Showing 90001 words to 93000 words out of 111817 words
Chapter 31 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf
taya ni bai wa Mami haƙuri, Insha
Allah next week zan shiga na bata haƙurin da kai na, and beb please ki yafe mini abubuwan da suka faru,
ba da intention nayi ba, sharrin shaiɗan ne da kuma soyayyanki."
Maganansa dariya ya bani, amma duk da haka na maste, ko kallonsa na ƙi yi, har Ya Danish ya gama
shirmen maganganun sa ya tafi ko ƙala ban ce masa ba, yana barin wajan na ja dogon staki na shige gida,
ina faɗin, "Ni za'a renawa wayo ɗan iska mara kirki, in ma da wani salon ka zo to duk ina dai-dai da su."
Ya Danish cikin farin cikin ya bulbular da abin da ke ran sa ya tafi bayan ya ce mata, "ILOVE YOU BEB", ko
cikin gida bai koma ba, ya ja motansa yayi gaba, shi ko haka ma Alhamdulillahi ya gode wa Allahn da ya
jarabce da da soyayyanta.
Ni kuwa mita na dinga yi, har Mami ta gaji ta buge mini baki, tana tambayan menene ya faru, faɗa mata
nayi, maimakon ta goyi bayana, sai naga tana murmushi kawai, ganin haka ƙara kuluwa na yi, a haka kuma
da fushina nayi bacci, Allah ya so ma idan na tuno soja inajin kukan ya tsaya sai kuma dariya akan abin da
ya faru ranan.
Tun daga ranan duk bayan kwana biyu sai na ga ya Danish a Mubi, kuma idan ya zo ya dinga takura mini
kenan, wulaƙancin da ya mini, ba irin wan da ban rama ba, har ma da alakoro na masa, amma ko a jikinsa.
Mami ta dage da maganan aurena, yau Alhamis muna zaune, Mamina ta ci kwalliyanta, daman jiya ta yi
kistonta har da ƙunshi, ba tare da ta kalleni ba ta ce, "Faɗima."
Murmushi nayi na ce, "Naam Mamina."
Mami ta ce, "faɗima ki stayar da mutum ɗaya cikin masu nemanki, idan Aliyu ne ki faɗa masa ya turo, idan
kuma Danish ne, za mu yi magana da Abbaanku, daman ina tunanin ko shi zai ba da aurenki."
Murmushin taƙaici wan da ya fi kuka ciwo na yi, na ce, "Mami ban da uba ne? Ko da gaske ba ta hanyar
Sunna kika same ni ba, Mami wallahi idan ba auran mutum kika yi ba, ni ban yarda ya zama waliyina ba,
kuma Allah sai ana auren na gudu, nima na shiga duniya kawai kowa ya huta, nima na ɗaura daga inda kika
tsaya..."
Ban ida rufe baki ba na ji sauƙan mari a bakina, wan da take bakina ya fashe, Mami cikin surutu take cewa,
"Banafsha wato dan ina miki shiru, shi ne kika dage ko? To kuwa zan nuna miki ni ce mahaifiyarki ba ke kika
haife ni ba."
Idanuwana a bushe ba ko alaman hawaye na ɗago su, cikin dakiya na ce, "Mami ko kasheni za ki yi, ba zan
auri kowa ba sai kin yi aure, Mami ke fa ranan kika faɗa mini Allah na son mai haƙuri, to me yasa ke ba za
ki kasance cikin waɗanda Allah ke so ba? Me yasa ba za ki kasance cikin masu ɗaukan ƙaddaransu ba?
Mami me yayi zafi shi ba wuta ba, Mami duk fa tsanani na tare da sauƙi, Ya mahaifiyata ki yi haƙuri, amma
a yanzu ki samu Abbaa da maganar nan, kema kin san ba ki yi adalci ba Mami, kin ƙi sa kuma ki ce yayi wa
yarinyar ki walittaka, ki duba lamarin da kyau."
