Showing 72001 words to 75000 words out of 111817 words

Chapter 25 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf

Advertisement

16 Aug 2025

4052

dai bakyajin shawara ta Allah da
Manzonsa, to ni ba abinda zan ce, Allah rufa mana asiri kawai, amma dai aure ai abin so ne, kuma mutunci
ga ko wacce ƴa mace kema kin sani, to stakani da Allah ma wa ya ƙi ni'imar aure? Ai ko ba dan ci da sha ba
kana samu a gidanku, to ko dan John-thomas ai ka yi, indai Allah ya nufa kuma ya kawo miji to aure shi ne
rufin asirin ko wacce ɗiya mace, ni wani gulma na ji ma nake son miki ke ma, bansan ko kin ji ba dai."

Yau ba mu ce mashine ya kai mu ƙofan gida ba, sauƙa muka yi muna tafiya muna kan hiranmu, cewa nayi,
"Gulman menene haka?"

Umaima ta ce, "kinsan ashe dukan da Umma ta mini wai har da kishi, tana dukana tana surutu ni bana
fahimta da yake na jibgu, sai ranan nake jin Abbaa na magana wai saboda ya ce zai auri Maminmu ne,
kuma sai ya aure ta."

Ajiyan zuciya na sauƙe dan na tuna abinda Mami ta yi ranan dan na mata wannan maganan, kallon
Umaima nayi na ce, "To ke kina goyon bayan auren kuwa? Dan ni gaskiya ina jin ta Ummu kaman dai bai
kamata ba, kar ta ce Mamina ta ci amanarta, dan nima na ji gulman."

Murmushi Umaima ta yi ta ce, "chaɓ! Ai ba ki sani ba masoyiya, Ummu kam ta amince kuma kaman ma
har da shawaranta, nidai wallahi zan so haka, shikkenan mu koma zama gida ɗaya, ba wanda zai hanani
zuwa gidan Mami ko miki magana tun da mun zama ƴaran baba ɗaya, kin ga ko aurenmu ma sai Abbaa ya
mana tare."
Murmushi nayi na ce, "ta kwana gidan sauƙi, Allah taimaka ya tabbatar da alkairi, nima zan dage da damun
Mamina ayi ma da wuri kowa ya huta."

Dariya muka yi dukkanmu cikin farin ciki muka cigaba da tafiya, yau ma dai kaman jiya a ƙofan gida muka
samu Ya Danish a zaune, ba tare da na kallesa ba na yiwa Umaima sallama na juya na wuce gidanmu,
Umaima gaishesa ta yi a storace, amma sai ya amsa bakomai kaman bai ganta tare da ni ba, hamdala tayi
ta shige gida.
Ya Danish ci-gaba yayi da kallona har na ɓacewa ganinsa, sannan ya sauƙe nauyayyan ajiyan zuciya a fili ya
ce, "jarabawa kenan, ko iya haka Allah ya saka miki abubuwan da nake miki, tun da ga shi kin hanani
sukuni kin hana zuciyata nustuwa."

Ni kuwa ina shigewa gidanmu na samu ba kowa a palourn, ina ƙoƙarin shiga ɗakina aka yi sallama, juyawa
nayi na amsa jin muryan namiji, wani ɗan matashi ne, a mutunce muka amsa sai na ce, "wa kake nema
bawan Allah?"

Matashin yana murmushi ya ce, "Ko kece Hajiya Ramla?"

Kallonsa nayi da kyau, har zan ce a'a sai na ce,."Eh! ni ce, na faɗa ina murmushi dan kada yayi kokonto.

Washe baki matashin yayi ya ce,."Daman layinki aka bani, aka ce kina ji da al'amuran lalura tamu ta maza,.
shiyasa na zo" ya faɗa yana murmushi.

Murmushi nayi inajin kaman na ɗura masa ashar, amma na haƙura dan naci riban zance, na ce, "To fatan
da nauyinka ka zo, ina nufin maganan kuɗi."

Matashin murmushi yayi ya ce, "Hajiya dubu goma ce da ni a taimaka mini."

