Showing 39001 words to 42000 words out of 111817 words

Chapter 14 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf

Advertisement

16 Aug 2025

4051

musu wani irin mugun tsawa
ya ce, "shut-off!!"

Wani irin zabura dukansu suka yi, suka sha nistojin suka koma gefe suka zauna, duk suna muzurai kaman
ba su ke masa shagwaɓa yanzu ba, General da ke zaune a gefe yana kallonsu dariya yayi ya ce, "that's My
Man, yaran nan duk basa ji gwanda ma ka daina musu dariya."

Momsee murmushi ta yi ta ce, "da rabon dai za ka sha kunya Dear.."

Bata gama rufe baki ba kuwa, Bunayd ya nunawa yaran gefensa duk suka masto, murmushi ya sakar musu
ya ce, "Zan kai ku Insha Allah soon, muna zuwa za mu ɗauko Majeeder ita ma ta dawo nan ɗin, sai ku
daina damun mutane da Majeeder-majeeder."

Dukkansu murmushi suka yi, ƙaramar ciki mai shekaru 14 ta rungume hannunsa ta ce, "Allah bar mana kai
Yayanmu, Allah nuna mana matarka da yaranka."

Murmushi yayi ya shafa kanta ya ce, "Ameen Nabeela my love."

General kawar da kai yayi tare da haɗe fiska ya ce, "Daman an ce ba'a shiga tsakanin ƴan uwa, to kun fi
kusa, ni na daina saka baki ma a harkanku, yanzu nasan maganan Nabeel ma haka za ka biye masa, ko a
kanka aka fara yin ƙannene oho, to dai alhamdulillahi nima ina da su Allah ne ya ɗauki abinsa, kuma
ƙannen kowa ma za su mutu."
CAS Bunayd murmushi yayi tare da miƙewa ya je yayi hugging na General ya ce, "Allah huci zuciyan
General namu."

Murmushi General ɗin ma yayi ya ce, "Ameen, kuma Allah ya muku albarka, Allah ƙara haɗa kawunanku,
yana da kyau kuje Kano ɗin, sannan idan zai yiwu ku taho da mamana Majeeder ɗin, duk ku zo mu zauna
ina kallonku hankalina kwance, aikin sojan ma na bar musu."

Duka yaran dariya suka saka har Momsee, Bunayd ya juya zai tafi sai ya tuna glass nasa ya bari a palourn
sama, kallon yaran yayi ya ce, "Suhaila je sama ki ɗauko mini glass na."

Yarinya mai kimanin shekaru 17 ne ta miƙe, da alama ita ce Suhaila ɗin, General kallon Bunayd yayi ya ce,
"ka fa gama aikin naka da wuri ka dawo."

Murmushi kawai Bunayd yayi ya amshi glass nasa da Suhaila ke miƙa masa, ya ce, "goodnight General
namu, Momsee goodnight, my love's goodnight."

Duk amsa masa suka yi, ya fice yana murmushi kawai, dan yasan idan ya staya to General zai iya hanasa
tafiyan ma gaba-ɗaya, General ma da murmushi ya bi sa da kallo har ya fice, sannan ya sauƙe ajiyan zuciya,
kallonsa ya maida kan yaran nasa ya ce, "tunda baku yi wa yayan naku karatunku ya saurara ba, sai ku
ɗauko ƙur'ananku ku kawo ni naji, duk wacce bata iya ba kuma tasan sauran."
Yaran miƙewa suka yi, kowacce ta ɗauko ƙur'aninta, General na sauraran karatunsu, suka gama ya musu
ƙari.

