Showing 30001 words to 33000 words out of 78880 words

Chapter 11 - YAR KANCE free pages na Maman Abdallah.doc

dace da a ganta bawai Kance ba, sai dai abun tsoron shi ne dawa take tare?'', ylta faWa tana firfito da idanu kamar yana gabanta.

''Ina zaki je kuma? Kinga idan har Algeriya zaki je ki jira ni mu tafi tare, dan ni ma banga abinda zai zaunar dani a garin nan ba, dan da alama ba?ar shekara ce wannan'' Ado ya faWa yana mai tashi daga zaune da yake a ?asa, tare da karkaWe tsantsaman wandonsa.

''Ba wani jiranka da zan yi, kowa yaji da kansa, mun haWe acan kawai'' Balki ta yi maganar tare da yanke wayar, tana wani yatsina ba?ar fuskarta, wanda sai ka fuskanceta da kyau zaka ga hudajin hancinta, dan ba lallai ka iya gane ina karan hancinta yake ba.

Ta fi mintuna goma tsaye a wajan tana tunanin abun yi, murmushin samun mafita ta yi kafin ta cira ?afa ta nufi gida, ko kuma in ce in da runfarta yake.

Akwatin ajiyarta ta buWe, ta shiga lissafin kuWaWen da idan ka ga yawan su sai ka kama kai, ace maka kuma daga mace kamarta aka samesu sai kayi mamaki matu?a, ko ma ka?i yarda sam.


Kajarta ta buWe ta fara zuba wannan manyan kuWaWen, da yake dama a shirye suke, dan duk dare na Ubangiji sai tayi musu zaman kansu bayan ta Wora sababbin zuwa wanda ta samu a rana.


Kaja (wata aba ce da tsofaffi suka fi yawan yin anfani da ita, bayan maWinka sun Win ka ta da sauran zaben da aka yi Winki, ko kuma wanda aka siyo aka yayyanka kawai dan a yi su da yawa a inda aka maida yin nasu sana'a, akan Winkata ne kamar suffar Wan ?aramin bahu haka, daga ?arshe sai a saka masa zif dan rufewa da buWewa, kafin kuma a yi masa maWauri guda biyu dan Waurawa. Sukan Waura ta ne a ?ugunsu, ko in ce tsatso, a ?asan zanin su) to komai kwakwar mutun ba lallai ya ita ganin kuWin ba, bare har kuma ya yi maka sata, saSanin jakar hannu.



Biyawa ta yi ta bukkar mai wayar nan ta bata wayar ta, da ?ar jakar kayanta da ba zasu wuce site biyar ba a hannunta, tanbayar duniya babu wacce Badarriya bata yi mata ba akan ina za taje, amma sam ta?i yi mata bayani. Sam bata so kowa yasan in da ta tafi gudun Sacin rana, kar aje mutun yasha matsa ya saki baki da hanci ya zayyano bayananta da in da take, wannan shi ne dalilin ta na ?in bari kowa yasan da tafiyar data ?udurta aranta za ta yi mai nisan zango, dan hatta da hajiyar ?an Kance wato hajiyar Suwaiba bata faWa wa ba, ba kuma zata yi tafiyar ta hannunta ba, ita ma da kuWinta, da alfarmarta za ta yi anfani ta yi tafiyar ta.


Koda ta iso ?ofar shagon Awwalu haka ta ce ''to mu Allah ya yi mana tashi mun yi gaba, waya kuma mutum ya ri?e a lahira ya bani'', tana kai wa nan ta yi gaba abunta, da wani Wanga??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????lallen zaninta.

''Ai kuwa baki isa ba wallahi, ai abun kunya ne ma shari'a ta haWa ni dake a lahira, ungo akwalar wayarki'' yaron ya faWa yana wurga mata wayar.
Aka kuwa yi sa'a wani mai mashine yazo a gujensa, ya bi takan wayar abinsa ba tare daya sani ba.

Wata shegiyar dariya ta yi tare da faWin ''ai kam shari'a sai dai idan har ba zaka mutu in mutu ba, ai ni hannu da hannu na baka waya ta, kai kuma sai ka wullo mini ita, kaga banda shari'a akan ri?e mini waya har da zunubin yiwa babban gabanka rashin kunya.''