Wani irin gululun baƙin ciki ne ya turnuƙe ni, wani irin kallon banza na zabga masa, tare da fara zaginsa
tass!tass!, haka na mishi na faɗa masa baƙaƙen maganganu sannan ba shiri ya juya, nima juyawa nayi ciki
kaman taƙaici zai hallaka ni.

Wucewa ɗakina nayi da haushi kaman ya kashe ni, nasan da yasan ni yarinyarta ne, to da shima ƙira na da
sunan da na tsana zai yi, duk wani mai zuwa wajan Mami nasan mai zan masa yanzu, dan insha Allah
Mamina aure za ta yi.

Abubuwan da zan yi na yi na kwanta, dan haushi ko zuwa gaishe da Mami ban yi ba, balle kuma na kula
abinci, baccina nayi ishashshe sai da lokaci ya tafi na tashi, alwala nayi tare da yin sallahn la'asar, fitowa
nayi na samu Mami na aikinta, ina tura baki na mata sannu ta amsa.

Mami ta ga yanda nayi kicin-kicin da fiska, sanin halin rigima irin nawa sai bata ce mini komai ba tun da
bata san abinda ya faru ba, haka ni kuma na gaji dan kai na naje na ɗiba abinci na ci, ina ci Mami ta
murmusa ta ce, "yunwa ai ba pendon mutum ba ne ko gwaggonsa."

Tura baki nayi ina gamawa na ce, "Mami, ashe Umaima bata da lafiya ne shiyasa bata je makarantar ba,
kuma har kwanaki suka yi a asibiti."

"Ashsha! Subhanallahi! Allah ya bata lafiya, ai ba mu da labari, in Allah ya yarda zan shiga na duba jikin
nata, kwana biyu ma Ummunku bata leƙo ba, tun da ta zo ta duba jikinki" faɗin Mami tana aikinta.

"Ameeen Mamina, yauwa Mami mun ji labarin wai za'a manna mana result, a taya mu da addu'a Mami
Allah sa mu ga alkairi, daman Alhaji ya ce zai mini kyauta ma" na faɗa ina murmushi dan jira nake kawai ya
tambayi abin da nake so, ni kuma na faɗa masa abinda na jima da ƙudurcewa a rai na.

Mami ta ce, "To Allah ya sa ku ga alkairi, mu kuma Allah sa mu ji alkairi, Alhaji kam yana can wata ƙasar ma
ai."

Tura baki nayi na ce, "Ai dai zai dawo Mami, kuma nasan zai mini kyauta na."

Murmushi Mami tayi ta ce, "To Allah dawo da shi lafiya."

Da, "Ameen na amsa."

Hira muka dinga yi da Mamina, amma ko sau ɗaya bata ambato Malam Abbo ba, balle na ji ko ya faɗa
mata wani abun, ganin haka sai na share lamarin nima, sai da na taya Mami aiki sannan na shirya tafiya
makarantar yamma.

Ɓangaren Ya Danish dai aiki ya kallesa, bai ankare ba sai ga shi wankin hula na neman kai sa dare, yanzu
gaba-ɗaya baya da aikin da ya wuce zama a waje yana jiran ganin giftawan Banafsha, ga shi tun zuwansa
bata je ko ƙofan gidan su ba balle kuma a kai ga ta shiga, shi abin ma damunsa yake yi, ga shi Abbaa ya
tuna masa saura musu sati biyu su kawo mata su yake jira ko ya aura musu ko ma wacece, Umma tun
zuwansa ta bi sa da maganan tun da yana da budurwa yayi magana sai a tura, ko kuma ya koma Camaroon
ya dubo a cikin yaran yayyunta ko akwai wacce ta masa, amma nan ma Danish yayi shiru abinsa, shi
damuwansa kawai rashin sukunin da zuciyansa ke ciki game da Banafsha.

Umaima ta fito a gida ta samu Ya Danish zaune a ƙofan gida, ganinsa sai ba ta yi gigin ko bin hanyan gidan
su Banafsha ba, duk da bata kalli ta fito ba, ta juya za ta tafi sai ya ƙira ta, juyowa Umaima ta yi ta ce, "Ga
ni yaya."

