Showing 108001 words to 111000 words out of 111817 words
Chapter 37 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf
jiran fashewa.
Momsee dai ko a jikinta ta tattara ta koma sashinta, Bunayd kuwa tuni ya fice daman a gidan, General ma
sun fita da Papi, Suhail yayi nasa wajan, Nabeel kuma yana can ɓangarensu.
Majeeder kuwa tun da Momsee ta bata nata kayan ankon da aka mata, ai farinciki kaman ta fire, daɗi
kawai take ji Papi zai kawo mata Aunty, kuma za'a taho mata da ƙawa, dan Papi bai faɗa ma Majeeder akan
cewa ƙawarta za ta yi aure ba, shungulloli sun sha kan sa, dan haka Majeeder ta sa rai, ba abinda take sai
labartawa su Ramla maganan ƙawarta kuma har ta saya mata gift.
Washegari juma'a, da ya kama ranan ɗaurin aure, da wuri tawagar Alhaji Mukhtar suka shirya, suka hau
jirgi sai Adamawa, sun isa da wuri, dan haka babu ɓata lokaci aka shirya motoci har da na sojoji suka kama
hanyan Mubi, Alhaji Mukhtar, General Sufyan, Alhaji Idris, Alhaji Tasi'u(baban Abeed), Suhail, Nabeel,
Bunayd, Abeed, da wasu sojoji abokanan aikin Abeed da na Air Force abokanan aikin Bunayd, motoci sun
kai Goma suka kama hanyan Mubi, wani irin mugun gudu suke, duk da gargadan hanyan amma cikin awa
uku suka isa garin Mubi dan ba maganan stayawa a checking point, masu checking point ɗin da kan su ke
yin tafiyan, suna isa kuma masallacin da za'a ɗaura auren suka nufa, dan lokacin juma'a ya riga da ya yi,
Alhaji Mukhtar dai ba abin da yake sai washe baki, shi kuwa Bunayd da ya jima da mancewa da wata idiot,
sai da suka shigo garin Mubi ya tuno ta, addu'a yayi Allah ya sa ya ganta, za ta yi stallen kwaɗo yau ɗin nan.
⭐⭐
Ɓangaren mu da Mamina shiri muke ba kama hannun yaro, tun da biki ya rage sati guda kuma, Mami da
kan ta tayi magana a tahfiz aka bani hutun wata guda, sai a satin da za mu tafi Abuja sannan zan dawo da
zuwa, amma zan cigaba da karatuna da komai a gidana har lokacin yayi, duk da College ma zai kama
hutunmu zai ƙare ne, nan da sati biyu, kenan bayan biki da sati guda, amma shi ma sai an yi wata guda zan
koma haka Mamina ta yanka mini.
Wani irin ciccikowa jikina yayi ko ta ina, kyau nayi sa na musamman, ƙamshi kuma kaman a jikina aka
halicci turare, fatan jikina kaman na jarirai, ga sulɓi ga yalƙi, ni da kai na nasan na sauya, Mami ta kashe
kuɗi, kuma mata mai gyaran jiki tayi aikinta yan da ya kamata.
Kaman yan da na sauya na haɗe, haka Mamina tayi mugun kyau, sharr da ita kaman bata haifi kamata ba,
musamman ma da take da ƙaramin ruwa, da kuma jiki mai kyau.
Shirin da ake yi a gidan Abbaa, za ka ɗauka ƴar cikinsa yake aurarwa, domin ya ma hana Mami a ɗaura
komai a gidanmu, sai dai abin da ya kama dole.
Abu na farko da ya bani mamaki, shi ne ganin mutanen unguwa da ke gulman Mamina, duk sun zo taron
da aka fara, duk da yake dai nasan Mamina ba ruwanta, lafiya lau take zaune da kowa, domin tun da nake
da wayona, to bansan wanda zan nuna na ce, ga abokin faɗan Mamina ba, to ganin mutanen anguwa sai
nayi hamdala, dan nasan wannan ma wata ni'ima ce ta Ubangiji, masu zaginka kuma su dawo suna cin
albarkacinka.
