Showing 102001 words to 105000 words out of 111817 words
Chapter 35 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf
wannan sirrin bane, amma hakan bai damu Malam Abbo ba, shi
dai burinsa ya mallakeni, kuma kaman kullum yau ma sai da yayi maganan yaushe zai turo magabatan sa.
Marairaicewa Malam Abbo yayi kaman mai shirin yin kuka, idanuwansa a kai na ya ce, "Sayyadata a
taimaka mini, nasan ke ce baki ba da order ba tukunna, dan Umma kam mun jima da yin magana ta ba da
nata, dan Allah a taimaki documents nawa ai mini signing, wannan contract ɗin yana buƙatan approval
naki ranki ya daɗe shugabar duniyar zuciyata."
Dariya na yi ɗan dai-dai, tare da sanya tafukan hannayena na kulle fiskana, a hankali na ce,
"Wai..waii..Uhmn..wai ba..wai ka..tu.roo."
Malam Abbo karkaɓe kunnensa yayi tare da juya mini su yana saurarena, cewa yayi, "rankishidaɗe ƙara
faɗa na ji, na tabbatar ba labarin gizo da kullum kunnena ki bani bane."
Ƙasa nayi da kai na, na ce, "Wai ranan juma'a, su abbanmu za su iya zuwa."
Malam Abbo dan murna ji yake kaman ya rungume Banafsha, gaba-ɗaya farin ciki ya hanasa jimawa yau,
da wuri ya mini sallama ya tafi, ni dai sai dariya kawai nake yi, ina mamaki kaman wan da aka basa kujeran
Makka, wani abu ne ya faɗo mini a rai, a hankali na sauƙe ajiyan zuciya tare da faɗin, "Allah rufa mana asiri
duniya da lahira, wato duk iya ɗaukin da namiji ke yi wajan ganin ya aure ki, da duk soyayyan nan, shi ne a
watarana baya hana shi kuma ya buɗi baki ya ce, ya sake ki, to Allah kyauta."
Bayan fitan Malam Abbo, naje na kulle mana ƙofan gida, sannan na dawo na wuce ɗakina a gajiye, wasta
ruwa nayi tare da bin lafiyan gadona na kwanta, ko ɗakin Mami ban je ba, balle na mata sai da safe.
Washe-gari Litinin muka tafi College, dan yanzu mun fara test, kuma ba jimawa za'a fara exam's ɗin ma.
Mun cinye wannan satin lafiya, ranan juma'a muna dawowa makaranta, tun da na ga Mota a ƙofan
gidanmu, to ko ba'a faɗa ba nasan Alhaji ne ya zo, karo na farko da zuwansa ya mini daɗi, tun da nasan
yanzu kam in Allah ya yarda nan da wasu satuka, zai zama mijin Mamina.
Shiga gidan nayi ɗauke da sallama a bakina, Alhaji kaɗai na gani zaune a palourn yana danna wayansa, ina
murmushi na ƙarisa tare da stungunawa, kai na a ƙasa na gaishe sa, yana murmushi shi ma ya amsa ya ce,
"sannunku da dawowa ƴar albarka."
Amsawa nayi na tambayesa ya hanya, ya su Majeeder, jin ban mance sunanta ba, sai ya murmusa ya ce,
"Duk suna lafiya tana gaisheki, wai yaushe zan kai mata ƙawarta."
Murmushi kawai nayi na miƙe na shige ɗakina, bayan na masa a huta gajiya.
Ina shiga ɗakina na faɗa kan gado na cikin farin ciki, gani nake ma kaman gobe ne za'a ɗaura auren
Mamina, wani abu ne ya faɗo mini a rai, wan da ya sa na ji ba daɗi, a hankali na furta, "Umaimatyna ba
zan so yin nesa da ke ba, nasan ba zan taɓa samun ƙawa, Aminiya kuma ƴar uwa irinki ba", a hankali na
goge ƙwallan da ya zubo mini sannan na miƙe na rage kayan jikina, ruwa na wásta na saka kaya mara nauyi
na jawo system na ina game abina.