CAS Bunayd yana ficewa a palourn ya maida glass nasa, tare da haɗe girar sama da ta ƙasa, hannayensa ya
jefa a aljihunsa yana taku cikin ƙasaita, yana fitowa tuni aka buɗe masa ƙofan mota, yana shiga aka kulle
suka yi wa mota key, kaman yanda suka zo da mugun gudu haka suka juya da gudun ta da gari, kai sojojin
nan basa tausayin kwalta aradu.
Maimakon su ɗauki hanyan banana island sai suka ɗau wani hanyan daban, a gaban wani ɗanƙareren gate
suka buga horn, suna shigewa suka yi parking, ko da aka buɗe masa ƙofa yanzunma sai da ya ɗau mintuna
sannan ya fito, haɗaɗɗen arnen club ne na gani na faɗa, wanda shegun ƙasa kawai ke zuwansa, wajan ya
haɗu ya gaji da haɗuwa, tun daga haraban wajan za ka ga kowa da gang nasu, daga masu shanye-shayensu
sai masu romance, wasu kuma sex ɗin suke a idon jama'a hankali kwance, mata kuwa gasunan daga masu
yawo stirara, sai masu mutunci waɗanda ke saka pant ba bra ko kuma bra da pant.

CAS Bunayd tunda ya sauƙa a motan matan wajan ke binsa da kallo, wata ma shafe-shafe suke yi da wani
amma ta janye jiki ta tunkaro Bunayd tana girgiza, mata ne suka zagayesa kaman za su yi bandansa kowa
na iya juyinta dan ya gani ko zai ƙyasa, amma kaman yanda suka saba kullum hakan ne ta faru, idan mace
za ta staya setin idonsa ta buɗe ƙafa to ba zai kalleta ba balle yasan da halittanta a wajan, ko kallonsu baya
yi haka ya ci gaba da tafiyansa yana jin waƙansa ta headphone ɗin, sai dai yana ta jan guntun staki kawai
saboda haushi, shi gani yake duk basu waye ba tukunna, basu san rayuwa ba, cikin club ɗin ya shiga, classic
Bar ya nufa, vip na manya, a wani table ya sama wa kansa wajan zama, ga wani ɗan babban mutun da
wata mace suna lashe juna, guntun tsaki ya ja tare ɗan buga table ɗin ya ce, "kabar wannan shashancin ko
nayi tafiyana" cikin yarbanci yayi maganan.

Babban mutumin wanda da alama Yoruba ne, da sauri ya ture yarinyar gefe ya ce, "Yi haƙuri bansan ka iso
ba."

Staki Bunayd yaja ya ce, "kana karɓan salihin iskanci ina za ka sani, da nayi magana kuma ka ji, da yake
Palace ɗin ya jima da hucewa yayi sanyi, da mai ɗumi kake karɓa ai da ko ihu nayi ba ji na za ka yi ba."

Mutumin dai haƙuri ya bawa Bunayd, sannan suka tattauna abinda ya kawo sa, suna gamawa ba ɓata
lokaci ya miƙe, sai da ya je wajan rawa ya ɗan taɓa, tunda mata suka fara yanyame sa ya buga musu rashin
kirki ya fito yana ta jan staki yana cewa, "aikin banza aikin wofi, za ku tadawa mutum Moransa bayan
kunsan Palace naku ya salafce, da masu Palace da ɗumi ake harka ba wanda suka barsa ya gama shan iska
ba", haka ya dinga surutu har ya shiga motansa suka nufi gida, yana isa ya wásta ruwa ya haye makeken
gadonsa yana juyi, ko da baccin ya gagaresa miƙewa yayi ya ɗaura alwala ya tada nafila kawai.



# Hareeyh
# 09161720046

# 07015870735

# ������
# � &
# ���



'YAR KARUWA

Officially




Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)


SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)


TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma ɗaukacin member's namu.


PAGE NAKU NE

Duka members na ƳAR KARUWA FAN'S CLUB na gode sosai-sosai da addu'oenku gare ni, jiki da sauƙi sosai
alhamdulillahi, ina mai fatan kuma kun mini uzuri na rashin ji na kwana biyu zuwa uku, fan's da ke sauran
groups ku ma ina matuƙar Godiya da addu'a, JIKAR IYA fan's, STAR LADY fan's duka da sauran groups da
ban ambaci sunansu ba ma ina matuƙar Godiya da addu'a, kuma wannan page naku ne gaba-ɗaya, lurv
you all ♥️





مهللا ىلص و ملس ىلع ديس ان هللوسر SAW



️ 46 _ 50



Sai can stakiyan dare sannan Bunayd ya shafa addu'ansa ya kwanta, ba jimawa bacci yayi awun gaba da
shi.
**

Ni kuwa Banafsha ina son zuwa wajan Umaima, amma na haƙura na kama kai na, dan tunda naga motan
ya Danish gabana ya faɗi, yanzu ko hanya banason haɗawa da shi, saboda ni ba zan iya haƙura da faɗa
masa magana ba, shi kuma nasan ba zai fasa ci mini mutunci ba.

