Showing 3001 words to 6000 words out of 111817 words
Chapter 2 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf
sai Umaima ta dube ni cikin tsananin kuka ta ce, "Banafshaty wallahi idan kika ja
abu ya same ki ba zan taɓa yafe miki ba" tana gama faɗa kawai ta fashe da kuka mai nuni da tausayina da
take ji, ta rungumeni nima kukan nake jikina sai rawa yake yi ga kuma ya ɗau wani azababben zafi kaman
garwashi.
Wannan littafi FREE BOOK ne in Allah ya yarda, dan Allah fan's ku nunamin soyayya kaman ko yaushe,
sharhinku shi ne ƙwarin guiwa na, bana son tnx Sharhi nake so, ban yi niyan yin sa a paid ba kuma bana so
ya koma paid, love U all My fan's ♥️
***
INA KUKE MASU SANA'A, SANA'A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE
DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana'ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai
tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko
07015870735
WhatsApp and call
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com
Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo
#
# &
#
'YAR KARUWA
Officially
Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)
SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)
TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma ɗaukacin member's namu.
PAGE NAKU NE
Ƙanwa eclemah (Amarya)
Fatan ayi biki lafiya a gama lafiya, Allah ba da zaman lafiya, ya sa ɗakinki ne har mutuwa, congratulations.
My Heartbeat (ukhtynh)
2 month's Anvsy. Allah ya ƙaro zaman lafiya da ƙaunar juna ke da sweet babynki, Allah ya raba lafiya
مهللا ىلص و ملس ىلع ديس ان هللوسر SAW
️ 6 _ 10
A Haka Ummu ta shigo ta same mu muna ta aikin kuka, Umaima nayi nima ina yi kuma har yanzu ina fama
da tarin da kuma zafin jikin, Ummu ganin haka rai ɓace ta rufe Umaima da faɗa sannan ta ɗaga ni ta bani
magani, da ƙyar na haɗiye maganin kaman zan amayo da 'yan hanji na, Ummu koran Umaima a ɗakin tayi
ta dinga shafa min kai na ba jimawa bacci yayi gaba da ni ina ta faman ajiyan zuciya, sai da nayi bacci
sannan Ummu ta miƙe ta fice tana bina da addu'a.
Umaima taya Ummu aiki ta yi har dai lokaci ya ja, na sha bacci na sosai duk da ba na daɗi ba ne, sai can
yamma na farka, kuma a dai-dai lokacin Umaima ta shigo fes da ita dan har ta yi wanka, a kan ta na sauƙe
idanuwa na da suka mini mugun nauyi, murmushi ta sakar mini tana tambayan ya jikin nawa, da kai na
bata amsa na kuma mayar da idanuwana na lumshe su in ambaton Allah a zuciyana dan har yanzu ba wai
naji abinda ke damuna ya tafi duka ba ne.
Muna ɗaki Mamina ta shigo cikin gidan, a palour ta samu Ummu zaune tana waya, Ummu kaste ƙiran tayi
ta tari Mami da murmushi suka gaisa, Ummu ko kaɗan bata cewa Mami komai akan abinda ya faru ba dan
kuwa in da sabo to an saba da hakan tsakanina da Mamina.
Mami ce ta numfasa tare da cewa, "Ummu ina yarinyar taki ta shiga?"
Ummu na murmushi ta ce, "suna ɗaki da mutumiyar ta, da bacci take yi amma ina ji yanzu ta tashi dan na
jiyo mostinsu."
Da yake Mami ta kan shigo gidan sa'i da lokaci idan irin haka ta faru, kuma ta san ɗakin da nake zama idan
na shigo, sai ta wuce ɗakin da muke, da sallama ta shigo, Umaima ce ta amsa da ƙarfi, amma ni ciki-ciki na
amsa kuma ba tare da na buɗe idanuwana ba, Mami ganina a kwance bata kawo komai a ranta ba ta
murmusa tare da ƙarasowa bakin gadon, sai da ta amsa gaisuwan da Umaima ke mata sannan ta ce,
"boɗɗin Maminta taso mu tafi ko."
A hankali na buɗe idanuwana da suka kumbura ga kuma hawaye kwance a cikinsu na zubawa Mamina su,
ban ce komai ba kuma ban mosta ba dan bana jin zan iya tashuwa balle tafiya, Mamina tana kallon yanayi
na ta shiga damuwa dan bata san banda lafiya ba ne, a rikice ta zauna bakin gadon ta taɓa jikina, da yake
zuwa lokacin zazzaɓin ya sauƙa, to zafin jikin ba sosai ba, amma duk da haka da ɗumi, Mamina duk ta bi ta
rikice, kaman za tayi kuka ta ce, "boɗɗi me ke damunki?"