Duk da Malam Abbo Ustaz ne kuma ɗan shi'a, amma bai hanani yin event ko ɗaya ba, dan ni ce na yanke
ba wani abin da zan yi sai walima, Umaima kuma ta ce ban isa ba, dan ga classmates namu na college duk
sun yi anko, ta dage sai mun yi ko bridal shower ne, idan ya so sai ayi walima da kuma Arab day, da farko
Mami bata ce mana komai ba, har sai da ta ga na dage ba za'a yi ba, sannan ta saka baki akan mu yi tun da
shi mijin bai hana ba, dan haka Umaima ta fitar da komai ta tsara shi, da ƴan College da suka zama ƙawaye
su ma, har anko da komai an yi, ana shiga satin biki muka fara hidindimu.
Ranan Litinin muka sha ƙunshinmu ni da ƙawayena, muka dinga ɗaukan photuna, Mamina ce ta biya mana
komai, dan kuɗaɗen da Malam Abbo ya bani na hidima suna wajanta, sannan wan da Alhaji ya bayar nawa
da nata duk suna wajanta, washe-gari talata muka yi Arab day namu, na saka dogon rigan da Alhaji ya
kawo mini daga Egypt, aka mini rolling na kuma sanya Safan hannu da ƙafa, fiskana ma ba abin da ake kallo
sai idanuwana, ƙawaye ma suka sha nasu dogayen rigunan, kyau muka yi sosai, a haraban gidan Mami
muka yi abinmu.
Washe-gari Laraba muka yi bridal shower, wannan a palourn Mami muka yi decoration, muka yi iya ni da
ƙawayena, ranan Mamina ma tayi ƙunshinta, washegari Alhamis aka yi walima a tahfiz namu, a ranan
kuma aka yi chin-chin da komai a gidan Abbaa.
Abu na farko da ya fara jawo ƙananun magana, shi ne dangin Ango ba su zo da yawa ba wajan waliman, to
dai ni ban ce komai ba, komai aka yi da ido nake bi da kuma addu'a, Mamina ma ta musu uzuri, ta dai
kwaɓi masu ƙananun maganganun akan ayi shiru.
Dare nayi kuma sai ga su, sun kawo kayan aure niƙi-niƙi, cikin mutunci da fara'a aka tarbe su, sai dai
saɓanin haka aka gani a tattare da su, dan gaba-ɗaya ba fara'a ba komai kaman dole aka musu, ga shi
Mamina bata wajan, nan ƙananun magana ya fara kacaɓewa, sai da Ummu da sauran manyan matan suka
dakatar, abun tarban kayan ma da ake yi, sunƙi ɗauka, sai Ummu ce ta bi su da shi har waje ta basu haƙuri,
aka samu wata dattijuwa dama-dama a cikin su, ta amsa suka yi sallama, suka tafi.
Maganganu kam yanzu sun samu wajan zama, dan shafi aka buɗe musamman a kansu ana yi, kaya yayi
kyau sun yi ƙoƙari, akwatuna waɗanda ake yayi guda huɗu da kit, ga kuma na iyaye da na dangi, ga kayan
rufi duka, jama'a na kallon kaya suna surutunsu.
Mami abun bai mata daɗi ba, kuma ya dameta, magana tayi abar zancen haka, sannan fa jama'an suka
stagaita, wasu ma da suka gama kallon kayan suka tafi, wai sun yi zuciya Mami ta yi magana, mutane ikon
Allah kenan, lokacin da ake jefanmu da baƙaƙen maganganu har da su, yanzu kuma da Allah yayi Allahnsa
ya kawo mana sanadin rufin asirinmu, shi ne za su kawo wasu magana daga abu kaɗan wan da daman an
san dole ne samun saɓani, musamman a hidiman biki, dole sai ana haƙuri kuma an haɗa da uzuri.
A haka aka gama kallon kayaki aka rufe, kowa ya nemi wajan kwanciyansa ya kwanta, sai dai ɓangaren
Mami ranan bata yi bacci ba sam, damuwa ya taru ya mata yawa, gani take kaman daren nan ba zai wuce
ba, balle kuma gari ya waye, tun da Mami take bata taɓa ganin dare mai matuƙar stayi ba irin wannan
daren, wan da take ganinsa kaman almara, wai a washe-gari juma'a ne ɗaurin aurenta ita da ƴar ta, farin
cikinta, gudan jininta, yarinyar da ta sadaukarwa komai nata, ta zaɓi rayuwa da ita akan tare da iyayenta.
