Showing 21001 words to 24000 words out of 111817 words
Chapter 8 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf
na goge su ko na hana su
gangarowa ba na sauƙe ajiyan zuciya da kuma hamdala, ko babu komai zan ji sanyi a rai na idan nayi
hawayen, tun ranan na kasa kuka balle hawaye har yau, kuma zuwa makaranta ya zamo mini dole, sannan
dagewa da karatu ya zamo mini dole shi ma, a hankali na buɗe baki da muryana da ke rawa na ce, "Malam
zan je makarantar Insha Allah, kuma zan dage sosai, mun gode Allah saka da alkairi."
Murmushi Malam Abbo ya saki wanda nima Uwar batoorl bansan na me bane, amma dai da alama da
wani abun, cewa yayi, "ki mini magana da Umma zan tafi."
Tashuwa nayi na nufi ɗakin Mamina, da sallama na tura ƙofan na shiga, bayan ta amsa mini, na faɗa mata
Malaminmu na mata magana zai tafi, Mami ta amsa akan tana zuwa ni kuma na juya na koma palourn,
samun Malam Abbo nayi har ya miƙe ma, kallo ɗaya na masa na ɗauke kai na faɗa masa tana zuwa, ban
gama rufe baki ba sai ga Mamina ta iso, Malam Abbo durƙusawa yayi yana faɗa wa Mami zai tafi, ni kuma
gaba nayi na fice ma a palourn gaba-ɗaya ina yabawa da girmama Mamina da Malam Abbo yayi, sosai naji
daɗin yanda yayi ba tare da girman kai ba.
Mami ganin na fice a palourn sai ta buƙaci Malam Abbo ya tashi, tashuwa yayi ya zauna ita ma ta zauna,
kansa a ƙasa cikin ládabi ya ce, "Umma mun gama magana da Malama Faɗima, kuma nayi duk abinda ya
dace wanda nasan zai sa ta dawo normal, Insha Allah ina da tabbacin har makarantar bokon za taje."
Mami farinciki kaman tayi yaya, tana murmushi da jinjina ƙoƙarin Malam Abbo ta ce, "Nagode sosai
Malam, Allah saka da alkairi, Allah maka albarka, Nagode sosai."
Malam Abbo miƙewa yayi bayan sun gana magana ya fice, Mami sai godiya take masa, ta miƙa masa kuɗi
ma ya ƙi amsa, a stakar gidan suka same ni staye, Mami ta dubeni ta ce, "Banafsha sai ki takawa malamin
naku ko."
Amsawa Mami nayi, ita kuma ta juya ta koma cikin gida cike da farin ciki, ko ba komai yanzu 'yar ta za ta
saki ranta, ta daina saka damuwa a ranta.
Ni kuma kaman yanda Mamina ta faɗa hakan nayi, tare muka fice da Malam Abbo a gidanmu, yana min
faɗa, cewa yayi, "Malama Faɗima, komai na rayuwa da kike gani haƙuri ake yi da shi, kuma ƙoƙari ake yi
wajan ganin mutum ya cinye jarabawan mahaliccinsa, saboda samun gwaggwaɓan rabo da sakamako mai
kyau a duniya da kuma ranan karɓan sakamako, ita kuma jarabawa a zagaye da mu take ko ta ina, a iya
karatunki nasan kin sani, ayoyi da dama na ƙur'ani sun kawo hakan, sannan akwai wasu hadisan ma da
suka kawo haka, Malama Faɗima hatta rayuwa da kike gani da Allah ya mana ya kuma azurtamu da lafiya
to shi ma jarabawa ne, Allah ya jarabce mu da lafiya ne dan ya ga ya za mu yi da lafiyan, aljanna za mu
nema da shi ko kuwa za mu dage wajan saɓa masa ne, rashin lafiya ma jarabta ce dan ya ga mutum zai yi
haƙuri ya yarda da Allah ne ya ɗaura masa cutan ko kuwa zai dinga zargin mutane akan da saka hannunsu,
haka zalika akan dukiya da rashin dukiya, akan haihuwa da rashin haihuwa, akan tashuwa ka rayu da
iyayenka da kuma rayuwa ba tare da su ba, haka akan aure da rashin yin aure, komai da yake zagaye da
ɗan Adam na jarabta ce daga mahaliccinsa, kuma Allah na so ne mu ci wannan jarabawan, ina fatan kin
fahimta kuma za ki dage wajan ganin kema kin cinye naki jarabawan?" Faɗin Malam Abbo da ya dakata da
tafiya ya zuba mini idanuwansa dai-dai mun shige ƙofan gidan su Umaima, kuma cikin rashin sa'a sai ga Ya
Danish a waje shi da abokinsa kasancewan yau Lahadi yana gida bai koma ba tukunna.