Nan ma shiru nayi ban ce komai ba, Mamina cikin damuwa ta ce, "Banafsha ki daina saka abu a ranki, ki
saki ranki mamana, ki dinga taya ni da addu'a kawai dan wani abin nima ba da son raina nake yi ba, tashi
muje gida kiyi wanka."
Yanzunma dai ban ce komai ba sai ƙoƙarin miƙewa da nayi ina runste idanuwana dan har yanzu kai na
yana mugun sara mini, amma tunda Mami ta ce mu tafi ba zan iya mata musu ba dan Allah ma ya gani ina
ƙaunar mahaifiyata ina son mahaifiyata fiye da yacce nake son kai na, duk wani mafarki na da buri na ita ce
ba wanda na sani sai ita ba wanda ido na ya taɓa gani da za'a nuna ace ɗan uwanane ko wani nawa sai ita,
ita kaɗai gare ni shiyasa bana haɗa soyayyan da nake mata da na kowa.
Miƙewa nayi amma ganin jiri na neman yasar da ni sai Mamina ta hau da ni bayanta kasancewar ba wani
nauyi ne da ni ba duk da dai in ka ganni za ka ɗauka nafi shekaruna, ko na kai irin ishirin da ɗori hakannan.
Fitowa muka yi a ɗakin ina bayan Mami na lafe abuna, Ummu ganin mu sai ta girgiza kai tare da yin
murmushi ta ce "Yau kuma taɓaran Banafsha ya tashi, har goyo ya kai a mata, ah lallai ƴar gidan Mami jin
daɗi ya zauna miki."
Umaima tana murmushi ta ce "Nima Mami biyo ki zan yi a goya ni nima dan masoyiya ta fini nauyi ma."
Mamina murmushi tayi wanda ako da yaushe yake zama makari sannan sirri na kyau da Allah ya mata, dan
in ka kalli Mamina za ka ranste balarabiya ce ko bafulatana amma kuma duk ba abinda ya haɗa mu da yare
biyun, bayan su Ummu sun gama zolayansu Mami ta fice da ni a bayanta tana murmushi muka yi gidanmu,
kasancewan ba nisa tsakanin gidanmu da na su ƙawata Umaima.
Jahar Adamawa a ƙaramar hukumar Mubi anguwan Kwaccam, nan ne anguwan mu, anguwa ne na masu
saka ido da kuma damuwa da rayuwar da bata shafe su ba, mutane masu kiwon mutum ba dabba ba,
komai aka yi idanuwansu na kai, ɗan madai-daicin gidanmu flat ne mai ɗauke da center palour sai kuma
ɗakuna guda uku wanda ko wanne akwai banɗaki a ciki sannan daga gefe akwai kitchen, ba abinda
Mamina bata saka mana ba na more rayuwa a gidan, dai-dai buƙatan talaka mai rufin asiri, wanda in ka
samu irin sa dole ka ce Alhamdulillahi! dan kuwa wani ko kwatan-kwatansa nema yake bai samu ba, a filin
gidan namu akwai kitchen a waje sannan da banɗaki, gidan bashi da wani faɗi sosai kuma ciki duka
interlock ne.
Har ɗakin da yake nawa Mami na ta kai ni ta kwantar da ni a kan madai-daicin gadona, juyawa tayi ta fice
a ɗakin sai can ta dawo da abinci a plate da ruwa a cup da kuma magani.
Ɗagani tayi ta zaunar da ni tana jero mini sannu ta ce, "FAƊIMAH tashi ki ci abinci ki samu kisha magani,
kinji ko ƴar albarka ta Maminta."
Miƙewa nayi na zauna tare da zuba wa Mami idanuwana, kallon mahaifiyata nake yi ina mai jin ƙaunanta
na ƙaruwa a raina yana tsigar mini a ko wani sassa na zuciyata, ina jin ina ma muyi rayuwanmu mu
biyunmu a haka ba tare da wasu sun shigo ciki ba, ina jin ina ma shikkenan Mamina ta daina wannan
rayuwan, mu zauna haka abunmu ta kula da ni nima na kula da ita, amma sai dai kashh! nasan hakan ba
mai yiwuwa bane, tana ƙaunata tana tausayina amma wannan rayuwa ya zamo ƙaddara a garemu ni da
ita, kuma amsa sunan 'YAR KARUWA ƙaddara na ne, sai dai na yi haƙuri na karɓe sa da hannu bibbiyu.
A baki take bani abincin ina ci kaman zan yi kuka, saboda a rayuwata ni bana ƙaunar cin abinci wanda ta
wannan dalili ne har ulcer yayi nasaran mini mugun kamu, amma a haka Mami ta cigaba da bani har na
kawar da kai na ƙoshi, sannan ta ɗau magani ta ɓare ta miƙo mini, nan fa gizo ke saƙar dan kuwa wannan
ga'bar ita ce daru, nan na fara hawaye ina kuka ina girgiza kai banason sha.
