Showing 66001 words to 69000 words out of 111817 words

Chapter 23 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf

Advertisement

16 Aug 2025

4077

shaƙu da Bunayd ba, amma yanzu
ƙaunar yaronta take yi, bata jin za ta iya faɗan wani mugun abu a kansa balle ya shiga wani hali tunda ta
haife sa komin yaya bakinta zai iya kamasa, sai dai idan mugun fata yake mata ba kishiya to zata nuna masa
ita ce mahaifiyarsa tana da iko da shi kuma.

Wuni suka yi cikin nishaɗi, Papi da Affa sai ƙara tattaunawa suka yi akan abinda ya kamata.

Sai da su General suka yi sati guda, sannan suka tattara suka koma Lagos, Bunayd ma ya bi su dan sun
gama maganan komai na bikin da Abeed, yanda komai zai tafi, dan a ranan da suka koma Lagos a ranan
Abeed ma ya wuce Adamawa.

Papi sai sati na sama zai yi tafiya nasa, amma kuma busy ya ƙi barinsa ya je ya kalli masoyiyarsa kamun ya
tafi tunda har wata biyu zai yi, sai waya kawai suka yi ya tura mata duk abinda ya kamata, kaman yanda ya
faɗa dai bai ƙara mata maganan aure ba, sai dai ya mata faɗan ta kula.

Majeeder ta bi su Affa General sun koma tare, Hajiya Sa'adatu kaman za ta haɗiye rai dan masifa, Alhaji
kuwa ya ce tunda yarinyar sa ce shi ya ga daman ta bi su, idan abun bai mata ba ta yi zuciya ta haiho wata
yarinyar ko wani yaron, Hajiya cikin masifa ta ce ita ta gama haihuwa da shi idan ya ga dama ya sayar da
yaran.
Papi ko sati guda bai yi ba saboda ɓaci ran da Hajiya ke cusa masa, haka ya tattara ya tafi tafiyansa abunsa,
Suhail ma bai kai sati ba ya koma Turkish ɗin sa, Nabeel kuwa Bunayd ya masa komai da ya kamata a Spain
ya ci-gaba da karatunsa a can, shi ma yana zaune a gidan Bunayd.

Rayuwa na tafiya ta ko wani ɓangare lafiya sai godiya ga Allah inda yanzu haka auren Abeed saura sati
guda, kuma CAS Bunayd ya shirya tare da su Suhaila, Ramla, Majeeder da Nabeela duka ya taho da su, sun
ce su ma za su zo da bikin.

Suna isowa yayi magana da Abeed ya kai su Majeeder gidan su Nusaiba Amarya, ta tarbe su hannu
bibbiyu, duk anko da ake da komai Bunayd ya yi musu, ana fara shagalin biki kuwa kullum da kansa yake
kai su wajan event ɗin da za'a yi kuma ya basu kuɗi a hannunsa, duk abinda ya ke yana zuwa da sauran
abokanansu da suke gari, idan ka ga shungullan da Bunayd ke yi za ka ɗauka shi ne Angon, sosai Bunayd
yake da kirki kuma ba shi da girman kai.

Yau take Thursday wanda a washe-gari juma'a za'a ɗaura aure, kuma sai washe-gari Ango zai zo, yana can
Adamawa a wani daji gaba da Michika kamun a isa Mubi, shi da abokanan aikinsa suna fama da ƴan
ta'adda masu addabar mutane sai dai mu ce Allah ya ɗaura su a kan su.

Ɓangaren Amare yau walima ake yi, Bunayd ya kai su Majeeder da suka sha Arabian gown's suka shuka yi
kyau Masha Allah, yana sauƙe su ya miƙa musu kuɗi ya ce, "Ku ji wa'azi mai kyau kuma ku yi aiki da shi."

Suhaila ce ta yi dariya ta ce, "yaya dama ai indai ka ji wa'azi dole ka yi aiki da shi, musamman idan ka zo
dan wa'azin ne."

