Showing 9001 words to 12000 words out of 111817 words
Chapter 4 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf
ta ce, "Ummu wallahi ya Danish ne ya biyo ni."
Kaɗa kai kawai Ummu tayi ta ce, "Nasan za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya, to Allah ya kyauta kawai,
Danish ko kaɗan baya ji bansan me Banafsha ta ci masa ba, dan nasan ba zai wuce dan ita ya biyo ki ba,
wuce kije ki huta ki ɗiba abinci a kitchen ki ci, shi kuma zai shigo ya same ni."
Amsawa Umaima tayi ta wuce cikin ɗakinsu ta sauya kaya ta watsa ruwa tayi sallah sannan ta ɗibo abinci
ta dawo palourn tana ci tana kallo sai ga Nana ta shigo, kallonta tayi ta ce, "Ke kuma daga ina?"
"Tayani tambayan ta dai", faɗin Ummu da ke zaune ita ma tana kallon.
Nana tura baki tayi ta ce, "Daga gidan babban yaya nake", tana faɗa ta wuce ɗakin su.
Ni kuwa ina shiga gidamu na tarar Mamina tana shanya kaya na da ta gama wanke wa, rungumeta nayi na
ce, "Sannu da aiki Mamina, maimakon ki bari idan na dawo nayi ko da gobe ne tunda bamu da class."
"Parrot daga dawowa sai surutu wuce ciki ai na gama wankin" faɗin Mamina tana min murmushinta mai
stada.
Nima murmushin nayi na shige ciki ina jin farin ciki haka kawai bansan dalili ba, Uniform nawa na cire
sannan na fito palourn namu na tarar komai a gyare staff ko ina sai tashin ƙamshi yake kawai, "Uhmn!
Mamina kenan ga tsafta ga son ƙamshi, ga kuma kyau Allah barmun ke Uwata ya kuma dai-daita
rayuwarmu", abinda na faɗa kenan na wuce kitchen namu, abinci na ɗibo shinkafa da miya da ya ji ice-fish
ga coslow a gefe, ɗan kaɗan na ɗibo kaman an roƙo, wanda ko yaro aka bawa zai cinye tass bai ƙoshi ba,
na dawo palour na zauna ina addu'an kar Mamina ta shigo ban fara ci ba ta gane ban ɗibo da yawa ba.
Nasa cokali zan fara ci sai kawai Mami ta shigo, rau-rau nayi da idanuwa na kana gani kaga na mara
gaskiya, kallo ɗaya Mami tamini da ni da plate ɗin dake gabana ta girgiza kai ta wuce ɗakin ta bata ce
komai ba, ganin ta shiga ɗaki da mugun sauri nima nayi nawa dakin, naci abincin na sha ruwa sannan na
tashi na ɗauro alwala nayi sallahn azahar.
Kyautan da Alhaji ya kawo min na jida na kai wa Mamina, nan ta dinga jin daɗi tana masa addu'a, sai ta ce,
"Yauwa BANAFSHA kinga ma kin tuno min, dama ya ce na tambaya makarantar ku ana musabaƙa ne ko
kuwa ba kwa yi, in bakwa yi sai a sanja miki wai dan musabaƙa na ƙara sa yaro zama mai hazaƙa da
ƙoƙari."
"Uhmn! Mami nifa ban cika son musabaƙan nan bane, dan ana ce masa wai karatun riya ko kuma gasar
karatu wanda aka maida shi tamkar abin jan fitina, a makarantar mu ana yi nice kawai bana so dan
kwanaki ma Umaima ta ce mu yi naƙi, duk da kuwa malaman na zaɓan mu, amma sai mu bada uzuri."
Murmushi Mami tayi ta ce, "Eh tom kinga dai cewa kika yi wasu ne suke faɗin hakan, ba wai duka mutanen
duniya ke faɗa ba, amma yanzu ke a me kika ɗauki musabaƙa akan ra'ayinki?"
