Showing 78001 words to 81000 words out of 111817 words
Chapter 27 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf
Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)
SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)
TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma ɗaukacin member's namu.
PAGE NAKU NE
My ƙawas Oum inaya.
Nana ƙanwar Soja.
Aunty Salma (maman humaira da bashir)
مهللا ىلص و ملس ىلع ديس ان هللوسر SAW
Noted: afuwan fan's, mastayin Bunayd na Air Force ba CAS bane, wato Chief of the air staff, mastiyinsa
ACM ne, Air Chief Marshal, a yi haƙuri da mistake ɗin, shi CAS a land army ne, ACM ne Air Force, kuma
Bunayd Sojan sama ne Air Force kenan, abin ne da rikitarwa sorry for the mistake.
️ 76 _ 80
Driver na parking, Bunayd ya fito a rikice, amma idan ka kallesa ka ranste ma rigima yake ba'a cikin
damuwa yake ba, amma kuma shi ya san damuwan da yake ciki na abinda ya samu Abeed, cikin hanzari
suka shige ciki, sojan da ke tare da Abeed ne ya musu jagora har ɗakin da Abeed ke ciki, ya so shiga amma
kuma aka tsayar da shi, sakamakon taimakon gaggawa da ake kan bai wa Abeed ɗin.
ACM Bunayd stayuwa yayi a bakin ƙofan ya na safa da Marwa, da ya kasa haƙuri sai ya juya kawai, dai-dai
lokacin kuma ya samu kuma ana rikici tsakanin Nurses da wata kyakkyawar matashiyar budurwa, da ke
rikice kaman wata mara ishashshen hankali, taɓe baki yayi zai fice sai idanuwansa suka sauƙa akan mara
lafiyan da ke kwance a gadon ɗaukan marassa lafiya, ɓata rai yayi ya nufe su gadan-gadan.
Banafsha tun barowansu gida kuka take yi, Abbaa saboda ɓacin rai ko magana ya kasa yi, sai ya Sadeeq ne
ke ƙoƙarin bata baki akan tayi haƙuri, amma ta ƙi shiru har suka isa General hospital ɗin.
Abbaa kuma layin babban yaya ya ƙira, yana ɗauka Abbaa bai tsaya amsa sallaman da yake masa ba ya ce,
"kabeeru ka je gidan Mamin Banafsha ka ɗau uwarku, kuma kar ka kuskura ka shigar mini da ita gidana,
idan ƙafanta ya taka gidana ko gawanta ne, to ban yafe maka ba, kuma kuna farfaɗo da ita ta kwana cikin
shiri dan ƴan sanda suna hanya."
Babban yaya cikin tashin hankali ya miƙe, daman yana wajan aikinsa ne, gareji yake yi, cewa yayi, "Abbaa
me ya faru? Me ya kai Umma gidan Mami?"
Guntun tsaki Abbaa ya ja, ya ce, "kana tambayana ne, ni na san irin haukan da ke damun uwarku, to dai ka
ji abinda na ce, mu yanzu haka ma muna general hospital", Abbaa bai jira me babban yaya zai ƙara faɗa
ba, kawai ya kashe wayansa yana yin ƙwafa kawai.
kusan tare motan su Abbaa suka iso da su Bunayd, Bunayd suna shigewa, su Abbaa kuma cikin gaggawa
aka ɗauko gadon ɗaukan mara lafiya aka ɗaura Mami a kai, suna shiga ciki Nurse ɗin ta dube su ta ce,
"kunsan ba'a attending irin waɗannan patient's ɗin sai da police ko?"
Abbaa ya ce, "Ku yi haƙuri ku fara ceton rayuwanta baiwar Allah, police kam dama dole ne ku gan su, dole
su shigo cikin lamarin nan."
Ya Sadeeq dialing layin Ya Farooq yayi amma ba ya shiga, dan ya Farooq ma a general hospital ɗin yake aiki,
Banafsha cikin shessheƙa ta ce, "Dan Allah dan Annabi ku taimaka ku fara bata agajin gaggawa tukunna, ai
an ce muku police ɗin za su zo."