Bunayd girgiza kai yayi ya ce, "wa ya faɗa Miki? Ai da yawa mutane suna jin wa'azi ne kawai ba aiki suke da
shi ba, a cikin malamai wasu masu yin ma ba wai suna yin abinda suke faɗan ba ne, shiyasa aka ce ka yi
abinda Malam ya ce ba abinda ya yi ba, dan haka ku ɗauka kuma ku yi aiki da shi."

Nabeela murmushi tayi ta ce, "Inshà Allah yaya za mu ɗauka mu yi aiki da shi."

"Good! Nabeela my love" Bunayd ya faɗa yana murmushi.

Majeeder ta ce, "yaya ka zo da wuri ka kai mu yawo."

Bunayd ya ce, "ku mastalanku kenan ba'a haɗa hanya da ku, yara sai son yawa, to driver ne ma zai zo ya
ɗauke ku ba ni ba" yana faɗa ya yiwa motansa key ya tafi.

Duk tura baki suka yi suka shige, sannan suka samu waje suka zauna, wa'azi ne ake mai kyau mai kuma
rasta jiki, wanda ba iya Amarya zai amfana ba, duk wata mace da ta ji ta yi aiki da shi to zai amfane ta
duniya da lahira, dan misali ake mana da rayuwan da Nana Faɗima AS ta yi a gidan mijinta sayyadina Ali
AS, dan haka mata wannan kyakkyawan tunatarwa ce gare mu, ki duba Allahn da ya ce a zauna a gidan miji
a yi haƙuri, ki kuma aro halayyan Nana faɗima AS za ki ji daɗin zaman gidan miji, kuma za ki yi alfahari da
hakan duniya da lahira, Allah ya sa mu dace, ya ƙara mana zaman lafiya a dakunanmu, ƙannenmu da
yayunmu, da yaranmu, da iyayenmu marassa aure duk Allah ya haɗa su da na gari ya kuma ba su haƙurin
zama.

Duk kwanakin nan da Bunayd yayi a gidansa na Kano yake kwana, iyakacinsa da gidan Papi idan ya zo
ɗaukan ƙannensa ko ya dawo da su, Hajiya Sa'adatu ita haka ya mata ko babu komai tunda dai ya baro su
General, bata san biki ne ma ya kawo sa ba, shi kuwa idan ya zo zai gaisheta zai mata ladabin da ya kamata,
kawai dai baya sakewa da ita ne, dan Bunayd na da ilimi kuma yana aiki da iliminsa, ya san ita mahaifiya ce
kuma yasan haƙƙinta da ke kansa, sannan ya san hannunka ba zai ruɓe ka yankesa ka yasar ba, uwa ta
wuce wasa.

Bayan Bunayd ya baro wajan su Majeeder, yana cikin driving ƙira ya shigo wayansa, ganin layin Abeed sai
ya ɗauka yana murmushi ya ce, "Palace is loading, Ango mai jiran gado, Dragon za'a sha aiki" ya ƙarishe
yana dariya.

A maimakon ya ji muryan Abeed sai ya ji muryan wani daban, hankali a tashe yake magana ya ce, "Bunayd
an samu mastala fa."

Bunayd ya ce, "Me ya faru? Ina shi Captain Abeed ɗin?"

Wanda ke maganan ya ce, "Wallahi a tarzomansu da ƴan ta'adda shi ne aka samu akasi, duk da mun gama
da su amma dai an harbesa, mummunan rauni ya samu kuma daman ya ce, duk abinda ya faru kai kaɗai
za'a kira kar a faɗawa iyayensa."

Hankali a tashe Bunayd ya ja wani wawan birki ya ce, "Yanzu kuna ina?"

"Muna babban asibitin cikin Mubi."