Hawaye kawai Mami ta ji yana bin kuncinta, karo na farko tun da ta baro iyayenta, ta ji tana matuƙar
kewansu, tana jin ina za ta gan su, su nuna mata gata a wannan rana ita da ƴar ta, Mami kuka ta yi
ishashshe, har sai da ta ƙoshi da kukan, sannan ta tashi ta ɗaura alwala ta zo ta tada nafila, kwata-kwata
bata kwanta ba balle ta yi bacci, har asuba ta kawo kai addu'oen alkairi take yi wa kan ta da yarinyarta, sai
da aka yi sallahn asuba, ta yi nata sallahn sannan ta kwanta, da niyan anjuma za ta bawa Banafsha labarin
komai, kaman yan da ta mata alƙawari.
A ɓangarena baccin nima dai rabi da rabi na yi sa, ƙarshe da na gaji da juye-juye, miƙewa nayi na ɗauro
alwala na zo nayi nafila da addu'oe, addu'a na yi ga mahaifina idan yana raye ko yana mace, sannan nayi ga
mahaifiyata ina mai mata addu'an, Allah sa mutuwa ce za ta fitar da ita a wannan gidan aure da za ta shiga,
na yi wa al'umman Annabi, sannan nima na yi wa kai na, ina idarwa na bi lafiyan gado na kwanta, ina mai
jin nistuwa na stirgani, cikin ƙanƙanin lokaci kuma bacci yayi awun gaba da ni.
Abu da duk su Mami basu sani ba, kuma ba su da labari, shi ne wani gagarumin ƙaramin yaƙi ake a
ɓangaren su Malam Abbo.
Kaman yan da muka sani tun farkon labari, Malam Abbo ɗan shi'a ne, iyayensa shi'a suke gaba da baya,
ƙarshenta ma babansa shi ne limamin babban masallacin su na juma'a, na ƴan shi'a.
Imam Adamu, wan da suke ƙira da Abiy, yaransu 7 shi da matarsa, Malama Hauwa'u, akwai babba wacce
mace ce, Aunty Mardiyya, sai namiji Ya Hussain, sai Ya Hassan, sai Aunty Sajeeda, sai Aunty Zakiyya, ɗan
Autan shi ne Ali(Malam Abbo).
Daga ƴan uwansa har iyayensa duka suna matuƙar ƙaunarsa, su a al'adansu ma ba ruwansu da musabaƙa,
amma saboda soyayyan da Abiy yake yi wa Malam Abbo, ya bar sa ya shiga tahfiz yayi musabaƙa, wan da
ya kai sa har matakin nasaran, da ya ciwo kujeran Makka, da kuma aka ɗauki nauyin karatunsa a Madina.
Yayyunsa maza da mata duk sun yi aure, kuma duka ƴan uwansu shi'an suka aura, to da Malam Abbo ya
kawo maganan auren Banafsha, duk sun amsa sun yi na'am saboda tunaninsu ita ma ɗaya daga cikinsu ne,
da suka ji tana tahfiz ɗin ma ba su ce komai ba, tun da sun san ta kusa gamawa, kuma Malam Abbo na
makarantar, duk abin da Malam Abbo ke yi ko ya saɓawa starinsu, to sau tari Abiy yana masa uzuri, kuma
yana tausan Ummi dan sosai Abiy yake ƙaunar Ali.
Ƴan uwan Abiy su suka fara yin bincike, nan suka ji labarin Maman Banafsha karuwa ce, yanzu ne ita ma za
ta yi auren, ko da suka samu Abiy da maganan, ƙiran Malam Abbo yayi ya tambayesa akan ko ya san da
labarin, Malam Abbo amsawa yayi da ya sani, kuma a haka yake son aurenta, jihadi zai yi, ai ba'a haramta
auren karuwa ba balle kuma ƴar ta, wacce bata ji ba bata gani ba, babu ruwanta.
