Showing 33001 words to 36000 words out of 111817 words
Chapter 12 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf
kaɗai a gida."
Haka ya ƙara marairaicewa kaman ɗan goye ya ce, "General zan dawo da gaske fa", magiya Bunayd ya
dinga yi da gaske, sannan General ya amince akan idan ya gama ya dawo, sosai General yake ƙaunan
Bunayd, shi ya sakalta shi, ya shagwaɓa shi.
General ya ce, "To kai ka ce small boy ne kai, yaya kuma ya ce aure za kayi, dan kada ka shuka rashin ji, dan
nasan dai ba lalacewa za ka yi ba, sai dai shuka rashin ji ɗin."
Murmushi CAS Bunayd yayi ya ce, "General ka ƙyale Sir, ni har yanzu gaskiya banga wacce ta mini ba."
General ya ce, "Amma dai kasan halin yaya ba, staff zai aura maka wata, gwanda kawai ka nemi nistasttiya
tun wuri ku dai-daita, ni bana son a maka abinda baka so."
CAS Bunayd ɓata fiska yayi ya ce, "General to gaskiya da ace Sir yasan irin macen da nake so, ai ba mastala
ya zaɓa mini, amma ga shi kai ma da muke tare kana cewa nistasttiya balle kuma Sir, ai sai ya ce shi kuma
kamila mai kwana da hijabi tana guma Palace zai nema mini, gaskiya a barni na nemi irin wacce nake so."
General cikin soyayya da lallashi ya ce, "To wacce irin mace kake so my Man? Ka ce ba nistasttiya ba, kuma
ba kamila ba, Ustaziya kake so kenan?"
CAS Bunayd ji yake kaman ya ƙwala ihu dan taƙaici, kaman zai yi kuka ya ce, "General ni ko ɗaya ba su nake
so ba."
"To wai wacce irin mace kake so?"
"Gaskiya General ni bana son mata masu saka hijabin nan, ƴan ƙauye ne, gaskiya ni banason nistasttiyan
mace."
Da mamaki General da Hajiya Huraira (Momsee), suke kallon Bunayd, Momsee ce ta ce, "To Bunayd wace
irin mace kake so? Kowa na fatan samun nistasttiyan mace amma ka ce ba haka ba."
"Momsee ni nafison mace wacce ta waye tasan rayuwa, tasan duniya, amma nistatststun nan basu san kan
rayuwa ba, basa bada Palace yanda ya kamata."
General ya ce, "shi kuma Palace ɗin menene? Ai mace nistasttiya ita ce jin daɗin duniya."
"General ni nafison wacce take nan tantiriya-tantiriya, ko gantalalliya-gantalalliya haka nan, ko
stagera-tsagera ko kuma wayayyiya wacce dai ba kamila ba, wacce dai tasan rayuwa, nistasttiyan nan cutan
ta zan yi, kaga ni ba nistastte bane, kuma ni Soja ne, nistasttiya ai sai malamin islamiyya, ustazu."
Momsee dariya kawai ta yi, shi kuwa General sake baki yayi ganin ikon Allah, ganin da gaske CAS Bunayd ya
dage shi iya gaskiyansa yake faɗa, abinda yake so yake faɗa, ikon Allah, da mamaki ya ce, "ubanwa ya ce
maka kai ba nistastte bane?"
Bunayd ya ce, "Abeed ne ya faɗa General."
Girgiza kai kawai General yayi, tunda yasan Abeed kuma ya san waye Bunayd ɗin da rashin jin sa, kawai
soyayyan da yake masa ya saka yake lallaɓasa, rarrashinsa ya dinga yi amma ya dage firr shi baya son
nistasttiya, in kuma Alhaji zai sama masa wacce yake so, to ya basa zaɓi, shi normal ne kawai, ai
damuwansu yayi aure ne, to zai yi kawai a samu kalar wacce yake so, General dai kama haɓa yayi yana
ganin ikon Allah, amma tunda dai ya amince zai yi auren da sauƙi, kuma daman hakan na ɗaya daga cikin
abinda yasa yake son sa sosai, Bunayd baya musu da su ko kaɗan, kuma yana jin maganansu yana musu
biyayya, halayyansa masu kyau ne, dan ya fi ƙannensa har da matan jin magana, shi dai bar shi da abin
raha, ita kuwa Momsee ba abinda take yi sai dariya, ganin Bunayd ya girma da gaske amma kuma ƙuruciya
na damunsa, dan idan ba ƙuruciya ba mutun ya dage baya son kamilar mace saliha, ya ce sai gantalalliya.