Bunayd bai jira ƙara jin komai ba ya kashe wayansa ya juya sai airport, hankali tashe yayi duk abinda ya
kamata, jirginsu ya ɗaga sai Adamawa, jirginsu na sauƙa daman ya riga ya gama magana da sauran
abokanansa da ke nan a air force base na cikin jimeta, mota aka turo mata da drivern da zai kai sa har cikin
Mubi, ba ɓata lokaci suka kama hanya, suna tafiya amma Bunayd gani yake basa isa da wuri, tun da yake

bai taɓa wuce cikin Adamawa ba, ba local government da ya sani, bai san nisan Mubi ya kai haka ba, ji yake
kaman ya fire ya gansa a gaban abokinsa.



Yau Lahadi Banafsha ta warke daga cutan period ta yi rass abinta ta gama, wanka ta sha sharr da ita suna
zaune da Mami suna hira kaman ba komai, sallama suka jiyo, wanda daga ji Banafsha ta gane muryan waye
ne, zuciyanta ne ya stinke sai kuma ta saki murmushi lokaci guda, Mami dubanta tayi ta ce, "amsa
sallaman mana, ki je ki duba waye ne."
Miƙewa nayi na shige ɗakina na sako hijabi sannan na fito na wuce, kaman yanda na zatan kuwa shi ne,
Malam Abbo ne, murmushi nayi tare da yin ƙasa da kai na tare da masa sannu da zuwa, amsawa yayi, na
ce masa ina zuwa, sai na koma cikin gida na faɗawa Mamina Malam Abbo ne, murmushi tayi ta girgiza kai
kawai ta ce, "Sai ki ce ya shigo ko."
Komawa nayi na masa iso, muka shigo palourn lokacin Mamina ta riga da ta shige ɗakinta.

Malam Abbo zama yayi ni kuma na wuce na kawo masa ruwa da abinci duka, yau ma kaman ranan
murmushi yayi ya ce, "Lallai ni ɗan gata ne kullum har da abinci, ki ce idan zan zo zance za daina cika cikina
da tuwon Ummina."

Murmushi nayi tare da yin ƙasa da kai na ban ce komai ba.

Ƙara gaisawa muka yi bayan ya sha ruwa, sannan na ce, "Malam a yi haƙuri wannan satin ban samu zuwa
ba, na faɗawa Umaima ta faɗa banji daɗi ba ne."

Murmushi Malam Abbo yayi ya ce, "To ai ni yanzu ba abinda ya shafi makaranta bane ya kawo ni, batu ne
akan rayuwata, farincikinka, cikar burina, muradina, maganar soyayyata da ƙauna ce ta kawo ni Sayyadata
Roohi ta."

Wani kunya ne ya rufe Banafsha da ya sanyata kulle fiskanta da tafin hannunta, wani irin soyayyan Malam
Abbo ne ya stirga mata duk wani sassa na jikinta lokaci guda ba zato ba tsammani, sai dai kaman daga
sama take jin maganganun Maminta na dawo mata, sai kuma wani damuwa ya maye gurbin farincikin,
wanda har Malam Abbo sai da yayi mamakin ganin yanayinta ya sauya sosai, ba tare da ya ankara ba ya
kuma jin tana cewa, "Malam Abbo ka yi haƙuri, abinda na faɗa maka da farko shi ne har yanzu, ba zan iya
aure da mugun tabon da ke tare da ni ba" ta na ƙarishe maganan kaman zan yi kuka, saboda ni da kai na
ina jin ciwon abinda nake faɗa.

Malam Abbo murmushi yayi ya ce, "Ni ma kuma ina kan baka na, ina ƙaunarki har gobe, duk wannan amsa
naki ban gamsu da su ba Roohi, amma zan yi abinda ya kamata, sai dai dan Allah ko ne na yi kada ki ga
laifina soyayyanki ne ya ja."

Shiru nayi ban ce komai ba, saboda kokawa nake da zuciyata na samu da rashi da nake gani a filin Allah.

Malam Abbo ba tare da damuwan komai ba ya ce, "kwana biyu Umaima ma bata ke makarantan ba, fatan
dai lafiya?"

