Showing 42001 words to 45000 words out of 111817 words

Chapter 15 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf

Advertisement

16 Aug 2025

4078

muci
tare.

Alhaji kuwa yana ficewa a gidan ya je hotel ya kama ɗaki, a can har yayi sallahn Magrib da isha'i, har wajan
ƙarfe tara yana can, gaba-ɗaya damuwa ta cika shi, lamarin Mami ya fara basa storo, niya yayi ya koma
cikin Yola a daren zuwa gobe ya wuce Kano, amma ya kasa baya jin zai iya tafiya bai sanya Ramlatunsa a
ido ba, kwana a hotel ɗin ma ba zai iya ba, haka ya tattara wajan ƙarfe goma ya dawo, lokacin kuma dagani
har Mamina babu wanda ya saka wani abu a cikinsa, Mami ko fitowa bata yi ba, ni kuma na kasa cin
abincin ni kaɗai, sai da Alhaji ya shigo sannan lokacin naji mostin Mamina, har ɗakina ta shigo ta ƙirani
muka je muka ci abincin, Alhaji dai taɓawa kawai yayi dan kar masoyiyarsa taji babu daɗi.

Har muka gama cin abinci na musu sai da safe ba wanda ya yiwa wani magana a cikinsu, nidai ina shigewa
ɗakina na gabatar da abubuwan da suka kamata, sannan nabi lafiyan gadona na kwanta.

Alhaji ma stame hannunsa yayi ya tashi ya shige ɗakinsa, Mami cikin damuwa ta tattare komai, sannan ta
nufi ɗakin Alhaji, lokacin shi kuma ya fito wanka kenan, murmushi Alhaji ya sakar mata ya ce, "Masoyiya je
ki wásta ruwa kema ina zuwa."

Mami jiki a sanyaye ta buɗe baki ta ce, "Alhaji ka yi haƙuri idan na ɓata maka rai.."

Dakatar da ita Alhaji yayi yana murmushi ya ce, "kije ki wásta ruwa ina zuwa, kar ki damu kanki ba komai."

Ba musu Mami ta juya, ɗakinta ta koma ta shige wanka kaman yanda Alhaji ya ce, Alhaji Mukhtar kuwa
murmushinsa yake yi har ta fice, sannan ya shirya, ƙira ne ya shigo wayansa, yana murmushi ya ɗauka tare
da amsa sallaman da aka masa a wayan, cewa yayi, "Allah taimaki General."

General a nasa ɓangaren murmushi yayi ya ce، "Yaya anwuni lafiya ya fama da jama'a?"

"Alhamdulillahi General, ya yaran ya kuma ɗan ka mara jin magana?."

General ɗan dariya yayi ya ce, "yaya wani rashin ji my Man yayi kuma?"

"Au kana tambaya ne? Tun wuri dai ka faɗa masa yabar ƙirana da Sir idan ba haka ba zan saɓa masa, tunda
ya renaka yana faɗa maka General kana amsawa to nidai zan saɓa masa ne, yara ne duk sun mayar da
mutane kaman sa'o'insu."

"Ayi haƙuri yaya."

"Haƙurin dama za ka bayar ai na sani, wannan yaron da macece na tabbata kana aurar da shi za'a dawo
maka da ɗan ka, duk la bi ka sakalta shi ka shagwaɓa shi, Allah ya so ma Sojan sama ya ke, da na ƙasa ne
kam ai nasan ba iyawa zai yi ba, yanzu ma tausayin matar da za ta zauna da Bunayd nake yi."

Dariya General yayi ya ce, "Amma dai yaya ba abinda za mu ce sai godiya, ai in akwai abinda ya fi aikin soja
staff my Man zai iya, kuma ai sojojin sama sun fi na ƙasa baiwa, saboda ikon Allah kawai ke sa mutum yana
sama kuma ya iya yin yaƙi, sannan duk macen da ta samu Bunayd to ina mai tayata murna ta samu miji
nagari."
Girgiza kai Alhaji yayi ya ce, "shi yaron naka ne miji na gari a haka? Allah dai ya haɗa sa da wacce za ta iya
da shi."