General ajiyan zuciya ya sauƙe ya ce, "To daman ma babban abinda ya sa na ƙira ka, ba akan ka dawo
bane, dan nasan muddin baka yi niyan dawowa ba tuni ka kanainaye ni da magana na ƙyaleka, ga shi kuma
na haƙura dan dole, Man kai kam ai mace bata isa ta maka daɗin baki ba, Allah shirya mana kai."
CAS Bunayd na murmushi ya ce, "Ameen Ya Rabbi my General."
General sai da ya dara kawai ya girgiza kai ya ce, "akan maganan ƙannenka ne, da farko Suhail na kai sa
makarantar sojoji shi ma ya gado ni, amma yaron nan ya gudo haka na kylesa, aka tura sa Turkish ɗin da
yake so, ya karanto duk shirmen da yaga dama, yanzu kuma Nabeel ya ɗau ƙafansa, dan tsabar yaran nan
duk sun mai da ni abin wasansu wai shi ɗin ma yaro da shi yana cewa ba zai je ba, baya so, bansan mene
mastalansu da aikin Soja ba, yara duk basa kishin kansu balle ƙasar su, ba za su tsaya su kare ƙasar su
yanda muke fafatawa ba."
Bunayd murmushi kawai yayi ya ce, "General wallahi ba ko kaffara, Suhail ne ya zuga Nabeel wai wahala
ake, amma ba komai zan yi wa Nabeel ɗin magana."
"Good boy! Allah muku albarka duka my Man, idan kuma yaƙi ji ka kai sa guard room ba ruwana" faɗin
General yana murmushi.
CAS Bunayd ya ce, "Ba za'a je ga guard room ba ma General."
Dariya General yayi ya ce, "Daman nasan haka za ka ce ai, tunda ka fi kowa son ƙanne a duniya, duk kai ma
ka sakalta yaran nan, amma dai tunda suna jin magananka da sauƙi, ni na rasa ya ake suke storonka ma
yanda kake buɗe musu haƙorankan nan."
Murmushi kawai CAS Bunayd yayi bai ce komai ba, ya shafa kistonsa yana lumshe idanuwansa kaman mai
jin bacci.
Momsee ganin Bunayd na ƙoƙarin yin bacci sai tayi murmushi ta ce, "To muje a ci abinci dama kai muke
jira."
Duk miƙewa suka yi suka sauƙo dinning na ƙasa, kowa ya samu waje ya zauna, yaran mata ne guda uku
suka fito, kyawawa da su masu kama da General, kuma daman Bunayd da General yake kama shi ma, ɗaya
a cikinsu ba za ta haura shekara sha tara ba 19 mai suna Ramla, sai ɗaya ba za ta haura 17 ba ita kuma
sunanta Suhaila, sai kuma autar cikinsu da ba za ta haura 14 ba mai suna Nabeela, duk a niste suka gaishe
da Bunayd ya amsa fiskan nan a sake yana musu murmushi, General ne yayi magana ya ce, "table
manners, kowa ya ci abinci ayi shiru."
Duk stitt suka yi baka jin ƙaran komai, sai na spoon da plate da suke karo, yayin da CAS Bunayd kuwa rabin
hankalinsa ke kan wayansa yana sakin murmushi.
⭐⭐
Banafsha suna dawowa daga wajan musabaƙa aka sallami kowa ya koma gida bayan an ƙara ƙarfafa musu
guiwa su dage, tunda sun ga yacce rashin ƙwarin guiwa ke sa wasu faɗuwa, babu confidence.
