Showing 15001 words to 18000 words out of 111817 words

Chapter 6 - 'YAR KARUWA Book 1 by Uwar Batoorl.pdf

Advertisement

16 Aug 2025

4074

sauqin gaske, sai kunzooooooo🤊

# ����𝙚��
# 𝙇�𝙠𝙚 &
# ��𝙖�𝙚


👄'YAR KARUWA👄💅

Officially

�𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)



SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)


TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma É—aukacin member's namu.


PAGE NAKU NE

Dr seeyath (besty lurv)
Heartbeat (ukhtynh)
Deejatou na Marubuciyar sarauniyar kyau.


مهللا ىلص و ملس ىلع ديس ان هللوسر SAW 🖤


í ¼íµ¿ï¸ 21 _ 25


Lumshe idanuwana nayi, muka haÉ—a baki duka wajan amsa sallaman su Abbaa.
Nana dake zaune a gefena tashuwa tayi da gudu ta nufi wajan Abba ta rungume sa tana faÉ—in, "Sannu da
dawowa Abba na."

Abbaa murmushi yayi ya ce, "Yauwá maman Abbaa sannunku ko", mayar da kallonsa yayi kan mu ni da
Umaima ya ce, "Ummul-khultum da FaÉ—imah babu yiwa Abbaa oyoyo ko? Yanzu kam yarana sun girma
sun zama budurwaye, an daina mini oyoyo" ya faÉ—a yana sakar mana murmushi.

Cikin jin kunya nayi ƙasa da kai na ina murmushi, Umaima ma murmushin tayi muka haɗa baki wajan
cewa, "Abbaa sannu da dawowa."

"Yauwá ƴan biyun Abbaa, ƴan albarka sannunku ko."

Ummu idanuwanta akan mijinta ta ce, "Alhaji in dai ka biye musu ba za ka huta ba fa."

Murmusawa Abbaa yayi, ya miƙe ya nufi ɗakin Ummu ita ma ta tashi ta mara masa baya, Umma Sabeera
taɓe baki tayi ta bi Ummu da kallon banza, sannan ta juyo kanmu, amma kamun tayi magana muka haɗa
baki har da Nana muka ce, "Umma sannu da dawowa."

Umma wani dogon tsaki ta ja ta ce, "mstwwww! Iyayen kalen dangi, Allah ya rufamin asiri na zama uwarki
tun da dai ni ba karuwa ba ce" ta ƙarishe maganan kaman tana yi da sa'arta ba sa'ar ƴar cikinta ba.

Ni kuma a take naji raina ya ɓaci, sai naji gidan ya gundure ni ma, miƙewa nayi zan fice ba tare da na kuma
yin ko tari ba, sai Umaima ta tashi ta riƙo hannuna kamun ta buɗe baki ta yi magana, Umma ta rigata ta ce,
"Umaima kika kuskura kika ƙara taka ƙafanki kin ji waallahi to sai nayi mugun saɓa miki, shashasha kawai
mara zuciya."
Umaima tura baki ta yi, da yake shagwaɓaɓɓiya ce sosai har da ɗan buga ƙafanta ta ce, "Masoyiya kiyi
haƙuri kinji, ki dawo mu zauna."

Kallonta nayi da idanuwana da har sun tara ƙwalla na ce, "A'a Umaima, ki ji maganan Umma, nima gida
zan tafi dare tayi", ina gama faÉ—an haka na juya ina danne hawayena.
Umaima biyo ni tayi ban sani ba, muna zuwa dai-dai bakin ƙofa kawai na ji sauƙan mari, ina ɗagowa naga
Umaima ta dafe fiskanta, cikin ranaza duka muka kalli wanda ya mare ta, ashe ya Danish tare da su Umma
ya shigo, duk abinda ya faru akan idonsa, daman yana staye a bakin ƙofan yana jin mu, haushinsa da
tausayin Umaima ne ya rufe ni, na ƙwace hannuna a riƙon da Umaima ta mini, na fice da gudu dan muddin
na staya to zan iya ramawa Umaima ko da kuwa kashe ni Ya Danish zai yi.

