Showing 60001 words to 63000 words out of 78880 words

Chapter 21 - YAR KANCE free pages na Maman Abdallah.doc

faWin ''?atan banza kawai da kuka baya masa wahala, a haka zaka tisa ?ar mutane a gaba kana mata kuka akan abu kaWan, an dai ji kunya. Mama yunwa nake ji aradu'', ya faWa tana mai langwaSar dakai bayan ta gama yiwa Yusuf tsiya.

Da murmushi Maman ta kalleshi da ce wa ''ai kam dai tuni Annarku tasa aka kai muku baku abincin Wakunan Yusuf, yana can yarona'', ya faWa cike da mangari da kuma yabo wa kyakkyawan halayyar daya gada daga iyayensa.

Danvun shinkafar da yaji man gyaWa da kuma zogale, shi suka tarar duk ya cike Wakin da ?amshi, sai da suka yi ?a? kafin suka Wora da ruwa, mintuna biyar bayan gama cin abincin Abdallah bai Wora ba ya yi musu sallama ya bar gidan.

Wata kasuwar ta daban ya wuce kai tsaye, ina da ya haWo kayan abinci masu yawon gaske, kayan shayi da sauran kayan kicthing wanda yasan babu su a sashensa, kala da kalar madarar ruwa da lemuka duk sai da ya siya.

Sosai ya kashe kudaWe anan ma, sai da ya tabbatar ya siyi duk wani abun anfani wanda zata nema, ya biya ta wani restaurante ya siya mata abinci kafin ya wuce gida, mota sha?e da kaya na uban mamaki.

A nasa tunanin Ummy bata dawo ba, shi yasa kai tsaye ya wuce sashensa da ledar abincinta a hannunsa bayan ya kulle motarsa, da nufin sai zuwa dare ?afa ta Wauke zai shigar da kayan sashensa.

Wani sanyi ne yaji ya daki hancinsa lokacin daya buWe kofar, lumshe idanu yayi haWi da buWe su a lokaci guda, so yake ya iya tantance daga a inda yasan kakar ?anshin, ganin kamar abun zai Sata masa lokaci kawai sai ya gajarta tunanin yabar wajan kai tsaye ta wuce Wakinta.

Kamar yasan ?ofar a buWe sai bai babbuga ba, kawai turawa ta yi ya shiga kai tsaye da ?aramar sallama a bakinsa.

Fitowarta daga wanka kenan, babu komai a jikinta sai dogon hijabin da ta saka tun daga bayin, cak taSa ta tsaya ganinsa a ?ofar Wakin a lokacin da bata yi tsammani ba.

Ajiye ledar hannunsa ya yi a ?asa haWi da buWa mata hannayensa alamar tazo gare shi, kallon kanta tayi tun daga sama har ?afafuwanta kafin ta kuma kallonsa.

?aga mata kai ya yi irin kar taji komai Win nan, kuma yana jira ya jita a jikinsa.

Babu yadda ta iya ta fara tattaki zuwa inda yake, kamar wasa sai jin ta faWa ?urjinsa da dukkanin nutsuwarta.

A hankali ta maida hannayensa ya zagayeta dasu, tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, cikin muryar nutsuwa ta ce ''sannu da zuwa.''

A hankali ya iya amsa ta da ''yawwa sannu Noor, madallah da wannan tarbar arziki, daga yanzu irinta nake san in samu a duk sanda na Wauki sa'o'i kida biyu ne bana bana kusa da ke, ina fatan zan samu?'' ya faWa yana mai ?ara matseta a jikinsa, dan wallahi ba ?aryata abun yana masa daWi idan har ya haWa jikinsa na nata, musamman ma daga jiya zuwa yau Win nan.

Da in sha Allahu ta amsa masa.

A bakin gado ya zauna yana mai kiran ''wash na gaji, gaji'' ita ma kusa da shi tazo ta zauna bayan ta Wauko ledar abincin da ya shigo da ita a hannunsa.

''Sannu ko! Allah ya bada lada'', ta faWa cikin marerecewar mirya da kuma fuska kamar wacce za ta yi kuka, wai ita a dole sannu take yi wa miji.