Malam Abbo ne ya biyo su Banafsha yana taka musu, yana ƙara basu shawarwari yanda za su yi karatunsu
hankali kwance ba tare da yawan idanuwan jama'a a kansu ya dame su ba, ko ya hana su yin nasara, su
Umaima dai suna ta sauraronsa har ba su ankare ba suka fara hango gida, Malam Abbo ma na farga ba
ashe ya biyo su har gida, kuma tun daga nesa Umaima da Banafsha suka hangi Ya Danish a ƙofan gida
kuma ya kallesu.
Malam Abbo sallama ya musu zai juya, sai Banafsha ta langwaɓar da kai ta ce, "Malam ba ka faɗa mana
abinda ya hanaka zuwa ba, in rashin lafiya ne ai sai mu dage da addu'a, Allah bawa malaminmu lafiya."
Umaima duk ta sture ko sauraran su Banafsha bata yi, kuma ta kasa tafiya tabar Banafsha, ga shi Ya Danish
ya zuba musu na mujiya ko ƙiftawa ba ya yi, kuma fiskan nan a haɗe, kana gani kasan yau akwai bala'i.
Malam Abbo yana murmushi ya ce, "Na ɗan yi tafiya ne urgent zuwa Borno, afuwan ko Malama Faɗima."
Banafsha murmushi ta sakar masa mai rikitasa ta ce, "tunda Malam ya dawo lafiya Alhamdulillahi, sannu
da gajiyan hanya, gobe kada a mance mana tsarabanmu Malam", ita fa Banafsha duk saboda Ya Danish ya
ƙulu take yi.
Malam Abbo da ya susuce, murmushi kawai yake sakarwa Banafsha kaman ba lafiya ba, har ya buɗe baki
dan faɗa mata akwai maganan da yake son faɗa mata, amma sai ya fasa kawai ya dake, ya musu sallama ya
juya, zuciyansa cike da wani irin ƙaunar ɗalibarsa Faɗima.
Banafsha da gangan ta staya tana yiwa Malam Abbo bye-bye, duk da ya riga ya juya, amma yi take dan Ya
Danish, har da ɗaga hannu sama ta yi alaman love, Umaima da ta gaji da haukan Banafsha sai wucewa tayi
ta ce, "Sai kin iso, tunda ba ki san ruwan da ke gaban mu yana jiranmu ba, yau nasan nidai na gama yawo
na kaɗe, Ya Danish zai targaɗa ni.
Banafsha na murmushi ta juyo, daga inda take ta harari Ya Danish sannan ta bi Umaima da sauri tana faɗin,
"jirani Umaimaty, zan je wajan Ummu."
# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735
#
# &
#
'YAR KARUWA
Officially
Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)
SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)
TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma ɗaukacin member's namu.
PAGE NAKI NE
Hareeyh (Uwar batoorl)
Masu Sharhi sun ƙare, dole na bawa kai ka page, nima na ɗana ladan typing.
مهللا ىلص و ملس ىلع ديس ان هللوسر SAW
️ 41 _ 45
Umaima tuni tayi nisa da tafiya ko jin Banafsha bata yi.
Sai da suka iso dai-dai wajan su Ya Danish sannan Banafsha ta ce, "Umaima na fasa binki."
Ai da sauri Umaima ta ƙankamo hijabin Banafsha ta ce, "wallahi kin yi kaɗan Masoyiya, tunda kika ja mana
ruwa dole ruwan nan ya dake mu tare, ba inda za ki je."