'Tuf! Ya tofar da yawu a gefen sa irin can da yawarkin nan, ita kuma kaWa kai ta yi ta tafiyarta.

Yafi mintuna biyar zaune akan bencin dake ?ofar shagon nasa, irin wanda ake tana da dan masu zaman ?ofar shago, ko kuma Wan bin layi yayin da aka taru wajan yin siyayya. Mi?ewa ya yi yaje ya tattaro ragargazaazzar wayar nan, leda ya samu ya zuba tarkace ya Waure ya jefa a kwandon ajiyarsa, a hakan ma yana gudurawa ransa sai ya yi mata rashin kirki a duk sanda yaga tazo koda wucewa ne ta ?ofar shagonsa.



Gidan Alhaji Muhammad Usmane

A hankali yake buga kofar daki. Cikin barcin ta mai cike da nishaWi take jin kamar ana buga kofar, ahankali ta ziroda ?afafuwanta daga kan gadon da ta cire shakka ta bararraje kafin barcin ya dauke.

Har takai bakin ?ofar, ta Wora hannunta akan key Win dake sar?afe da jikin kofar da nufin buWewa sai kuma ta tuna da wani abu.

Da sauri ta shiga kallon jikinta, doguwar riga ce a jikinta irin wacce ya siyo Wazu ba jimawa, shi ne yana fita ta kuma sanSalo wani wanka irin na akwai ruwa da sabulu din nan kafin rabi jikinta da wannan rigar.

Wata iriyar kunya taji ta rufe ta, wai kar ya ganta ba malulluSi a jikinta, tiri-titi ta yi tana neman wani abun da zata saka, amma sai ta rasa.

Da gudu ta koma bayi in da ta shanya hijabinta na wajan Rammatu da tazo gidan da shi a jikinta, bayan Wazu tana gwagwarmayar yin wanka duka ya ji?e, ita kuma sai ta ?arasa saka shi a ruwan ta murje shi, yanzun koda ta dauko shi da ?ar sauran leman shi, amma haka nan ta yarSa a jikinta tana nufo ?ofar Wakin a karo na biyu.

''Kina kusa kuwa? Ko dai kina barci ne'' Abdallah ya faWa yana mai kara kunnensa na Sangaren dama a jikin ?ofar, kamar wanda zai iya jiyo nunfashinta a tanan idan har ya tabbata barcin take yi kamar yadda ya yi zato.

Jin alamar tana buWe wa ne yasa ya Wan yi baya da plate Win sa a hannu, kanta a ?asa lokacin daya buWe, raSawa ta yi gefe ta bashi hanya domin shiga, ba musu kuwa ya shige tana bin bayansa daga baya.

A ?asan carpet Win nan yanzun ma ya ajiye abincin nan, tun daga ?afarta ya soma kallonta har izuwa fuskarta, da sauri ya kauda kai daga gare ta, dan wani shawarci mai kama da ya lura ko zai ga ta fara ?irgen dangi yazo masa a tunaninsa.

''Ki zauna mana'' ya faWa lokacin da shima ya ke zaman, tare da tan?ware ?afafuwansa kamar irin zaman cin abinci'n nan.

Juyawa ta yi ta kalli bakin ?ofa, sai ta ganta a buWe, tunda shi ya fara shigowa ai dama ita ya kamata a ce ta rufe.
Kafin ta gama wancan tunanin ta ke ta sakawa ?ofar key ta dawo.

A Wan nesa dashi kaWan ta zauna, tana wasa da gefen hijabinta, ''ki matsin ki ci abinci, wa ke na kawo shi Waki nan'', Wan shiru ta yi kafin ta cika umarninsa na farko, matsawar kusa dashi ta yi kamar yadda ya ce, sai dai a umarnin na biyu sai ta no?e kai ?asa, cikin sanyin muryarta ta ce ''bana jin yunwa fa, ai ban daWe da cin abinci ba'' ta faWa kanta a ?asa.

''?ago kanki ki kalle ni'' ya faWa lokacin da yake bude plate Win abincin.

A wannan karon kasa cika umarninsa ta yi, dan ba zata iya yarda su haWa ido haka da garaje ba akan kuskure ba.

