Showing 36001 words to 39000 words out of 111817 words
Chapter 13 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf
Danish, na tsaneka
kaman yanda ka tsaneni, banason kallonka, ka dena taɓa ni idan ba haka ba zan iya illataka."
Danish murmushin mugunta ya saki ya ce, "bayan kisa kiyi abinda za ki iya yi, ba dai ni kike faɗa wa
maganan banza ba, to zan gwada miki iskanci irin nawa ganin idonki dan ki sani, ko a cikin kwartayenki
babu sa'a na balle ke ƙaramar karuwa, har ni za ki cewa ba'a ɗan iska ɗaya sai biyu, to kuwa yau zan nuna
miki irin nawa iskancin, gobe ko da kuɗi ba za ki yiwa wani ba balle ni Danish."
Miƙewa nayi tare da sakin murmushi mai nuni da bai san abinda yake faɗa ba, kallonsa nayi sama da ƙasa
duk da belt na wandonsa da yake ƙoƙarin cirewa amma hakan bai dame ni ba, sai ma dogon stakin da naja
na ce, "Na faɗa, na kuma faɗa, kuma zan ƙara faɗa, jikin Banafsha ya fi ƙarfinka Danish, na wuce sa'ar
yinka, kai mata-maza nake maka kallo, ka je a kuma maka kaciya sannan ka tunkare ni, " ina gama magana
na yi hanyan fita.
Wannan karon cikin zafin rai ya jawo ni ya haɗa ni da bango har sai da na buge kai na, a cikin mugun ɓacin
rai ya ce, "Zan kuma gwada miki cewan nafi ƙarfinki yanzu, sai na miki kaca-kaca, sai na illataki, sai na miki
abinda babu wanda ya taɓa miki irinsa duk yawon iskancinki, za ki ga mata-maza ganin idonki yau" yana
gama magana cikin zafi ya ja hijabin jikina ya yage sa, saboda kada nayi ihu ya haɗe bakinmu waje guda
sannan ya fara kiciniyar cire mini kayan makarantan da ke jikina, ni kuwa tunda ya haɗe bakinmu waje
guda tuni wani irin storo ya ziyarce ni, banason zina, na tsani zina, bana son mai aikatasa, ko mahaifiyata
babu yanda na iya da ita ne shiyasa, ita ɗin ƙaddarata ce.
Abbaa da Ummu dawowansu kenan daga asibitin da suka je, da yake a waje Abbaa ya bar mota, to tun
shigowansu suke jin kaman ana kokuwa a sashin su Sadeeq, har za su wuce sai Ummu ta ce su duba dai su
gani ko lafiya, Abbaa ba musu suka juya suka nufi ƙofan palourn samarin, suna isa kuwa suka jiyo kaman
shessheƙan kukan mace, da sauri Abbaa ya tura ƙofan.
Kiciniyar ƙwacewa na fara yi, ina son nayi ihun naiman taimako ganin ya Danish da gaske yake, amma yaƙi
bani daman hakan, ba shan bakina yake ba amma ya rufe mini baki da nasa, nan muka fara kokawa da Ya
Danish, da yake ya fi ƙarfina sai samun galaba yake a kai na, har ya kai ni ƙasa ya danneni, kaman yanda
zuciyana ke buganawa nakan iya jiyo nasa sautin bugun zuciyan tunda ƙirjinmu ya haɗe waje guda, yana
ƙoƙarin zare wandon jikina kawai aka banko ƙofa aka shigo, waye za mu gani? Abbaa ne da Ummu, cikin
hanzari Abbaa ya zo ya janye ya Danish tare da kwashe shi da maruka, Ummu kuma ta ɗaga ni tana kuka ta
ja hannuna, bata koma cikin gidan da ni ba ta yafa mini ɗankwalinta hannunta cikin hannuna tayi gidanmu
da ni, nima a nawa ɓangaren hawaye kawai nake yi dan nayi mugun storata, stanar Ya Danish ya ƙara rufe
ni, nayi nadaman sanin wannan gidan nasu a rayuwata, tuna har ya haɗa bakinsa da nawa sai kawai na
fashe da kuka na faɗa jikin Ummu dai-dai mun shiga haraban gidanmu.