Abiy nusar da ƴan uwansa yayi akan kada su damu, sannan kada ma su yi aji maganan a bakinsu, ai ba
komai a ciki tun da akwai a cikin magabata wan da yayi irin auren, shi karuwan ma ya aura da kan sa, kuma
ƴar karuwa ai ba ana nufin karuwa ba ce, sannan idan aka ce ana ƙyamatan su ko a ce ba za'a aureta ba, so
ake ta lalace kenan, dan haka da Abiy yayi nasiha sai suka ji, suka ci-gaba da shirin aure, amma yayyunsa
mata duk basu sani ba.
To abu na farko da ya fara kunno kai shi ne, abokin Malam Abbo ne da kansa Zubair, ya tafi gidan babban
addansu Aunty Mardiyya, kaman abin kirki ta tarbesa har tana zolayansa su angwaye ne, bayan sun gaisa
sai Zubair ya karkace hulansa, rass ya zayyanowa Aunty Mardiyya ƙarya da gaskiya, ya kawo aya da hadisi
yayi backing na maganansa da shi, ai zina bashi ce, abin da yake gudu kada a zo nan gaba a zuria'a abu yayi
ba kyau.
Aunty Mardiyya kuwa ta ɗau zance ta zauna a kai daɓas, abin ka da mata sai s hankali, har da godewa
Zubair tayi, yana tafiya ta ƙira sauran ƴan uwanta a waya, suka gama magana washe-gari suka haɗu a gida
duka, Ummi suka fara samu suka zazzage mata komai, duk da tasan da zancen amma da yake, ƙarya da
gaskiya ne Zubair ya faɗa, sai ya ƙara cika Ummi fam ta ce nan duniya Ali ba zai auri Faɗiman ba, tun da
kalan tarbiyyanta kenan.
Abiy na dawowa shi ma Ummi ta hau bam-bami, wai ya sakalta Ali da yawa, ya sake masa sosai, ya rasa ƴar
da zai aura sai mara tarbiyya to bata amince ba, Ummi na yi su Aunty Mardiyya na yi su ma, Abiy sai da ya
gama sauraransu ya jira suka gama, sannan ya fara musu nasiha ya faɗa musu gaskiyan abin, amma Aunty
Mardiyya ta ce ai abokinsa ne ya faɗa kuma shi ma malami ne a makarantar, ba zai yi ƙarya ba, Abiy tun
yana nasiha har ya koma faɗa, sai da ya fatattake su ya korasu gidajensu, sannan ya samu salama, amma
Ummi ta ƙi haƙura, har dai ran Abiy ya ɓaci, shi ma ya ce sai anyi, ita kuma ta ce ba za'a yi ba.
Su Aunty Mardiyya kuwa sai da suka ƙara zuwa ga baffanunsu, suka faɗa musu komai sannan suka koma
gidajensu, baffanunsu suka samu Abiy da maganan, rai a ɓace ya ce ya gama magana, indai Ali bai auri
Faɗima ba to Allah ne bai nufa ba.
Rikici ya ɓullo ta nan, wannan ma ya ɓullo ta nan, masu kawo gulma kuwa daban-daban, kowa kuma da
karyan da yake shararawa har biki ya zo, duk rikicin Ummi da yaranta Abiy yayi jan ido sosai, dan dole suke
komai ba dan sun so ba.
Har labari ya kuma isa ga Ummi da su Aunty Mardiyya, na cewa Banafsha ta yi bridal shower sun ta yin
rawa da ƙawayenta, magulmata suka kuma ɗaura ƙarin gishiri, maganan Arabiyan day ma duka an ce sun
yi rawan banza, nan fa Ummi ta ƙara kumbura, su Aunty Mardiyya suka ce ba mai zuwa wajan walima,
Ummi ta hana kowa leƙawa, sai matan su Ya Hassan ne aka samu suka je, su ma mazajensu ne suka
stawatar musu da Abiy yayi magana.
Wajan kai kayan aure kuma Aunty Zakiyya da Aunty Sajeeda, tare da su aka kai, amma a hakan ma sai da
Abiy ya nuna ɓacin ransa sosai, kuma ya ajiye musu sharaɗin, idan suka yi faɗa ko wani abun tashin hankali
to bai yafe ba, dan Abiy sosai yake ganin mutuncin iyayen Banafsha, tun da tare da shi aka je tambayan
auren.