"Ni Mami na ɗauke sa tamkar dai wata hanya da dama da ake bawa ɗalibi dan ganin yan inganta
karatunsa, a zahiri za kayi karatu ne dan kar ka faɗi amma a ainafin niyar abun an saka shi ne dan ka ƙara
mai da hankali akan karatu."
"Yauwa yarinyar kirki Nana Faɗima batoorler, kin fahimta da kyau haka nake so dama ako da yaushe
tunanin ki yasha ban-ban da na sauran mutane, ta ko wacce siga ki kasance kin ɗauko halayyan mai
sunanki, abinda nake so ki ƙara akan wannan tunanin naki shi ne ki ɗauko hadisi na farko a cikin arba'una
Hadith ki ƙara a kai."
Kallon Mamina nayi na ce, "Mami hadisin na nufin dai komai ana yin sa ne da niya kuma komai kayi yana
tafiya ne da niyan ka."
"Good girl! Kinga kuwa ashe in kika ƙuduri naki niyan daban ba dan riya ba ko gasa kinga ke daban saura
daban, Allah subhanahu wata'ala yace "muna duba ne zuwa ga zuqatan ku ba jikkunanku ba" kinga kuwa
abinda ka ƙudurta a zuciyanka shi ne abu na musamman da Allah zai tuhume ka akai."
Murmushi nayi cikin gamsuwa da zancen Mami na na ce, "Shikkenan Mami, na fahimta in Allah ya yarda
zan gyara niya na."
"Yauwa ina so wani musabaƙan ya zama da ke aciki, sannan ki dage ta yanda al'umman Annabi SAW za
suyi alfahari da haihuwanki, ki kulle idonki ki toshe kunnenki kawai ki fuskanci abinda kika sa a gaba inhar
dai bai saɓawa mahaliccin ki ba, ki kula sosai a ko ina ki riƙe mutuncin kanki dan shi ne ƙimarki da darajarki
a gidan mijinki, Allah ya miki albarka ya albarkaci dukkan rayuwanki FAƊIMAH."
Duk maganan da Mamina ke yi idanuwa na kan ta ina kallon ta ina mamaki a zuciyata da lamarin Mamina,
anya lafiya? Mamina tana da ilimin boko da Arabic fiye da tunani na, Mami tasan hukuncin ko wanni laifi
da ayar da aka sauƙe hukuncin barin ma dai Zina, amma me yasa Mami na ta zaɓi rayuwar karuwanci? Me
yasa ta zaɓi take sanin ta? Me yasa ta kauda kai akan ayar Allah? Ta zaɓi zubar mana da mutunci akan
adana mana shi, sannan sai tace na riqe mutunci na, koma dai menene addu'a ita ce maganin ko wacce
iriyar cuta da musiban rayuwa, in Allah ya yarda ni kuma zan dage da kai kukana ga Allah na dage da
addu'a...
Maganan da Mamina ke yi shi ya dawar da ni daga duniyan zancen-zuci zuci da na faɗa, "Banafsha me kike
tunani haka? Cewar Mamina idanuwanta a kai na.
Buɗe baki na yi da niyan faɗa mata amma sai na kasa kawai na ce, "Mami ina tunanin assignment da aka
bamu ne gashi hangout na yana wajan Umaima."
"To maza tashi kije ki karɓo daga nan ki gaida min Ummun ku."
Miƙewa nayi na tafi ɗakina dan saka hijab amma ina shiga ganin mayafin dogon rigan material dake jikina
sai na fasa ɗaukan hijab, na ɗau mayafin tunda dai gidan su Umaima kawai zan je.
Ina fitowa Mami ta kalle ni ganin mayafi na saka ba hijab ba sai tace "Banafsha ke kuma ina za ki da mayafi
ba hijabi?"
"Mami Allah ba inda zan je, iyakaci na gidan su Umaima kuma ina karɓa zan dawo."