General dariya ya kuma yi ya ce, "Nikam ka tuna mini magananmu da shi ranan ma, ya ce na faɗa maka ka
nema masa mata wacce za ta dace da shi, ya yarda zai yi auren, kasan yaron nawa da biyayya yake, ga jin
magana."

Taɓe baki Alhaji yayi ya ce, "Ni ba zan nemawa Bunayd mata ba ya zo ya sa naji kunya, kai dai da kake
ubansa sai ka nema masa, koma mene stakaninku ni nawa kallo, yadai tabbatar ya samu matar dan na gaji
da kallonsa haka, mutum na neman kai shekaru arba'in amma ya kasa ajiye mata."

Cikin raha da ɗan faɗa-faɗa Alhaji yayi waya da General har suka yi sallama kaman kada su kashe, General
ma ya sanar da Alhaji za su shigo duka da yaran Insha Allah ba jimawa, Alhaji ya ce Allah ya kawo su lafiya,
bayan sun yi sallama sai Alhaji ya miƙe dan tafiya ga masoyiyarsa, yana buɗe ƙofa zai fita ita kuma ta sako
kai za ta shigo har kusan karo suka yi, kallonta yayi yana murmushi ya ce, "Na ɓata lokaci ko Hajiyata?"
Mami jinjina kai kawai tayi ta juya, ɗakin Mami suka shiga, Alhaji ya samu waje ya zauna, ta zauna gefensa,
dukkansu shiru suka yi, sai Alhaji ne ya gaji da shirun ya ce, "Allah ya baki haƙuri, Allah ya huci zuciyanki
Ramlatu."

Ajiyan zuciya Mami ta sauƙe ta ce, "Kai ma Allah ya huci zuciyanka Alhaji, in Allah ya yarda ba jimawa zan
sanar da kai komai a kai na, ka yi haƙuri."

Murmushi yayi ya ce, "Bakomai Ramla, yauwa inason faɗa miki daman, bayan kyautan da zan wa Banafsha
idan Allah ya sa result nata yayi kyau, to yanzu ina son kiyi haƙuri ki barta ta riƙe waya."

Mami ba tare da ta ɗaura idonta akan Alhaji ba ta ce, "a'a Alhaji ba yanzu ba tukunna."

"Meyasa ba yanzu ba Ramla?" Faɗin Alhaji yana kallon Mami.

Mami ta ce, "Alhaji har yanzu Banafsha yarinya ce, bana son waya ya zama sanadiyyar lalacewan tarbiyan
ta, nafi son idan ta samu miji to Masha Allah! Idan ya aureta sai ya saya mata, nan ba mastala matarsa ce,
amma ni yanzu storon yarinya ta riƙe waya nake yi."

Murmushi Alhaji yayi ya ce, "Eh to wani gefen da gaskiyanki, wani ɓangaren kuma ba gaskiya a magananki,
domin komai da kike gani a rayuwa yana da ɓangare mai kyau da kuma ɓangare mara kyau, tabbas a
wannan zamani da muke ciki, ƙaramin abu ne yarinyarka a ɓata mata tarbiya ta waya, musamman
ƙawayen banza da fasiƙancin neman jinsi yayi yawa, ko kuwa ɓata garin samari, amma fa ina son ki sani,
wani a wayan nan zai iya shuka abin alkairin da zai kai sa aljanna, sannan wani a babu wayan ma yana iya
lalacewa, addu'a ita ce ke stare komai ta kare kowa, Banafsha yanzu ba yarinya ba ce, ko saboda abinda ya
shafi makaranta yana da kyau ki barta ta riƙe waya, yanzu suna final year nasu ne, to wani abun tana
buƙatan waya."

Mami shiru tayi bata ce komai ba, ganin haka kuma Alhaji yasan me take nufi na bata yarda ba, sai kawai
ya ƙyale maganan, nan suka kama hiransu kaman ba abinda ya haɗa su ɗazu har Mami ta fara gyangyaɗi,
Alhaji ya ce su kwanta, ba jimawa Mami tayi bacci shi kuma Alhaji a sulale ya tashi ya fice a ɗakin.

Washe-gari da wuri Banafsha ta tashi sakamakon ranan asabar ne akwai zuwa tahfiz dan ba su da lecture
ba za su shiga makaranta da wuri ba.