Abbaa kuwa ba abinda yake yi sai aikin marin ya Danish yana faɗin, "Ni za ka tozarta Danish? Ni za ka
wulaƙanta a garinnan? Yarinyar mutane za ka yiwa fyaɗe dan baka da kirki? To wallahi gwanda na kashe ka
na huta da ina gani na bari ka ƙetawa yarinyar mutane mutunci, abun kunya za ka jawo mini ina zaune
lafiya."
Ya Danish ko ajikinsa maganan Abbaa bai damesa ba, shi haushi ɗaya yake ciki kawai da bai koyawa
Banafsha hankali ba, ƙwace kansa yayi ya fice tare da barin gidan gaba-ɗaya, a lokacin ya shige motansa
yabar mubi ya nufi Camaroon tun weekend ɗin bata ƙare ba.
Abbaa cikin haushi yayi cikin gidan, nan kuma ya tarar da Umaima na aikin kuka, kallonta yayi har yanzu
ransa a ɓace ya ce, "Me ya same ki?"
Umaima cikin kuka ta nunawa Abbaa hannunta, ta kuma faɗa masa duk abinda ya faru, ƙara tunzura
Abbaa yayi, ransa ya kuma ɓaci, lallaɓa Umaima yayi ya shige ɗakin Ummu dan idan yaje wajan Umma
yanzu ya tabbata zai yi abinda ba zai yi kyawun gani ko ji ba, amma dai dole ya ɗau mummunan mataki
akan Umma da Danish, dole ya take musu birki zuwa yanzu, abu shekaru da shekaru amma kullum cikin
stanan yarinya da tsangwamarta, to zai nuna musu iyakar su, yasan abinda zai yi.
Ummu stayar da nata hawayen tayi ta ce, "kiyi haƙuri Umaima, in Allah ya yarda haka ba zai ƙara faruwa
ba, Abbaanku zai ɗau mataki kin ji?"
Ɗagawa Ummu kai kawai nayi ina stagaita kukana, sai da Ummu ta rarrasheni sosai sannan ta ce, "Da
banso ɓoye lwa Maminki wannan abinda ya faru ba, amma kiyi haƙuri kada ki faɗa mata kinji, ki bari muji
daga bakin Abbaanku, amma dai ba wai ina nufin hanaki zuwa wajan ƙawarki ba kinji, kiyi haƙuri ki rage
shiga gidan can, in Allah ya yarda komai zai dai-daita, kada ki faɗawa Maminki dan hankalinta zai tashi
sosai, kuma ba za taji daɗi ba, kede ki kiyaye, kada ki ƙara ko haɗa hanya ne da shi."
Jinjina kai kawai nayi, tare da share hawayena, Ummu ta fice ta koma gida ni kuma na shige cikin
palournmu, cikin rashin sa'a na samu Mamina zaune a palour, kai na a ƙasa na seta muryana na ce, "Sannu
da gida Mami" ina gama faɗa nayi ɗakina da sauri.
Mami da kallo ta bini, ganin ina ɗingisa ƙafana, ga shi kuma wani ɗankwali na rufe kai na da shi a
maimakon taga hijabin makaranta, tun ɗaxu tasan muke dawowa amma taganni shiru, sai abin ya dame ta,
tashuwa tayi tabi bayana, amma tana shiga ta samu har na shige banɗaki, daga waje ta ce, "lafiyanki kuwa
Banafsha?"
Daga cikin banɗakin na ce, "Lafiya lau Mami, wanka nake yi."
Mamina ba dan ta yarda ba ta fice kawai, ni kuwa a banɗaki sai da na gama shan kukana, sannan na dirje
jikina kaman ba gobe, sai da jikina ya fara zafi sannan na fito, da haushin Ya Danish ya haɗa jikinsa da
nawa, sallah nayi na miƙa kukana wajan Allah sannan na yi addu'an musabaƙan gobe Allah bamu sa'a, sai
da nayi isha'i sannan na fita, abincin dare na ɗiba na ci ɗan dai-dai, Mami ta sani gaba da tambayan me ya
hanani dawowa da wuri? Me ya samu hijabin makarantana? Duk tambayoyin Mamina amsa guda take
samu, ba komai ba kuma abinda ya faru, da ta gaji sai ta ƙyale ni ta tambayi batun musabaƙa nan ma na
faɗa mata sai gobe za muyi namu in Allah ya yarda, addu'an sa'a ta mini, can ba jimawa na mata sai da
safe na shige ɗakina, yau gaba-ɗaya na kasa karatu saboda taƙaici, karshe kawai kwanciya nayi dan nayi
bacci ko zan samu nustuwa.