Banafsha na danne dariyanta, suka gaishe da su ya Farooq, Umaima ce kawai ta gaishe da Ya Danish,
amma Banafsha ko kallon inda yake bata yi ba, nunawa tayi ma kaman bata san da halittansa a wajan ba,
shi kuwa Danish aikon masifan da ya ƙulla ko gaisuwan Umaima bai amsa ba, buri yake kawai Banafsha ta
shiga gidansu, yau sai ya seta mata hankali ya gyara mata wajen zama, ga shi Abbaa ba ya gida balle ya
ƙwace ta, dan cike yake da haushin abinda ta masa ranan, kuma tsaff ya shirya muguntan da zai mata, ta
yacce ko da kuɗi aka haɗa ta akan ta ƙara faɗa masa magana ba za ta iya ba.
Umaima haka ta maƙalƙale Banafsha sai da suka shiga gidan tare, suna shigewa Danish ya mike stamm! Ya
rufa musu baya yana sakin murmushin mugunta, cikin dabara ya faɗawa su Farooq bari ya ɗauko abu a
ɗakinsa ya dawo.
Yana shiga ya samu har sun shige cikin gida, ƙwafa yayi tare da sakin murmushi ya wuce part nasu na maza
da yake ta bakin ƙofa yana jiran fitowanta.
Umaima suna shiga cikin gidan ta saki hamadala tare da cewa, "To nidai na stira, saura ke mai fita ki koma
gida, Allah shiga tsakaninki da masifan da ke bakin ƙofa yana jiran fitowanki."
Banafsha Murmushi kawai ta sakar wa Umaima, ta nufi ɗakin Ummu, amma a bakin ƙofan suka kusa yin
karo da Nana ta ce, "Banafshaty, ai Ummu ta bi Abbaa sun je asibiti dubiya tun ɗaxu."
Umaima ma fitowa tayi a ɗakinsu ta ce, "sorry masoyiya mancewa nayi ban faɗa miki Ummu bata nan ba,
duk storon Ya Danish ne ya cika ni, matar abokin Abbaa ce babu lafiya، shi ne suka je gaisheta a asibiti."
Harara na aikawa Umaima dan taban haushi, storonsa sai ka ce ya zama wani mala'ikan mutuwa, ba tare
da na saurareta ba na juya zan fice, Umma da fitowanta ɗaki kenan, ƙwafa tayi ta ce, "Idan na kuma ƙara
ganinki a cikin gidannan ni nasan abinda zan miki, yarinya gaba-ɗaya bata da zuciya, wato har gida kike bin
kabeeru ko? To kuwa zan baki mamaki idan kika ce za ki ɗaura shegun fistararrun idanuwanki akan yarana,
ki ƙare can ke da karuwar uwarki, kuma idan ma shanyewa yarinyata zuciya kika yi take binki a baya kaman
bindi, to ki sani ina dai-dai da maitanki, idan baki ƙyale mini yara kin fita harkansu ba to ba shakka zan
saɓa miki."
Umaima ta buɗe baki za tayi magana sai Umma ta kwashe ta da mari, saurin juyowa nayi rai na a ɓace
saboda maganganun Umma, idanuwana akan Umaima na mata alama da ido kada ta ce komai, matar
babban yaya ce ta aiko mini da harata tare da yin staki ta ce, "Wallahi idan baki fita harkan mijina ba sai na
miki illa, shegiya, ƴar iska, ƴar karuwa..."
Kamun ta rufe baki tuni na dira gabanta na kwasheta da maruka biyu ba ruwana da cikin jikinta, amma
kamun na ɗago tuni Umma ta kwashe ni da marin nima ji kawai kake tassss! tasss!, cikin masifa Umma ta
ce, "Dan uwarki har kin isa ki taɓa mini surka yar gidan mutunci? Kina ƴar karuwa, ƴar shege"
Ba tare da na tankawa Umma ba, na kuma ɗaga hannuna na kwashe matar yaya babba da maruka,
zuciyana na tafasa na ce, "ki bari manyan da babu yacce na iya da su suyi, dan su zan iya ƙyale su, idan ma
basu riƙe girmansu ba to ni san basu mastayinsu, amma ke kika ce za ki shiga stabgata zan iya fige miki
gashin mugun waje, ni ɗin nan ban da kirki ban da mutunci, kibar ganin wasu nayi ina shiru ki ɗauka ke ma
za ki ci banza, wallahi kika masta a lamarina sai na saka zuciyanki ta buga, ƴar iskan kai na ce ni ɗin nan,
mijinki da ya mini to ko kallonsa ba za kiyi ba balle ya aure ki."
