Showing 24001 words to 27000 words out of 111817 words

Chapter 9 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf

Advertisement

16 Aug 2025

4029


مهللا ىلص و ملس ىلع ديس ان هللوسر SAW



️ 31 _ 35


Washe-gari Abbaa da kansa ya saka Nana ta kawo wa Umaima uniform nata gidanmu, Umma sai cin rai
take yi tana ta fushi akan Umaima ta kwana a gidanmu, amma Abbaa ko a jikinsa, Umma haushi kaman ya
kasheta ga shi Ya Danish ba ya gida, kuma babban yaya ba ruwansa, ya mus'ab da ke Camaroon ma ko
yana nan ba ruwansa, Ya Danish ne daman mai biye mata.
Mun yi wanka mun shirya tsaff muka fito, abin karyawanmu da komai muka samu Mami ta jera mana a kan
centre carpet na palourn, zama muka yi muka cika cikinmu yanda ya kamata, sannan muka yiwa Mami
sallama ta ba mu kuɗin mashine da na kashewa muka fice, cikin sa'a muka samu mashine kuwa da wuri, ya
ajiye mu a makaranta muka shige hall na exam.
Haka rayuwa ta dinga tafiya da daɗi da babu daɗi dai sai haƙuri, mastalolin rayuwa da ƙalubalen rayuwa
gare ni kullum ƙara gaba suke yi, saboda daga halayyan Mamina babu wanda ya canja kullum gaba-gaba
abun yake yi, ni a tunanina abinda wancan stohon ya mini zai sanya Mamina gyara kura-kuranta, amma ina
Mamina ci-gaba tayi da harkokinta, sam-sam Mamina bata jin ƙira dan ta riga da tayi nisa, kullum dai
magana guda ne, idan na ce ta dena wannan rayuwa, sai ta mammakeni kuma ta ce sana'a ce dan ta rufa
mana asiri,nidai wannan sana'a banga alfanunta ba, sai dai ban da yacce zan yi idan ba addu'a ba.

Maganan makaranta kuwa na dage sosai na mayar da hankali muna exam's namu hankali kwance, sannan
a tahfiz ma ina ƙoƙari yanda ya kamata, tsakanina da Malam Abbo kuwa yanzu ya zama kaman yayana dan
yana yawan mini faɗa da nasiha, sannan wani irin shaƙuwa na neman shigowa tsakaninmu wanda ni dai
ban farga da hakan ba sai da shaƙuwan tayi nisa.
Sati biyu muka kwashe muna exam's, sai ranan Alhamis muka kammala, daga ranan kuma muka yi wa
makaranta bye-bye, saboda musabaƙan namu week da za'a shiga ne.

Kaman ko wanne weekend, yau ma da yake Saturday da wuri muka je tahfiz muka dawo, tun daga
compound na gidanmu da na shigo na ga wata dalleliyar haɗɗaɗɗiyar Mota, lumshe ido nayi kawai ina
ambaton sunan Allah dan nasan ba zai wuce wani baƙon Mamina tayi ba, taɓe baki nayi ina faɗin ko wani
jarababben ne da sanyin safiya haka oho, sai da na seta zuciyata na shanye taƙaicin da zan tarar a ciki tun
ban shiga ba, sannan na tura ƙofan palourn na shiga da sallama, daga muryan wanda ya amsa mini
sallaman na sheda baƙon da Mami ta yi da sassafen.

Ƙarisa shiga palourn nayi kai na a sunkuye, durƙusawa nayi har ƙasa na ce, "Sannu da zuwa Alhaji."

Alhaji Mukhtar na washe baki ya ce, "Sannu ƴar albarka, sannunku da dawowa ko."

Amsawa na yi har yanzu ban ɗago ba balle mu haɗa ido, a haka na gaishe sa ya amsa, ya ce na je na huta
na karya zuwa anjuma zai ji karatun nawa, ba musu na amsa na miƙe na shige ɗakina, ina shiga na faɗa
kan gado tare da ɗaga hannayena sama na ce, "Ya Rabbi ga bayinka nan, ka fi ni sanin abinda suke ciki, ya
Rabbi ka shirya su ka gyara rayuwansu, ya Rabbi kada ka kama zuri'arsu da laifin da basu ji ba, ba su gani
ba, don kuwa ƙur'ani mai girma ya ce "az- zina dailun (zina bashi ce)", Allah ka shiryamu duka, ka shiga
stakaninmu da biyan bashin da ba mu ci ba", ina ƙarishe addu'ana na miƙe na cire uniform nawa, ina
ƙoƙarin fita sai Mamina ta shigo, murmushi ta sakar mini ta ce, "Sayyada Faɗimah a zo a karya, kada ulcer
ta kama mini 'yar fari, 'yar auta."