Ummu haka ta koma gida ta rarrashi Abbaa da ya bari ya bi abun a sannu, dan Abbaa ya faɗa mata duk
abinda Umaima ta faɗa masa, kuma Ummu bata yi musu ba dan tasan staff Umma Sabeera za ta aikata
abinda ya fi haka ma, saboda irin stanar da ta yiwa Banafsha mara dalili, Ummu dai wani abu take tunani a
ranta amma ta bari ba yanzu za ta bawa Abbaa shawaran ba, yanzu dai ya kwantar da hankalinsa tukunna,
sai da ta samarwa mijinta nustuwa, sannan taje wajan Umaima ta rarrasheta ta bata abinci a baki ta bata
magani ta shafa mata na shafawa, dan babban yaya sai da ya kai ta chemist kamun ya tafi, ita ma Umaima
bata iya karatu cikin wannan daren ba, kwanciya kawai tayi baccin wahala yayi gaba da ita.
Yaya babba kuwa ransa yanda yayi mugun ɓaci, ko takan matarsa Hindatu bai bi ba, haka zalika wai ita ma
fushi take da shi, an mareta bai yi komai ba sai ma haƙurin da ya bawa Banafsha, ga shi kuma a gabanta ya
riƙo hannun Banafsha, kuma ita ko sannu bai ce mata ba, sai ta hau dokin zuciya.
Washe-gari Lahadi da wuri su Banafsha suka tafi makaranta, daganan aka wuce wajan musabaƙa, yau da
makarantan su Banafsha aka fara, cikin ikon Allah suka yi lafiya suka gama, aka cigaba da sauran
makarantun da suka rage, har sai yamma yau ma aka tashi, amma yau kam an kammala sai jiran sakamako.
Bayan wani lokaci su Banafsha suka cigaba da zuwa tahfiz, kuma a lokacin hutun boko ya kusa ƙare wa, a
haka har sakamakon musabaƙa ya fito, Banafsha ce tazo ta ɗaya, sai Umaima da wata yarinya daga wani
makaranta daban suka yi bracket suka zo na biyu, makarantar su Banafsha dai su ne na farko, sai
makarantar su ɗaya yarinyan su kuma na biyu, haka dai har wanda suka zo na ƙarshe, kuma an yanke a iya
na ɗaya zuwa na biyar ne za'a je na jiha da su nan gaba, dan wannan da aka yi iya na cikin mubi ne, yanzu
nan gaba na Adamawa State gaba ɗaya za'a yi kamun kuma aje ga na State da State, wannan nasara ba
ƙaramar daɗi ta yiwa malaman su Banafsha ba, kyautar da suka ciyo kuma anbar wa makaranta za'a ƙara
gyara abubuwan da ya kamata.
Sai da aka kwashe wata guda Ya Danish bai kuma zuwa weekend ba, wanda ganin haka sai Banafsha ta
cigaba da shiga gidan, saboda Abbaa da kansa ya bata haƙuri kuma ya ce kada ta yarda ta ce za ta daina
shigowa, ita ma gidansu ne kuma shi mahaifinta ne, Umma dai taƙaici kaman ta kashe kanta, duk da
girman Umaima kuwa hakan bai hanata jibganta muddin ta gansu da Banafsha, Ummu abun ya isheta dan
haka ta yanke hukunci, ta samu Abbaa ta faɗa masa ita dai a shawaranta tana ganin ya auri Mamin
Banafsha kawai, Abbaa ba ƙaramin daɗin shawaran Ummu ya ji ba, tunda ita da kanta tayi maganan to
yasan ba za ta kawo masa mastala ba, ya amsa shawaran zai auri Mami ko dan Umma ta gyara halinta, dan
yasan tabbas ya auri Mami to Umma za ta dawo hayyacinta, sannan ya faɗa mata shi ma zai ƙira Danish ya
fito da mata yayi aure, tunda iskanci yake ji, abin nasa tun daga gida zai fara danne yaran mutane, to bai
isa ba gwanda yayi aure kamun ya jajuɓo musu abin kunya, nan ma Ummu tayi na'am da wannan
hukuncin, ta bisu da addu'an alkairi a cikin lamarin auren daga na Abbaa har na Danish ɗin, amma tare da
Farooq za'a haɗasu su fito da matan auren, tunda daman sa'anni ne su ɗin, wannan hukunci Ummu da
Abbaa suka yanke, da yake Ummu matar rufin asiri ce kuma mace ce ta gari fatan samun ko wani namiji,
shiyasa take ta daban a wajan Abbaa, ita ya aura daga baya, amma baya jin zai iya samun wata kamarta,
sosai Abbaa ke ƙaunar Ummu, kuma halayyanta masu kyau ne suke jawo hakan, yana son Umma Sabeera
ma, amma dai halayyanta sai a hankali suna ɓata masa rai.