Mami masifa ta fara mini, in da take shiga ba nan take fita ba, ni kuma yau na dage ba zan yi aure ba sai ta
yi, saboda ɓacin ran da Mami ke ciki tuni ta fara jibgana yan da muka saba idan na mata irin magannan,
duk dukan da Mami ke mini bakina bai mutu ba, kuma babu ko ɗigon hawaye, abu ɗaya kawai nake faɗi,
"wallahi Mami ko kasheni za ki yi, ki kashe ni, na yafe miki kuma, amma ba zan yi aure ba sai kin yi..."
Ban fasa surutu ba, Mami bata fasa dukana ba, muna cikin haka sai ganin Alhaji Mukhtar muka yi, ba zato
ba tsammani, Alhaji da sauri ya janye Mami ya riƙe hannayenta yana faɗin, "Ramla ba ki da hankali ne? Me
ke damunki? Kashe ta za ki yi?"
Mami kawai fashewa tayi da kuka ta ce, "gwanda na kashe ta na huta, tun da baƙin ciki da damuwa ita ma
take son cusa mini, in kai ta mahaifinta an faɗa mata tana da uba ne? Bayan sanadinta na rabu da kowa
nawa, farin ciki na, mai so na, iyayena, dangina,mastayi na, da komai nawa, duk dan saboda ita na haƙura
da su, na zaɓe ta akan kowa nawa, har sau nawa take so na dinga sadaukar mata da farin ciki na? Haka iya
wan da na mata bai isheta ba?"
Jin furcin Mami tuni hawaye yayi shaɓe-shaɓe a fiskana, kuka na kama bilhaƙƙi kaman rai na zai fita, me
Mami take nufi da bata san uba na ba? Mutum na fita a jikin bishiya ne? Ko mace na haihuwa ita kaɗai ba
tare da namiji ba? Ɗagowa nayi ina kuka na ce, "Mami bayan jin wannan furucin naki, sai na kuma samun
ƙwarin guiwan ƙin aure, Mami ba zan yi aure ba sai kin yi, kuma sai kin koma ga danginki.."
Kamun na rufe baki Mami ta iyo kai na, ta hau jibgana, da ƙyar kuma Alhaji ya riƙe ta bayan ya ce na tafi,
haka na tashi ina haɗa hanya na nufi ɗakina, amma ina shigewa kamun na isa ga gadona, tuni wani mugun
jiri ya ɗibeni, inajin jiri-jiri, baya na yi luuu na faɗi, lokaci guda numfashina ya ɗauke.
Ɓangaren Mami kuka ta dinga yi sai da Alhaji ya dage da lallashi, cikin soyayya yake lallashinta ya ce, "haba
Ramla, da girmanki da tunaninki da komai naki, kike irin wannan furucin? Me yasa ne wai ke baki yarda da
ƙaddara ba? Me yasa ba za ki mata abin da take so ba?"
Mami kuka ta dinga yi mai matuƙar ciwo da cin zuciya, ba abinda take nanata wa sai istigfari, bayan Alhaji
ya gama lallashinta da mata nasiha, sai ya ga kawai ta miƙe stuttt! Kaman wacce aka stikare ta, share
hawayenta ta ci-gaba da yi, tana faɗin, "faɗima zan yi abin da kike so in zai sa ki farin ciki ki kuma yar da ki
yi aure.." tana magana ta wuce ɗakin Banafsha, sai dai tana shiga daga bakin ƙofa ta tarar da ita a yashe a
ƙasa bata ko numfashi.
Mami ganin haka, ihu ta stala tare da faɗin, "innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Faɗimana kada ki mini haka."
Alhaji jin ihunta ya shigo da sauri, ganin halin da Banafsha ke ciki, da sauri ya ɗauke ta yayi waje da ita,
Mami haka ta bi sa ba mayafi, sai shi ne ya koma ya ɗauko mata, sannan ya ja mota suka yi asibiti, Mami
sai ƙoƙari take wajan danne ƙwallan da ke fito mata, kada ta yi hawaye wa yarinyarta.
General hospital Alhaji ya kai su, suna isa kuwa cikin sa'a suka samu Dr Arshan na duty, yana ganin Mami
ya ganeta, nan yasa aka yi da Banafsha emergency, sai da ya dubata sannan ya sanar da su Mami kada su
ɗaga hankali, suma ne tayi saboda wani abu da ta gani ko ta ji ya sa bugun zuciyanta ƙaruwa, ya firgita ta,
amma zuwa ba jimawa za ta iya farfaɗo wa, ko zuwa gobe.