Magiyan duniya su Banafsha sun yi, amma amsa guda Nurses ɗin ke basu, ba'a amsan irin wannan
mastalan ba tare da police ba, domin yan da mace-mace ke yawa ana ɗaure likitoci basu ji ba kuma ba su
gani ba to dole sai da shedan police, dan ko ma mene ya biyo baya to dai ba za'a ga laifin likita ba balle har
a ɗaure sa, Abbaa ransa ne yayi mugun ɓaci, dan haka ya sa Ya Sadeeq ya dubo musu wani likita abokin ya
Farooq, Abbaa kuma ya ɗau waya ya ƙira babban yaya ya kuma faɗa masa ya turo musu police tukunna.
Banafsha fa ta ƙulu ta kai wuya cikin karaji da masifa ta fara balbala bala'i, cewa take, "Amma dai wallahi
ku kam an yi marassa imani, marassa tausayi, asararru kawai, daman dan uban me kuka yi karatun naku,
kuma aka baku daman aiki a asibiti, gomnati ta gina asibiti kuma ta ɗauke ku aiki, take biyanku albashi, ba
duk dan al'umma ba? To in Allah ya yarda Mamina ba abinda zai sameta, shegu, munafukai, marassa
imani, ƴan uwan fir'auna kawai, kuma nima zan zama likitan nan, aka kawo mamanku duk ni da kai na zan
ƙarisa su...." masifa kawai Banafsha ke yi, kaman wacce aka aiko daga sama, Abbaa sai tausanta yake
amma ta ƙi yin shiru, kuma a dai-dai lokacin Bunayd da ya ga duk abinda ke faruwa, ya iso wajan rai a
ɓace.
ACM Bunayd ko kallon inda Banafsha ke masifanta bai yi ba ya kalli Abbaa, a ɗan daƙile ya ce, "sorry Sir!
Za'a dubata yanzu."
Shi da kansa ya tura gadon Mami, sai sauran sojojin suka zo da gudu suka amshi gadon suka tura, likitan da
ke duba Abeed ne ya fito, ganin su da wata patient ɗin, take ya saka aka kai ta ɗakin ba da agajin gaggawa
ba tare da ya tambaya ba ko ya ce wani abu.
Abbaa kaman zai rungume Bunayd ya ce, "Allah maka albarka likita, mun gode, Allah saka da alkairi ya rufa
asiri duniya da lahira, idan ana samun irinku a likitoci ai ba wanda zai mutu saboda irin haka, sai dai in
lokacinsa ne yayi, Mun gode bawan Allah" Abbaa ya faɗa dan duk ɗaukan sa Bunayd irin likitoci masu
taimako da tausayin nan ne.
Bunayd murmushin da ko leɓensa bai kai ba yayi ya ce, "Ba komai Sir, your welcome."
Banafsha tun da aka yi gaba da gadon da Maminta ke kai sai ta kuma ƙaro sabon walaƙanci, duban Nurses
ɗin ta yi ta ce, "Munafukan Allah to ahirr ɗin ku za'a duba Mamina, kuma ba ɗan banzan police ɗin da za
mu ƙira balle kuma Soja, ƴan baƙin ciki kawai, so suke na zama marainiya gaba da baya ba uwa ba uba, to
ta Allah ba ta ku ba..." Masifanta ta ci gaba da yi har ta ƙarisa wajan su Abbaa.
Duk abin da Banafsha ke faɗa a kunnen Bunayd yana ji, surutun nata bai dame sa ba tun da ya saba da na
ƙannensa, amma maganganun nata ma dariya yake basa, kallo ɗaya ya mata ya kawar da kai kaman bai
kalleta ba yana yastina fiska, ba tare da ta masa godiya ba ta wuce su ta ƙarisa ƙofan ɗakin da ta ga an
shigar da Maminta, bata hango kowa a ciki ba sai Maminta, juyawa ta yi kuma kaman za ta yi kuka ta ce,
"Abbaa ka ga mugaye, su ma ba dan Allah suka karɓe ta ba, ga shi sun ajiye ta ita kaɗai, so suke ta mutu,
wayyoo ba'a ƙaunata ana son Mamina ta mutu."