Wankan juma'a muka yi ni da Mamina dukanmu, idan ka kallemu ka ɗauka ba uwa da ƴa bace, kaman yaya
da ƙanwa haka muke, muna zaune Mamina na mini photo da wayanta sai ga Alhaji ya dawo, duk sannu da
dawowa muka masa, ya amsa tare da miƙo mini ledan staraban juma'a, sai bayan Alhaji ya huta sannan ya
ƙira ni, zuwa nayi na zauna cikin ladabi, duk da banson alaƙan Alhaji Mukhtar da Mamina, amma ya zama
dole a gareni yin biyayya, dole ne a ce da mijin iya baba, yana kula da ni yana ɗawainiya da ni kaman ƴar
cikinsa, kalmansa na ɗazu da ya ce shi angon Mamina ne da yardan Allah sai ya sa stanansa da nake ya ɗan
ragu, yanzu ba abinda ya rage mini sai dagewa wajan ganin Mamina ta yarda da maganan auren, tunda na
ga alaman ita ce bata so.

Alhaji hankalinsa ya mayar kai na ya ce, "Banafsha a bani labarin yanda musabaƙan ta gudana."

Kai na a ƙasa na fara zayyanowa Alhaji komai yanda aka yi, da matuƙar farinciki ya ce, "ke ɗin ce dai kika zo
ta ɗaya?"

Jinjina kai nayi alaman eh, nima fiskana ba yabo ba fallasa, Alhaji kabbara yayi ya ce, "Masha Allah! Lallai
kinyi ƙoƙari, kuma abu ya mini daɗi sosai ba kaɗan ba, yanzu dai yaushe kuma za ku yi na cikin
Adamawan?"

"In Allah ya yarda ba jimawa, duk da dai ba su faɗa mana ba, an dai ce mu dage da karatu, kamun su
yayemu ne za'a yi har na State da State duka Insha Allahu" na faɗa kai na a ƙasa.

Alhaji murmushi yayi ya ce, "Allah nuna mana da rai da lafiya, amma yaye ku ɗin zai kai shekara ne?"

"A'a, watanni ne kawai in Allah ya yarda."

"To Masha Allah! Yanzu dai nima akwai nawa kyautan da zan miki bayan na makaranta, amma dai bari mu
jira fitowan result naki tukunna, idan shi ma yayi kyau, to sai ki faɗa duk abinda kike so Insha Allah, idan
bai fi ƙarfina ba zan miki shi."

Murmushi nayi kawai kai na a ƙasa na ce, "Nagode, Allah ƙara girma ya ƙara buɗi."

Mamina da murmushi ta shigo palourn ta zauna ta ce, "Banafsha je wajan Ummunku za ta baki saƙo ki
kawo mini."

Miƙewa nayi na je ɗaki na sako hijabi na, sai na dawo na yiwa su Mami na fice, tunda na fito a gidanmu
gabana ke faɗuwa dan bana son ganin ya Danish, sai dai Allah ya taimake ni ban hango motansa a waje ba,
har na shiga cikin gidan duka ban ga motansa ba, hamadala nayi na shige da sauri, da Umma na fara yin
tozali, tuni na kawar da kai na ban ƙara kallonta ba, dan gani nake idan na ganta ma ya Danish nake kallo,
daga nesa na ce, "Umma barka da yamma."