Umma tsaki taja ta ce, "Ka mini dai-dai Danish, Allah ya maka albarka, ke kuma dan ubanki wuce ciki tun
da ita ba ƙanwar uwarki ba ce, munafukan yarinya sai liƙewa ƴar karuwa mara tarbiyya take yi, dan son
zubarwa mutane mutunci, shashashar yarinya kawai."

Da gudu Umaima ta wuce É—akinsu tana kuka, Umma ganin ya Danish ya fice sai ta wuce nata É—akin ita ma,
tana hararan É—akin Ummu.

Ya Danish kuwa ashe bin bayana yayi, amma ya tarar na jima da shigewa gidanmu, sai guntun tsakin da
yaja ya ce, "Wallahi da na kama ki cikin daren nan zan gwada miki digiri na a iskanci, ni É—in babban É—an
iska ne, amma babu komai, muddin kura na yawo zabo na yawo to watarana za'a haÉ—u, sai na tabbatar na
gyara miki zama."
Ina shiga gidanmu na share hawayena na kuma seta kai na, ba tare da na ƙarewa palourn kallo ba na wuce
cikin ɗakina, dan bana ƙaunar ƙara wani mummunan ganin irin na ɗazu.

Washegari da ya kama asabar da sassafe na gama duk ayyukan da zan yi, ganin Mami bata fito ba cikin
taƙaici na fice a gidan ban tunkari ɗakinta ba, dan nasan rashin fitowan ta ba zai wuce tana tare da yaron
da na gansu tare jiya ba.

Ina fitowa na nufi gidan su Umaima dan mu wuce Tahfiz, amma sai na haɗu da Abbaa a ƙofa yana ƙoƙarin
fitowa, ganinsa sai na tsugunna na ce, "Ina kwana Abbaa."

Abba na murmushi ya ce, "lafiya Alhamdulillahi FaÉ—imah, ina kika tsaya haka baki tafi makaranta ba har
yanzu?"

"Uhmm! Abbaa na tsaya aiki ne, kuma na biyowa Umaima mu tafi tare ne."

Abbaa murmushi yayi ya ce, "Ai Ummul-khultum ta jima a makaranta FaÉ—ima, ina ji Mamana ma yanzu ta
fitaba jimawa."

Miƙewa nayi na ce, "To Abbaa sai mun dawo."

"A dawo lafiya FaÉ—ima, Allah ya taimaka ya ba da sa'a."

Da "Ameen" na amsa na wuce cikin sauri, dan ina storon dukan latti.

Ban bi kan kwalta ba sai nabi ta cikin anguwa duk da kuwa nasan da sassafen nan kam iyayen sa ido basu
zauna ba, tunda tukunna yanzu safiya ne, ina isa makaranta na hangi Nana tana shiga ajinsu, nima ajinmu
na wuce na shiga da sallama inda na tarar ko malam bai shigo ba, hamdala nayi sannan na nufi kujeran da
muke zama da Umaima na samawa kai na mazauni, na dubi Umaima na ce, "Sabahul khair ya Aminiyaty."
Murmushi tayi ta rungumeni ta ce, "Masoyiya yau kuma Æ´ar larabci ne tun malam bai shigo ba?"

"Na'am yau larabce malam za muyi, me yasa kika taho kika barni amma?" Na faÉ—a ina hararanta da
manyan idanuwa na.

"Banafshaty wallahi ke dai kin sani, labarin gizo ba ya wuce na ƙoƙi, in dai ya Danish na gari to fa sai dai
haƙuri za muyi, Umma ce ta sanya ya sako ni gaba dan kar na biya miki, to da muka zo gada ya juya nima
sai na juya aikam muka ci karo da shi, nan ya rakoni a guje na ƙariso har cikin makarantar nan" faɗin
Umaima tana tura baki kaman ya Danish É—in ko Umma wani yana kallonta.
Na buÉ—e baki zan yi magana sai malam ya shigo, nan muka dinga gaishe sa shi cikin harshen larabci shima
yana amsa mana da larabcin.