Ya Danish ya ce, "Ita mara kunyar ƙawar taki ba za ta je makaranta ba ne?"

Umaima dai a storace ta ce, "Nima ban sani ba yaya."

Staki Danish yayi, ya buɗe baki zai yi wani maganan sai ga Banafsha ta fito, a ɓoye kada Umaima ta gane ya
sauƙe ajiyan zuciya tare da cewa, "To sai ki tashi ku tafi ai tun da ba kya ji, kuma ki tabbatar kin kula sosai."

Umaima miƙewa tayi a storace ta bar wajan, suna tafiya da Banafsha ta sauƙe ajiyan zuciya ta ce,
"Masoyiya ba za ki ce mini sannu ba."

Taɓe baki nayi na ce, "akan me?"

Hararana Umaima tayi ta ce, "Ba ki ga ya Danish da ya stayar da ni bane, wai tambayana ya ke ba za ki je
bane, na ce su ya Danish an fara dawowa hanya, ya fara gane Annabi ya kafu, yanzu zan samu peace of
mind, dan yanzu ya zama miskilin dole ma."

Kafaɗa na ɗage irin ko a jikina ɗin nan, na ce, "shi ya jiyo " daga haka ban kuma cewa komai ba, har muka
isa muka yi karatunmu muka dawo.

Mun dawo ma a ƙofa muka samu Ya Danish, nan kowa ya kama hanyan gidan su.

Da dare muna zaune muna kallo da Mamina sai ta dube ni ta ce, "Faɗima."

Hankalina na kan kallo na ce, "na'am Mami."

"Ina son ki bani hankalinki, za mu yi magana mai muhimmanci."

Ɗauke idanuwana akan TV nayi, na ce, "Ina sauraranki Mamina."

Gyaɗa kai tayi ba ko alaman murmushi a fiskanta ta ce, "Ina son ki faɗa mini ya kuka yi da malaminki, da ya
faɗa miki tasa maganan ke me kika faɗa masa?"

Ni tun da naga Mami bata mini maganan Malam Abbo ba, tun jiya sai na mance da kashinsa ma, amma jin
tambayan da ta mini yanzu sai na cunna baki na ce, "Ni ba abinda na ce masa."

Ƙara tamke fiska Mami tayi ta ce, "Kinsan bana wasa da ke ko? To maza ina sauraranki faɗa mini abinda na
tambayeki."

Tura baki nayi cikin shagwaɓa na ce, "cewa yayi yana so na zai aure ni" ina faɗan haka sai nayi shiru.

"Da ya faɗa miki hakan, sai ke kuma kika ce masa me?" Mami ta tambaya tana jefa mini mugun kallo.

Kaman zan yi kuka na ce, "Mami Allah gaskiya na faɗa masa, ya ce yana so na zai aure ni, sai ni kuma na
faɗa masa gaskiya ba aure zan yi ba, ai gaskiya ce Mami, ni ba zan yi aure ba, tun yanzu ana mayar da ni
saniyar ware akan jarabawan da Allah ya mini, idan nayi aure dangin miji da miji su dinga gallazawa
rayuwata kenan su ma.."
Wani mugun stawan da Mami ta buga mini, shi ya sanya ni yin shiru na haɗiye sauran maganata, cikin
tsawa ta ce, "Idan ba ki yi aure ba dan ƙaniyanki me za ki yi? Banafsha ki fita a idona na rufe, kada ki bari
rai na ya ɓaci fa zan saɓa miki, idan ba ki yi auren ba so kike na saka ki a gaba kaman television ina kallonki
ko kuwa na kwaɗaki a tire kaman kwaɗo na cinye? To ki mai da hankalinki."
Tura baki nayi, ciki-ciki na ce, "Ni dai ba auren da zan yi, haka kawai a dinga ce mini ƴar mace, a ce mini ƴar
karuwa, ni rayuwata gaba-ɗaya ba wani farin ciki kenan."