Mamina cigaba da rayuwanta tayi, wannan ya zo yau gobe kuma wani daban ya zo, ni har mamaki nake yi
ma a ina Mamina ke samo wasu mutanen, gata nan dai ba wai mai yawan fita ba ce, amma kuma jama'a
ne da ita kaman mai kasa kanta a tire ta fita da shi, Alhaji Mukhtar kuwa har yau bai zo gidanmu ba, kuma
wannan karon ne kawai ya jima, dan wata har da sati guda kenan bai zo ba.
Tsakanin yaya babba da matarsa kuwa, mata da miji sai Allah, tuni suka shirya bayan ta gama ginɗaya masa
sharuɗan ya fita harkan Banafsha, sannan ta basa haƙuri, shi dai kallonta kawai yake yana murmushin
shiririta irin nata, in ba haukan kishi da ya rufe mata ido ba, ai da yana son Banafsha to ba ita zai aura ba,
Banafshan zai aura tunda tare ta gansu, kawai ya amsa haƙurin ne ita ma ya bata sun dai-daita, tunda duk
sun gaji da fushin da suke yi da juna.
Malam Abbo da Banafsha kuwa yanzu stakaninsu ba'a magana, ɗalibai har sun fara ƙus-ƙus ɗin soyayya
Malam Abbo ke yi da Banafsha, Umaima ta samu Banafsha ta mata maganam, amma Banafsha ta nuna
mata babu komai tsakaninsu, Umaima ma shiru tayi dai tana kallonsu, Banafsha kuwa duk bata kallon
abinda ake nufi, ita ta ɗau hakan shaƙuwa ce kawai, yayinda Malam Abbo ke fama da zuciyarsa, kuma
zuwa yanzu yana jin ba zai iya haƙura ba, idan bai bayyana mata ba zuciyarsa akwai mastala, shiri yake
kawai gadan-gadan na tunkarar Banafsha ya baje mata sirrin ƙalbinsa.
Bayan sati biyu muka koma boko inda muka fara sabon aji, semester na farko a ajinmu na ƙarshe, in Allah
ya yarda mun kusa gama College of health, ranan juma'a mun je school mun dawo ni da Umaima hankali
kwance, mashine ya kawo mu har ƙofan gida, muna sauƙa na hangi motan Ya Danish, nice ma na kula da
shi da yake na gane motan nasa, amma Umaima bata kula ba sai hira take mini, ina ganin motan naji
haushi ta kama ni amma na kawar, muka yi sallama da Umaima ta wuce gidansu, na shige namu gidan, tun
da na hangi mota danƙareriya a cikin gidanmu na ce to Alhaji ya samu zuwa kenan, ajiyan zuciya nayi na
shige palourn da sallama, samunsa nayi shi kaɗai zaune a palourn yana waya, stugunnawa nayi na gaishesa
ya amsa mini da kai kawai yana murmushi, dan da alama waya mai muhimmanci yake yi, miƙewa nayi na
shige ɗakina.
Ya Danish da ya kwashe wata guda bai dawo ba, Abbaa ne ya ƙira sa yana buƙatan ganinsa idan bai zo ba
zai saɓa masa, shiyasa ma ya zo wannan weekend ɗin, amma ba dan yaso ba, kuma bai haƙura ba shi sai
ya koyawa Banafsha hankali.