Tsaki kawai Umma ta ja, wanda ina da tabbacin har da harara ta haɗo mini da shi, ban staya ƙara yin wani
maganan ba na nufi ɗakin Ummu, kuma dai-dai lokacin ta fito, sai da naga Ummu sannan na saki raina na
yi murmushi, ita ma Ummu murmushin ta mini ta ce, "ƴar gidan Maminta an shigo ne."

Ɗaga kai nayi ina buɗe haƙora na, gaishe da Ummu nayi ta amsa, sannan na ce, "Ummu inji Mamina wai
na zo za ki bani saƙo na kai mata."

Murmushi Ummu tayi tana miƙo mini saƙon ta ce, "Daga zuwa sai tafiya, yau ko ta kan Umaima ba za'a bi
bane?"

Ni gaba-ɗaya da yake cikin sauri nake nabar gidan, sai yanzu na tuno da wata Umaima ma, sosa kai nayi na
ce, "Ummu bari na dubota, idan na fito sai a bani saƙon", ina gama faɗa na juya na shiga ɗakin su Umaima
da sallama.

Umaima baccinta take sha hankali kwance, ganin haka kawai na ƙyaleta na fito, ba dan ina sauri banson
haɗuwa da ya Danish ba ai da na sola mata dundu na tashe ta, kawai ta ci sa'a ne, faɗawa Ummu nayi tana
bacci a bani saƙon kawai na tafi, Ummu ta bani na amsa na musu sai anjima na fice.

Bayan fitan Banafsha a palourn sai Mami ta tashi a inda take zaune ta dawo kujeran da Alhaji ke zaune,
kallonta Alhaji yayi yana murmushinsa ya ce, "Amaryata ya aka yi?"

Tura baki Mami tayi da shagwaɓa ta ce, "kaga banaso Alhaji, haka kawai za ka ɓata mini rai, ni bansan ma
me yasa nake sonka har haka na kasa rabuwa da kai ba, kuma kullun cikin ɓata mini rai kake yi, yanzu ko so
na ka daina kullum faɗa kake nema da ni", ta faɗa tana juyawa wai tayi fushi.

Murmushi Alhaji yayi ya ce, "Allah ne ya ɗaura miki soyayyata kaman yanda nima ya ɗaura mini ƙaunarki
da sonki, kuma in Allah ya yarda zan mallakeki, nidai yanzu roƙo na ɗaya ki faɗa mini abu game da
danginki, kinƙi bani labarinki kuma kinƙi aminta da aurena, meyasa kike mini haka Ramla? Ina sonki da
yawa fa ki taimakeni ki amince da auren nan dan Allah, kar Banafsha ta samu miji a ce za'a yi bikinta kina
zaman kanki, sam-sam abin bai yi tsari ba, dan Allah ki amince da maganan auren nan Ramla, wallahi ni
kaɗai nasan halin da nake ciki na rashin mallakanki, ni ba zan iya ci-gaba da saɓa wa Allah ba balle na kai
ga aikata babban zunubi, ita zina bashi ce kayi da mahaifiyar wani sai anyi da taka, ka yi da ƴqar wani sai
anyi da taka, kayi da matar wani sai anyi da taka, kayi da ƙanwar wani sai an yi da taka, ni kuma ko ɗaya
bana addu'an haka, dan Allah Ramla ki amince mini muyi komai akan Sunna."

Mami ɓata fiska tayi ko kallon Alhaji taƙi yi, Alhaji kaman zai yi kuka ya kamo hannun Mami amma ta
ƙwace, riƙo hannunta ya kuma yi ya ce, "Please Ramla say something, dan Allah ki ce kin amince, ko
mutum daya a danginki sai mu nema a mana aurenmu, idan bakya so ma sai a ɗaura mana haka al'umman
Annabi su zama shaidu da waliyai, dan Allah Ramla, wallahi na miki alƙawarin zamowa uba nagari abin
alfahari ga yarinyarki da ma sauran da za ki haifa mini, na miki alƙawarin zamowa miji na gari jajirtacce
gare ki, wanda zai tsaya miki a komai ya kuma kula da duk abinda ya shafe ki, sam-sam kada kiji da matata
kiyi tunanin ina da mata, banda zafi kam, amma na isa da gidana, dan Allah ki ce kin amince."