Rintse ido ta yi ta buWe, ta kuma rintsewa kafin ta buWe, take jikinta ya hau karkarwa, haka kawai a bazata taga mutun a daf da ita da kurasar daya Wan goga.mata haWaWWiyar miyar da aka yi domin ta, bai kuma jira wani abun ba ya saka hannu ya tallafe kanta ta baya da Waya hannun, Waya kuma ya nufi bakinta da lumar abinci.

Sau ukutake buWe ido sai kuma ta rufe, da mi zata kira wannan abun? Shin ta karSa ko a'a, taga ana aure a cikin nan garin da ma garinsu, ma'aurata kan zauna gida Waya a Waki Waya duk tasan wannan, amma a taSa jikin mutum ya hallara wannan sanin ne batada shi, tunda ba wani makaranta ba take.

''Ki karSa mana'', taji muryarsa a cikin kunnen ta, dan sai da ya sauya dai-dai sautin kunnen kafin ya yi maganar.

Kuma rintse idon ta yi kafin ta buWe su akan farin hannunsa, ko a jajjayan buzayen da take gani a garin nan bata taSa ganin mai kalar fatan nan ba, su sauran garinsu m yakan sa Wan ja haka, amma shi sak fari ne mai yalwataccen kwantaccen gashin jikin Waya yawaita har a hannayensa, dan iya hannunta gani, da ace wani sashe na jikinsa ta gani to ba lallai ta iya magantuwa ba.

A hankali ta buWe bakin ya saka mata na farko, sai ta janyo plate Win da nufin sa hannunta dan ta ci da kanta. Amma sai girgiza mata kai ya yi, yana ?o?arin ciro wata gurasar ya ke faWin ''ai Waya ake yi dani yarinya, daga yanzun a duk sanda kika min gardama akan cin abinci to ni ne da hannuna zan baki shi, maza baWe baki'' ya kuma tunkararta da wata lomar.
Ba yadda ta iya haka ta buWe baki ta karSa, a haka har sai da ya bata gurasa biyu, yana shirin fasa ta ukun ya ji tana faWin ''dan Allah! Wallahi na ?oshi'', Wan murmushi ya yi kafin ya ce ''kin tabbata?'' Ya tambaye ta.

Kai kawai ta jinjina masa, ba tare da ya kuma ce mata komai ba ya rufe sauran abincin yana shirin mi?ewa.
''To kai fa? Naga baka ci ba'' ta yi maganar kamar ba ita ta yi ba, kanta a ?asa.

Kallonta ya yi kallo irin na ?urulla, kafin ya buWa baki da ce wa ''mai ya faru? Kin canja kaya kuma kika maida wannan hijab Win'', haka kawai ya samu kansa da faWar abinda ba akan maudu'insa ba suke.

Sadda kanta a ?asa ta yi abun yana ?ara bata kunya, can kuma sai ta Wago da nufin ta saci kallonsa, sai kuma aka yi rashin sa'a shima ita Win yake kallo, ai da sauri ta yi kasa da kanta.

''Uhum! Ina sauraron ki'' ya faWa yana mai kallon agogon dake Wakin.
''Eh na yi wanka ne, shi ne na saka Waya daga cikin kayan nan'', in jita da faWa.

''To maganar hijabin fa? Daga yanzu bana so idan har ba sallah ce za kiyi ba kina saka hijabi aka kawai, ki maida hankali sosai akan komai da zan ajiye miki, banasan wasa da ibada, ki tabbatar komai yana tafiya yadda ya dace, duk wani abinda babu ko wanda kike bu?atarsa to kanki tsaye ki faWa mini, Ni sunana Abdallah, kuma zaki iya kirana da sunana hakan shi ne dai-dai'' ya faWa yana mi?ewa da plate Winsa a hannunsa.

''In sha Allah'', wannan ita kalmar daya fito daga bakinta. Jinjina kai ya yi yana nufar kofar Wakin danufin fita, sai da ya kama mabuWin ?ofar kafin ya juyo yana ce wa ''zan ci abinci amma sai dai idan za'a ramawa Kura aniyarta'', ya faWa da wani tsadadden murmushi akan fuskarsa.