Alhaji da Mami ne suke zaune a kan Banafsha, Alhaji sai tausan Mami yake yana bata baki, har dare sannan
ta farfaɗo tana sumbatu, Mami cikin hanzari ta rungumeta tana faɗin ta nistu ga ta nan kusa da ita, Alhaji
kuma ya ƙira likita, sai da ya mata allura sannan a hankali kuma ta koma bacci yayi gaba da ita, tana sakin
ajiyan zuciya.
Washegari da ta farka jikin ya zama normal, sai da ta ci abinci ta yi sallolinta, sannan Mami ta fara magana
cikin lallashi, cewa tayi, "Faɗima ki kwantar da hankalinki kin ji, Inshà Allahu Maminki za ta yi duk abin da
kike so da kuma abin da zai saki farinciki, zan yi aure kaman yan da kike so, sannan zan ba ki labarin
dangina, zuwa gaba kuma Insha Allah zan haɗa ki da su."
Ina daga kwance amma a take na tashi na zauna, kallon Mamina nake cikin farin ciki da ƙaunarta, me nake
nema a duniya ina da Mamina? Tuni ma na ji ciwon da ke damuna duk sun fece, karo na farko a rayuwa da
naji tabbas mastalana sun ƙare, ko ba komai indai Mamina za ta yi aure to shikkenan, alhamdulillahi abin
da nake so kenan, ko maganan danginta bai dameni irin maganan ta yi aure ba, ai rungume Mami nayi
cikin farin ciki, ina sauƙe ajiyan zuciya, yayinda Mami kuma ke ƙoƙarin mayar da ƙwallan da ke son zubo
mata.
Dr Arshan ya zo ya duba ni, da mamaki ya tambayi me ya faru haka, har komai da ke damuna ya setu, daga
yanayin bugun zuciya na har jinina da ke neman hawa ya wuce misali, murmushi kawai na masa da yake
mun ɗan saba kwanaki da Mami ta kwanta.
Sai yamma sannan aka sallamemu, Alhaji ya jido mu muka dawo gida, bayan ya siya duk wani magani nawa
da ake buƙata, kuma ya bi mun saya fruits da sauran su.
Muna dawowa gida da yake juma'a ne yamma ma ta riga da ta yi, sai ga Umaima ta shigo, ɗakina muka
wuce da ita bayan ta gaishe da su Mami, muna shiga ta tambayi me ya faru bata ganni ba tun jiya, kawai
faɗa mata nayi ban da lafiya ne, mun je asibiti kuma Dr Arshan ma ya ce a gaisheta.
Amsawa tayi ta mini Allah ƙara sauƙi, sai da muka taɓa hira sannan na shiga na wasta ruwa, na zo na
kwanta, ita kuma Umaima ta yi wa su Mami sallama ta fice.
Mami ta biyo ni har ɗaki ta bani magani da abinci, sannan ta mini sai da safe bayan ta ƙara kwantar mini
da hankali, kwanciya nayi ba jimawa bacci yayi gaba da ni.
A ɓangarena da yake yanzu na samu nistuwa, ba jimawa bacci yayi gaba da ni hankali kwance.
Mami kuwa gaba-ɗaya kan ta chaji ya ɗauka, dan haka ba su wani yi dogon hira da Alhaji ba, ta tashi ta
shige ɗakinta, wanka ta yi ta shirya staff sannan ta fito, sai da safe ta yiwa Alhaji, kallonta yayi yana
murmushi ya ce, "Ramla sai da safe kuma, ba za ki ce nazo mu kwanta ba? Ko kin manta ke kika ce na
dawo kina buƙatata?"
Mami murmushin yaƙe tayi ta ce, "Ai nasan ko na ce ba zuwa za ka yi ba, dan haka Allah tashe mu lafiya",
ta faɗa tare da shigewa ɗakinta.
