikin damuwa, ita ko ta rasa mijin aure me ya kai ta haɗa hanya da Umma,
balle har su haɗa miji, ita auren da ma gaba-ɗaya babu shi a lissafinta.

Umma kuwa da harara ta bi Mami da shi har ya fice a gidan, sannan ta juyo ga Ummu ta ja staki tare da
cewa, "aikin banza aikin wofi, kuma wallahi dan ki ji ba gwaninta kika yi ba, tunda abin ba ni kaɗai ta shafa
ba, miji nawa ne kuma naki."

Ummu murmushi tayi ba tare da ta tankawa Umma ba ta shige ɗakinta, tana koɗa halin kishi irin na
Umma.

Mamina ko da ta koma gida, ɓoye damuwanta ta yi, ban ga alama ba kuma bata sanar da ni ba, ɓangaren
su Ummu ma ba wanda ya yiwa Abbaa maganan abin da ya faru, Umaima dai ba yanda ta iya da halin
Umma, ko mene mahaifiya ce dole ta ji magananta.

Washegari asabar sai ga ya Danish da sassafe, sai da Abbaa ya dawo sannan suka zauna shi da Ya Danish,
Ya Farooq da kuma babban yaya.

Abbaa ne ya fara magana ya ce, "Farooq da Danish na baku lokaci, kuma ga shi lokacin kun cinye sa
murƙus, ba wanda ya bani amsa mai kyau a cikinku, hukuncin nawa kuke so na zartar ko?"

Danish ƙasa yayi da kansa yana sosa ƙeya, shi kuma Farooq murmushi yayi, sai yaya babba ya ce, "A yi
haƙuri a ƙara musu lokaci Abbaa, kasan yanzun lamarin daga matan har mazan sai a hankali."

Wani kallo Abbaa ya yiwa yaya babba ya ce, "To ubana ba zan ƙara musu lokaci ba, kai da kake da mata
yanzu baka jin ka cika mutum, baka jin wani nustuwa ta daban? Ai duk namijin da ya kai riƙe mata muka ba
shi da ita, to ba'a niste yake ba, kawai a gansa haka ne a ƙyalesa, an faɗa maka gauranci daɗi ne da ita?
Balle kuma ga wanda ke ƙoƙarin ƙewata ƴar mutane mutunci, to ba lokacin da zan ƙara musu, ko su fidda
mata aje a tambayo musu ko kuwa ni da kai na nayi musu matan, idan ma idanuwansu sun makance ne, to
nawa a buɗe suke tarr! Ai duk cikinsu ba wanda zai ce ba shi da budurwa, to ba za'a yaudari yaran mutane
da ni ba dan haka kun ji me na faɗa ai, babu ɗaga ƙafa."

Ya Farooq ƙasa yayi da kai ya ce, "Abbaa ni dai ina jira ne daman ka ƙira mu, amma mun gama magana da
wacce nake nema, iyayenta kuma sun ce na turo manyana daman."

Jinjina kai Abbaa yayi ya ce,"To ka taimaki kan ka, inba haka ba kuwa za ka ga yanda ake yiwa namiji auren
dole, to kai kuma Malam Danish ina sauraranka ya muke ciki? Ka samu ne ko na bada sadakanka?"

Daga Abbaa da yayi maganan, har su yaya babba ba wanda maganan bai sa dariya ba, ya Danish sosa ƙeya
yayi ya ce, "Abbaa nima dai na ba da kai na sadaka wa wata."

"To Masha Allah! Duk Allah ya muku albarka, kun taimaki kan ku" Abbaa ya faɗa yana murmushi.

Yaya babba ya ce, "To sai ku faɗa mana yaran gidan waye ne, dan a shirya maganan zuwa magana da
iyayensu."

Ya Farooq ya ce, "Sunanta Ruƙayya gidansu na anguwan Kaban."