Mami ta ce, "Banafsha kinsan Allah zan saɓa miki a kan wannan maganan, ke baki san cewa Allah ma da
kansa yana tausayawa duk budurwa ko saurayin da suka mutu ba aure, kuma sun kai yin auren ba, idan ba
ki yi auren ba me za ki yi? Me damuwanki da maganan mutane? Banason shashanci da rashin hankalinkin
nan."
Tura baki nayi na ce, "Ni dai ba wani auren da zan yi, aka masta mini kuma shikkenan sai na shiga duniya,
daman gado ba karambani ba."

Ranƙwashi Mami ta mini mai kyau ma kuwa, sannan ta ce, "To zan gani cikinmu wa ya isa da wani, tun da
har kin yi girman da ina faɗa kina faɗa, kuma ki tabbatar Inshà Allah tun yanzu za ki fara shirin aure,
muddin ya ce yanzu za'a yi auren, to ko bokon ma stayar da ita za'a yi, aure zan miki."

Kuka kawai na saka ina bubbuga ƙafa, cewa nake, "nidai ba auren da zan yi sai an kai ni wajan dangin
babana, su za su aurar da ni, kawai in ana so naji magana nayi biyayya a kai ni wajan dangin babana, ai ba'a
jikin bishiya aka ɓanɓaro ni ba, nidai dangin babana."

Mami ikon Allah ta staya gani, saboda Banafsha dagewa tayi ita sai dangin babanta za'a kai ta sannan ya
yarda ta yi aure, numfasawa Mami tayi ta ce, "Banafsha ko kina so ko bakya so za ki yi aure Insha Allah,
indai ni ce mahaifiyarki kuma na isa da ke, dangin ubanki kuma kibar maganansu idan ba haka ba zan saɓa
miki, zan yi shawara da wanda ya kamata a je neman aurenki wajansa, ke kuma ki saurari Malam Aliyu,
idan ba haka ba ni da ke ne, sai na niƙa ki a gidan nan."

Tura baki nayi na ce, "nidai ko dole za'a mini to a haɗa ni da dangin ubana tukunna, sai an mini abinda
nake so sai na yarda, kuma idan ba haka ba sai dai ke ma Mami ki yi haƙuri ki yi abinda kike so nayi."

Mami wani kallo ta aika mini da shi ta ce, "tashi ki bani waje kamun na karyaki, ai kin girma yanzu wuyanki
ya kai yanka, duk maganan da kike so faɗa mini kike yi."

Miƙewa nayi sumui-sumui na wuce ɗakina, ina shiga na saki murmushi, domin ni ko kaɗan maganan auren
Malam Abbo ba baƙin ciki ba ne gare ni, maganan auren Malam Abbo alkairi ne gare ni, domin da wannan
batu zan yi ƙoƙari wajan gani lamuran Mamina sun saitu, alhamdulillahi! Daman Allah subhanahu wata'ala
ya ce, FA'INNA MA'AL USRI YUSRAH, duk wani tsanani na tare da sauƙi, to yanzu ina ganin na fara tinkaro
stanin sauƙi da kuma farin ciki na rayuwata, a haka ina zancen-zuci ina murmushi ban ankare ba, har
ɓarawon bacci yayi gaba da ni.

Washegari Lahadi muka je makaranta safe da yamma duka tare da Umaima muka dawo, kuma duk ya
Danish na nan yana kallonmu bai ce mata komai ba, ni kuma ko gigin shiga gidan su ban yi ba dan bana ko
ƙaunar kallonsa balle haɗa inuwa da shi, stakanina da Mamina kuma bata ƙara mini maganan Malam Abbo
ba, illa iyaka da ta ce mini na sauraresa.
Wannan karon Ya Danish bai koma ba har sai washegari Litinin, a hakan ma wai dan Umma tana surutun
bata gane ma abinda ke damunsa shiyasa ya shirya zai koma, dai-dai lokacin da muka fito tafiya College shi
ma ya fito, ni da Umaima tafiyanmu muka yi za ku nemi mashine, amma sai ya tsaya a gabanmu ba tare da
ya juyo ya kalle mu ba ya ce, "ku shigo."
Kallon sama da ƙasa na yi wa motar sannan na kawar da kai, Umaima jin ya ƙara magana sai ta riƙo
hannuna ta ce, "masoyiya ki yi haƙuri mu shiga ya sauƙe mu."