Malam Abbo nan ya sa muka yi muraja'a aka fara karɓan hadda, kusan sai da rabin ajin suka bada hadda
kamun aka iso kan mu, Umaima ce ta fara rero nata karatun cikin zazzaƙar muryanta har ta idar ita ma ba
ɓata ko ɗaya, sai kabbara kawai ake yi, tana gamawa malam ya dube ni ya ce, "Bismillah malama Faɗimah
Sufyan."
Sanin idan an ƙira sunan mutum an iso kan sa kenan, sai na gyara zama na nayi ƙasa da kai na, na fara
rero haddan Suratul Taubah, karatu nake cikin muryana mai sanyawa mai sauraro nistuwa inda ba iya Æ´an
ajin ba hatta Malamin namu in dai zan yi karatu to idanuwan sa na kai na, sai da na kai ayaa sannan na
share hawayen dake idanuwana dan ayoyin cikin Suratul Taubah in kasan fassaran su to dole jikinka yayi
sanyi duk da wani sashin nata akan kafirai masu munafurtan Addinin Allah suke, wani gefen kuma akan
yaƙin Manzon Allah SAW ne.

Malam Abbo har nayi shiru idanuwan sa na kaina, sannan ya cigaba da ƙiran sunan sauran ana bada
hadda har dai muka gama karatun.

Bayan ya ƙara mana mun maimaita sai ya fita, nan malamin Tauhidi ya shigo, bayan ya fita shi ma
malamin da ke É—aukan mu Hadith ya shigo.

Tun ƙarfe 6:30am da muka je makaranta mu ne ba'a tashemu ba sai ƙarfe 10:30am.

Ana tashi ni da Umaima sai bamu tafi ba muka nufi office na Malam Abbo, sallama muka yi da neman
izinin shiga sannan ya umurce mu da mu shigo, durƙusawa muka yi duka, amma sai ya mana nuni da
kujera nan muka zauna, sai da ya gama haÉ—a litattafan gabansa kamun ya É—ago ya kallemu, da larabci ya
ce, "lafia kuwa?"
Ƙasa nayi da kai na sannan na fara koro masa bayani akan musabaƙa, kallona yayi ya ce, "Faɗimah ai kun
makara sai dai na gaba kuma, tun farko kun nuna ba za kuyi ba wanda dama dan na saka baki shiyasa aka
barku a makarantar ba'a kore ku ba, sai dai ku bari na wani shekaran, domin waÉ—anda suka yi yanzu, su
za'a je na gari da gari da su."
Marairaice wa nayi kaman zan yi kuka, nan muka dinga basa haƙuri, dan munsan Malam Abbo in yayi
magana dole a saka mu a masu yi, ba wani babba ba ne shi amma kuma ana ji da shi a malaman
makarantan saboda iliminsa, numfasawa yayi ya ce, "Shikkenan zan yi iya ƙoƙarina naga anyi da ku in Allah
ya yarda, amma fa sai kun ƙara dagewa da muraja'a, dan an jima da yin nisa a karatun da ya shafi

musabaƙan, muddin kuna buƙatan a yi da ku to sai kun dage dan a maye gurbin waɗanda ba sa mayar da
hankali da ku."

Nan muka dinga godiya muka tabbatar masa da in Allah ya yarda za mu dage, ba za mu basa kunya ba,
sannan ya sallamemu muka tashi muka fito a office É—in, gaba É—aya makarantar muka bari muna farin ciki
dan duk mun saka rai akan wannan musabaƙa, sai addu'a muke kwarara wa malam Abbo.

Malam Abbo bin bayan su yayi da kallo yana murmushi, dan ya rasa dalili baya iya yiwa wannan yarinya
musu in za ta faÉ—i abu ko kuma idan abu ya shafe ta..., shigowan wani Malami ne ya dakatar da shi daga
tunanin da yake yi, yana murmushi.

Zama a kujeran dake kallon sa matashin malamin yayi ya ce, "Haydar na fa raba ka da maganan yarinyar
nan, kasan dai wacece mahaifiyar ta da kuma sana'ar ta ko?"