Mamina ta ce, "Amma dai kinsan gidan su Umaima ba su kaɗai bane ko, kinsan akwai maza ba iya mata ba
ne, kuma ba muharramanki ba, yanzu ko muharraminka ma ba ko wani irin shiga ake so ka yi ya gani ba
balle wanda ba muharraminka ba, maza koma ki sako hijabinki bana son shirme, yarinya ta girma bata san
ya girma ba."
Marairaicewa nayi na ce, "Allah yanzun nan zan dawo Mamina."
"Tom maza kiyi sauri ki dawo, kinsan ba son fitanki da mayafi nake ba tunda kema kinsan ƙirar da Allah ya
miki yarinyar fuk-fuk kaman kazar gona."
Murmushi nayi kawai na fice tun da dai ta barni na tafi hakan, amma inajin kunya dan nasan nufin Mami,
Allah ya wadata ni da arziqin mazaunai wanda kaga ƙuguna ka ranste nasan maza, ƙirji na kuwa Masha
Allah dan suma Allah ya azurta ni da su, shiyasa Mamina idan ta tashi take cemun kazar gona (brolas)
fuk-fuk, ga shi idan ina tafiya komai na jikina mostawa yake, kuma dai ba rigima nake ba haka Allah yayo ni.
Da sallama na tura ƙofan gidan na shiga, kaina a qasa na tunkari hanyan shiga babban palourn gidan, ban
ankare ba kawai na ji ni nayi karo da mutum, nayi baya zan faɗi haka wanda muka yi karon nan ko ya
hanani faɗuwan ta hanyan tare ni, sai da na zauna da ɗuwawuna daɓass a ƙasa.
Ƴar ƙaramar ƙara na saki na ce, "Washh! Wayyo Allah!! Mamina mazaunaina sun yi targaɗe."
Stakin da aka ja shi ya sanya ni dawowa hayyacina, na ɗago fiska a hasale cikin tarin taƙaici da masifa, duk
da ganin wanda muka yi karo da shi ɗin amma hakan bai sanya ni shanye haushin tsakin da yamun ba, da
ƙyar na miƙe ina riƙe ƙugu na ce, "Mstww!! Mutun ba abinda ya iya sai son taɓawa mutane jiki wai ahakan
shi kamemme ne kuma nagari, to kai ɗin ma dai ba wani na kirki ba ne", ina gama faɗa na yayiɓo mayafina
da yayi gefe na miƙe zan wuce amma sai ya yi saurin shan gaba na yana ƙaremun kallo sama da ƙasa.
Tufar da yawu yayi sannan ya ce, "ƙaramar ƴar iska ba ki da abinda zan kalla ma balle na taɓa."
Hararansa nayi cikin ɓacin ran abinda ya mini, nima na tufar da yawu kaman yanda ya yi, amma yawuna
direct sai akan takalmin sa, na murguɗa masa baki tare da harara na ce, "Alhamdulillahi tunda ni ƙaramar
ƴar iska ce, kai kuma sannu babban ɗan iska mai digiri mai son taɓa mata to wallahi dan kaji Banafsha
ƙwalelen ka ce, dan ni ba irin su bane nafi ƙarfinka, sai gani sai hange daga nesa, ƙwalelen biri da hantar
kura."
A zuciye Ya Danish ya ɗaga hannu da niyan sauƙe mini mari, har na runste ido ina jiran sauƙan mari sai
muryan Ummu ne ya sauƙa a kunnenmu, wanda yayi nasaran tsayar da shi Allah ya taimake ni, cikin ɓacin
rai ya juya yabar wajan yana min kallon da nasan fassaransa bai wuce karki sake mu haɗu ba ne.
Ummu ƙarasowa tayi ta ce, "Banafsha mai Danish ya miki? Naji ihunki."