Bata san irin hakan kansa Abdallah ya jishi na daban ba, yakan ji kansa kamar yana yawo a sarari ne bayan ya jima yana tafiya cikin dubu mai tsanani, da yasan haka shau?in so yake da ya daWe da farawa tun kafin yanzu, ''to amma dawa za kayi idan har ya kasance wannan ita ce ?addarka? Haka kuma Allah ya ?addara ita ce matarka ta farko'' ya yi maganar a zuciyarsa.

''Bacci ya Wauke ni Wazun bayan fitarka, ban gusa a inda ka barni ba, sai kawai da naji ?aran wani abu mai kama da waya, shi ya tashe ni, ina dubawa sai naga ashe wayarka ka manta a kan kujera, kaga ni ma'' takai ?arashe a ?arshe da mi?a masa Wa?ar wayarsa.

Har hannunta ya haWa gaba Waya ya ri?e, a ranta ta ce ''shi dai wannan bawan Allah'n yana yawan san komai dai ya taSa mata jiki, to amma ai mijinki ne'' wata zuciyar ta kwaSeta. Jinjina kai ta yi jin ta gamsu da maganar daga Wayan sashe na zuciyarta zuwa wani sashen.

''Yawwa zo ki ga wani abu'' ya faWa lokaci Waya yana mai ?are haWe Wan sararin dake tsakaninsu.

?arawa mai karfi ?arfi, in ji ?an magana a duk lokacin da talaka ya yi wa mai kuWi ihsani, to anan ma hakan ce ta faru, ya yin da ya haWe Wan tsakanin dmdaya rarraba su, ita kuma sai ta kwantar da kanta a kan kafaWarsa ya yin da Wayan hannunta ta zagayo dashi ta aWora shi a Wayar kafaWar daga baya, sai abin ya wani bada color.

Ajiyar zuciya Abdallah ya sauke kafin ya ce ''in ce dai kinyi sallah ko? Na ji kince ba jimawa da kika tashi a bacci tun bayan fitata.''

''Ina farkawa da ita na fara ai, sai bayan dana gama ne na Wan hura falon haWi da fesa Waya daga cikin turarukan da ka siyo mini, daga bisani na shiga wanka, fitowana kenan dai-dai shigowarka.'' ta amsa shi dai-dai da tanbayar da ya yi mata.

''Ma sha Allah, haka nake so in ji, ki kula sosai dan Allah, bana san wasa da ibada, sannan kuma duk abinda kike bu?ata nome wanda zaki faWa wa, ni kuma na yi miki al?awari zan na magance miki matsalolin ki akan kari da yardar Allah, yanzun na haWo miki duka wasu nau'uka na kayan abinci, na siyo komai na bu?ata abubuwan da babu kuma bayan kin duba sai ki faWa mini za siyo su da yardar Ubangiji. Sai dai ki maida hankali sosai dan Allah Noor, a yanzu bana da wata hanyar da ta wuce wannan, in killace ki a wuri guda har ranar da Ubangiji zai kawo mana mafitar da zamu bayyana a matsayin ma'auratan da kowa zai san da wannan ala?a a tsakanin mu, wato (Aure), dan Ummy ta ji ?anshin kirki zata iya tunanin ko daga magwabata ne, amma akasin hakan taji yau taji gobe to tabbas zata fara tunanin daga ina ?aurin ko kuma wani abuai kama da haka yake fitowa, duk dare zan na fitar da dattin da zaki dinga tarasu wuri guda ne, irin sharar kayan miya idan kin cire da dai sauransu, saboda kar a samu matsala, dan ba wai iyayena ba, ko ?an aikin gidan nan bana so su gane da akwai ki a sashen nan har sai lokaci ya nuna mana.'' ya Wan nunfasa kafin ya Wora da ''duk da yake ma dayawan abubuwan duka na kwali na siyo bawai masu Waita ba, kama daga albasa, tafarnuwa, citta, da makamantansu, a hankali zaki fuskanci yadda ake amfani da komai Noor, matu?ar kika maida hankalinki akan wannan'' ya nuna wayar dake hannunsa, ya ci-gaba da ''wannan wayata ce, dama na gama program akan zan bar miki ita a wurin ki, gidan nan da wifi mike aiki, bawai ?an cikin gida ko ma'aikatan cikinsa ba, hatta da sauran jama'ar dake zagaye damu suna anfana dashi, dan ko yanzu dazan shigo gidan nan dayawan matasa ne kewaye da katangar gidan nan suna anfani dashi, wanda bana Bara Waukan biyu sun san code Win dake buWe shi ne daga bakin makusantansu, ?o?arin a cikin ma'aikata, saboda haka, nan shi ne...........''