Da yake ita Win bahausa ce firrrrr, kuma ko mutum bai iya hausa ba idan har yana zaune dasu inna Balki to tabbas sai ya koyi yadda zai zagi ubansa a fakaice wannan ?a'ida ne.

Hannu tasa ta rufe fuskarta alamar ta ji kunya, shi kuma Abdallah ganin hakan ne yasa ya buWe ?ofar yana ?ar dariya ya fice.

Ta Wan jima anan zaune kafin ta tashi da nufin rufe Wakin, shi kuma a tacan ya tuna da bai kawo mata ruwa ba shi ne ya Wauko faro guda mai sanyi da nufin ya bata.

Dai-dai lokacin da ta buga ?ofar dan rufewa a dai-dai lokacin ya ziro kanshi domin shigowa, ai kuwa ji kake gum ta rafke masa goshi.

''Ash'' kawai ya faWa yana dafe wajan. Da hanzarin ta ?arasa buWe ?ofar tana rarraba ido, tama rasa miye za ta yi, cikin tashin hankali ta ce ''kayi ha?uri dan Allah, wallahi ban lura ba ne'' kamar za ta yi kuka haka ta yi maganar.

Ruwan ya mi?a mata yana shirin juyawa, da hannunsa dafe da goshi, tsak yaja ya tsaya jin ta ri?e masa tsintsiyar hannu, a hankali ya juyo yana kallonta, kanta a ?asa, sai wasa da babbar yatsar ?afarta ta dama da take yi a ?asa.

Sosai ya juyo ya fuskanceta, har yanzu bata saki hannun ba. Taku biyu zuwa uku tayi da baya, ya yin da shi kuma yake binta ta gaba, hannun nasa ta saki, ta dage ta Waga kai wai taga wajan da ta buga masa ?ofar.

''Subahanallahi'' ta faWa lokacin da taga har wajen ya Wan gunbura. ?aWWage ta fara yi wai tsawonta yakai in da zata ga wajan sosai.
Bisa umarnin zuciyarsa ya gurfanar da giuwarsa Waya a ?asa, ya yin daya to?are Wayar ?afar a ?asa ita ma.

''Yanzu zo ki duba ki gani'' ya faWa yana kamo hannunta zuwa gabansa.
Cike da kunya take kallon wajan, kafin da juriya da kuma tsantsar yarinta takai hannunta kan goshinsa, a hankali ta fara Wan murza wajen tana masa tofi a dai-dai wajen wai tana masa addu'a, irin yadda ake yiwa yara idan suka ji ciwo'n nan.

Wani abu mai kama da shau?i Abdallah ya fara ji atattare da yarinyar, babu shakka yanzun ya gama yardar wa kansa ce wa son yarinyar yake, kuma shi ne dalilin ma da yasa har ya kasa sukuni jin tana cikin damuwa har sai da ya kuSutar da ita, ya yin da shi ya jefa kanshi cikin damuwa da rayuwar Soye-Soye da kuma Soye abu, yanzun abinda zai faru nan gaba shi yake tunawa, amma game da yadda zai tafiyar da ita, ya raineta, ya kuma ginata akan ?aunarsa har ya gama nazartar duk hanyar da zai bi, koma miye zai faru bayan iyayensa sun gano da wata a cikin rayuwarsa to shi dai abu Waya yasa ni shi ne yana santa, kuma yana ?aunarta. Allah shi yasan abinda yasa ya jefa hakan a cikin ransa, tashi Waya daga kallon wannan video ya fara jin iya so ya kuma ganin yarinyar da sai ta yi tsanani za tayi shekaru goma sha biyar, kuma ba ?ar kowa ba, ba ?ar garinsu ba, ba ?abilar su Waya ba, ba kuma lallai a karSeta a duka danginsu ba, idan kuwa ya ce duka to yana nufin duka har iyayensa na asali wato Dady da kuma Mamma.

''Laa kaga wajen har ya watse, amma da zafi sosai ko?'' ta yi maganar kamar wacce taga wani sabon ciwon a jikinsa.