Ɓangaren Malam Abbo tun a ranar yana barin wajan Banafsha, ya samu mahaifinsa da maganan ya samu
mata a nema masa aurenta, Iman Adamu wan da suke ƙira da Abiy, ba tare da jan magana ba ya yi na'am
da batun yaron nasa, domin Malam Abbo shi ne ɗan Auta a wajan iyayensa Imam Adamu (Abiy), da
Malama Hauwa'u (Ummi), iyayensa da yayyunsa biyar duka suna ƙaunarsa, musamman yayyunsa mata da
kuma Abiy.
Daman Abiy ya jima yana bin sa akan ya kawo mata yayi aure, amma Malam Abbo yana zillewa, ƙyalesa
kawai Abiy ke yi dan shi ɗan so ne, kuma shi kaɗai ne ya rage ba su aurar ba, to yanzu jin wannan batun ba
ƙaramin farantawa Abiy yayi ba, tun da ya san yaron nasu yana da ilimin addini da na zamani, kuma yana
da nustuwa, ba zai zaɓowa kan sa matar da bata dace ba, dan haka amsawa yayi akan ranan juma'an za su
je ba ɓata lokaci ma Insha Allahu.
Washe-gari Abiy ya yiwa Ummi maganan, ita ma ta yi addu'an Allah sanya alkairi, sannan aka sanar da
yayyunsa duka mata da mazan, babban yayansa Ya Hussain shi Abiy ya aika ya ƙira masa baffanunsu.
Bayan baffanun sun zo Abiy ya sanar musu, su ɗin ma addu'an sanya alkairi suka yi, domin duk sun san tun
da Abiy ya amshi batun, to ba wani mastala daga ɓangaren matar da Aliyu ke so ɗin.
Malam Abbo ya sanar da Banafsha akan iyayensa za su zo ranan juma'a, kuma da yamma, dan haka tuni
Banafsha ta sanar da Mami, ita kuma ta sanar da Alhaji har ya ce ta faɗawa Abbaanmu ma dan a fita
haƙƙinsa, tun da shi ma a ɗiya ya ɗauki Banafsha, dan haka duk kowa na cikin shiri.
Duk neman auren yayyun Aliyu da ake zuwa, Abiy ba ya zuwa ƙannensa ke zuwa, amma wannan karon tun
da ɗan autansa ne, juma'a nayi ya shirya da shi za'a je, su Ya Hussain da baffanunsu sai zolayan Abiy suke,
wai yana banbanci ya fi son Aliyu, shi dai murmusawa kawai yake yi, ya ce musu ai auren na daban ne
shiyasa, ga Aliyu ga kuma faɗima, ai babban lamari ne, aure ne na manyan iyaye, dole ya je da kan sa, suna
nishaɗinsu haka suka kamo hanyan gidan su Banafsha.
A ɓangaren su Alhaji kuwa, da farko kaman za su koma gidan Abbaa su tari baƙin, amma kuma sai suka
zauna a gidan Mami tun da duk ɗaya ne, palourn ya sha gyara sai ƙamshi kawai ke tashi.
Mami sai da ta gama shirya delicious, sannan suka tafi gidan Abbaa ita da Banafsha.
Ko da su Abiy suka iso, babban yaya ne ya musu iso, cikin fara'a su Alhaji suka tarbesu, babban yaya ya je
kitchen ya jido kayakin da Mami ta nuna masa akan na baƙin ne idan sun zo, jere musu yayi a gabansu.
Sai da suka gaggaisa, sannan suka taɓa abin da yaya babba ya jere musu a gabansu, bayan sun gama
sannan suka fara magana cikin mutuntaka da girmama juna.
Duk abinda ya kamata sun magantu a kai, yarinya tana karatu kuma an amince za ta ci-gaba, Alhaji ya faɗa
musu mahaifinta ya rasu amma dai su ne waliyanta, an gama tattauna komai an kuma stayar da biki wata
biyu kacal, sannan duk abubuwan da suka kamata za'a yi su kamun bikin, amma sun biya kuɗin na gani ina
so dubu ɗari.