Malam Abbo na murmushi ya ce, "Zubair ko me na ce maka ba zaka fahimta ba, amma ina tausayin
yarinyar nan akan jarabawan rayuwa da suke ciki da mahaifiyar ta, kuma tsakani da Allah da aure nake
ƙaunar ta, sai dai a yanzu tana ɗalibata banjin zan iya furta mata, amma in Allah ya yarda muna yaye su
tunda ba zai wuce shekara guda ba zan bayyana mata komai a yi bikinmu akan lokaci da yardan Allah."
"Hmmn! haydar kenan, kana tunanin wannan yarinya ta dace da zamowa uwa ga yaranka? Kasan fa ance
zina bashi ce to baka tunanin laifin kaka ya shafi jikokinta?"

Malam Abbo hallau murmushin ya kuma yi ya ce, "Zubair ina sonta, ina ƙaunarta a haka, kuma in Allah ya
yarda ba wannan abu da kake fata, ita ma mahaifiyar nata Allah ya dai-daita al'amuranta ya shirya ta, in
Allah yasa FaÉ—imah rabon Aliyu haidar ce, kuma alkairi gare ni to Allah Ubangiji ya mallaka mini ita, ya
rabamu da sharrin masu sharri da masu mugayen magana irinka" ya ƙarishe maganan yana mai da kansa
kan takardun gabansa yana murmushi.

Malam Zubair taɓe baki yayi ya ce, "kayi nisa baka jin ƙira, kuma koma menene kai za ka jiyo."

"Sosaima in dai akan soyayyan Faɗimah-batoola ne, to bana jin komai ba ma iya ƙira ba, ban da mastala da
Ummi da kuma Malam duk nasan za su amince dan haka ma na fasa sai ta kammala makaranta, dan a bari
ya huce shi yake kawo rabon wani, dan haka ana kammala musabaƙa zan fito da buƙatata in Allah ya
yarda, kuma Insha Allahu zan samu karɓuwa."
Malam Zubair miƙewa yayi ya fice a office ɗin bai ce komai ba dan yana cike da haushin abokin nasa da ya
kasa fahimtar sa.

Malam Abbo kuma cigaba da dudduba takardun yayi, dan yana azumin kamawan sabon watan musulunci
dan haka sai yamma zai koma yayi wanka ya dawo kamun É—alibai sun zo tunda ranar weekend safe da
yamma ne makarantan nasu.

Cikin farinciki Umaima da Banafsha ke tafiya, Umaima ta ce, "heehuhuuu! wa ya ga su Ummu-khultum É—in
Abbaa an zama Hajiya, hhhh! Hajiya Umaima sama, Hajiya Umaima ƙasa, ai wallahi kullum cikin dariya
nake dan haƙori yayi ta qyalli, ga mu da wushirya dukanmu, ya kika hango mu masoyiya?"

Murmushi nayi na ce, "Kai Umaima kin cika zumuÉ—i wallahi, yanzu in bamu samu ba fa?"

Æata fiska Umaima tayi ta harareni ta ce, "Kai amma masoyiya a'uzubillah da wannan mugun fatan, ai in
Allah ya yarda mu ne za mu cinye, dan haka in Allah ya yarda zuwa Makka very soon, Madinatul
Munawwara is loading."

Kallonta nayi na ce, "Amma kinsan wannan na iya cikin Mubi ne ko? Ba lallai mu samu kujera ba, dama dai
na jiha da jiha ne ko kuwa ƙasa da ƙasa, wannan kam in Allah ya yarda za'a samu."

Murmushi Umaima tamun ta ce, "koma dai menene in Allah ya yarda mun kusa zuwa Makka...." Maganan
dake bakinta ne ya maƙale sakamakon abinda muka ji ana faɗa a bayanmu.

''ƳAR KARUWA ! Woooo!! 'YAR KARUWA!!! mai kyawun ɗan maciji, asa hijabi kaman musulman ƙwarai a
je makaranta da najasa a jiki, ake É—aukan Qur'ani wa ma ya sani ko malaman ma raba musu majalisar ake
yi, 'YAR KARUWA!! WOOOO!!!!"