Abbaa ƙarisowa yayi wajanta ya ce, "ki yi shiru Faɗima, wannan likita mai mutuncin ya sa za'a dubata kin
ji."
Banafsha kwaɓe fiska ta yi ta ce, "tun da dai ba zai duba Mamina da kan sa ba, to ba shi da wani mutunci
shi ma, shi ɗin banza, to ya duba ta da kansa mana indai da gaske yake yana da imani kuma shi na gari ne
ba kaman sauran ba, ni wallahi ba za'a yaudareni a banza ba a bar uwata ta mutu ba, aikin banza daga shi
har sauran har Umma duk in Mamina ta mutu sai na yi Shari'a da su, ko kuma na bi rana na kashe su, bin
dare ma ai storo ce, ni da ranan Allah ido na kallon ido zan ƙaddamar musu."
Tana rufe baki sai ga likita ya iso wajan da sauri, bai shiga ɗakin da Mami ke ciki ba ya wuce inda zai kai sa
ɗakin da Abeed ya ke, da sauri Bunayd ya stayar da shi, cikin turanci ya masa magana akan tun da sun yi
aikin Abeed ɗin su duba matar mana kada a rasa ta.
Likita duban Bunayd yayi ya ce, "sorry Oga, an mata abinda ya kamata, raunin nata ba sosai bane, idan
muka gama da shi za'a dubata."
Kamun Bunayd ya buɗe bakin ba da amsa, tuni Banafsha ta diro a gaban likita idanuwanta rufe ta ce,
"wallahi ƙarya kake, maƙaryacin likitan da bai san aikinsa ba, wuƙa aka yage Mamina da shi, kuma ka ce
raunin ba sosai ba ne, kai kasan jinin da ya fita a jikinta ne ma, wa ma ya sani ko har kayan cikinta sun
yanyanke, to nima ɗalibar malaman lafiya ce, ina College kuma ina last year, dan haka kada ka wani faɗa
mana ƙarya mun san me ne a aikin muka, kuma ba inda za ka tafi idan ba ka shiga ɗakin da aka kwantar da
Mamina ka duba ta ba."
Daga likita har Bunayd baki suka sake suna kallon ikon Allah, ganin yanda budurwan ta dage da masifa iya
ƙarfinta, likitan ya kasa haƙuri sai da ya dara ya ce, "To masifaffiyar likita, tun da kinsan komai kuma kin
kusa gama College sai mu baki kayan aiki ki duba Momin taki ko."
Banafsha sai kuma ta shagwaɓe ta ce, "dan Allah duba Mamina ka ƙyale wancan ɗin, ai shi ma ka duba sa,
ka koyo adalci mana likita, ai in ba ka practicing to ba za ka iya riƙe mata biyu ba, kawai Mami ma s dubata
tun da shi ma an duba sa."
Bunayd bai kalli Banafsha ba, amma yana sauraranta, ji yake kaman ya kwanta a ƙasa ya ta dariya har
cikinsa yayi ciwo, wai ai ta kusa gama College ita ma likita ce, murmushi yayi har sai da haƙoransa suka
bayyana, sannan ya kuma magana da turanci ya ce, "ka turo wani likitan ya duba ta, please a yi a gama da
Captain namu dan transfer muke so a mana zuwa Kano."
Banafsha ma ta ƙi kallon Bunayd, likitan take kallo ta ce, "wallahi ban yarda ba, ni kai ka mini, kai nake so
ka duba Mamina, wani likitan ya je ya duba Captain ɗin nasu, tun da ba mu na Captain namu bane, ni
Mamina ce Captain tawa."
Bunayd murmushi ya kuma yi tare da yi wa likitan magana da ido, sai ya juya wajan Abbaa da yayi poster
yana ganin ikon Allah, Abbaa bai taɓa sanin haka Banafsha take ba sai yau, Bunayd murmushi yayi ya ce,
"ina so za mu yi magana Sir."