Tsawon mintuna goma sha biyar yana nuna mata yadda za ta yi anfani da wayar nan,Waya-Waya zata sauke abu idan ya yi mata, babu laifi kuma ta fahimta.

Ba da farko ya yi tunanin zai cire layin dake cikin wayar, amma daga baya ya canja sharawa akan ya bar mata duka har layin, da yake dama ba kowa yasan dashi ba, daga shi sai iyayensa, sai kuma Yusuf, tare da Wayan abokinsa Mufaddal, wanda shi Win Balaraben ?asar Algeriya ne, wanda a yanzun haka yana ?asar Ghana ne, ya je wani taron ?ara wa juna sani na manya-manyan Liki???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?tocin mata dake Afirka da gwamnatin ?asar ta shirya a babban Sirnin su Accra.

To zaibiya ce wa daga su babu wanda yasan da wannan layi nasa, saboda haka yabar mata shi kodan idan ya fita yana kiranta a wayar yana jin lafiyarta.


Bayan sallar isha'i Abdallah ya gama shirin zuwa gidan su Angel sai baza kanshi yake, shi kansa daya kalli kansa a babban marubin dake Wakinsa sai da ya murmusa, dama ace Noor ce da wannan damar ma, ace wannan shirin da nayi wurinta zance zance, kai da abun ya yi mugun bada citta.

Marairaicewa ya yi yana kuma kallon kansa haWi da shafar sajensa da ce wa ''wallahi kishin kaina nake ji akan ki Noor, ba dan wane irin kamu ne kika mini a lokaci ?an?ani ba, Ni dai abu Waya dana sani shi ne ina sanki! Ina ?aunarki! Kuma ina fatan mu kasance da juna har karshen rayuwa, ke wallahi idan da so samu ne ko mutuwa idan tazo ta Wauke mu a tare dangi samun salama, dan babban tashin hankali na ne ace in mutu in barki kiso wani a bayana, haka kuma ko na rayu ba lallai in iya yin komai kamar mai hankali ba idan har kece kika rigani gidan gaskiya, maganar gaskiya ki so ni koda rabin yadda nake sanki ne, hakan zai sa in ji daWi kuma in samu nutsuwar zuciyata, ki yarda dani shi ne fatana, zama a matsayin mijinki shi ne burina, ki kirani jagoranki shi ne mafarkina, ki bani yara daga gareki shi ne alfahari na, a karshe ki rayu dani shi ne cikar burin....''

Raf!!! Raf!! Raf! Ya ji ana yi masa tafi daga ?ofar shigowa Wakin, dubawar da zai yi ba sai Ummy ya hango da mirron da yake fuskanta ba, ras! ?irjnsa ya yi masa mugun bugu da ?arfin gaske, wanda har saida ya saka hannu ya dafe saitin zuciyarsa.

''Ya da dafe ?irji kuma? Ko duka cikin bitar ne? Naga yarona ya daddage yana ta rattabo zance kamar wani mai sauye bayanen dake jikin shafin jarida zuwa ga maWaukakin sauti na murya ko kuma magana'' ce war Ummy dake dafe da kofar shigowa, ita bata shigo ba sannan kuma bata saki hanyar ba.

Abdallah ba lallai ma yaji abinda ta faWa ba, dan tuni ya fara tunanin mafita, yau idan Ummy taga ko jin motsin Noor a Sangaren nan da wane baki zai kare kansa ba? Ba wannan bane karan farko da Ummy'n take yi masa dirar mikiya ba, wannan yana daga cikin salon bada irin nata tarbiyya, a ce war ''a yanzu lura da tarbiyyar yara kamata yayi iyaye su dinga cire Wan ba a ciki, a wannan fagen babu ce wa wai wannan namiji ne, bai kamata kana matse masa wuri ba, a'a! Ai wallahi duk uwar da take irin wannan tunani to tabbas kamar ta Wura wajen ajiya a jarka ne ba tare da tasa murfi ta rufe ba, saboda saida lalataccen saurayi akan yi fanWararriyar yarinya budurwa, dan kafin kaji ance wata ta farwa wani, za kaji an ce wani ya faWa wata, to kunga ni? Wannan shine dalilinta na ce wata?ila iya Abdallah kaWai Allah ya nufa su raina kuma su bashi tarbiyya, to miye zai sa suyi sakakin da zai iya lalacewa? Duk da dayawan iyaye bada ransu yaransu mata da maza kan lalace ba, amma a mafiya yawan lokuta sakaci shi ne babban matakin da yake kaisu ga wannan matsayi, Allah ya dube mu kuma ya shirya mana zuri'a baki Waya.''