Zuwa yanzu Mami ji take kaman ta kwaɗawa Alhaji mari, sai ƙoƙarin kwace hannunta take yi, ƙarshe Alhaji
kawai sai ya rungumeta ƙam a ƙirjinsa, a take suka sauƙe wani nauyayyen ajiyan zuciya kaman waɗanda
suka yi kokawa ko kuma suka yi gudu, Mami lafewa tayi a jikin Alhaji, ba zato ba tsammani yaji hawayenta
na ɗiga a kan hannunsa, Alhaji hankalinsa a tashe ya dubeta cikin damuwa ya ce, "Ramla akan aure kike
kuka? Dan na ce ki amince ki aure ni? Shikkenan kiyi haƙuri Allah huci zuciyanki, dama kullum idan nayi
magana a faɗa muke ƙare wa hakan baya damuna، to faɗa da sauƙi akan hawayenki, hawayenki masu
stada ne a gare ni ba zan jure zubansu ba, idan wani yayi sila ma sai inda ƙarfina ya ƙare balle a ce ni da kai
na, Allah ya baki haƙuri, in Allah ya yarda daga yau na daina miki maganan aure, in Allah ya ƙaddara hakan,
to Allah fahimtar da ke da kansa ya tabbatar mana da alkairi, inkuma babu hakan a ƙaddaranmu shi ma
Allah zaɓa mana abinda ya fi alkairi, Allah bamu ikon tuba kamun mutuwa, Allah sa mu gama da duniya
lafiya muna amintattun bayi salihai", Alhaji na gama magana ya miƙe ya ɗau key na motansa ya fice.

Mami zama tayi a wajan tana risgan kukanta kaman wacce aka aiko wa saƙon mutuwa, a haka har
Banafsha ta shigo ta sameta tana kukan, bata ma ji shigowanta ba sai ji tayi muryanta na rawa tana faɗin,
"Mamina me ya sameki? Me ya faru?" Haka na ƙarishe maganan nima cikin tashin hankali ganin Mamina
na kuka."
Mami ƙoƙari tayi ta stayar da kukan ta ce, "Bakomai Banafsha, ki ɗaura mana abincin dare", tana gama
faɗa ta miƙe ta amshi saƙonta ta shige ɗakinta, ni kuma guntun ƙwallan da ya zubo mini na share ina

addu'an Allah ya yayewa Mamina damuwan da ke damunta, haka na miƙe na yi sallahn la'asar, sannan na
shige kitchen na ɗaura mana tuwon dare, duk da ina cikin damuwan abinda ke damun Mamina, amma na
tsaya nayi aiki mai kyau, na yi girki na gama, na share palourn har stakar gidanmu tass, na gyara har ɗakin
Alhaji ko ina na gidan ya ɗau kyalli, na kunna turaren wuta ko ta ina, ɗakin Mamina na shiga da sallama, sai
lokacin na samu tana nata sallahn, banɗakinta na fara wankewa sannan na share ɗakin na kunna turaren
wuta, har na fice tana jan carbi, ɗakina na koma na gyara abuna, sai da na gama na shiga wanka na ɗaura
alwala tunda Magrib ya kusa, dogon rigana ƴar kanti na saka ta shan iska, zama nayi ina jan carbi har sai da
aka yi sallah nayi nima sannan na shafa addu'a na fice.

Palourn namu shiru har lokacin Mamina bata dawo ba, Alhaji kuma da naji shiru ni na ɗauka ya tafi ma, sai
na je ɗakin Mamina da sallama na shiga, samunta nayi yanzu ma akan sallaya, jikina a sanyaye na ƙarisa
gabanta na durƙusa na ce, "Mami abincin na gama."

Ba tare da Mamina ta kalleni ba ta ce, "ki ɗiba naki ki ci, sai zuwa anjima zan ci, ki sakawa Alhaji a kula."

Amsawa nayi na fice a ɗakin, yanda Mami ta ce haka nayi, amma ni ban ɗiba ba, ina dai jiran Mamina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login