Abbaa jinjina kai yayi ya ce, "Madalla! Allah tabbatar da alkairi, kai kuma Danish fa."

Danish sosa kai ya fara yi, yana in-ina, "uhmñ...umn..am..dama...daman ba..am Abbaa dama dai ni ba wai
mun dai-daita da ita ba ne, izini za'a nema mini tukunna."

Kallonsa Abbaa yayi ya ce, "To malam Danish, masu bin starin addini yanda ya kamata, hakan ma yayi ai
Allah muku albarka, wacece, in ya so gobe ko jibi sai a tambayo maka."

Danish ƙasa yayi da kai ya ce, "am Faɗima ce, ina...ina..ina nufin Banafsha."

Ba iya Abbaa ke kallon Danish da mamaki ba, hatta ya Farooq da babban yaya kallon mamaki suke bin
Danish da shi, gani suke dai kaman bai san abinda yake faɗa ba, kamun Abbaa yayi magana tuni yaya
babba ya ce, "Amma dai Danish baka san sunan wa ka ƙira ba ko? Banafsha dai kake nufi ƙawar Umaima,
yarinyar Mami?"

Abbaa ya ɗaura da cewa, "Banafsha da ka mayar da ita kuran wasanka ƴar gidan amaryan da zan aura
Ramla, ita kake nufi ko wata daban?"

Maganan Abbaa duk dariya ya basu wai ƴar gidan Amaryan da zai aura, amma suka maste kawai suna
sauraran Danish, shi kuma cikin tabbatarwa ya ce, "Ita dai Abbaa, ka yi haƙuri, wlh ita nake so."

Jinjina kai Abbaa yayi ya ce, "riƙe haƙurinka idan ka je wajanta zai maka amfani, ni ai mai farin ciki da
hakan ne, zan yi addu'an Allah tabbatar da alkairi, Uba ya auri uwa, ɗan sa ya auri yarinya, Masha Allah, in
Allah ya yarda zan yi magana da ita idan na je zance."

Ya Danish murmushi yayi yana addu'an komai ya zo da sauƙi, shi ya rasa irin Soyayyan Banafsha da ya mara
diran mikiya, ya Farooq dai mamaki yake har yanzu, yana kuma tunanin yanda za'a kaya da Umma idan ta ji
wannan magana, yaya babba kuma dai kallon Danish bai san abinda yake ba yake masa, saboda ko shi da
yake namiji idan aka ce shi ne suka wannan ƴar stama da mutum to ba zai yarda ya so shi ba balle aure,
lallai akwai aiki a gaban Danish, haka zaman nasu ya waste bayan sun ɗan tattauna abubuwan da ya
kamata.

Ya Danish washe-gari da sassafe ya bar gari baya son ma ya haɗa ko ido da Umma, dan yasan idan ta ji
labari to akwai yin ta, amma bai da mastala tun da Abbaa ya yarda kuma zai tsaya masa, yanzu a yanda
yake ji ba abinda ba zai iya yi ba akan soyayyan Banafsha, Allah-Allah yake a tambayo masa ya fara zuwa ya
samu ya kori wannan saurayin nata, shi ana tambayo masa to kusan kullum sai an gansa a Mubi.
Ranan Lahadi kaman kullum Malam Abbo ya zo muka sha hiranmu, ya ce zai turo amma na ce masa ya
dakata tukunna, haka ya haƙura ba dan ya so ba, Mami ta ƙira mini Alhaji mun gaisa na faɗa masa result
na yayi kyau, ya tambayi abinda nake so, amma na ce sai ya dawo, idan ya zo zan faɗa masa, haka muka yi
sallama akan ba zai wuce wata guda ba zai dawo, Mamina kuwa ko da ta ƙara mini maganan aure to abin
da na faɗa mata ranan shi na maimaita, sai kuma ta koma lallashina ganin na dage.