''Ummy yanzu nake shirin fitowa fa! Shi ne kika biyo ni'' ya faWa a shagwaSe.

''Eh Yaya yake nemanka ai, kuma har kiranka yayi baka Waga ba, amma ina ka jefa wayar to?''

Kusan a tare suke takawa da nufin barin sashen, ya yin da yake bata amsar tambayar da ta yi masa, hankalinsa bai kwanta ba har saida yaga sun bar sashen, kafin ya sauke wata ajiyar zuciya mai ?arfin gaske, a ransa ya ce ''na yanzun kam na sha da ikon Allah.''

A nan falon ma haka Abby ya yi ta kwarzanta yaron nasa yana yabawa da wankan daya Waukan, harma da ?ar zolaya ya haWa ce wa ''irin wannan wanka haka? To ko zan yi maka rakiya ne?'' ya faWa cike da zolaya.

Sako Dady ya bawa Abdallah ya isar masa a kan hanyarsa ta zuwa gidan Alhusai (wato mahaifin Angel).

Sallama ya yi musu haWi da neman addu'ar su, suka kuma bisa da ita mai tarin ma'ana, ta ce da ro?ar masa harma abinda bai tambaya ba.

Yaso ace Noor ta fara ganin wannan wanka nasa kafin kowa, amma Allah bai nufa hakan zai faru ba, amma ba komai, zai jira idan ya dawo zai nuna mata, ko dan yaga yadda ta Wauki irin wannan wanka nasa.

?aramar riga ce mai gajeran hannu kalar wake-wake, mai shige da iniforme Win sojoji, sai ba?in wando irin mai aljifai dayawa Win nan, ?arsiriryar agogon dake Wauke a tsintsiyar hannunsa shi ya ?ara ?awata kyaukyawar fatar hannunsa dake cike da gar-gasa, wanda za'a iya ce wa Abdallah mutun ne mai yawan gashin jiki, musamman ?irjinsa, a wani sa'in har abinda yake gyara sajensa yake sakawa ya Wan rage shi.

Takalmin dake ?afarsa ma kalar rigarsa ce, sai ya haWe da kayan, suma suka haWe dashi suka bada kala.

Sosai ya yi mamakin irin shirin tarbansa daya tarar anyi a gidan, haka duk da bai kira ya faWa mata zuwansa sa ba, gashi abinci ma kala uku aka yi kawai domin sa, haka ma lemu kala biyu aka haWa masa.

Zaune yake a Waya daga cikin kujeran falon gidan, bayan sun gama gaisawa da Mami ta wuce Wakinta, su Tonton Alhusain basu da sauran yaran gidan maza da ?ar Auta letyl Gaisha (mai sunan Ummy) sun fita siyayya.

Da sallama a bakinta ta shigo falon, kanta a ?asahar ta iso dai-dai kujerar dake kallon wacce yake zaune a kai, Wan risinawa ta yi haWi da ''Barka da yamma yaya Abdallah.'' Ba yabo baffallasa ya ce ''Barka dai, ya kike?''
Da ''Alhamdulillah'' ta amsa, lokaci Waya tana zama a kujera, ta fara wasa da yatsun hannunta.