Alhaji murmushin shi ma yayi kawai tare da girgiza kai, ya ce, "Allah shirya mini ke cikin gaggawa ya nusar
da ke gaskiya, ina matuƙar ƙaunarki da kuma buƙatanki Ramla, amma zan ci gaba da kiyaye wa har zuwa
lokacin da zan mallake ki, sannan ke ma ina addu'an Allah baki ikon jure naki buƙatan, Allah stayar da duk
wani mummunan ƙaddaran rayuwanki haka nan."
Mami ko da ta shiga ɗaki, neman baccin tayi sama ƙasa ta rasa shi, kwanciya kawai ta yi tare da zubawa
saman ɗakin nata ido, lissafi take akan yanzu wa za ta aura? Alhaji tana son sa ba kaɗan ba, amma tana
tunanin kar nan gaba zargi ya zo cikin aurensu ko wani abu daban, tun da ita zuciya sai a hankali balle ma
da a wannan harkan ya sameta, sannan Abbaa kuma tana gudun a ƙara samun akasi da Umma, ko kuwa
Ummu ma ta kasa haƙuri nan gaba da kawo gori da tashin hankali stakaninsu, kishi masifa ce, duk iya
daurewanka watarana sai an samu akasi, sannan bata buƙatan auren da za ta yi saki ya biyo baya, Abbaa
tun da ya saki Umma uwar ƴaƴansa tana ganin ita ma zai iya sakinta watarana idan ta aure sa, Alhaji kuma
idan ya zarge ta zai iya sakinta shi ma, kuma bata fata da addu'an tayi aure ta fita, cikin mugun damuwa
Mami ta busar da zazzafan iska a bakinta, a hankali ta buɗe baki ta ce, "Allah ka mini zaɓin alkairi, Allah
Astagfirullah! Na tuba maka Ubangiji na."
Haka Mami ta kasance cikin zullumi, wan da har kan ta ya fara ciwo saboda tunani da nazari, so take ta yi
auren saboda Allah kuma saboda Banafsha ma ta yi, ita ba ta da farin cikin da ya wuce mata tilon ƴar ta,
kuma bata da burin da ya wuce ta aurar da ita cikin aminci da mutunci, dan haka za ta iya yin komai dan
Banafsha, har da bayar da ran ta ma.
Daga ƙarshe Mami yanke hukuncin yin istihara ta yi(neman zaɓin Allah), tashuwa ta yi ta ɗaura alwala ta zo
ta tayar da nafilanta raka'a biyu, sai da ta idar sannan ta karanto addu'anta ta gabatar da buƙatanta ga
mahaliccinta, sai da ta idar ta shafa sannan ta samu nustuwa ta bi lafiyan gado ta kwanta.
Shi addu'an istihara ba wa iya aure ake yi wa ba, domin an karɓo daga jabir ibn Abdallah, cewa mun
kasance tare da Manzon Allah SAW yana nusar da mu duk abin da za mu yi, mu nemi zaɓin Allah a
kai(istihara), sannan yana koya mana addu'an, kaman yan da yake koya mana Surah daga cikin Alƙur'ani
mai girma, kuma ita sallar istihara ba dole sai da dare ake yin ta ba, ana iya yin ta da safiya, da marece, da
dare, da rana, hatta bayan la'asar da ba'a mata nafila, to mutum zai iya yin wannan sallah ta istihara, raka'a
biyu sallama ɗaya, idan mutum ya idar, zai karanto addu'an kaman haka :-
ALLAHUMMAH INNI ASTAKIRUKA BI ILMIKA, WA ASTAƘDIRUKA BI ƘUDRATIKA, WA AS'ALUKA MIN
FAD'LIKAL AZIM, FA'INNAKA TAƘDIRU WALA AƘDIRU, WA TA'ALAMU WALA A'ALAMU, WA ANTA ALLAMUL
GAIBU, ALLAHUMMAH IN KUNTA TA'ALAMU ANNA HAZAL AMRA ( sai ka faɗi abin da kayi sallahn saboda
shi anan ) KAIRUN LEE WA FI DINI, WA MA'ASHI, WA AƘIBATI AMRI, FAKDURHU LEE WA YASSIRHU LEE,
SUMMA BARIK LEE FIHI, WA IN KUNTA TA'ALAMU ANNA HAZAL AMRA SHARRUN LEE WA FI DINI WA
MA'ASHI, WA AƘIBATI AMRI FASRIFHU ANNI, WASRIFNI ANHU, WAƘDUR LIYAL KAIRA HAISU KANA
SUMMA RADDINI BIHI.
wannan ita ce addu'an, Ubangiji Allah ya tabbatar mana da alakiran rayuwanmu, Allah ya sa mu dace.