Abbaa gefe suna yi da Bunayd, ya ce, "Ina sauraranka likita."
Bunayd kiston kan sa ya shafa ya ce, "Sir ni ba likita ba ne, ni Soja ne, muma mun kawo wani ɗan uwanmu
ne ya samu hatsari."
Abbaa baki ya buɗe ya ce, "Ai ko na ji, amma dai kai a sojojin ma daban kake, ai ko likitoci ka fi su imani da
tausayi, Allah kuma ya basa lafiya, ka yi haƙuri da shirmen Faɗima, ba haka take ba kawai abinda ya samu
mahaifiyarta ne ya rikita ta haka."
Bunayd cewa yayi, "Ba komai..", zai yi magana sai ƙira ya shigo wayan Abbaa, haƙuri Abbaa ya bai wa
Bunayd sannan yayi picking, "ina cikin asibitin kuna ta ina?" Faɗin Abbaa da ke kare da waya a kunnensa.
Yaya babba ya ce, "Abba ka fito bamu san a ciki ta ina ba."
Abbaa ya ce, "To ganinan", yana faɗa ya kashe wayansa, sannan ya dubi Bunayd ya ce, "bawan Allah bari
na zo, Yarona ya taho da polisawan ne."
Bunayd gyaɗa kai kawai yayi ya juya wajan likitan.
Likita dan dolensa sai da ya shiga ɗakin da Mami ke kwance, sannan ya fito ya tafi ɗakin da Abeed ya ke,
jaraban masifan Banafsha dariya ma yake basa, sai ya ji ta burgesa.
Bunayd bayan ya je office na likitan, bayani ya masa dangane da Abeed, akan sun yi duk abin da ya kamata,
gobe ma za su iya ɗaukan sa su tafi Kano ɗin, harbin bai yi muni sosai ba a cinya ne kuma an cire
alburushin, sai su ƙarisa jinyan a asibitin Kano, dan zai fi samun kulawa sosai ma, Bunayd hamdala yayi,
sannan ya ce, "likita wannan matar fa?"
Murmushi likitan yayi ya ce, "Ni da farko na ɗauka ma ai duk tafiyanku guda, sai da masifaffiyar likita ta yi
bayani" likita ya faɗa yana murmushi.
Bunayd murmushi shi ma yayi dan ya tuna kalaman Faɗima, kaman yan da ya ji sunanta a bakin dattijon
ɗazu, cewa yayi, "likita, ita ya nata condition ɗin? Komai zai tafi dai-dai a nan ko ita ma a sanja mata asibiti,
ko da a cikin Yola ne."
Murmushi likitan yayi ya ce, "a'a Oga, ita matar fa kaman yan da na faɗa raunin nata da sauƙi, anyi niyan
caka mata wuƙan a ƙirji ne, amma sai ya kauce ya kar ci cikinta, bai ma shiga sosai ba, sai dai daman abin
da ya sa muke so a ce sun zo da police saboda maganin samun mastala ne, ya kamata wanda ya mata haka
a hukunta sa, dan gaskiya kasheta aka yi niyan yi, amma aka bar ta a nan asibitin ma komai zai tafi dai-dai,
in Allah ya yarda za mu yi iya bakin ƙoƙarinmu muyi duk abinda ya kamata."
Bunayd gyaɗa kai yayi ya ce, "good, Allah bata lafiya" yana gama magana ya sallami likitan ya fita, lokacin
dare ta yi sosai-sosai.
Abbaa ma bayani ya yi wa polisawan, suka samu likitan shi ma ya musu bayani, sannan ya faɗa musu Soja
ne ya shiga lamarin shiyasa ya amshe ta ma, samun Bunayd suka yi, cikin girmamawa suka gode masa,
amma Bunayd gyaɗa musu kai kawai yayi bai ko kallesu ba, sannan a gadarance ya ce, "Ku tabbatar kun
mata duk wani hukunci yan da ya kamata dai-dai, she attempt to commit a murder, dan haka idan na ji
ba'a mata hukuncin da ya kamata ba, ku ne za ku yi facing na hukuncin" yana gama magana ya miƙe ya yi
gaba.