Murmushin nima na yiwa Mamina ban ce komai ba, na bi bayanta muka fice, abin karyawa na samu ta
zubo mana ni da ita, zama nayi amma na kasa cin abincin, kasancewan Alhaji Mukhtar na palourn duk da
dai hankalinsa na kan wayansa ne, Mamina ganin naƙi ci sai ta gusturo sinasir ɗin ta kai mini baki, ni kuma
na buɗe bakina a hankali ina karɓa, a haka ta dinga bani a baki har na ƙoshi, sannan ta cigaba da cin nata,
Alhaji Mukhtar da ke kallonmu sai yayi murmushi ya ce, "Lallai Ramlah kin shagwaɓa mini yarinya da yawa,
budurwa da ita kina mai da ta 'yar goye, yarinyar kirki kar ki biyewa Maminki fa, ke babba ce yanzu."

Ƙasa nayi da kai na ina murmushi, Mamina kuwa kallon soyaya ta yiwa Alhajin nata ta ce, "wannan
jaririyar ce babba? Banafsha ta wuce na sa zani n goya ta ne Alhaji? Ita ce fa 'yar fari kuma 'yar autan
Maminta."

Alhaji Mukhtar ma yana murmushin ya ce, "Amma dai wasa kike yi, Banafsha kar ki yarda fa ta ce miki
auta, ƙannenki na zuwa."

Mamina ta ce, "bayan ita ba kowa, daga ita ba ƙari, tal ɗin Maminta, shalele gudan stokar miya."

Alhaji idanuwansa akan wayansa ya ce, "yarinya ɗaya bata ishe mu ba, dole ki haifo mini wasu."

Kai na a ƙasa ina sauraran maganan su Mamina, jin abinda Alhaji ya ce sai nayi saurin ɗagowa dan na kalli
yanayin Mamina, a tunanina zan ga tayi murmushi dan ita ma tana son haifa mini ƙanne, amma sai
saɓanin hakan na gani, Mamina ta haɗe fiskanta ta yi kicin-kicin da shi, Alhaji Mukhtar kuwa hankalinsa
kwance yana lasta wayarsa sai ma murmushin da yake yi, dan yasan ya stokano masoyiyarsa Mami kuma
shi daman burinsa kenan, saboda wani shiri da yake yi na daban.

Mamina ganin ma yana murmushinsa ya manna mata hauka, sai ta miƙe ta wuce ɗakinta, ni kuma na
tattare kwanukan na mayar kitchen, har da wanda Alhaji ya ci abinci a ciki, na Juyo zan shige ɗaki sai Alhaji
ya dakatar da ni ya ce na zo, dawowa nayi na samu waje a nesa da shi na zauna a ƙasa, yana murmushi ya
ce, "Yarinyata Banafsha ya karatun? Fatan kun gama exam's lafiya?"
Kai na a ƙasa na ce, "Lafiya Alhamdulillahi, Alhaji."

"To Masha Allah! Allah sa result tayi kyau, Ya karatun musabaƙan kuma? Yaushe za ku yi?"

Kai na a ƙasa har yanzu na basa amsa da ranan da za mu yi, jinjina kai yayi ya ce, "To shikkenan, zuwa dare
Insha Allah za mu duba karatun, yanzu je ki huta, zuwa anjima za mu je anguwa Insha Allah."

Miƙewa nayi na masa a huta gajiya na shige ɗaki na, shi ma miƙewa yayi ya shige ɗaya ɗakin, ruwa ya
wasta ya kwanta tare da jawo wayansa yayi dialing wani number da sunan "My Son" ya ke ɓaro-ɓato, ba
jimawa aka ɗauka, Alhaji Mukhtar yana murmushi ya ce, "Chief of the air staff."