Ya Danish yana zaune a bayan motansa, sai abokinsa ɗaya na zaune a plastic chair, da kuma Ya Farooq
shima yana zaune a kujeran roba, ya Farooq ɗan farin Ummu ne, kuma kusan sa'a haka suke shi da Ya
Danish, shiyasa suke yawan zama tare, muddin Ya Danish na gari to za ka gansu tare da wannan abokin
nasu mai suna IB.
Ya Danish tun fitowanmu idanuwansa suka sauƙa a cikin nawa, wani irin kallon banza kallon tsana yake
jifana da shi, ni kuwa ganin ya zuba mana ido sai na dinga sakarwa Malam Abbo murmushi, har dai muka
tsaya ɗan gaba da su kaɗan, wani kallo na yiwa Ya Danish wanda shi kaɗai yasan fassaranshi ta 'yar staman
da ke tsakaninmu, sannan na mayar da hankalina kan Malam Abbo ina masa magana, Ya Danish kuwa a
nasa ɓangaren wani wawan dogon staki ya ja, wanda sai da Ya Farooq da ya IB suka tambayesa menene,
amma ya musu banza.
Idanuwana akan malam Abbo ina ƙayataccen murmushi na ce, "in Allah ya yarda Malam zan dage, wajan
ganin na cinye tawa jarabawar, sannan na maka alƙawarin dagewa a karatu da zuwa makaranta, nagode
sosai Malam, Allah ya biya ka da mafificin alkairi, Allah ya biya iyayenka da aljanna, Allah ya sa ka rabu da
su lafiya nagode sosai."
Tunda na fara magana Malam Abbo ya zuba mini idanuwansa masu ɗauke da sinadaran da ke saka ni jin
kunya, amma duk da haka ban kawar da nawa idon ba sai ma wani murmushin da nake sakar masa, wanda
duk saboda Ya Danish na daure nake yin hakan, shi kuwa Malam Abbo tuni ya susuce wajan kallona, inada
tabbacin ya tafi wata duniya ta daban, ganin kaman hankalinsa ba ya wajan sai na ɗan mosta yastuna a
gaban idanuwansa na ce, "Malam muje ko."
Firgit Malam Abbo ya dawo daga duniyan da yake, yana mai dannewa dan kada na fahimta, ganin har
yanzu da murmushi akan fiskana sai shi ma ya sakar mini tare da faɗin, "Malama Faɗima rakiyan ya isa
haka, ki juya nagode ko."
Ba tare da musu ba na gyaɗa kai tare da masa addu'an a koma lafiya na ƙara da godiya, ban juya ba sai da
Malam Abbo ya juya ya fara tafiya, na ɗaga masa hannu sannan ganin ya ɓacewa ganina sai na juyo ina ta
murmushi ni kaɗai, har na mance da abinda ke damuna domin kuwa nasihan Malam Abbo ya shiga jikina
ba kaɗan ba.
Ina juyawa kuwa idanuwana karaf a cikin na Ya Danish, wani killer smile na sakar masa tare da cigaba da
tafiya na, wannan karon ma ƙwafa Ya Danish yayi, wanda ya sanya su Ya Farooq bin inda yake kallo da
idanuwansu, Ya Farooq suna ganin ni ce sai kawai suka yi dariya, daga Ya Farooq har Ya IB sun san za'a rina,
Ya Farooq ne ya ƙwala mini ƙira tare da cewa Ya Danish, "Amma dai ka ji jiki wallahi, Allah taro ka Danish,
ka saki ranka ka daina haushi da yarinya a banza, ita bata damu da tsabgarka ba amma ka bi ka azalzali
yarinya."