Cikin damuwa na ɗago kai na, amma muna haɗa ido sai naji wani iri, tuni nayi ƙasa da kai na na ce, "Amma
bansan me ya sameta ba, bansan ko wani abun ya faru ba, dan nima yau ne naji daɗin jikin nawa, sai dai in
Allah ya yarda gobe da safe zan shiga na dubata kamun mu wuce makaranta."

Jinjina kai Malam Abbo yayi ya ce, "Hakan ma yayi Sayyadata, Allah ya yarda ya kuma nuna mana da rai da
lafiya, sannan kuma Allah nuna mana bikinmu, ranar da Malama Faɗima za ta zama mallakin Aliyu bawan
Allah."

Shiru na yi ban kuma cewa komai ba, Malam Abbo dai sai hiransa yake mini na soyayya, duk da ina jin daɗi
da kuma sanyi a rai na amma na kasa nuna hakan dan bana son na yaudari malam Abbo ko kaɗan, sai da
lokaci ya ja idan yayi magana sai dai na ce Uhmn! Ko uhun!, Ganin dare na ƙoƙarin yi suka ya dube ni yana
sakar mini murmushi wanda yake daga zuciyansa ya ce, "Nikam zan tafi Sayyadata sai na ƙara zuwa kuma."
Ba tare da na kallesa ba na miƙe na ce, "Bari na ƙira Mamina ko gaisawa ba ku yi ba."

Murmushi Malam Abbo yayi ya ce, "Umma ta zama surkuwata kunyarta nake ji, ki bari zan zo daga baya na
gaisheta daban, yanzu kunya nake ji dan yau wajanki na zo."

Abinda Malam Abbo ya faɗa dariya ya bani, dan haka murmusawa nayi, kawai muka yi sallama na rakasa
har ƙofan gida, kallona yayi ya ce, "Ina matukar ƙaunarki Sayyadata."

Kallon juna muka yi na ƴan second's, inajin kaman na faɗa abinda ke rai na, amma ba dama, ganin kuka na
neman zuwa mini sai na juya da sauri na kulle ƙofa na koma ciki.

Malam Abbo murmushi yayi dan shi ya riga ya sanya a ransa indai Faɗima rabonsa ce to zai sameta, yasan
mai zai yi, in Allah ya yarda zai mallaketa.

Ni kuma ina share hawayena na shige ciki, kusan karo muka yi da Mamina, girgiza kai tayi.

Mamina ta ce, "lafiya kuwa? Me ya faru? Me ya sameki? Yanzu nake cewa bari na bi bayanki kin zauna a
waje me ya faru?"

Share hawayena nayi na seta kai na, cikin dakewa na ce, "Ba komai Mami."

Ganin dare yayi duk yin Mami, sai ta ƙyale kawai ta wuce ɗakinta na wuce nawa, ina addu'an Allah ya sa
lafiya an ce Umaima ita ma kwana biyu ba ta je makaranta ba, da tunanin haka na kwana a rai na.



Masu Sharhi ina matuƙar Godiya Uwar batoorl taku.



# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735

# ������
# � &
# ���



'YAR KARUWA

Officially



Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)



SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)


TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma ɗaukacin member's namu.



PAGE NAKI NE

Surayyatou nah



مهللا ىلص و ملس ىلع ديس ان هللوسر SAW



BUNAYD: is a name use for baby boy's, that mean's sᴛʀᴏɴɢ, sᴛᴏʀᴍʏ ᴀɴᴅ ᴘᴏᴡᴇʀғᴜʟ, and also is a name
that identify a specific ethnic, like halimatu-sa'adiya, the real name is halima, sa'adiya is her ethnic name.
Bunayd or Bunaid, in other face mean is ethnic name which located in Pakistan, in Muslim's society, the
name is usually use as nick name for those with name Muhammad.
The name origin is Pakistan.