Washe-gari da safe sai da na lallaɓa na yi wa Mamina ayyukanta, sannan na shirya na fito muka wuce
tahfiz tare da Umaima, ga mamaki na Ya Danish na tsaye a ƙofa yana bi na da kallo har muka wuce, amma
ni ko nunawa nasan da halittansa a wajan ban yi ba.
Mun je mun yi karatu sannan an yanke tafiyanmu musabaƙa a cikin jimeta nan da sati biyu, akan mu sanar
wa iyayenmu, kamun malamai za su zo har gida a sanar wa iyayen duk wan da za'a je da shi.
Ana tashinmu muka kamo hanyan gida, tafiya muke muna hira, faɗa wa Umaima nake Dr Arshan fa kaman
son ta yake, dariya tayi ta ce, "ai ke dai sam bakya gani da kyau, kina ji mutum ya ce yana da mata kuma ba
zai ƙara aure ba, balle a masa maganan adalci, shi ne kike wannan batun."
Dariya nayi sabo da na tuna, masifan da nayi ranan akan ya duba ɗan uwan soja, bai Duba Mamina ba, shi
ne na ce masa baya da adalci, ba zai iya riƙe mata biyu ba, haka muna hiranmu muka tinkaro gida, tun
daga nesa na hangi mutum staye a ƙofan gidanmu, kuma sarai na gane Ya Danish ne, haɗe fiska nayi tare
da jan staki na ce, "Mutum ba zuciya sam-sam haka Allah ya yi sa, ka gama ci mini mutunci ka zo kana
ƙoƙarin lashe aman da ka yi."
Umaima murmushi tayi dan ta san da wa nake yi, kallon ƙofan gidan mu tayi ta ce, "Masoyiya a taimaki
yayana, Allah jiya ma in faɗa miki shi ya sanya ni zuwa na dubo ki ko lafiya, da na ce masa ba ki da lafiya
kada ki ga yan da hankalinsa ya tashi, har ya bani tausayi, na ce Allah mai iko, kaman ba shi ya gama miko
rashin kirki ba, ga shi Allah ya jarabce sa da son ki, dan Allah Masoyiya ki yi haƙuri ki yafe masa ki kula sa."
Taɓe baki nayi na ce, "ke baki san waye yayanki ba ne shi yasa, baki san me ya mini ba, ni da ya Danish ko
shi kaɗai ya rage namiji a duniya to ba zan aure sa ba, Malam Abbo na zan aura, Insha Allah."
Sallama muka yi da Umaima ta shige gidansu, nima na wuce namu, ina isowa ƙofanmu kaman yan da ya
saba ya fara mini magiya, tambayan ya jikina yake yi amma na yi banza da shi na shige gida.
Bayan na karya na huta sai Alhaji yayi ƙira na, zuwa nayi cikin ladabi na gaishesa, amsawa yayi tare da
tambayan ya karatun namu da kuma jikinsa.
Murmushi nayi na ce, "Alhamdulillah!"
Jinjina kai Alhaji yayi tare da miƙo mini, leda mai ɗan girma ya ce, "Ga kyautan ki da na yi alƙawari, sannan
an faɗa mini result naki, yayi kyau sosai a ƙara mai da hankali, yanzu kuma sai ki faɗi abin da kike so ko ƴar
gidan Mami, idan bai fi ƙarfi na ba, Inshà Allah zan miki koma menene."
Tun da Alhaji ya fara magana, nayi ƙasa da kai na ina wasa da yastuna, na jima da tanadar amsan da zan
bawa Alhaji idan ya bani wannan daman, amma kunya nake ji na rasa ta ina zan fara, ajiyan zuciya na
sauƙe