Ya Danish kallon banza ya yiwa ya Farooq tare da yin ƙwafa, ni kuwa ganin ya Farooq ne ya ƙira ni sai na
taho cikin tafiyana ta nistuwa da ɗaukan hankali, har na iso inda suke zaune, ɗan rusunawa nayi na ce, "Ya
Farooq ina wuni, Ya IB barka da yamma."
Ya Farooq da Ya IB duk amsawa suka yi da murmushi, Ya Farooq ya ce, "Daga ina haka da yamman nan
sistor?"
Langwaɓar da kai nayi gefe guda tare da kulle idona ina murmushi na ce, "saurayina ne ya zo zance, shi ne
na rakasa."
Tun kamun na rufe baki ya Danish ya ja wani dogon tsaki, daman shi kaɗai ya ganni basu ganni da saurayin
ba, kuma ga haushin na gaida su ban gaishe sa ba saboda na renasa, Ya Farooq ko kallon Ya Danish bai yi
ba duk da yasan yayi tsaki, murmushi ya sakar mini ya ce, "inye! Su sistor har an girma an yi saurayi,
daman Umaima ta faɗa mini gobe za ku fara exam's, ashe next year ana gama school sai biki kenan?"
Rufe fiskana nayi da tafin hannayena sannan na Jinjina kai alaman eh, Ya IB ne yayi dariya ya ce, "Yaran
yanzu ba kunya, har da kai kike ɗagawa, shikkenan Allah nuna mana da rai da lafiya, Allah tabbatar da
alkairi."
Da "Ameen" na amsa ina yin ƙasa da kai na tare da wasa da yastu na, Ya Danish da ya cika ya gama cika,
wani banzan tsawa ya mini ya ce, "Keeeeeeeeeeee! Dallah ɓace ma mutane a kai, 'yar iska kawai,
shashasha ƙwaila, mara tarbiyya."
Duk da storon da stawan nasa ya bani amma hakan bai saka na tafi ba sai da na tsaya na sakar masa wani
killer smile ɗin, na kashe masa ido guda na ce, "ai ba'a ɗan iska ɗaya, sai dai biyu, kaga kuwa ni kaɗai ba
iya yin iskancin da kai na zan yi ba, dole tare da kai nake yi" Ina gama faɗan haka na juya na shige
gidannasu, hankalina kwance.
Ya Farooq da Ya IB duk dariya suka kama yi, suna faɗin ai ga abinda suke guje masa kenan, ga shi tun ina
storonsa amma ya saka na daina storonsa balle storon faɗa masa magana, na gaishe da kowa amma banda
shi, kuma duk shi ya jawo ba kowa ba.
A tsakar gidan na haɗu da Umma Sabeera, ɗan rusunawa nayi na gaisheta amma ta aika mini da harara ta
ce, "Ke dan uwarki karuwa ki fice mana a gida tunda ba gidan ubanki ba ne.."
Kamun ta ƙarisa maganan tuni muryan Abbaa ya dakatar da ita, ta hanyar cewa, "Sabeera ki fita a
idanuwana na kulle, ke Faɗima maza zo ki shige inga gidan nawa ne ko nata, idan ta isa ta hana wanda na
bari ya shiga gidan."
Kai na a ƙasa ba tare da damuwa ko ɗigo a fiskana ba, na gaishe da Abbaa ya amsa, sannan na miƙe na
shige gidan ina magana a zuciyata ni ɗaya, ba dan Umma Sabeera na cin albarkacin Umaima da Abbaa ba,
ai da tuni ita ma na fara kasa mata hali na tasan banda sauƙi, ni ɗin do me i do you ce, back to back aradu,
kana mini ina ramawa ba barin bashi kuma ba ruwana da girmanka.