Bayan sun gama magana suka sallami juna, su Alhaji har da raka su suka yi, Abiy suka koma cikin farin ciki
da yaba karamci irin na iyayen matar da Aliyunsa zai aura, ko da suka bawa Ummi labari ita ma taji daɗi,
kuma daman sun dawo da abun sha da sauran abubuwan da Mami ta yi, Ummi sai da ta turawa sauran
yayyun Malam Abbo mata a gidajensu, su ma sun ji daɗi ƙaninsu ya samu ƴar gidan mutunci.
Abbaa tuni suka zama abokai da Alhaji duk da dai kowa na kishin ɗan uwansa, sai da suka magantu sannan
Abbaa ya masa sallama ya koma gidansa, sannan Mami ta dawo, ita dai Banafsha tana can tare da Umaima
suna ta yiwa juna stiya.
Mami ta shigo da sallama, ta samu Alhaji na tattare mata palourn, murmushi Mami tayi ta staya tana
kallonsa, Alhaji dagewa yayi har da shara, abun sai ya bawa Mami dariya ta amsa tana faɗin, "rufa mini
asiri Alhaji, shara dai da kanka."
Alhaji ƙin bari yayi, dan dole Mami ta haƙura suka gyara wajan tare, sannan suka zauna, kuɗin ya ɗauka ya
miƙa mata tare da faɗa mata duk yan da suka yi da iyayen Aliyun.
Mami wani irin wawan ajiyan zuciya ta sauƙe, danne abin da take ji tayi, cikin dauriya ta murmusa ta ce,
"Alhaji kai ma ai mahaifinta ne yanzu, musamman da za ka auri mahaifiyarta, ka ajiye mana kuɗin a
wajanka, hakan da kuka yi ma bakomai yayi, Allah ya nuna mana da rai da lafiya, tun da sun amince da
maganan karatunta."
Jinjina kai Alhaji yayi, tare da sakar wa masoyiyarsa Mami murmushi, na jin daɗin furucin da tayi, cewa
yayi, "To yanzu na yarinyarmu nan da wata biyu idan Allah ya yarda, mu kuma fa sai nan da yaushe? Sati
biyu ko ɗaya ma yayi ai ko?", ya faɗa yana jifanta da kallon da ita kaɗai ta san fassaranshi.
Mami murmushi tayi ta ce, "Ah! Da sati ɗaya kam ai gwanda kawai a ce gobe."
"Ai da na fi farin ciki ma idan ya kasance goben, kin ga ango nake tun yau ma", Alhaji ya faɗa yana
murmushi.
Mami ta murmusa ta ce, "Allah huci zuciyan Angon Ramla to, yanzu dai a bar shi yan da muka yi da farkon,
a bar shi rana ɗaya da na Banafsha, idan ya so bayan sati guda sai na tare, kasan ba zai yiwu ayi tun yanzu
na bar ta ita kaɗai a nan ba, idan muka tafi kuma zai iya yi wa iyayen mijinta nisa, bana son a samu wani
mastala kuma."
Jinjina kai Alhaji yayi ya ce, "Duk yan da kika ce haka za'a yi Amaryan Mukhtar, duk da dai ba'a so ba ƙanin
miji ya fi miji kyau, amma maganan sai bayan sati ki tare ni ban yarda ba, ana wastewa a hidiman
Banafsha, muma za mu yi namu hidiman, sannan yanzu ya za'a yi da batun zuwanki Makka ɗin?"
Mami ta ce, "shi ma dai a bari sai na aurar da yarinyata, dan a yanzu ba zan iya tafiya ko ina na bar ta ba,
gwanda ma idan na kai ta gidan miji."
Murmushi Alhaji yayi ya ce, "Yau da gobe duk ɗaya ne a wajan Allah, kuma ga mai nisan kwana, Allah nuna
mana da rai da lafiya, Allah kuma ya tabbatar da alkairi, yanzu dai da yardan Allah nan da wata biyu nima
Ango ne."
Mami ta ce, "Ango na Ramla ba."
Alhaji dan farin ciki hulansa ya cire ya mikawa Mami wai ya bata kyauta, saboda cewa da tayi Angon
Ramla, Mami sai dariya take, haka suka dinga hiransu cikin nishaɗi.
Malam Abbo tun da Abiy ya faɗa masa yan da aka yanke, farinciki kaman ya kashe sa, wato da yardan Allah
nan da wata biyu Sayyada Faɗima ta zama mallakinsa, ranan kwana yayi nafilan godiya ga Allah da ƙara
neman alkairin wannan al'amari.