Kallona Mami tayi cikin lallashi da ta saba min a duk lokacin da zata ban magani ta ce, "Haba Sayyada
Faɗimah shugabar mata, Nana Faɗimah, Fatima Bintu, batooler, Faɗimatu zahra'u, Sadiƙa, yarinyar kirki
jaruma, da girmanki ai sai dai magani ya ji storonki, takwara ga ɗiyar ma'aiki SAW, yi haquri kibar kukan ki
karɓa kinji zan baki abu mai daɗi."
Ina kukan ina yarfe hannu na karɓa na sha, ajiyan zuciya na dinga jerowa kamun na koma na kwanta amma
Mami ta tashe ni wai na wasta ruwa, langwaɓe kai nayi cikin shagwaɓa na ce, "Mami nikam ba zan iya ba
sai anjima."
Kallona tayi ta murmusa sannan ta ɗaga ni ta fara cire min kayan jiki na, tana gamawa ta ɗaura min towel
tana cewa, "Yanzu Banafsha da girmanki kike so ki ce sai na miki wanka, kin fa zama budurwa yanzu,
shekaru ishirin 20 ba wasa ba, ko in na aurar da ke haka zaki sa surki na sai ya dinga miki wanka kullum
kaman bai da aikin yi?"
Tura baki nayi idanuna har ya kawo ƙwalla dan maganan da tayi na ce, "Mami ni ki bari bana so, ba ruwana
da maganan nan, kuma ba ruwa na da namiji balle aure."
Mami ajiyan zuciya ta sauƙe kamun ta zauna tana kallona cikin yanayi na muhimmin magana za ta yi, sai ta
ce, "Banafsha, na hane ki wannan magana, banda abinda ya ragemun a rayuwata a yanzu sai ganin na
aurar da ke, domin kuwa aure shine mutunci ko wacce ɗiya mace kuma buri ga iyayenta suga sun miƙata
gidan miji lafiya cikin mutunci, in Allah ya yarda mijin da zai auri Banafshan Mami sai ya kasance mai
matuƙar sa'a, wanda ba shi da stara, in Allah ya yarda za ki rayu a gidan mijinki rayuwa ta matar Sarki."
Wannan magana da Mamina tayi ba ƙaramin fama min ciwon dake zuciyata yayi ba, kuka ne ya ƙwace mun
ba tare da nayi niyan kukan ba, cikin kukan na ce, "Mami ashe mutuncin ko wacce ɗiya mace aure ne?
Mamina kinsan da hakan amma me yasa kika take sanin? Mami kema fa kina da iyayen amma me yasa ke
ba zaki cika musu nasu burin ba ki riƙe mutuncinki, sannan kuma ki zauna a gidan miji, meyasa Mamina?
Meyasa kika zaɓar mana wannan rayuwa? Why Mami?" Na ƙarishe maganan cikin matsanancin kuka mai
cin rai."
Miƙewa Mamina tayi ranta a matuƙar ɓace, wanda na tabbatar rashin lafiyan dake damu na shine kawai
ya cece ni daga samun sadakan mari ko kuwa duka daga Mami, a fusace ta nuna ni da yasta cikin fushi da
ɗaga murya ta ce, "Banafsha, kar ki yarda ki tunzura ni har ɓacin rai yasa na miki baki."
Kallon Mamina nayi ina kan kuka na ce, "Mami wallahi ko kin stine mini ba zai taɓa kama ni ba har abada
in dai akan wannan maganan ne, domin Allah ya faɗa ba ya kama bawansa da laifin da bai aikata ba, Allah
ba azzalumi bane, sannan Allah ya sani gaskiya ce kuma Allah da kansa ya ce ko iyayenmu ke yin ba dai-dai
ba mu faɗa musu gaskiya komin ɗacinta, dan Allah Mamina kiyi haƙuri gaskiya ce na faɗa, amma in har na
ɓata miki rai to ki yafe ni, kada kiyi fushi da ni, Allah huci zuciyanki Mamina."
"Tashi kije ki wasta ruwa kuma kina fitowa ki tabbatar kin yi sallah kamun ki kwanta" Mami na gama faɗan
haka ta fice a ɗakin.
Tashuwa nayi na shiga banɗaki ina cike da tunani dan zuwa wannan lokaci idanuwana sun kafe ba hawaye,
kukan yau kuma ya tsaya sai kuma na gobe, dan wannan wani abu ne gare ni da kullum shine sana'a ta
kuma ƙalubale na, ba ranar da gari zai waye har rana ya faɗi ban yi kuka akan halin Mamina ba ko wani
abun idan ta mini.