Abbaa ya dubi Umma bayan shigewana ya ce, "Sabeera indai kina da kunya to kin ji shi, ƴar cikinki amma
kike mata abu kaman sa'arki, yanzu da ta rama zagin fa? Ƙawar ƴar ki ce fa ba wai babbar mace ba ce, ki
gyara halinki idan ba haka ba wallahi za ki sa nayi abinda ban yi niya ba, indai akan mahaifiyarta kike
wannan abun, to sai na aure ta naga abinda za ki yi, ko kuwa na zama dadironta na ga ƙarshen rashin
tunaninki da rashin hankalinki..." haka Abbaa ya dinga yiwa Umma Sabeera faɗa kaman wanda aka aiko sa
da wahayin faɗan, ita kuwa Umma wani irin stanata ne ya ƙara rufeta, tana jin za ta iya kasheni ma akan
abinda Abbaa ya faɗa, na ya haɗa alaƙa da Mamina.
Ni kuwa ina shigewa ciki na gaishe da Ummu sama-sama, da yake nasan abinda na shuka a waje da wuri na
fito na ce Umaima ta zo ta rakani, so nake kamun Abbaa ya fita na gudu gida, idan ta Ya Danish ne banda
mastala zan iya tsayuwa mu daku ma, amma kuma Umma ita nake shakka saboda mijinta da 'yar ta, kada
ta ce za ta taɓa ni kuma ba iya ƙyalewa zan yi ba.
Umaima sai mita take daga zuwana zan tafi, ko labarta mata yanda muka yi da Malam Abbo ban yi ba,
haka dai na yafito ta muka fito, Allah ya taimaka lokacin Umma ta shige ɗakin Abbaa da ke ta cikin gidan,
hamdala nayi muka nufi waje, muna ficewa a gidan kuwa muka kusa yin karo da Ya Danish, wani mugun
kallo ya aikawa Umaima amma ta kawar da kai kaman bata ga ni ba, tsawa ya daka mata da mugun ƙarfi ya
ce, "kin juya kin koma gida ne ko sai na iso wajan na ɓaɓɓallaki? Ban hanaki haɗa hanya da yarinyar nan
ba?"
Kamun mu yi wani mosti sai muka kuma jiyo muryan Abbaa, ashe yana bayanmu bai fita ba, dan-ƙwalo ya
aika wa Ya Danish, sannan ya ce, "ke Umaima wuce ku tafi, idan kun je ki kwana a can, sai naga ko akwai
wanda ya haifa mini ke, da zai mini iko da yarinya."
Fakan idon Abbaa nayi na murguɗa wa ya Danish baki tare da gwalo, na kuma masa magana da ido wanda
na tabbata ya fahimci abinda nake nufi, daga kallon da ya mini, jan hannun Umaima nayi muka yi wa
Abbaa sai da safe muka wuce gidanmu, shi kuma ya Danish fasa shiga gidan yayi daga wajan ya shige
motansa yayi gaba saboda Ya Danish akwai zuciya, Abbaa ma wucews inda zai tafi yayi.
Malam Abbo tun da ya juya ya tafi babu abinda yake tinanowa sai murmushin da Banafsha ke sakar masa,
da kuma kallon da take masa, tuni ya ƙara matowa a kanta, nan ya ci alwashin ya kusa bayyanar mata da
saƙon zuciyarsa.
Muna shiga gidanmu Umaima ta dinga dariya kaman ba lafiya ba, kallonta nayi na ce, "an fara sanyi kuma
ai, hauka ta fara mostawa."
Tana dariyan ta ce, "Masoyiya ba za ki fahimta ba, ni ba haukar ce ta mosta ba, abinda Abbaa yayi ne ya
mini sweet, ga shi Ya Danish ya ja an ce na kwana anan, wayyo mi farinciki kashe ni, yau za mu kwana
karatu saboda peppernmu na gobe, Allah ya yiwa Ya Danish albarka, Allah ya sa watarana Umma ma tayi a
gaban Abbaa, ya ce ya bawa Maminmu ni kyauta, heee!hu!hu!"