Abbaa ya taya Danish baƙin ciki sosai na rashin Banafsha, amma babu komai ai matar mutum kabarinsa ce,
Allah ya basa ta gari wacce ta fi ta, dan haka sai ya yanke hukuncin ɗagawa Danish ƙafa, sai zuwa gaba
kuma ya masa maganan aure, amma tun da an riga da an fara na Ya Farooq to in Allah ya yarda shi kam
za'a yi.
Alhaji sai da yayi sati guda sannan ya tattara ya shirya komawa Kano, bayan sun yanke magana da Mami,
ya faɗa mata ko stinke kada ta saya na maganan Banafsha, komai yayi alƙawarin mata, hatta da stinstiyan
shara duk zai saya, abinda ya kama na kuɗi ma ta masa magana, Mami har rasa abin da za ta cewa Alhaji
take, illa iyakaci ta ɗau aniyan zama da shi, cikin soyayya da ƙauna da kulawa da tarairaya da haƙuri da
kuma Amana, cikin daɗi da rashinsa duk za ta jure ta yi haƙuri ta zauna da shi, saboda shi ne kawai
halaccin da za ta masa ta saka masa, akan kyautatawan da yake mata, ita da gudan jininta.
Tun da aka yanke kwanakin auren, Mami ke stuma kan ta da ƴar ta, yanzu ko ina Banafsha za ta je sai da
niƙab da Safa, Allah ya taimake ta a college ba'a yi magana akan sakawan ba.
Bayan wata guda suka fara exam's, in da a tahfiz kuma suka dage da karatu maganan musabaƙan da za su
yi a Abuja nan da wata biyu, kuma suna yi da sati guda za'a yayesu a tahfiz ɗin.
Umaima idan ka kalli bussyn da take yi tun yanzu ka ɗauka ita ce Amaryan, duk da karatu da suka mai da
hankali akai arabi da boko, amma bai hana Umaima shirye-shirye ba.
Ɓangaren Umma an kuma sauraran ƙaranta, in da aka yanke mata hukuncin ɗaurin rai da rai, a hakan ma
saboda Mami ta yafe mata shi yasa ba'a yi maganan tara da za ta biya ba, wannan hukuncin ba wanda ya
yiwa daɗi, musamman yaran Umma, Umaima ta yi kuka kaman za ta kashe kanta, yaya babba da ya
Mus'ab duk sun fawwalawa Allah, suna dai kan addu'an Allah sa haka shi ne sanadin shiryuwan
mahaifiyarsu.
Ya Danish kam ba'a maganansa, tun da ya kasa kunne da kyau ya ji tabbacin aure Banafsha za ta yi,
shikkenan ya yiwa Mubi ƙaura, musamman da Ummansa bata nan, Abbaa ya masa uzuri tun da yasan zafin
ya haɗu masa biyu ne.
Sati biyu muka yi muka kammala exam's namu, shikkenan kuma muka ajiye maganan zuwa college a gefe,
tahfiz ɗin ma ba kullum nake zuwa ba, a rana sau ɗaya nake zuwa kuma sai yamma, yanzu da biki ya rage
sati biyu Mami a cikin kuɗaɗen da Alhaji ya turo mata, ta ɗauko mana mai gyaran jiki, a nan Mubi matar
take amma asalinta Kanuriya ce, ni da Mamina wani irin sihirtaccen kyau na musamman muka yi, kuma
Alhaji tun da ya tafi bai kuma zuwa ba, sai dai su yi waya da Mami kawai, ni ma mun yi waya, duk abin da
nake buƙata kuma ya tambayeni akan na faɗa masa, ni dai iyakaci na ce komai aka mini dai-dai ne Allah
saka da alheri.