Wani haɗaɗɗen murya ne ya murmusa yanda sai da sound na murmushin ya fito, sannan cikin yanga ya
ce, " morning Sir."

Alhaji Mukhtar murmushi yayi tare da girgiza kai ya ce, "BUNAYD Allah ya shiryeka."

A hankali kaman mai raɗa ya ce, "Ameen Papi."

"Ya General?"

"General yana gidansa Sir."

Girgiza kai Alhaji ya kuma yi ya ce, "zan saɓa maka Bunayd, ina ubanka kana ce mini wani Sir."

Murmushi ya kuma yi ya ce, "sorry Sir!"

Alhaji ya ce, "Ubanka General ne Sir, yaushe za ka shigo Kano?"

"Soon zan shigo, kasan za'a yi bikin Abeed in next 3 months."

Alhaji ya ce, "Masha Allah! Ya fi masa ai yayi aurensa, kada ya biyewa duniya wai sai yayi iyayi, yanzu
mutuwa araha take, kar mutum yaga kullum yana sama kaman stunstu ya ɗauka shi ba mutuwan zai yi ba,
to azara'ilu ko a duniyar wata kake lokacinka na cika zai zare ranka, balle jirgi da nawa aka yi, idan akwai
mai ƙararren kwana a ciki ai hastari jirgi ke yi, to gwanda tun wuri kasan abinda ka adana kamun ka wuce
babu masu maka addu'a."

Bunayd a ɗaya ɓangaren murmushi yayi bai ce komai ba dan yasan da shi Papi ke yi, Alhaji ya kuma cewa,
"ko ka fito da mata ko kuma daga kai har ubanka General ku ji anbada ka sadaka, sadaka yalla zan ba da kai
a masallaci, in ana ƙiran macen sadaka ta Annabi, to kai za ka zama na Annabi, bari lokacin da na ɗiba
maka su cika."
"Byee Sir, my regards to Adamawa" yana gama faɗa kitt ya daste ƙiran.

Alhaji murmushi yayi tare da cewa, "Allah ya muku albarka" yana gama faɗa ya gyara kwanciyansa ba
jimawa bacci tayi gaba da shi.

Ɓangaren Mami ma tana barin palourn ta bi lafiyar gado ta koma baccinta, cike da taƙaicin Alhaji Mukhtar,
maganansa ya wuce stakaninsu ga shi har a gaban yarinyarta yana faɗa mata maganan aure, ita kuma ga
shi duk abinda zai mata ta kasa rabuwa da shi, a rayuwanta gaba-ɗaya wannan ne karo na biyu da taji tana
matuƙar son wani har tana jin ba za ta iya rabuwa da shi ha, Alhaji Mukhtar na cin albarkacin wannan
soyayyan idan ba haka ba, da tuni ba wannan maganan ake yi ba.

Ɓangarena ma baccin ne yayi gaba da ni, sai wajan azahar na tashi, fitowa nayi naji gidan shiru alaman
duk basu tashi baccin ba, sai na shige kitchen na kunna gass na hau haɗa mana abincin rana, fried rice da
yaji ice fish da haɗin coslow na mana, sai da na gama sannan na koma ɗakina lokacin ana ƙoƙarin shiga
sallah, wanka nayi na ɗaura alwala na gabatar da sallah na sannan na fito dan tashin Mamina, amma sai na

same ta zaune a palourn ta sha kyau, ina isa wajanta da murmushi sai kuma ga Alhaji ya shigo, alama daga
masallaci yake, ƙasa nayi da kai na, Mamina ta ce, "je ki kawo mana abincin mu ci, mu yi la'asar za mu fita
duka da Alhaji."