Tura baki nayi na faɗawa Ummu yanda aka yi, nan ta ƙara bani haƙuri ta ja hannuna muka shige cikin gidan
ina ji a raina kaman na koma na ƙarisa gaya masa maganan dake rai na tunda shi ya ce babban ɗan iska ne
shi, ni ba ruwana ka gayamun A na ƙarisa maka har Z, bancika magana ba amma aka taɓoni antaɓo
stuliyan dodo, ba wani kirki bane da ni, na iya tijara sosai.
Umaima da ta shigo palourn hannun ta riƙe da wayar Ummu da ake ƙira, miƙa mata tayi Ummu ta amsa
tayi ɗakinta ita kuma ta zauna gefe na tana cewa, "Masoyiya me ya faru?"
Hararanta nayi na ce wannan mugun yayan naku mana shi yasa nayi targaɗe a mazaunaina, yanzu har ji
nake sunamun ciwo, kuma Allah sai na rama."
Umaima da ta fahimci wanda nake nufi sai tayi murmushi ta ce, "ya Danish ba shi da kirki ko kaɗan nima
ɗazu saura kaɗan ya sanya ni na rasa haƙora na wai akan ya ganmu tare, bansan me kika tsare masa ba
wallahi ya cika takura."
Taɓe baki nayi nace "oho masa kuma haka zai ganni ya barni dan ni muruccin kam duste ne atou, kuma in
bai da kirki ne nima ban da shi, ni ko mutunci ma ban da shi, idanuna ba ruwa sai na masa stirara tsaff idan
yayi wasa, dan ba kunyan ganinsa ba wando zan yi ba, ai shi ya nema, wa ya ce ya ƙirani yar iska,ya ce ƴar
karuwa hakan bai ishesa ba sai ya ƙara da ƴar iska, to wataƙila dai da shi na taɓa iskancin."
Umaima tana dariyan maganana ta ce, "Masoyiya ko dan ya ganki ba hijabi ne ya rikice har ya sanya kika
targaɗa mazaunanki? Ya ga kaya" ta ƙarishe maganan tana wani dariyan.
***
INA KUKE MASU SANA'A, SANA'A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE
DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana'ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai
tallata haja, a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
07015870735
WhatsApp ko call
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com
Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo
#
# &
#
'YAR KARUWA
Officially
Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)
SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)
TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma ɗaukacin member's namu.
PAGE NAKU NE
Mrs Isham
Maman Abdallah(mutan Nijar)
Autar Marubuta
Ɓingel kabi
مهللا ىلص و ملس ىلع ديس ان هللوسر SAW
️ 16 _ 20
Hararanta nayi na ce "Munafuka mai ƙarawa wuta fetur, to ni me ma ya fito a jikina da za'a gani? Uhmñ!
Inma dai hakan ne to ya sani ƙwalelensa ya gani, wannan jikin yafi ƙarfin wanda bai iya sarrafa kalaman
bakinsa ba, banda lokacin maza balle irinsa mata-maza, mstwwww! Za ki sa ma raina ya ɓaci wallahi" na
faɗa ina kai mata bugun wasa a cinya.
Umaima na dariya ta ce, "Auchh! mai targaɗe a mazaunai nima targaɗa mini cinya za kiyi ne, ki cuci mijina
da yarana? Ayi haquri a mana afuwa ni da yayana kar ran masoyiya ya ɓaci, yanzu dai ya Maminmu take?"
"Mami na can gidanta, ita ma kinsanta da zuciya yanzuma sai da nace assignment aka bamu, hangout
nawa na hannunki kamun ta barni na shigo, kuma kaman tasan mugun nan yana gari, fa shi na mata ƙarya
kuma Allah ya kama ni, Allah na tuba.
Umaima ta murmusa ta ce, "Ya Danish ai sai shiriyan Allah, yanzu dai tashi muje na gaisar da Mami kamun
sai mu wuce wajan gadan kwaccam yin aikan Ummu, dan tsakanin yau da dare ko gobe da safe Umma da
Abba za su dawo kuma kinsan da safe muna zuwa Tahfiz."