Malam Abbo ma shiri yake yi a nasa ɓangaren ba kama hannun yaro, gidan da za mu zauna da komai an
gama gyarawa, sun kawo kuɗin goro, kayan aure ma sun haɗa, amma sai aure saura kwanaki za'a kawo,
sadaki kuma sai ranan aure, Malam Abbo da yake ɗan gata ne, duk da shirin aure da yake yi amma ko rama
bai yi ba, sai ma wani kumatu da ya ƙara da kyau, saboda suna da rufin asiri kuma kusan komai yayyunsa
da iyayensa ke masa, zuwa yanzu kuma da ya rage sati biyu kwata-kwata baya samun zuwa wajena, kuma
ko naje tahfiz ba wai magana muke da ya shafi bikinmu ba.
⭐⭐
Captain Abeed da Amaryansa soyayyansu suke sha, tare da renon cikinsu da yanzu yake wata uku, Abeed
ririta ta yake tamkar ƙwai.
General da Momsee sai da suka yi wata guda mai kyau sannan suka dawo, kaya niƙi-niƙi, kayaki masu kyau
da kuɗin gaske.
Da yake duk basu san wa Papi zai aura ba, to duk ɗaukansu ko budurwa ce, kayaki suka haɗo har da sanji
Momsee ta dawo da shi, su Suhaila sai farinciki da murna kaman wani an ce kayan nasu ne, Allah-Allah
suke lokacin biki yayi su tattara su tafi Kano.
ACM Bunayd ƙiran Papi yayi ya faɗa masa akan kaya sun zama ready yaushe za'a kai, amma Papi ya ce ya
bari tukunna sai ya yi wa Amaryansa magana, Bunayd dariya ya dinga yi wai shikkenan Mom ta gama
yawo, Amarya ta mallake Papi tun ba'a kawo ta ba, idan aka kawo ta kuma ai Mom ta koma ƴar kallo.
Akwatuna goma sha biyu ciff, ga kuma guda shida a gefe na Mom, dan Momsee ta ce basu isa ba sai an
haɗowa Hajiya Sa'adatu na faɗan kishiya, ko da tana da nata kuɗin amma wannan ya kamata a mata, dan
haka shirya kaya aka yi ana jiran maganan Papi, yana cewa Yes za'a sako su a jirgi a taho Kano da su.
Tun da aka saka rana Alhaji Mukhtar ya sanar da General Sufyan, maganan yan da auren zai kasance da
komai, dan haka Momsee tuni suka fidda ankon su, idan an kawo Amarya ranan Monday washe-gari
Tuesday za su yi walima, Wednesday kuma a yi family and friends, ɗaurin aure kuma su General duk za su
je Mubin a ɗaura a can.
Duk shirin da Momsee ke yi wa su Ramla su Suhaila, to tana yi da Majeeder, dan tasan ba lallai Hajiya
Sa'adatu ta saurari maganan shiri ba balle ta yi wani abu wa Majeeder, Bunayd kuma duk da haka ya
turawa Majeeder kuɗi sabo da kisto da ƙunshi da sauransu, kuma Papi ma ya mata ɗinkuna da duk abin da
ya kamata, dan haka Majeeder haɗaɗɗen gift ta saya, ta ajiyewa ƙawarta da za su zo tare da amaryan Papi.
Har biki saura wata Hajiya Sa'adatu bata da labari, ta ga dai Alhaji ya ƙara gyara ɗaya part ɗin a sama, bata
dai ce masa komai ba, har biki ya rage saura sati biyu, ya saka aka kawo wasu ranstastun haɗaɗɗun
furniture's, sai da ya gama shirya komai, sannan ya tura mata kuɗi masu yawan gaske.
Hajiya Sa'adatu ganin abin na Alhaji ya ƙi ci, kuma ya ƙi cinyewa, ta riga ta gama shirin kwanciyanta dan a
gajiye take jiya ta dawo da ƙasar waje akan issuen business nata, kuɗin da Alhaji ya tura mata ta gani,
kallon kuɗin tayi da kyau, tasan idan yayi niya yana bata kuɗi ba ruwansa da tana nata business ɗin, amma
kuma wannan na me?, duk da gajiyan da take ji hakan bai hanata miƙewa ta nufi ɗakinsa ba.
Alhaji na kwance yana waya da Amaryansa cikin soyayya, sai Hajiya Sa'adatu ta turo ƙofa ta shigo, kallonta
yayi amma bai dai na wayan ba, ita kuwa da mamakin take bin laɓɓansa da kallo dan