Miƙewa nayi na haɗo mana abincin, na Alhaji na ajiye masa, na ajiyewa Mamina nata, sannan na juya,
nawa na ɗebo na shige ɗaki, ina ci ina game a wayan Mamina da na ɗauko, binciken da na saba yi ko zan ci
karo da layin wani ɗan uwan Mamina a wayanta na yi, amma ba ko alaman abinda ya shafi layin wani nata,
ganin haka sai na dinga game kawai ina cin abinci, har aka ƙira la'asar, sannan nayi sallah na kuma wanka
na sanya riga da skirt na swiss-less, ba ƙaramin kyau kayan ya mini ba, kuma ya zauna a jikina ɗamas,
mayafina na yafa na fito, lokacin Alhaji da Mamina ma sun shirya, Mami kallo ɗaya ta mini ta ce na koma
na sako hijabi, cunna baki nayi ina shagwaɓe fiska na ce tayi haƙuri, amma ta dage sai na sako hijabi, Alhaji
ne ya bata haƙuri tunda a mota ne ta kyale ni da mayafin tunda ba ƙarami bane, Mamina da ƙyar ta ƙyale
ni tana wasta mini mugun kallo, wanda nasan nufinsa bai wuce ta ce nasan halittan da Allah ya mini ko ina
a cike amma bana son hijabi, ni abun har ɗaure mini kai yake yi, Mamina kaman wacce ta fito a jikin
bishiya ba iyayene suka haifeta ba, ko kaɗan bata damu da kanta ba, burinta a rayuwanta komai nine, bata
damu da mutuncinta ba tana kule-kulen maza, amma ni ko saurayi har yau bani da kuma ta hanani waya
ma, ajiyan zuciya kawai na sauƙe tunda ta bar ni naje hakan ba komai, Allah dai shi ne mai starewa.

Tare muka fito duka, Alhaji ya shiga mazaunin driver, Mami ta zauna a gefensa kujeran mai zaman banza, ni
kuma na buɗe gate, sai da motan ta fita sannan na kulle gidan gaba-ɗaya na nufi motan, a ƙofan gidan su
Umaima na hango ya Danish da yake shigewa gidan bai ma kalleni ba shi, murmushi na sake na abinda na
rashin mutuncin da na shirya masa, gidan baya na shige Alhaji ya ja mota muka shige gari, Japsal
Shopping-mall muka fara zuwa, waje ne na sayayya kuma kayaki ne masu kyau da kuɗi a can, sayayya
Alhaji ya mana ba kaɗan ba, kama daga dangin kayan sawa, kayan kwalliya, kayan abinci, kayan abun sha
da su snacks, muna gamawa da sayayya kuma ya wuce da mu ADU, nan ma sai da ya mana ordern abinda
za mu ci, kowa aka kawo masa abinda yake so, muka cika ciki, muka yi takeaway, ƙara zaga gari yayi da mu,
yawo muka yi sosai kaman ba gobe, idan ka ganmu za ka ɗauka Mami da Alhaji, mata da miji ne da kuma
ni ƴar su.

Sai da yamma tayi liss muka dawo da kaya niƙi-niƙi, Alhaji ya kashe kuɗi ba kaɗan ba, kuma ya ce kada
Mami ta yi girkin dare, wannan takeaway ya ishe mu, idan da wani abin ma zai fita ya nemo, ni kuwa
daman na jidowa Umaimata nata tunda nasan mayyar ice cream ce ita da naman kaza, muna iso wa, na
sauƙa na buɗe ƙofa Alhaji ya shige da motansa, kayan da na jidowa Umaima na ɗauka na ce, "Mamina bari
na bawa Umaima nata", kamun Mami tayi magana tuni na fice a gidan da sauri saboda kada ta dakatar da
ni, ai kuwa hakan aka yi, ƙwala mini ƙira ta dinga yi amma na gudu, Alhaji murmushi yayi tare da riƙo
hannun Mami ya ce, "Amarya ta mu shiga ciki ko."

Wani kallo Mami ta masa tare da ƙwace hannunta ta shige fuuuu! Ga haushin Alhaji ga haushin Banafsha
ta fita ba hijabi.

Ni kuwa ina shiga gidan su Umaima na dinga leƙe-leƙen Ya Danish, amma ban gansa ba, kuma dai motansa
na gida, nasan ba zai wuce yana part nasu ba, shigewa cikin gidan nayi ba kowa a palourn, sallama nayi na
nufi ɗakin su Umaima, samunta nayi tana guga, murmushi na sakar mata, ta ce, "Masoyiya irin wannan
kyau haka, komai Masha Allah! Daga ina?"
Ledan hannuna na miƙa mata na ce, "Ga tsaraba tawan."

Umaima kaman za ta fire ta ce, "Wayyo! Allah bar mini ke Banafsha, Mamina Allah ƙara buɗi, wayyo
naman kaza da ice cream, kutt har da shawarma, oyoyo chocolate" faɗin Umaima tana dariya.