Mun ci-gaba da zuwa makaranta boko da tahfiz tare da Umaima har yau da ta kama Alhamis, da yake ba
mu da class da safe, to ba mu je da wuri ba, sai wajan ƙarfe goma muka bar gida muka tafi College.

Abbaa ya ƙara wa Mami sati guda akan watan da ya bata, to yau Alhamis ya yanke ranan juma'a zai je
wajan Mami, sai ya ce bari ya sanar da su Umma maganan auren Danish dan su san da shi, don abun ya
yiwa Abbaa daɗi ko ba komai hakan ma zai ƙara nistar da Umma.

Ƙiran Umma da Ummu Abbaa yayi, gyaran murya yayi ya ce, "Sai ku fara shirin da ya kamata, na tarban
abokiyar zamanku, da kuma matan yaranku, zan faɗa muku ne na fita haƙƙinku ba wai dan dole ne sai na
faɗa muku ba, Farooq ya samo mata a nan anguwan Kaban, sai kuma Danish a nan gida ya samu tasa
matar, Faɗima yake so, kun ga abu ya zo gidan sauƙi, tuwo na mai na, ni ina son uwa, yarona kuma yana
son yarinyar, dan haka ina gargaɗan ku da yin tashin hankali, Sabeera wancan karon ki daka mini yarinya
akan kishinki na hauka, kina ga na zuba miki ido ban ɗau mataki ba, kin ɗauka banza kika daka ba, to zan
ɗau mataki, kuma kika yi wannan karon to matakin da zan ɗauka zai baki mamakin da ba ki taɓa zato ba,
aure ba gudu ba ja da baya daga ni har Danish Insha Allahu, indai Allah ya nufa to sai mun aure su."

Ummu da mamaki take kallon Abbaa, ta ce, "Danish dai ke son Banafsha? Anya ka ji da kyau?"

Abbaa jinjina kai kawai yayi bai ce uffan ba.

Umma kuwa saboda haushi ma ta kasa cewa komai, miƙewa tayi ta fice, Abbaa kuma taɓe baki yayi bai ko
stayar da ita ba, dan yanzu halin Umma ya fara gimsarshi, Ummu kallon Abbaa tayi ta ce, "kana ganin
hakan ya dace? Ba za'a ja wa yarinyar nan mastala sosai a rayuwanta ba, a yanzu ma kusan kullum cikin
kuka take da damuwa da mahaifiyarta, idan aka mata irin wannan auren kana ga yayi? Ni bana tunanin ma
daga ita har mahaifiyarta za su amince da wannan batun, duk da babu wanda yasan abinda ya faru ranan."

Abbaa murmushi yayi ya ce, "ke dai ki ce Allah tabbatar da abinda ya ke alkairi."

Ajiyan zuciya Ummu ta sauƙe, ta ce, "Ameen summa Ameen."

Umma tana shiga gida ta shige ɗakinta, gabas da yamma kudu da arewa ta rasa me za ta yi ta huce, ta rasa
wani mataki za ta ɗauka, wai yau Danish da ke goyon bayanta ne ya kwaye mata zani a kasuwa, ya rasa wa
zai so sai fistararriyar yarinyar nan, tana fama da Umaima ta raba su, sai kuma shi ya kawo magana mai
gaba-ɗaya, maganan aure, to ba zai saɓu ba, dole ta ɗau mummunan mataki, wayanta ta ɗauka ta
dannawa layin Danish flashing, saboda cherge's na international call to sai dai ta yi flashing ba daman ƙira.

Ya Danish a nasa ɓangaren daman ya jima yana stumayen ƙiran Umma, dan haka yana ganin flashing nata
ya biyo ƙiran, Umma na ɗauka bata saurari ko sallaman da yake yi ba ta ce, "Danish ni za ka tozarta? Ni za
ka nunawa kai ɗan yau ne? To wallahi idan kaga ka auri yarinyar nan to ko bayan rai na ban amince ba, sai
dai ka mutu babu aure."
Danish ajiyan zuciya ya sauƙe ya buɗe baki zai yi magana, sai Umma ta dakatar da shi ta ce, "Idan ka
kuskura ka ce mini wani abu, to wa billahil Azeem ranka zai ɓaci, kai ka san halina fiye da kowa, to kada ka
yarda rai na ya ɓaci..", Umma na gama masifanta ta kashe wayanta tana huci.