Banafsha na fitowa gida sai ga Umaima na ƙoƙarin shigowa nasu gidan, murmushi suka sakarwa juna,
Umaima ta ce, "Masoyiya muyi sauri lokaci ya ƙure kada muyi latti."

"Aikam muka yi latti akwai mastala, yau ba shiga aji kenan sai dai mu dawo mu wuce College dan ba mai
taɓa mini lafiyar jikina" na faɗa tare da riƙe hannun Umaima muna tafiya, muna hiranmu a haka har muka
isa, Allah ya taimake mu ba'a fara tare lattin ba.

Mun yi karatun ranan mun gama har aka tashemu, mun fito muna tafiya ta hanyar da muke bi ta cikin
anguwa, sai gani muka yi mutun ya tsaya stegege a gabanmu, ganin wanene dukkanmu sai muka haɗa
fiska, Umaima ce ta buɗe baki tana hararansa ta ce, "Malam me damuwanka da mu? Yau kuma da me ka
zo?"
Garba kallon sama da ƙasa ya yiwa Umaima ya ce, "ke mastalana da ke shishshigi ya miki yawa, ina
ruwanki? Ko na miki magana? Na taɓa ƙiran sunanki? Dan Allah ki ƙyaleni nayi da wacce take gabana."

A zuciye Umaima ta buɗe baki za tayi magana amma sai na dakatar da ita, kallon uku saura kwata na wásta
masa sannan na riƙe hannun Umaima muka wuce, amma still Garba ya ƙara stayawa a gabanmu, a hasale
na ce, "ka ɓace mana a hanya."

Murmushi Garba yayi yana shafa suɗaɗɗen kansa da yaji askin tanƙwal ya ce, "stakani da Allah na kasa
nistuwa, wallahi soyayyanki ta mini mugun kamu, ni ba ruwana da sana'ar babarki, dan Allah ki so ni, kiyi
haƙuri da abinda na miki ranan."

Hararansa nayi kawai naja Umaima muka wuce abinmu, duk magiyan Garba ko ta kansa ba mu bi ba.

Muna komawa kuma muka shirya shirin tafiya makaranta, Alhaji ne ya kai mu bayan ya gama jinjina mana
na ƙoƙarin da muka yi, ya ce da Umaima ma ta dage nan gaba kada ta yi bracket, mudai cewa muka yi mun
gode, yana sauƙe mu muka shige school, class da muke da shi sai wajan ƙarfe sha biyu, mun yi kuma, mu
ne bamu bar makarantan ba sai wajan ƙarfe uku na yamma, muna dawowa Umaima ta shige gidansu na
shige namu.

Mami da Alhaji na samu suna zaune suna hiransu da fara'a, gaishesu nayi sannan na shige ɗakina, wanka
nayi tare da yin sallah, duk da yau ina jin wani yanayi hakan nan, marana ya fara ciwo-ciwo ga ƙafana ya
fara kama mini, haka dai a daddafe nayi ayyukan da zan yi ma gida na shirya zuwa tahfiz na yamma, da
Umaima muka tafi, yau bayan antashi Malam Abbo ya faɗa mini anjuma zai zo wajena akwai maganan da
yake so muyi, nidai nasan ban aikata wani laifin ba, amma na amsa masa sai ya zo, muna komawa gida na
samu Alhaji da Mamina za su fita, nima ta ce na shirya muje wanke kai, na ce a'a ni sai gobe, a dawo lafiya
na musu, kallo na kunna kawai na kwanta amma inajin ciwon maran nawa na ƙaruwa.

Abbaa tunda Ya Danish ya zo jiya ba su zauna ba, sai yau ya faɗa masa da dare yana son magana da su shi
da Ya Farooq, duk amsawa suka yi, dare nayi bayan sun yi sallahn isha'i suka amsa kiran Abbaa, a palournsa
da ke cikin compound ɗin gidan suka zauna, ga Umma ga Ummu gasunan su ma, Abba gyaran murya yayi
tare da mayar da kallonsa kan Umma ya ce, "Sabeera da ke zan fara, saboda kece babba kuma mahaifiya,
duk turban da kika nunawa na ƙasa da ke, musamman yaranki to shi za su bi, duk da bansan me yarinyar
nan Banafsha da mahaifiyarta suka tsare miki ba, amma na sha faɗa miki ki gyara halayyanki akan su,

inason ki faɗa mini me mastalarki da su, dan duk abinda kuka yi ranan da matar kabeeru ya dawo
kunnena."