Zama nayi a gefen gadonta na ce, "Mun godewa Allah da ba'a ƙauye kike ba, ko gidan talakawa da abin ya
fi haka, Abbaa yana da kuɗinsa, yayyunki ma haka, kuma Umma na business, Ummu ma ba'a bar ta a baya
ba, kuma babu wanda ba ya saya miki, amma idan kika ga kaza da ice cream kaman me, gaskiya idan Allah

ya kai mu Abuja za ki ba da mu, muna zuwa saudi kuwa nasan sai na dinga riƙe ki, saboda kada a samu
masu jan ki da dajaja(kaza da larabci), kinsan larabawan Makkah wasu yan albarka ne, wasunsu iskanci
suke da mutane."

Hararana Umaima tayi ta ce, "To zabiya, kanki ake ji, ki bari idan munje makkan sai mu tabbatar, ba kyau
shedan zurrr."

Nima rama hararan nayi ma miƙe na ce, "sai anjuma bari na shirya ki same ni a ƙofa mu wuce tahfiz."

Amsawa Umaima tayi, na fice na shige ɗakin Ummu na gaisheta, sannan na fito ina ta kan leƙe-leƙe ban
hango sa ba, yaya babba ne ya shigo gidan, da murmushi na ɗan rusuna na ce, "Sai babban yaya! Allah
taimaki babban yaya."

Dariya yaya babba yayi, ya ce, "sistor ba'a raba ki da abin dariya, kun gama exam's lafiya?"

"Alhamdulillahi babban yaya, ya Auntynmu."

"Tana lafiya, tunda kun ƙi zuwa gidan mu, ga baki ga hanci amma bakwa son shiga, daga ke har Umaima,
bealkysou ce kawai ke shiga."

Murmushi nayi na ɗan sosa kai, dariya yayi ya ce, "Allah shiryaki sistor, wannan kyau haka daga ina zuwa
ina?"

Na buɗe baki zan basa amsa cikin kunya, sai muka jiyo muryan Umma tana masifa wai ta ƙirasa ya tsaya
magana da fistararriyar yarinyar nan ƴar karuwa, yaya babba haƙuri ya bani da ido kawai ya wuce, ni kuwa
fakan idon sa nayi ganin ya juya na aikawa Umma da murguɗa baki, juyawa nayi ina tafiya na, kaman daga
sama kawai naji an zuba mini ranƙwashi aka ce, "Dan uwarki, fistararriya uwar tawa kike wa gastine da
baki?"

Ina ɗagowa, idanuwana suka sauƙa akan Ya Danish, cikin zafin ranƙwashin na ɗaga hannu zan maresa,
amma sai ya riƙe hannun nawa ƙam na kasa mosta sa balle ƙwace sa, wani kallo ya wasta mini ya ce,
"mara tarbiyya kawai, dube ki haka kike yawo, uban wa za ki ja hankalinsa da wannan ƙazamin jikin naki,
mai rijiyan kasuwa kowa zura gugansa yake, mara aji kawai."
Taƙaici ne ya rufe ni na maganganun sa, na ma rasa da me zan rama ga shi har yanzu ya ƙi sake mini
hannuna, idanuwana ne ke ƙoƙarin kawo ƙwalla, amma ƙoƙari nake wajan maida su, cikin dakewar zuciya
na ce, "sake mini hannuna ni ba sa'ar yinka ba ce, wanda bai san darajar uwar wani ba balle a kai ga tasa"
ina faɗa na ƙwace da ƙarfi, sai da na staya na ƙare masa kallo sama da ƙasa sannan naja staki na ce, "Ni ko
iskancin nake yi ai kasan na wuce wa irinka, na wuce yinka, na fi ƙarfinka, ba ka da abinda za ka isar da ni,
ka yi kaɗan abinka yayi kaɗan, ka je a sake maka kaciya tukunna, riƙe hannuna ba zai sa naji komai a kanka
ba, saboda kallon jariri nake maka, abinka kuɓewa ma ta fi sa a waje na, mtsww!" Ina gama faɗan haka na
juya da sauri-sauri na bar sa a wajan tsaye da buhun mamaki, ni ko ina ficewa na juya na harari gidan,
sannan na murmusa dan nasan ko banza na faɗa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login