Hararan Umaima kawai na yi muka shige palourn namu, ban sanar mata abinda ya faru stakanina da
Umma ba ɗazu, domin duk son da Umaima ke mini to fa uwa-uwace, kuma wannan ba baƙon abu bane,
hantara daga wajan Umma da Ya Danish ba sabo bane a wajena.
Da sallama muka shiga palourn amma ba kowa shiru, ɗakina muka wuce direct muka yi alwala tare da yin
sallah, mun idar muka fito palour muka samu Mamina zaune tana cin abinci, ganina da Umaima bata yi
mamaki ba, kuma bata tambaya ba, domin ba wannan ne karo na farko da Umaima ke kwana a gidanmu
ba, ni ce kawai Mamina bata barina na kwana a gidan su Umaima saboda wai gidanmu ya mata girma ita
kaɗai, ta fi son tana jin mostina.
Mami ta sani na ɗebo mana namu abincin, muka ci muna kallo hankali kwance, hira muka ɗan taɓa da
Mami sannan nake faɗa mata ma yanda muka yi da Malam Abbo akan maganan musabaƙa da hukuncin
makaranta, da mamaki dai na kalli Umaima hankalinta kwance bata tashi hankali ba, Mami ce dai ta nuna
ɗan damuwanta sannan ta mana faɗa sosai akan mu dage mu mayar da hankali, ta kuma ƙara mana da
nafilfilu da kuma addu'oe da za muyi saboda exam's da za mu fara gobe da yardan Allah, ba mu wani jima
ba na tashi na shige ɗaki bayan na yiwa Mamina sai da safe, ina shigewa Mami ta dubi Umaima ta ce,
"yarinyar Mami kada ki sanar da ita gaskiyan abinda ake ciki, ki ƙyaleta dai ku dage ku mayar da hankali,
kinga yanzu ta saki ranta, nasan idan ba ta haka aka ɓullo aka mata wayo ba, to Banafsha ta dinga cin rai
kenan."
Murmushi Umaima tayi ta ce, "Insha Allah! Mami ba zan sanar mata ba, zan dai nuna mata nima na damu
mu ƙara mayar da hankali."
"Yauwa ƴar kirki, Allah muku albarka duka ya ba ku sa'a ku ciyo na ɗaya a musabaƙa, flying color result a
boko" cewan Mami tana murmushi.
Umaima amsawa ta yi da, "Ameen" sannan ta yiwa Mami sai da safe ta shige ɗakin Banafsha, Mami ma
hamdala tayi sannan ta kashe kayan kallon ta koma nata ɗakin, sai da ta gabatar da shafa'i da wuturi da
wasu nafilfilun sannan ta kwanta.
Na fito wanka ina ƙoƙarin shumfiɗa darduma Umaima ta shigo, kallon yanayin fiskanta ya sa na tambayeta
ki lafiya, cikin damuwa Umaima ta ce, "Masoyiya maganan musabaƙan nan ne ya dame ni."
Kwantar mata da hankali nayi, na ce mu dage da addu'a da kuma karatu, sannan in Allah ya yarda ni ma
daga yau ba zan sake irin wannan dena zuwa makarantar ba, da ƙyar na shawo kan Umaima ta shige
wanka, tana fitowa ta saka kayana muka yi nafilfilunmu da addu'oe sosai, sannan muka kwanta, da asuba
kuwa muka tashi muka hau karatu saboda exam's.
Ya Danish taƙaici da ya cika sa ya masa dama-dama, ko gidan bai koma ba daga nan ya yiwa motansa key
ya wuce wajan aikinsa da ke Camaroon, idan ya koma Sunday da yamma sai Friday da yamma yake zuwa,
weekend kawai yake zuwa yi a mubi.
# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735
#
# &
#
'YAR KARUWA
Officially
Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)
SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)
TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma ɗaukacin member's namu.
PAGE NAKU NE
Habiba muhammad Yusuf
Ɓingel kabi
My Heartbeat
Masoyiya bealky