Umma Sabeera ɓata fiska tayi ta ce, "Ni ba abinda suka stare mini, halayyan mahaifiyarta ne kawai bana
so, kuma ta dena shiga stabgan yarinyata kada ta lalata mini tarbiyaanta, gida kuma ka ce naka ne, dan
haka ta shigo banda mastala."

Jinjina kai Abbaa yayi ya ce, "Hakan yayi kyau tunda kinsan gida nawa ne, kuma sai wanda na bawa ikon
shigowa zai shigo, dan haka kuma ina son ki sani ita Umaima ma yarinyata ce dan haka ni mastayina na
mahaifinta na bata daman kula Banafsha da shiga gidansu, in kuma kin ce a'a sai ki nema mata wani uban
bayan ni, lalacewa kuma idan Allah ya rubuto mata a ƙaddaranta to ko a ɗakin ki take akan gadonki to sai
ta lalace, sannan akan abinda kuka yi ranan zan ɗau mataki ba shiru nayi da na ƙyale ba" Abbaa ya faɗa
ransa a ɓace.

Umma dai fiskan nan a haɗe, Ummu kuwa kanta na ƙasa ma, Abbaa kallonsa ya kuma mayar wa kan
yaransa ya ce, "Ku ma na dawo kanku, musamman kai Danish, kasan abinda ka aikata ba sai na faɗa ba,
inason ka sani kai baka isa ka sani jin kunya ba, ni kuma ban haifi mara mutunci a cikina ba da yardan Allah,
idan ka ƙara kuskuren aikata irin wannan abun ba iya ga Banafsha ba, wallahi ko a can wajan aikinka naji
labari to ka tabbata zan cireka a cikin yarana, ka ji wallahi na ranste maka, bana son hauka da rashin
hankali, ina ruwanku da rayuwar su? Haka Allah ya iyo su kuma haka Allah ya so ganinsu, kowa da
ƙaddaransa da kuma jarabawansa, su wannan ne jarabawansu, ku zo a banza kuna uzzurawa kanku akan
rayuwan mutanen da ba ruwansu da ku, kuma wataƙila a wajan Allah sun fi ku mastayi da komai, ni ba
wanda ya bani mamaki sai kai Danish, da iliminka da tunaninka da tarbiyyanka da hankalinka, a bari ita
mahaifiyarka da matar wanka su mata ne, kuma mata daman tunaninsu sai a hankali, amma kai za ka haɗa
lissafinka da nasu kana na miji wanda ya isa ajiye iyali, to idan ka kuma gigin aikata irin wannan kuskuren
ranka zai yi mugun ɓaci, yarinya da tarbiyyanta da komai ta fi wani wanda ya ke ɗan babban Malami
nustuwa da komai amma kana neman aikata mata ba dai-dai ba, to wallahi kana ji na ka kiyaye, kuma daga
kai har ɗan uwanka ina mai umurtanku da ku fito da matan aurenku akan lokaci dan ba zan ɗau wannan
shirmen ba, tun kamun ku fara lalata yaran mutane gwanda na muku aure ku ɗin ma tunda duk kun kai
riƙe iyali har kun kai zama iyaye ma, abinda ya sa nayi ƙiranku kenan, kuma duk wanda ya ɓata lokaci zai ga
matakin da zan ɗauka, fatan kuna ji na Danish da Farooq?"

Dukkansu ɗaga kai suka yi alaman sun amsa, sannan Abbaa ya ƙara musu faɗa sosai ya ce ya sallamesu, su
tashi su basa waje, miƙewa suka yi suka fice, Danish fiskansa a haɗe, Farooq dai murmushi yake yi.