Cikin taƙaici muka juyo dukanmu ni da Umaima, murmushin da yafi kuka ciwo ne ya ƙwacemini ganin
Garba ne ke maganan kuma ga yara kusan uku a gefen sa yana sanya su faÉ—in Æ´ar karuwa, suna taya shi yin
haukan nasa wanda a tunaninsa yayi dan ya ƙuntata mini ne, bai san yayi a banza ba domin a yanzu ina jin
zan iya danne zuciyata ko ma me za'a ce mini, saboda sosai na ji faÉ—an da Umaima ta mini.
Umaima za tayi magana sai na yi saurin taran numfashinta na ce, "Umaima ki ƙyale sa da ƙaramin
haukansa, dan ina fara magana ko kuwa kika tanka masa to wallahi sai na kwaÉ—a masa mari, kinsan halina,
muje kawai ki ƙyale sa."
Hannunta na kama muka ci gaba da tafiya ina mata hira kaman ba abinda ke damu na amma ita kuma
kana ganinta kasan ta sanya abun a rai, ni ake yiwa isgilin amma ita yake damu, Umaima tawa kenan, ina
mugun ƙaunarta.

Tun daga nesa da muka hango ya Danish tare da abokin sa na yi gefe, ganin bai ganmu ba sai nayi saurin
sake hannunta tayi gaba ina bin bayanta ina magana kaman taƙi kulani, saboda kada na ja mata faɗa duk
da sai da na lallaɓata, sannan ta yarda da hakan, ina binta a baya ina cewa, "haba Umaima me yasa ba zaki
staya mu tafi tare ba? Yau duk kin ƙi kula ni me na miki ne wai?" Har muka isa wajan da yake staye da abokinsa abinda nake faɗa kenan kuma da ƙarfi yanda zai iya jiyo
mu, Umaima da ke ƙunshe dariyanta, tana wuce su ta shige gida tana dariya har da kama ciki, idanuwansu
duka biyu na kai na har na iso dai-dai su ina magana, na nufi hanyan gidansu Umaima zan shiga sai ya
sakarmun wani gigitaccen stawa ya ce, "Keeeeeeeeeeeeeee...! Kar ki sake ki shigar mana gida, tunda kuna
da naku ɓace mana a gaban gida."

Murmushi nayi wanda ya kawar da damuwan dake raina sannan na juyo na tako har inda suke dan dama
ina da cikin sa, stayawa nayi a gabansa ba tare da na kalli abokin sa ba na ce, "Mai digiri a iskanci tun da ba
gidan ubanka kai kaÉ—ai bane sai na shiga, kuma Allah ya sa ma muma muna da gidan kai ma ka sani,
mtswwww!", Juyawa nayi na shige gidansu Umaima hankalina kwance, rai na fess na ci masa mutunci a
gaban abokinsa, shi ma yaji idan da daÉ—i.

Rai a mugun ɓace ya juya zai biyo ni amma ganin Abbaa sai ya fasa ya tsaya yana huci, ni kuwa ganin bai
biyo ni ba ko da na leƙo naga Abbaa na ƙofan ai cikin sauri na fito na wuce gidanmu dan dama na riga na
gaishe da Abbaa, kuma dan nasan Abbaa na gida shiyasa na masa haka, saboda ba zai taɓa bari ya taɓa ni
ba.
Abokinsa yana dariyan abinda ya faru ya ce, "Danish wacece yarinyar nan haka?"

Ya Danish wani mugun staki ya ja, cikin taƙaici da haushina ya ce, "Mtsww! Dauda ka yi shiru kar ka
tambayeni komai, Hmmn! Har ni yarinyar nan za ta dage da qira É—an iska bayan ga ta cikakkiya tunda
uwarta karuwa ce, to wallahi ni nasan abinda zan mata" ya Danish kaman zai daki babu haka ya dinga huci,
abokinsa sai dariya ya ke, shi kuma duk ya bi ya cika yayi fam kaÉ—an yake jira ya fashe.
Mun yi hutun weekend cikin kwanciyar hankali da farincikin kasancewanmj cikin masu musabaƙa, dan
kuwa Malam Abbo (haydar) ya tsaya mana komai da mu ake damawa, taƙaicin rayuwa kuwa ba abinda ya
ragu sai ma ƙaruwa dan bazan fita na dawo gida ba tare da an jefe ni da mugun magana ba, tsakanina da

ya Danish kuwa ba komai sai tarin stana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login