Nan ma kafin ya bata amsa wani tunanin ya faWa da ce wa yanzu to ya zai yi idan yarinyar ta ce ba zata ?aunaceshi ba? ?ila ma zamansu ba wani tsayi zai yi sosai ba, tunda dama ba ita ce ta ce tana son ya aureta ba, kuma ba ita ta nemi alfarma ba, hasali ma ko sanin an Waura aurenta dashi bata yi ba, kawai sai ganinsa ta yi a lokacin da yake Waukar ta har a cikin gidansu.

?ir!!?ir! Yaji wayarsa ta fara ruri da neman agajin a kula ta, da azuma ya mi?e tsaye yana ?o?arin cirota daga aljihun wandonsa, bayan ya dawo daga duniyar nazarin daya lula.

''Kana ina? Ko bacci ka ke ne? Su Yaya fa sun iso, yanzun haka gasu nan a falo'' Ummy take faWa masa ce wa mahaifinsa ya iso.

Sai da ya dafe kansa kafin ya ce ''gani nan zuwa Ummy, ina Wan wani abu ne''.

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon ta, a hankali ya ce ki kula kin ji ko, zan shiga cikin gida yanzu, akwai wani abunda ya taso ne.''

Kai kawai ta Waga masa tana mai komawa bakin gado ta zauna tana wasa da yatsun hannayenta.

?arasowa ya yi daf da ita ya kama hannun yana jujjuyawa da faWin ''da wata matsalar ne?'', ita dariya ma yaso ya bata, ashe haka yake da surutu da kuma faWi ba'a tambayeka ba? Gashi ma kamar taSa jikinta baya masa komai, kuma bai maida shi wani abu na daban ba, to ai shikenan, shiWin malamin ta ne, kuma ya zama dole tana koyi dashi a kan wasu abubuwan, tunda ita ba sani ne da ita ba, bata san komai game da rayuwar aure ba.

''Babu komai, kayi sauri kaje ana kiranka fa, ba'a jinkirin zuwa a kira irin wannan'' ta faWa kamar ba ita ta yi maganar ba.

Da dan murmushi ya saki hannunta tare da fara tattaki, in da yabar Wakin cike da nazarin maganarta, kenan tana nufin ba'a wasa da kiran iyaye, tunda tana tunanin mahaifiyarsa ce ta kirasa, gaskiya yarinyar kirki ce, ina ma ita ma tasan asalin wace ita a rayuwa, ina ma bata shiga shakkar su waye iyayenta a sanda Baba Ado ya bijiro da batun auren ta, babu shakka yasan yanzun tana cikin damuwar rashin sanin hakan, kawai jurewa take da kuma duba da babu yadda za ta yi ne yasa ta kauda kai akan sanin asalin bayananta tun daga ranar da taje Kance izuwa yanzu da ta dawo Agadez ba'a matsayin ?ar Kance ba, a matsayin matar aure.

''Assalamu alaikum, oyoyo Dady barka da zuwa'' Abdallah ya haWe duka jumlar zancen dake bakinsa a guri guda, wato ga sallama, ga martaba, ga kuma sannu da zuwa.

Sai da ya ?arasa kicthing ya ajiye plates Win nan kafin ya dawo falon.
Kallonsa Ummy ta yi tana mai ce wa ''da kuma kace ba zaka ci abincin ba, ya aka yi ne?'', ta tambaye shi.

''Ai Ummy bayan shigarku Waki ne na kasa ha?ura, to ?anshin girkin ne ya cika miki hanci, ai ba shiri na Wauki plate na zuba, ganin babu kowa a falon yasa na tafi sashe na, Dady ina fatan dai kunci abincin Ummyna kunji yadda ya haWu ya yi daWi.''

Da Wan murmushin da bai kai har ciki ba Dady ya kalli Abdallah'n da ce wa ''ba zaka tambaya da autana ba, lallai Muhammad yaronka bashi da kara, to maganar da nake yi da ace tana gida lokacin da na tsira tafiyar nan ba yadda za'a yi bata ce sai anzo da ita ba, ba ma dan taga ku iyayenta ba a'a, kawai ita dai yayanta, da safe yaya Abdallah, ya yamma yaya Abdallah, ida bacci za ta yi to sai tayi zancen sa, amma kaga shi yanzu ko tambaya da ita ma baya yi'' Dady ya faWa kamar da Wan faWa-faWa.

''Ya dai Yaya? Miye kuma yarona ya yi yanzu har ake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login