️ 66 _ 70


Washe-gari da safe na shirya tafiya College da wuri, bayan na gaishe da Mamina ta amsa, sai na ce, "Mami
zan bi gidan su Umaima kamun na wuce, Malam Abbo ya ce mini ita ma kwana biyu ba ta je makaranta ba,
bansan ko me ya sameta ba."

Mami ta ce, "To a dawo lafiya, ki gaishe su, sannan ki kula sosai ko."

Ɗaga kai na nayi alaman na ji, sannan na mata sai na dawo na fice, ina ƙoƙarin shiga gidan su Umaima sai
ga ta ita ma ta fito da shirin zuwa College, murmushi muka sakarwa juna, na ce, "Umaimatyna."

Murmushi Umaima ta mini wanda hankalina bai kwanta da shi ba, ina tunanin ma na ƙarfin hali ne, bata
ce mini komai ba kawai ta riƙe hannuna muka yi gaba, ni bin ta nake kaman mara lafiya dan jikina yayi
sanyi, bansan me yasa tayi haka ba, amma dai na yi shiru, muka nemi mashine muka tafi College.

Mun wuni a makaranta muna ta lecture's, amma kwata-kwata na kasa ganewa Umaima, gaba ɗaya bata
son yin magana sosai, ƴar rigiman da muke yi da stokanan juna duk yau babu, sai dai murmushi kawai take
mini idan na yi magana, kasa jurewa nayi da hakan, ana tashinmu muna tafiya kan mu samu mashine na
ce, "Umaima me ya faru? Me na miki? Ko ba ki da lafiya ne?"
Mashine ta tare mana muka shiga, ƙara kallonta nayi na ce, "masoyiya me ke faruwa dan Allah?"

Umaima murmushi ta sakar mini ta ce, "Me ne kika damu kanki haka Banafshaty, lafiya fa ba komai."

Kallon Umaima kawai nake yi ba dan na yarda da abin da ta faɗa ba, numfasawa nayi na ce, "To me ya
hanaki zuwa makarantan tahfiz kwana biyu?"

Nan ma shiru Umaima tayi bata ce komai ba har muka isa gida, mashine na ajiye mu ta kalleni da
murmushin ƙarfin halin da take mini tun safe ta ce, "Banafshaty ki gaisar mini da Mami", ta faɗa tare da
yin gaba ta shige gidansu.

Haka Umaima ta tafi ta barni a staye a gantale ta shige gidansu, sai da na gaji da tsayuwa sannan na
numfasa na juya cikin damuwa na shige namu gidan.

Mamina na samu zaune a palourn tana waya, jakana na ajiye a kan kujera na shige jikin Mamina na lafe, ba
tare da na ankare na bacci ya fara yin gaba da ni, sai da Mamina ta gama wayan da take yi sannan ta shafa
kai na ta ce, "Fatu kulen Maminta, shugabar masu son jiki tashi kada ki karya ni."

Ni kuwa tuni na fara bacci ban ma ji me Mamina ke faɗa ba.

Mami sunkuyawa tayi ta kalli fiskana, ganin bacci na fara sai ta murmusa ta girgiza kai kawai, a hankali ta
bubbuga bayana ta ce, "tashi kije ki cire kayan makarantan, idan kin wasta ruwa sai ki kwanta ki yi baccin,
dan da alama yau kin ajiye wanda zai je miki tahfiz ɗin."

Cunna baki nayi, cikin shwagaɓa na ce, "Mami jikinki ne daɗin kwanciya shiyasa na ji bacci."

Murmushi Mami tayi ta ɗaga ni, amma na koma na lafe na ce, "Mami yau bansan me ya samu Umaima ba,
magana ma da ƙyar take mini."

"Ba sai ki tambayeta ko wani abun ya faru ba Banafsha" faɗin Mami tana ɗaga ni.

Zama nayi sannan na ce, "Mami wallahi na tambayeta, da farko ta yi shiru, daga baya ta ce ba komai."

"To wataƙila ko bata jin daɗine, ko kuma wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login