Polisawan amsawa suka yi, sannan suka tafi, tare da yaya babba da Abbaa suka koma aka ɗau Umma da ta
farka zuwa lokacin da mugun ciwon kai, daman tana gidan yaya babba ne, tana kallon su ta miƙe tana
muzurai, Abbaa staki kawai ya ja, ya ce, "ki je na sake ki, kuma aure ki sani ba gudu ba ja da baya, ke kin
fita a banza, ita kuma za ta shigo hankali kwance."
Umma za ta yi magana, polisawa suka tisa ƙeyarta sun ƙi bata daman magana, yaya babba gaba-ɗaya
yasan Umma bata kyauta ba, abin bai masa daɗi ba, amma dai uwa-uwa ce, sai ya ji ba daɗi sosai, har ya ji
haushin Danish dan shi ya ja komai, ya stani yarinya kuma ya dawo ya ce yana son ta, bayan shi ya ƙara
ingiza Umma har ta musu mugun stana, yanzu ga shi abinda ya faru."
Abbaa gida ya koma, ya faɗa wa Ummu abin da ke faruwa, Ummu hankalinta yayi mugun tashi, Abbaa ya
ƙira ya Sadeeq akan ya dawo da Banafsha gida, tun da dare ta yi, kuma ana kula da Mami, ya Sadeeq ya
amsa.
Banafsha na tsugunne gaban ɗakin da Mami take, sai ga ya Sadeeq, yana zuwa ya ce, "sistor ki zo mu je
gida ko, zuwa safiya sai mu dawo."
Tura baki Banafsha ta yi ta ce, "Ni dai ina nan da Mamina ba in da zan je."
Ya Sadeeq yayi-yayi ta ƙi, dan haka dan dole ya ƙyaleta, dan ko da ya faɗawa Abbaa ma cewa yayi a ƙyale
ta.
Bunayd ma an yi da shi ya koma hotel tun da Abeed ɗin na huta wa, amma ya ce yana nan kawai, ba dan
sojojin sun so ba, haka suka mara masa baya kwanan asibiti ya same su.
Bunayd shi ba kwanciya zai yi ba, dan haka zama yayi kawai a ɗakin da Abeed ɗin ya ke, idan ya gaji kuma
ya tashi ya fito.
Banafsha kuma likita ya faɗa mata ta shiga ciki ta kwanta, tun da daman Mami ita kaɗai ce a ɗakin, yau
Banafsha ta ga daren da bata taɓa gani ba a rayuwanta, don kuwa baccin ma gaba ɗaya ta kasa, ya
ƙauracewa idanuwanta, haka ta dinga juyi, ƙarshe alwala ta ɗauro ta ta da sallah, sai da ta yi nafilfiulunta
sannan ta miƙe ta fito.
Mutumin da Banafsha ta gani a tsaye shi ya storitata, za ta koma ciki sai ta jiyo daddaɗan muryansa na
faɗin, "storita kika yi?"
Banafsha tana jin muryan ta gane mai yin turanci ɗazu ne, tura baki tayi ta ƙarisa fitowa ta zauna, Bunayd
ma ya ƙariso wajan ya zauna ba tare da rata sosai stakaninsu ba, wayansa ya fidda yana lastawa ya ce,
"scared girl."
Cunna baki ta kuma yi ta ce, "Ni ba mastoraciya ba ce, ni bana storon kowa sai Allah, sai na yi kokawa da
aljani ma lafiya lau, duk wanda ya mini rashin kirki nima masa zan yi ba storo."
Taɓe baki Bunayd yayi ya ce, "Kuma kina gani aka yi wa Mom naki wannan abun ba ki ɗau mataki ba, ashe
kina da kirki."
Banafsha da ta tuno abinda Umma ta yi, ai a masifance ta ce, "wallahi na buga mata abu a kai ita ma