Kusan mintuna uku babu wanda ya ce komai, jin shurun ya Wan ?ara nisa yasa ta Wago fuskarta zuwa gare shi, har yanzu hankalinsa a waya, a bazata ya ji ta kuma ce wa ''Ya su Ummy da Abby? Fatan suna lafiya.''
Sai a lokacin ya ajiye wayar a gefen sa, ya haWe tafukan hannayensa biyu yana darzasu kamar mai jin sanyi, cikin muryar da take mugun tafiya da ita ya ce ''Suna nan lafiya ?alau'' daga haka bai kuma ce wa komai ba, shiru ya kuma riskar falon. Tasowa ta yi daga mazauninta ta iso kusa da wannan kayan abincin data shirya a ?asan carpet, ruwa ta fara zubawa a cup ta mi?a masa haWi da faWin ''Yaya ka sauko kaci abincin dana shirya domin ka'', karSar ruwan ya yi ya Wan kurSa ba yawa, kafin ya ajiye cup Win a gabansa yana kallonta, riga da wando ne a jikin, sai liffayar data yane jikinta dashi, bata yi kwalliya a farar fuskarta ba, sai Wan man leSe da ta shafa, ?amshi kam sai nata nashi uka haWu suka gauraye falon. ''Naga baki san da zuwana ba ko?'' ya faWa yana mai yi mata nuni da jerin cimar da ta ce ta haWa saboda shi.
''Hum! Ai kam dai Ummy ta faWa min kana zuwa, na rasa miye dalilin da yasa har yanzun ka kasa yarda dani yaya Abdallah, ni kaina nasan amsawa kawai kayi game da maganar auren mu, amma badan ina cikin tunaninka ba, miye laifin wanda ya ce yana sanka yaya Abdallah? Yanzun ka fitar da gwaninka shi ma laifi ne? Allah ya gani nidai ina sanka dominsa'' ta ?arashe maganar ta langwaSar da kai alamar ya ji tausayinta, ya sota kamar yadda ta mato akan shi.

''In ji waye ya faWa? Ki manta kawai, yanzu wane lokaci kike so aurenki ya kasance?'' ya jefa mata tambayar da ta ji ta har a cikin zuciyarta, dafe saitin ?irjinta ta yi lokacin da bakinta ya kasa rufuwa, cike da ruWewa ta ce ''Wai da gaske kake Yaya? Da wuri haka! Kai amma gaskiya nai....''

?aran kiran wayarsa da aka yi ne ya kace mata sauran zancen da ta Wauki, shiru ta yi har ya gama maganar da yake wacce ba lallai ta fahimci da wanda yake wayar ba.

''Uhuum! Ina jinki'' ya faWa yana maido da dubansa gareta. Kunya ta ji ta matu?ar kama ta, sai takai tafin hannayenta ta rufeta ruf, sosai ta yi mamakin kanta ita ma, ta yadda ta iya buWar baki take zuba da fayyace sirrin ranta a gaban wanda ta mato a kansa.

''Ba zaka ci abincin ba?'' ta kuma canja musu maudu'i.
Saukowa ya yi daga kan kujerar ya zauna a carpet, kamar yadda ya kasance tana zaune a kai ita ma tun lokacin da tazo ta bashi ruwa. Bawai yana jin yunwa ba ne a'a, kawai baya so ya karya mata ?warin guiwa ne, yadda ta zauna ta kashe kanta ta shirya masa wa'yannan ubannin ayyukan, ta yaya zai ?i koda WanWanawa ne.

A lokacin da take ?o?arin zuba masa abincin a sa'in suka ji sallamar...........


?AR KANCE

Page 19

__________Lokacin da take faman zuba masa abincin a sa'in suka ji sallamar mahaifinta da sauran ?an uwanta.

Cikin girmamawa Abdallah ya mi?e tsaye, tare da tarbar Tonton Win nasa yana gaishe shi kamar yadda yake yi masa a da can, san shi har ga Allah baya masa kallon suruki.

''Ya su yaya da Ummy'n ka? Fatan duk suna lafiya?'' ya tambaye shi bayan sun saki hannun juna daga musabihar da suka yi.
''Suna nan lafiyarsu ?alau, sun ce ma a gaishe ku'' ya bashi amsa lokacin yana wasa da ?ar Autar Mama.

Falo ya rage daga Abdallah sai Angel sai kuma Auta da ta ma?alewa Abdallah tun shigowarsu.
Bai fi cokali huWu ba abinda yaci ya ce alhamdulillahi. Narai-narai tayi da ido tana kallonsa, ''Yaya badai ka ce har ka ?oshi ba?'' ta faWa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login