Taɓe baki nayi ban ce komai ba na miƙe ina faɗin "mu tafi to."
Umaima ɗauko mayafi tayi ta yafa ta nufi hanyan fita tana cewa, "Masoyiya mu tafi kuma kin staya?.
Konawa nayi na zauna ban ce komai ba, sai Umaima ta ce, "Banafshaty zaman me kuma? Ko dai har yanzu
mazaunan ne?"
Hararanta nayi na ce, "Yanzu ke dai kinsan ba da mayafi za mu fita ba to me na saka mayafi? Ki koma ki
sako hijabi nima muna zuwa gidan Mami zan sanja dan tun daga gida ya Danish yamin rashin mutunci,
idan na fita kam nasan sai an kusa jefeni a tsaye."
Umaima babu musu ta juya ta koma ta sako hijabi har ƙasa kamun nan na miƙe muka fice a palourn, duk
sauri-sauri muke dan kar ya Danish ya ganmu domin staff zai hana mu fita tare, Allah ya taimake mu har
muka fice a gidan bamu gansa ba, daa sallama muka shiga gidan Mami amma ba kowa a palourn dan haka
ɗakin Mami muka nufa, kamun mu ƙarisa ɗakin sai Mami ta fito tana murmushi ganinmu tare.
"Yar Mami an sakoki gaba sai kinyi rakiya ko?" Mami ta faɗa tana kallon Umaima.
Murmushi Umaima tayi ta ce, "A'a Mami nice na ce zan zo gaishe da Maminmu."
Mami ta ce, "To Allah ya miki albarka ƴar Mami."
Tura baki nayi na ce, "Mami albarkan ita kaɗai banda ni?"
Umaima dariya ta sanya tana kallona ta ce, "Masoyiya ashe mun koma kishiyoyi?"
Hararan ta nayi na marairaice ina kallon Mami, amma Mami ko kallona bata yi ba ta ƙaraso palourn, nan
muka zauna Mami na ƙara tambayan mu game da karatu.
Can ganin lokaci na tafiya sai na dubi Umaima na mata magana aikanmu da Ummu ta yi.
Mami kallon ikon Allah take ta ce, "Yaran nan dama Ummun ku ta aike ku kuka tsaya aikin surutu baku tafi
ba? To Allah yasa ta zane ku maza-maza ku tashi kuje kar Magrib ya same ku a waje."
Miƙewa muka yi na ɗauko hijabi na muka fice a gidan muka nufi shagunan kan gadan kwaccam, muna
tafiya muna hira, ina murmushi na ce, "Umaima, Mami dai ta ce musabaƙan wannan shekara ayi da mu."
Duk da akan hanya muke amma farin cikin Umaima bai ɓoye ba kaman ta ɗaga ni sama haka ta dinga
murmushi, har da ɗan tsallenta ta ce, "Kai amma Allah dai ya bar mana Maminmu, Alhamdulillahi tayi
convincing naki yanzu kam kin cire wannan banzan ra'ayin naki, in Allah ya yarda kuwa bana da mu za'a je
Makka dan sai mun lashe."
Hararanta nayi na ce "Yanzu kin ga irinta ko, ba zaki ce bana sai mun haɗa ba wai da mu za'a je Makka,
yanzu damuwanki kyautan da zaki samu ba karatun ki ba ko?"
Umaima ta ce, "Uhmn! Masoyiya ba zaki gane ba, tabbas inaso karatu na ya kammalu zuwa yanzu ya
kamata ace mun haɗa, amma ina buƙatar zuwa Makka sosai dan akwai kukokin da nake so na kai wa
Ubangiji na a ƙasa mai starki duk da anan ɗin ma ina yi kuma bana cire ran yana amsuwa amma can ɗin
daban ne, sannan na kai ziyara ga ma'aiki SAW a madinatu.'
Idanuwa nane suka kawo ƙwalla jin abinda Umaima ta faɗa, domin kuwa ni ce na