Showing 111001 words to 111817 words out of 111817 words

Chapter 38 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf

Advertisement

16 Aug 2025

4072

da Mamina ta tashi, a makare ta tashi lokaci ya tafi dan kusan ƙarfe ɗaya ta
tashi, lokacin kuma an fara shirin tafiya masallaci, saboda biyu da rabi za'a ɗaura auren, ni da yake bansan
da Mami yau za ta bani labarin da ta faɗa ba, to sai ban damu ba, da aka ce tana bacci na bar ta, ba wanda
ya tashe ta, an bar ta wai ta huta.

Mami ta tashi lokaci ya ƙure, gaba-ɗaya bata ji daɗin hakan ba, dan ba ta tunanin akwai lokacin da za ta
samu a nitse su yi maganan, dan ana sauƙowa ɗaurin aure ba jimawa, za'a ce an zo ɗaukan Amarya, tun da
su a Mubi da yamma ake ɗaukan aure, ta rasa ya za ta yi, ga shi dai ana kai Amarya kuma shikkenan,

sannan wannan magana ba wan da za'a yi sa a waya ba ne, dan haka a lokacin ta saka a shirya Banafsha
tun da har ɗaya ta yi, idan an sauƙo ɗaurin aure kamun a ce anzo ɗaukanta, ko sama-sama za su yi
maganan, dan yin maganan a yau ya zama dole, idan ba yau ba, ba zasu samu lokaci ba, ita tana gidanta a
nan Mubi, ita kuma Kano za su wuce da Alhaji.
Shirya Banafsha aka yi cikin wani irin ranstaststen shinning les, fari da flower-flowern golden a
jikinsa(leshin Amare), ɗinkin dogon riga ne wan da yayi mugun bin jikinta ya zauna mata ɗasss!, Banafsha
bata son makeup dan haka simple aka mata kawai, aka aje mata wata shegiyar ɗauri, ta sanya sarƙan da
Alhaji ya kawo mata na gold da komansa, idan ka ga irin kyawun da Banafsha tayi ba hmmn, ba'a magana
kawai fan's, amma Banafsha ta haɗu iya haɗuwa, ta kashe su ta bada kala ta raya wanka, ta suturta kyau
yan da ya kamata, tun da aka gama kuwa sai pictures suke yi, har Mami ita ma ta fito da nata shirin cikin
wani haɗaɗɗen yadi mai laushi da ƙamshi, ita ma nata ɗinkin dogon riga ne, fan's uwa da ƴan duk sun yi
kyau sai sambarka da fatan Allah ba da zaman lafiya.

Umaima ma fa ba'a bar ta a baya ba, dan ƙawar Amarya ma Amarya ce, Umaima ta haɗe ta cakare ta sha
kyawunta kaman ita ce Amaryan, sai photuna kawai suke yi da sauran freind's, Mami magana ta yi wa
Banafsha akan zuwa anjima za su yi magana kamun a kai ta, Banafsha tun da Mami ta faɗi haka shikkenan
yanayinta ya fara sauyawa, ta fara tuna za ta rabu da Maminta, za su yi nisa, duk shagalin da ake kawai
dauriya take yi.



⭐⭐

Su Alhaji suna isowa suka haɗu da su Abbaa, nan aka dinga musabaha aka shige masallaci, General dai tun
da ya zo garin ya ji ya burgesa.

ACM Bunayd, da su Abeed da abokansu suna nasu gefen, bai kula da Abbaa ba, shi ma bai kula da shi ba,
haka su ya Sadeeq, kamun dai a shiga sallah cikin ikon Allah sai ga Dr Arshan, sosai yayi mamakin ganin
Bunayd, dan ya gane sa, nan suka gaisa cikin fara'a (kunsan Bunayd bai cika baƙin hali ba).

Dr Arshan yana ganin Abeed ya gane shi ne patient nasa tun ba'a faɗa masa ba, ya jiki ya tambaya suka
gaisa kaman abokanan da suka jima da sanin juna, Dr Arshan dai bai tambayesu me kuma suka zo yi Mubi
ba duk da ya san daga Kano dai suke, bari yayi akan ko an ƙara dawo da aikinsu nan ne, ko da ya tuno
Banafsha mutumiyar Soja, nan ya dinga dariya ya na faɗin Bunayd bai tambayi mutumiyar sa ba.
ACM ɓata fiska yayi, wai ya daina haɗa sa da idiot ɗin can, dan shi ko sunanta bai sani ba, Abeed kasa
kunne yake ya ji me ake ciki, yana jin maganan mace ne tuni ya amsa yana dariya, yana faɗin Dr Arshan ya
taimaka ya basa labari, Dr Arshan amsawa yayi akan zai basa amma sai sun fito sallah.

Nan suka shige masallacin su ma, suka bi sahu aka ta da sallah, Masha Allah, Allah ya ƙarawa musulunci
ɗaukaka, alfarman Rasulullahi SAW, wato idan ka ga taron jama'a yan da ake sallahn juma'a kaɗai abin
burgewane, ba ma sai an kai ga sallahn idi ba, alhamdulillahi bini'imatul Islam.


ME KUKE TUNANI DAI DA WANGA AURE NA MALAM ABBO DA MALAMA BANAFSHA?
FINALLY DAI ZA MU JI LABARIN MAMI, WACECE MAMI DA HAR TA RIƘE KARUWANCI A MASTAYIN SANA'A,
MENENE SANADI? ME SILA? ME YA JA? DUK SABODA ME? TANA DA DALILI KUWA KO SON ZUCIYA NE?
KUMA WAYE MAHAIFIN BANAFSHA?
MUJE ZUWA FAN'S.


NAN NE ƘARSHEN BOOK 1

SAI MUN HAƊU A BOOK 2 DA YARDAN ALLAH.

UWAR BATOORL ✍️


# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735

# ������
# � &
# ���

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login