Umma kuwa jin abinda na faɗa, a fusace ta iyo kai na tana masifa, amma sai Umaima ta tare ta tana kuka
tana cewa, "menene haka Umma? Dan Allah ki bari, da ƴar cikinki kike haka, wallahi idan Banafsha ta rama
marin da kika mata ba ruwana ba zan ji zafi ba ke kika nema...." Bata rufe baki ba amma ta hankaɗata gefe
ta iyo kai na, matar yaya babba kuwa da taji mari tuni ta zauna daɓas da cikinta a ƙasa ta kasa yin magana,
ga haushina ga kuma shakka na.
Wani irin kallo na yiwa Umma tun kamun ta iso gareni, sannan na juya, sai ji na nayi na ci karo da mutum,
idanuwana a rufe ban damu da wa nayi karo ba na ci gaba da tafiya, sai ji nayi an riƙe hannuna anyi baya
da ni, a hasale na ɗago jajayen idanuwana cike da masifa, amma sai tozali nayi da yaya babba, rai na ƙara
ɓaci yayi na ƙwace hannuna na juya, bi na yayi yana cewa, "kiyi haƙuri Banafsha, kada ki tafi a haka.."
Umma cikin ɓacin rai ta ce, "kabeeru idan ka kuma taku ɗaya sai na stine maka, dan Ubanka me haɗin ka
da ita? daman gaskiya Hindatu ke faɗa mini kenan? Tunda ga shi har haƙuri kake bata, bayan rashin kunyar
da ta mini, ta kuma mari matarka da juna biyu a jikinta."
Babban yaya stayuwa yayi rai a ɓace bai cewa Umma komai ba, dan shi Banafsha ta masa dai-dai ko me ta
musu su suka nema da kuɗinsu, kwafa yayi yana bin matar sa da mugun kallo, domin kusan duk abinda ya
faru akan idonsa ya faru, kuma yasan laifinta ne, daman tun ranan ya fara ganin take-takenta, Umma ma
harara ta aika masa da shi ta ce, "idan ka kuma yiwa yarinyar nan magana sai nayi mugun ɓata maka rai
wallahi."
Umaima da ke yashe a gefe can ta buge hannunta a jikin kujera har hannunta ya ɗan kumbura, kuka ta
sanya kawai, cikin gaggawa yaya babba yayi wajanta yana duba hannun nata, tausayinta ne ya rufesa ganin
har taji ciwo, dan sosai suke son Umaima yayyun nata.
Ni kuwa rai na a ɓace na fito bana ko kallon hanya haka nake tafiya kaman zan tashi sama, ba zato ba
tsammani naji anyi sama da ni, saboda ɓacin rai da nake ciki ko ƙoƙarin buɗe baki banyi ba balle ihu, sai
dai zillewa da nake ƙoƙarin yi dan bansan wa ya ɗaga ni ba, ganin da nayi an shiga sashin mazan da ni, nan
na tabbatar da mai wannan aikin, muna shiga ciki aka dire ni a ƙasa har sai da na ƙafata ta lanƙwashe ta
mini zafi.
Miƙawa nayi naja staki kawai na nufi ƙofan fita, dan ba sai na kalli waye bane, saboda nasan wa zai iya mini
wannan aikin marassa hankalin, hijabina ya rike tare da jawo ni baya ya hankaɗa ni kan kujeran zaman
mutun uku da ke cikin palourn, faɗawa nayi kai na buge bayana kuma, runste ido nayi tare da sakin ɗan
marayan ƙara, sai lokacin na ɗago idanuwana na sauƙe su a kan sa, wani malalacin ɗan iskan kallo na aika
masa da shi sannan na ce, "Wallahi ka fita a harkata idan ba haka ba zan iya kashe ka