Haka Umma ta wuni da bala'i da masifa, abin na cin ta kwata-kwata ta kasa haƙuri ta kasa nistuwa, har
yamma ta yi ta kasa haƙuri, wani abu ke ingiza ƙeyanta zuwa gidan Mami.

Yau har ƙarfe shida ta same mu a makaranta, sai da ta ɗora da mintuna sannan aka tashe mu, muka kamo
hanya muka dawo gida, Umaima ta wuce nasu nima na wuce namu gidan.

Muna zaune da Mamina bayan sallahn isha'i sai kawai ganin mutum muka yi a kan mu ba ko sallama, daga
ni har Mamina da mamaki muke kallon Umma Sabeera, dan nidai a iya sanina ban taɓa ganin ta shigo
gidan mu ba.

Kamun Mami ta yi wani yunƙurin buɗe baki tayi magana sai gani muka yi Umma Sabeera ta fito da wuƙa,
ta yi kan Mamina gadan-gadan, ihu na stala na yi kan Umma ina faɗin, "Me muka miki? Kashe mu za ki yi
Umma? Dan Allah ki yi haƙuri."

Umma tureni gefe tayi tana faɗin, "Wallahi idan ke mayya ce yau sai na kashe ki kowa ya huta, idan ya so
nima a kashe ni, haba dan Allah kin dameni kin addabeni kin staya mini a maƙoshi, abun ya wuce na aure
mini miji da za ki yi, ya koma har yarona kuka lashewa zuciya yana son yarinyarki, to indai ina raye ko aure
ɗaya ba zai ƙullu ba, wallahi ba za mu haɗa jini da karuwa kuma mayya ba."
Mami ƙoƙarin kare kanta take yi, amma Umma ta zuciya sosai, ƙoƙarin caka mata wuƙan take a ƙirji, suna
kokowa har dai Allah ya bawa Umma nasaran caka wa Mami wuƙa a ciki, ihun da Mami ta yi shi ya tattaro
mini sauran ƙarfin jikina, da kumburarren goshi na mike, na rarumi tire a gefe ba ƙwalawa Umma a kai,
faɗuwa ta yi, ga Mami a kwance cikin jini ga kuma Umma a kwance a sume, ihu na kuma saki na fice a
gidan da mugun gudu, cikin anguwa na yi ba hijabi ganin ba mutane sai na juya gidan su Umaima, a bakin
ƙofa na ci karo da Abbaa da ya fito saboda ihuna da yake jiyowa.

Kasa magana nayi sai kawai nuna masa gidanmu nake ina faɗin Mamina, ina kuka, Abbaa bai tsaya
tambaya na ba yayi gidanmu, muna shiga ya ga halin da Umma da Mami ke ciki, bai tsaya tambayan ba'a si
ba ya fice, tare da ya Sadeeq suka shigo, Mami kawai suka saka a mota, nima Ya Sadeeq ya ja hannuna na
shiga muka nufi asibiti, Abbaa ran sa a ɓace ko kallon Umma bai yi ba, General hospital Mubi muka nufa.

⭐⭐

CAS Bunayd suna tafiya yana jan staki ganin irin lokacin da suke ci, tafiya ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, har sai
bayan isha'i suka shigo mubi, hamdala yayi, sannan aka wuce da shi direct General hospital na mubi.


Ayi haƙuri rashin update jiya, jikinne sai a hankali kawai ku ta tayani da addu'a.




# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735

# ������
# � &
# ���



'YAR KARUWA

Officially


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login