Bayan fitan su Danish Abbaa ya kalli Umma ya ce, "Sabeera na ƙara dawowa kan ki, ki sani kema abinda
kika aikata zan ɗau mataki a kansa ba wai na yi shiru ba ne, matar dai da kika bi kika gallazawa kanki akan
ta kuma bata san kina yi ba, to ina so ki sani ita zan auro, wataƙila idan na aureta to za ki dawo hanya ki
koma hayyacinki, yarinyar ma nan za ta dawo da zama, kuma kika kuskura kika ce za ki aikata wani rashin
hankalin to zan nuna miki abinda ke kai na ya fi naki, ai mutum ba shi yake yin kansa ba, dan mahaifiyarta
na zaman kanta, ai ba yana nufin a staneta a stangwameta ba, ko akwai wanda yake zaɓawa kansa daga
cikin iyayen da zai fito? Kowa da kike gani Allah ne ya riga ya gama stara komai a kansa tun fil'azal, dan
haka ki dawo hayyacinki, bai kamata ke da za ki yiwa wasu faɗa, a ce ke da kanki kike aikata hakan ba, idan
kuka tsamgwami yarinya kuka dinga kyamatarta, wani hali kuke tunanin za ta faɗa? Ai sai ta zaɓi ita ma ta
shiga duniya tunda haka al'umma ke mata kallo, duk irin munin halin mutum, maganin zama da shi ake
sha, sannan a ja shi a jiki a dinga nusar da shi gaskiya ana nuna masa abinda ya kamata, amma idan aka
dinga ƙuntata masa to gaba-ɗaya ba za'a ribatu da mutum ba, yanzu idan yarinyar nan ta lalace kuma wani
a yaranki ya bi ta shi ma ya lalace ya za ki ji? Kuma wa gari ta waya? Amma idan ta shiryu bata lalace ba ai
ko ke hankalinki a kwance kinsan yaranki ba za su bita da ɓatanci ba idan ba maganan arziƙi ba, ba'a
kyamar mutum ko ƙuntata masa ko da kafiri ne balle kuma musulmi wanda ya ke salla kai ma kake sallah,
ya ambaci Allah da Manzonsa kai ma ka ambaci Allah da Manzonsa, akwai wani kissa na wani sahabin
Manzon Allah SAW da ya kwanta mini, amma dai shi ma akwai wani abu da yake yi wanda ya zamana
mutane na ƙyamatan shi, amma Annabi ya nusar da su hakan ba kyau ya ja bawan Allahn a jiki, daga

ƙarshe sai da ya zama sahabi mayaƙin Annabi SAW wanda ake ji da shi, to ba'a rena ɗan Adam duk yanda
ya je kuma ba'a ƙuntata masa, misalai dai da yawa akwai su kuma Annabi da kansa yayi magana akan
hakan, dan Allah dan Annabi ki kiyaye Sabeera, wannan yarinya tamkar Umaima haka take a wajanki,
Ummu-khultum ke ma abinda ya sa na ajiye ku, duk so nake ku gyara, mu gudu tare mu stira tare, duk da
bantaɓa jin kin yi musu wani abun da ba dai-dai ba amma a kiyaye saboda zuciya watarana sai a hankali,
kuma ku yi haƙuri amma zan ƙara aure, Insha Allahu dai ita Maman Banafsha zan aura, fatan za ku bani
haɗin kai kuma ku ci gaba da tayani da addu'an alkairi."

Ummu tana murmushi ta ce, "Allah taimaka ya kuma tabbatar da alkairi, Allah shige mana gaba ya sa mu fi
ƙarfin zuƙatanmu, Allah kuma ya baka ikon yin adalci."

Murmushi Abbaa yayi ya amsa da Ameen, sannan ya dubi Umma ya ce, "Sabeera ke kuma ba ki da abin
cewa ne?"

Umma cikin fushi ta miƙe fuuuu! zuciyanta na tafarfasa kaman za ta kifu akan Abbaa ta ce, "yanzu dan ka
gama rena mana hankali ka rasa wa za ka auro sai gantalalliyar karuwa da ta gama yawon karuwancinta,
wa ma ya sani ko tana ɗauke da ciwo, ka zo ka aurota ka raɓa mana, to wallahi ba da ni ba, kuma ban
yarda ba ban amince ba, idan ma auren za ka yi jaraba na damunka ba ka godewa Allah da mata biyun ba,
to sai dai ka auro wata amma banda wannan wastatstsiyar" tana gama faɗa ta fice.

Abbaa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login