Hararanta nayi ban ce komai ba, na sake hannunta na yi gaba, Umaima kaman za ta yi kuka, ta kalli Ya
Danish ta kalleni, Ya Danish kwallon Umaima yayi tare da yin ƙwafa ya ce, "Sai ku taka da ƙafanku ai" yana
gama faɗa yayi gaba da mugun gudu, yana wuce inda nake na ja staki tare da hararansa shi da motan nasa.

Umaima da ɗan sauri ta iskoni tana faɗin, "Masoyiya mu godewa Allah yanzu ya sha nistojin ya daina
bala'i, idan ba haka ba ai da tuni ya shuka mana, ke ma me ya sa za ki ƙi shiga?"

Hararan Umaima nayi na ce, "banason magana ki ƙyale ni, tun da dai naga ban hanaki shiga ba ke da
motan yayanki, aikin banza aikin wofi, kina wani cewa na shiga sai ka ce baki san irin abinda yake mini ba,
ko da ya ke ba laifinki ba ne, daman aka ce naka sai naka, ni bare ce stakaninku."

Umaima dariya tayi sosai ta ce, "rai na bai ɓaci ba sai ki fama, anji ɗin ke bare ce, mutum sai ka ce
kububuwa, rashin kirkin naki yau ni za ki yi wa kenan? To Allah huci zuciyanki."

Hararanta nayi na ce, "oho muku ke da yayanki, kuma dan ki ji mun ɓata ma kowa yayi hanyansa."

Murmushi Umaima ta yi ta ce, "Daman wallahi kaman kin san zaman lafiyanmu yayi yawa, ana ƙawance
ana ɓatawa ya fi daɗi da ƙargo, amma kullum ni baki haƙuri, ke kuma yin haƙuri, ya kamata ai ko casuwa
mu dinga yi, ko da yake ai ma Ummu ta ce mun yi dambe da muke yara, amma ni nake saka ki kuka."

Dariya maganan Umaima ya bani, dan haka na dara muka tari mashine muka wuce makarantar, muna
zuwa muka ci karo da kyakkyawan labari, an manna dodon bango, Umaima ta damu mu je mu gani, amma
na ce ta bari ba yanzu ba, tasan yanda muke ƴan sturut ɗin nan sai a maste mu ko a cika mana ciki da
warin hammata, ga kuma wani na stamin zafin da ake yi.
Sai da aka tashi sannan muka samu ganin result namu, amma duk da haka ba mu muka duba ba, dan duba
mana aka yi, alhamdulillahi dukkanmu result yayi kyau yanda ake so Masha Allah.

Muna komawa kowa yayi gidansu, da farin ciki na faɗawa Mami, har da ɗagani Mami tayi dan farin ciki,
saboda result yayi yanda ake so, sai godiya ga Allah.

Haka muka cinye wannan satin ma cikin farin cikin kyawun result namu, sannan a hadda an fara bitan
karatun musabaƙan da za mu yi a cikin jimeta da sauran makarantu na local government's ɗin Adamawa
State, tsakanina da Malam Abbo kuwa yanzu ina sauraransa amma dai bana sake jiki da shi sosai, dan har
yanzu ina kan bakana kar abu ta kwaɓe gaba ya ce na cutar da zuciyarsa ko kuma na yaudaresa, akwai abu
guda da ke burgeni da Malam Abbo, sam-sam a makaranta baya nuna ma akwai wani alaƙa na daban
stakaninmu, Malami da ɗalibarsa kaman baya haka muke, kuma ba ya zuwa zance sai ranan Lahadi ko
kuma Alhamis, da yake ba mu zuwa makaranta ran Alhamis, sam-sam ba ya takura mini, tun da ba ni da
waya, ta nan ɓangaren ma ba ya takura mini.

Tun da na fara sauraran Malam Abbo, sai kuma wani shaƙuwan ta shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login