Ina gama wanka na ɗaura alwala sannan na fito, ko mai ban shafa ba balle wani abun, humran da Mami ke
sayamun kawai na shafa a inda ya kamata na sassan jikina, sannan na buɗe drawern kayana na ciro simple
material riga da wando da mayafin sa wanda ɗinkin ke kama da Pakistan-dress, ina saka wa na ɗau hijab
na tada sallahn magrib, ina idarwa na ɗauki Qur'ani na fara karatu, nice ban tashi akan darduman ba har
sai da nayi sallahn isha'i na tabbatar hadda na ya zauna, sannan na naɗe na ajiye sa, da hijab ɗin jikina na
fito palourn namu, amma mutumin da na gani zaune a palourn namu shi ya sanya ni juyawa da sauri
wanda kamun ace na ƙarisa shigewa ɗaki Mami na da fitowan ta kenan ta ganni ta qwalamun ƙira, kuma
ƙiran nata ne ya tsayar da ni, ban shige ɗaki ba kuma ban juyo ba ina dai tsaye a wajan cikin taƙaici da
haushin mutumin da ya zo wajan Mamina.
Mami na kyakkyawa ce ta gasken-gaske, farar mace ce mai ƙaramin ruwa dan in ka ganta ba zaka ce ta
haife ni ba, tana da dogon hanci da tsayin gashi wanda hakan ke sanya wasu mutanen mata kallon
bafulatana, sannan tana da kyakkyawan ƙira, wanda har zuwa wannan lokacin da nima na zama budurwa
amma ƙirjinta basu kwanta ba ko dan ni kaɗai ta shayar ne oho, kuma Mamina tana gyaran jikinta sosai,
sannan tana da ƙugu wanda ke ɗaukan hankalin mutane dan nima a wajan ta na gado ƙugun da mazaunai,
wasu in suka ganni ma har cewa suke nima na biyewa Uwata na fara bin maza dan kusan kallon da mutane
ke mini kenan akan nima nasan maza na buɗe.
Jin muryan Mamina ta ƙara ƙiran sunana a karo na biyu, kuma nasan palourn take so na dawo, tura baki
nayi dan kuwa na tsani wannan mutumin da ke zaune a palourn namu, saboda duk cikin masu zuwa wajan
ta a manyan mutane shi yake ban haushi ganin babban mutum kaman sa ga kuɗi ga kyau amma yake
biyewa bin mata dan na tabbata yana da yaron da zai kusa sa'an Mami na dan daga ganinsa ya bai wa
shekaru hamsin 50 baya, saboda babban mutum ne sosai kyakkyawa har da furfuransa.
Wannan karon inajin muryan Mami na Juyo, cikin nistuwa nake tafiya kaman bana so, a haka na ƙariso
cikin palourn fiskana a haɗe, sam-sam babu annuri ko kaɗan, kallon da Mamina ta jefo mini shi ya sanya ni
tura baki ciki-ciki na ce, "Anwuni lafiya Alhaji?"
Alhaji mukhtar washe baki yayi dan sosai yake ƙaunar mahaifiyata, wanda wannan soyayyan da yake mata
shi ya sanya nima yake ƙaunata tamkar ƴar cikin sa, kayayyaki ne menene duk idan ya tashi zuwa sai ya
kawo min, kwanaki har ya sayamun waya babba mai kuɗi, amma kuma Mamina ta maida masa ta ce ba
zan riƙe waya tun yanzu ba.
Amsa gaisuwan yayi yana ta saka mini albarka, amma ni fiska na ko Annuri babu balle batun amsa albarkan
da yake sanya min, na tashi zan koma ciki sai ya tsayar da ni ta hanyar cewa "yarinyata Banafsha ga
tsaraban ki taho ki amsa."
Cikin taqaici na juyo, ji nake kaman na shaƙesa ya mutu na huta, durƙusawa nayi na miƙa hannayena
bibbiyu na karɓa abinda yake miƙa mini, na ce masa, "Nagode Alhaji, Allah ya ƙara arziƙi da ɗaukaka."
Yana murmushi da jin daɗin addu'a ta gare sa kullum, dan muddin zai min kyauta to ni kuma sai na
suburbuɗo masa addu'a ko ban yi niya ba, cewa yayi, "Ameen ya Rabbi! yarinyar kirki Allah ya miki
albarka ya albarkaci karatun ki ya baki miji na gari."
Amsa wannan addu'a sai Mami na ne tayi shi cikin fara'a dan tana ƙaunar mai ƙaunar gudan jininta,
yarinyar ta gudan ɗaya tal kaman stoka a cikin miya, ni kuwa tuni na jima da shigewa ɗakina inda nayi jifa
da ɗan ƙaramin jakan, dan abun hannunsa ba ya burgeni.
"Subhanallahi!" shi ne abinda baki na ya furta ganin wani haɗaɗɗen Qur'ani ɗan dai-dai ya faɗo ga carbin
irge(counter), ga kuma sallaya ɗan ƙarami, ga kuma ruwan zam-zam duka