Zubair abokin Malam Abbo ya gama nasa, amma ashe bayan nasa da sauran masu kawo gulma, dan Garba
ɗan gidan halliru yana gefe shi ma yana nasa shirin, tun da ya ce yana son Banafsha ta ƙi kulasa ta mayar
da shi mahaukaci, ya yi ƙoƙarin samu ya illatata amma ta tsallake, to alwashi ya ci na ba zai bari tayi aure
ba a garin muddin da ran sa, dan haka duk abin da ake yana bibiya, ganin ko ta ina Abiy yana dannewa yayi
haƙuri ya ce za'a yi auren a haka, to sai kuma ya ɗau wani shirin na daban, jira yake kawai gari ya waye
juma'a tayi ya ƙaddamar da ƙudurinsa.
Ya Danish babu shi babu labarinsa, ko da Abbaa ya ƙira sa akan yayi haƙuri, ya wastar da komai ya zo
ɗaurin auren, tun da ita ma kaman ƙanwarsa ce, amma ya Danish ya fara kwane-kwane, da Abbaa ya nuna
ran sa ya ɓaci sai ya amsa zai zo, amma daga suka gama magana sai ya kashe wayansa gaba ɗaya diff.
Malam Abbo Ango ya sha mai, duk wani badaƙala da ake da rikici, shi ko a jikinsa harkansa yake da
shirye-shiryensa, musamman ma da ya ga Abiy ya staya masa, sannan duk wani abu da zai haɗa sa da
Ummi kauce masa yake yi, dan abin da Abiy ya faɗa masa kenan, su bari sai anyi auren, sai su zauna su
fahimtar da ita kuma ya bata haƙuri, sannan ya masa faɗa akan labarin da ya ji, na faɗima sun yi bidi'a wai
bridal shower, haƙuri ya basa akan ba za'a kuma ba, za'a kiyaye, sannan yayi tafiyansa, dan haka Malam
Abbo ko gidan ba ya shigowa saboda batun Ummi, yana hidimansa, yana kuma maƙale da wayansa, dan
suna waya da Banafsha da layin Ummu.
Washe-gari juma'a, tun da gari ya waye ko wanne ɓangare ake shirye-shirye, amma dai shirin ya sha
bam-bam, domin ɓangaren su Ummi gaba-ɗaya yau rikicewa tayi, akan ba maganan wannan auren kuma
bata yarda da shi ba, su Aunty Mardiyya ma sun yi nasu tashin hankalin, baffanunsu ma sun zo da nasu
maganan na bidi'a-bidi'an da Banafsha tayi da ƙawayenta, ba su yarda da shi ba, ga kuma ƙishin-ƙishin ɗin
su Banafsha wai izala ne, da yake shi'a da izala sam-sam basa shiri.
Abiy idan ran sa yayi million to ya ɓaci, kan sa kuma ya ɗau chaji sosai, wato ka guji kaidin mata idan suka
ƙi abu, da farko sun ce ƴar karuwa ce, an zo an ce tana bin maza, an ce bata da tarbiyya, an ce ta yi bidi'a
har da rawan da bai dace ba, an ce..an ce..an ce ɗin da yawa ba kaɗan ba, duk kuma yana haƙuri saboda
yaro yana son yarinya, sannan yanzu ga wani batu na wai su izala ne, sannan wannan kam yasan ƴan
uwansa ba za su bari ba ko da ya stawatar, dan haka a ranan juma'an da kan sa ya bincika duk abin da ya
kamata, abin da ya jawo kuskure babba kuwa shi ne mahaifin Garba, wato malam halliru yana cikin
waɗanda Abiy yayi magana da su.
Lokacin sallah na yi, Malam Abbo ya shirya da abokanansa suka tafi masallaci, ba ma masallacin su da suka
saba sallah suka je ba, direct babban masallacin da za'a ɗaura auren a can suka nufa shi da tawagarsa ta
abokanansa.
Ɓangaren mu kuwa yan da shirin yake, komai dai-dai sai abin da ba za'a rasa ba na halin rayuwa,
gaba-ɗaya hidima ya sa ko