Bayan na wasta ruwa na huta, fitowa nayi dan na samu abinda zan sakawa hanjaye na, da Mamina muka
kusa yin karo tana ƙoƙarin shigowa ɗaki na, murmushi ta sakar mini ta ce, "Ai na ɗauka kin zama Amaryan
ƙulle ne, abincinma sai na zo na ce ki ci."
Cunna baki nayi cikin shagwaɓa na ce, "Uhmn! Ai gani nan na fito Mamina."
A gaba Mami ta saka ni har palourn, abincin da ta ɗebo mini ta nuna min na zauna na ci, zama nayi tare da
shagwaɓewa na ce, "Mami a bani a baki."
Girgiza kai kawai Mamina tayi ta ɗau cokalin ta fara bani a baki, a haka Alhaji da fitowansa kenan daga
ɗakinsa ya same mu, wata dakakkiyar haɗaɗɗiyar shadda ya saka yayi mugun kyau, Mamina tun da ya fito
ta ke ta binsa da kallo tana murmushi, nima murmushin nayi kai na a ƙasa, Mami ta ce, "Alhaji kyau haka
kaman sabon ango."
Alhaji Mukhtar hannunsa ya zura cikin aljihun garensa ya ce, "Sabon angon ne ma Insha Allahu, nan ba da
jimawa ba, angon Ramlatu."
Hararansa Mamina tayi, shi kuma idanuwansa ya mai da kai na, ya ce, "Yarinyata ya kamata yanzu dai ki
dinga yi wa Maminki faɗa tunda kin girma, Maminki bata son ta haifa miki ƙanne, ko kema bakya so?"
Girgiza kai nayi a hankali na ce, "Ina son ƙanne."
Mami hararana tayi, Alhaji kuma murmushi yayi ya ce, "To yanzu dai na yi latti kada na rasa sallahn
juma'an nan, bari idan na dawo za mu yi magana, ki labarta mini yanda musabaƙan naku ya tafi."
Daga ni har Mami a dawo lafiya kuka masa, sannan ya fice, Mami ta dubeni ta ce, "Faɗima kika ce kina son
ƙanne?"
Da sauri na ɗaga kai ina murmushi na ce, "Eh Mamina, ki haifa mini ƙani namiji tukunna, sai ki haifa mini
mace na dinga mata kisto, kinga nima na samu waɗanda zan dinga yiwa faɗa ina musu wasa, kuma ina
cewa ni auntynsu ce."
Hararana Mami ta yi ta ce, "Da dai maganan ki haifa mini jikoki haka kikayi da ya fi, amma kibar batun
ƙanne, ke kaɗai ma da Allah ya bani alhamdulillahi nagode masa, Allah miki albarka ya nuna mini aurenki,
Allah stare mini ke ya stare miki mutuncinki."
Wani ɓoyayyen ajiyan zuciya na sauƙe, ina ƙoƙarin kokawa da tunanin da ke son zuwa mini, hamdala nake
ta yi a zuciyana ina faɗin, "Ameen."
⭐⭐
CAS Bunayd suna cin abinci amma hankalinsa gaba-ɗaya yana kan waya, General ne yayi gyaran murya ya
ce, "My Man za mu ɓata fa."
Sosa ƙeya CAS Bunayd yayi ya rufe wayan, a hankali yake cin abinci cikin yanga kaman mace, sai da suka
gama ci duka sannan suka tashi suka koma cikin palourn da ke nan a downstairs, babbar budurwan ce ta
masto kusa da Bunayd ta ce, "Yaya yaushe za ka tuna promise da ka mana?"
Ɗagowa Bunayd yayi idanuwansa akan ƙanwar ta sa mai shekaru 19 ya ce, "Wanne alƙawarin fa Ramlah?"
Yarinyar marairaicewa tayi ta ce, "Yaya zuwa Kano fa, ka ce za ka kai mu wajan Majeeder."
Bunayd lumshe idanuwansa yayi, sannan ya buɗe su alaman irin ya mance ma da wannan maganan, ba
tare da ya kalleta ba ya ce, "banda yanzu sai wani lokacin."
Kaman za ta yi kuka ta fara masa magiya, sauran yaran ma mastowa suka yi, suka saka shi a gaba kaman za
su yi kuka, duk sun haɗa bakinsu suna cewa, "Please Our Air Force."
Gajiya da ihun nasu da yayi a kunnensa ya sanya shi haɗe fuska tare da buga